11&12
by @nkds
❤️BA DARAJA!!!❤🔥
©® Nainarh KD♡
Page 11–12
*
“Anty Hauwa'u, ki k'aramin fanken yunwa nake ji ban k'oshi ba.”
Yarinyar ta yi maganar jikinta ya na d'an rawa na tsoro yayin da take tsaye gaban kaskon da ake suyan fanken.
Hauwa'u ta bud'e baki zata bawa k'anwar nata amsa sai dai muryar Ruk'ayya ta katse ma ta hanzari, cikin ruwan masifa ta ce.
“Tun da fanken na uwarta ne ai sai ta k'ara miki na gani.”
Ta k'ari sa wurin tana zabga musu harara su duka sannan ta ci gaba.
“Saboda kece isashiya kowa an zuba masa bai yi k'orafi ba sai ke, to ba za'a k'ara ba b'ace min da gani kafin na sauya miki kamanni a wurin nan... Ke kuma da k'ara matan zakiyi ko?”
Ta mayar da akalan maganar nata ga Hauwa'u da tuni ta mik'e tsaye.
“A'a Anty, dama hak'uri zan bata, ammaaa Anty ki taimaka ki bata ko a nawa kason ne saboda Khadija tana da cin abinci sosai wanda aka bata zai isheta ba.”
Wani mugun duba da ta yi ma Hauwa'u shi ya sa yarinyar ta d'an ja da baya cikin tsoro. Tsaki Ruk'ayya taja tana zama tare da yin burus da su.
“Mommi yunwa...”
Khadijan ta sake fad'a abin tausayi.
“Ungo tun kafin ki cinye ni mayya!”
Ta fad'a a zafafe tana dangwara ma ta fanken mai zafi a hannu wanda da bata jima da tsamewa ba, k'ara yarinyar ta saki tare da saurin sakin fanken ya sauka a k'afar Ruk'ayya da ciki ya sa ta kumbura ai kuwa da zafin ya ziyarceta ai batasan lokacin da ta kifa ma ta mari ba da ya saka yarinyar yin taga-taga, ba tausayi Ruk'ayya ta sake kifa ma ta wani marin tana bala'i. Tsananin azaba tsoro da kuma zafin marin da suka ziyarci yarinyar lokaci guda ya sa ta yi taga-taga tare da yin baya cikin tsautsayi ta kifa a kan kaskon suyar fanken mai shak'e da mai.
Sakin k'arar azaba da ta yi ya yi daidai da ihun da Hauwa'u ta kurma da hakan ya yi daidai da shigowar Abbas da Halima idanunsu ya sauka akan abin da ya faru.
“A'uzubillahi mina shaitanirrajimmm!”
Halima ta fad'a cikin tsananin tashin hankali da tsoro tana ja baya yayin da batasan ta kusa sakin jaririyarta mai watanni uku ba saboda firgita da ta yi na mugun ganin da idanunta suka yi.
“Inna lillahi wa-inna ilayhi raji'oon³.”
Shi ne abin da ya fito daga bakin Abbas cikin tsananin kad'uwa da tashin hankali.
Halima ta yi saurin saita rik'on da ta yima jaririyar da ta fara kuka, tana jin duniyar na juya amma ta yi k'arfin halin mik'a jaririyar nata ga Abbas dake tsaye k'ik'am kamar an dasa shi, cikin sauri batama tsaya jiran ya rik'e 'yar da kyau ba, a hanzarce ta k'ari sa tare da sunkumar yarinyar da tsananin azaba ya sa kukan da take yi ma baya fita, da yake ta gaba ta kifa a kaskon shi ya sa da azabar man ya ziyarci gangar jikinta kuma ta sama zarafin d'agowa sai dai ta kife ta baya a k'asa.
Akan tabarmar da sauran yaran suke zazzaune kafin faruwar lamarin Halima ta aje ta. Da sauri ta juya zuwa ga butar ruwa, ta buɗe, ta fara zuba ruwa a jikin yarinyar, domin rage zafi da rage rad'ad'i da kuma kare fata.
“Sannu, Sannu kinji Khadija… ki yi hak'uri…” ta faɗa cikin kukan da ta saka rik'e wa, akwai ciwo a lamarin sosai, ace d'an ka ya k'one da mai dake kan wuta koma ba mai ba k'onuwa da ko wani irin abu ne wani azaba ne mai zaman kansa bare kuma k'una irin na mai. Kuma ga k'aramin yaro musamman ma ita Khadija da ya kasance ba kaya a jikinta, domin daga ita sai vest da k'aramin wando kasancewar ranar ba makaranta ya sa Hauwa'u ta ce sai sun karya zatayi musu wanka domin tun da Halima ta bar gidan suka tafi anguwa tare da Abbas tsawon kwanaki uku duka d'awainiyar yaran ya koma kanta bayan kuma ba haka aka yi da Ruk'ayya ba kafin tafiyar nasu.
Sai a lokacin Halima ta ɗago idanunta zuwa ga Ruk'ayya.
“ME YA FARU?!” ta tambaya da muryarta mai cike da firgici da kuma zargin da take k'ok'arin hana zuciyarta yi.
Ruk'ayya ta ja baya kad'an kamar ba ita ba… bakinta na rawa…
“Ni… ni ban sani ba… ta zo kusa da kaskon ne kawai...”
“KIYI MIN SHIRU!!!” ta katse ta cikin tsawa, zuciyarta na tafarfasa domin bama zata iya tsayawa sauraronta ba.
Ba ta ƙara cewa komai ba.
Ta rungume diyarta a jikinta, jikinta na rawa, zuciyarta cike da fargaba…
Sai a lokacin ne Abbas ya sama zarafin magana ya duba Ruk'ayya da kai tsaye ba zaka ce ga halin da take ciki ba.
“Rakiya mene ne abin da ya faru?”
Ya tambaya yana d'auke kallonsa da ga kan Halima da 'yar nata zuwa ga Ruk'ayya.
“Darling ka yarda dani tsautsayi ne wallahi.”
Ta fad'a kamar wacce aka shak'e.
Halima zatayi magana Abbas ya d'aga ma ta hannu sannan ya ce.
“Ya isa haka lamarin dai ya riga ya faru, sai dai ai fatan Allah ya tsare gaba ita kuma Allah ya bata sauk'i. Ruk'ayya jeki d'aki...”
“Ban gane ba, ta tafi d'aki shikenan ta k'ona min 'ya a banza ke nan, Abbas ya kamata kayi min adalci ka fara binciken abin da ya faru ba wai ka yanke hukunci ba, sanin kanka ne matarka ba k'aunar 'ya'yan nan take ba kuma wannan tafiyar da mukayi da kai ma bataso ba, nima kuma ba so nayi ba dan kawai ka dage ne, haushin ka barta ka tafi dani shi ya sa ta gaza hak'ura ta k'are akan yarinyar da bata ji ba bata gani ba...”
“Shut up Halima! Yaushe kika fara ja'inja dani ba nace a bar maganar ba, wannan wani irin abu kike fad'a ne ta ya ya Ruk'ayya zata k'ona miki 'ya da gangar wai bakisan k'addara da tsautsayi ba ne?”
Abbas ya katse ta cikin d'aga murya yana dangwara ma ta jaririyar da tuni ta fara kuka sannan ya ci gaba.
“Nace magana ta k'are kuma na k'ara jin kin tado da ita zan yi mugun sab'a miki. Bana son shashancin banza.”
Halima ji ta yi wasu hawaye sun ci gaba da yi ma ta tsere a dakalin fuskarta wannan wani irin son zuciya ne da Abbas a k'ona ma ta 'ya kuma yake fad'in wannan kalamai. Sai kace Khadijan ba 'yarsa bace.
“To ai shikenan. Allah ya sakama wanda aka zalunta”
Ta fad'a tana share hawayen da suka gagara dakatawa.
“Kiyi hak'uri please ba niyya ta na k'ona miki 'ya ba, duk ita ta ja amma...”
Wani irin rikitaccen duba da Halima ta d'ago tana yi ma ta ne ya sa ta yi ma zancen nata fasali sai ta mayar da dubanta ga Abbas.
“Darling please ka tayani bata hak'uri wallahi ba da niyya nayi ba.”
Jinjina ma ta kai ya yi ita kuma ta kama hanyar d'akinta, a zuciyarta take jin gwarama da yarinyar ta k'one domin koba komai takaicin da Halima ta k'unsa ya wanke ma ta nata takaicin na tafiya bikin da Abbas ya yi da Haliman bayan ita ya kamata ace da ita aka je, domin tun zuwanta gidan basu tab'a zuwa anguwa na kwana tare ba amma sun je da Halima wannan nema na biyu, zuciyarta bata yarda da batun Abbas na saboda cikin jikinta da ya tsufa ne ya sa zai tafi da Halima ba bayan kuma ita ya yi ma alk'awari, a ganinta koda ta shiga watan haihuwa ai da sauran lokaci bisa kwanakin da aka rubuta a takardar scanning d'in da ta yi.
Takaicinta bai k'aru ba sai ganin sun yi kwanaki uku bayan kwana biyu suka ce zasu yi, bikin da suka tafi dangin mahaifin Abbas ne shi ya sa ta kwalla fa rai, domin a ganinta ai Halima ita ta dad'e ta saba tana zuwa kuma an santa saboda haka wannan karon ita ya dace ta je ita ma a santa, amma shi ne Halima ta yi makirci da k'ulla-k'ulla aka tafi da ita. Shi ya sa kuwa a kwanakin ba k'aramin aya ta gasawa yaran a hannu ba dan ma Allah ya taimaki Saddiqa tana wurin Mahaifiyarta da yake bata da lafiya shi ya sa ta nema da a bata yarinyar na wani lokaci.
“Karka tab'a ta Dan Allah.”
Halima ta fad'a a zafafe cikin sauri kamar wacce aka zabura, da mamaki Abbas ya dubeta.
“Me kike nufi?”
“Abin da kaji shi nake nufi Abbansu tun da har baka damu da ita ba baka k'aunar 'ya'yana to duk wasu kulawarka basu da amfani saboda haka karka tab'a ta.”
Wannan karon a d'an hasale yake dubanta kafin ya fara magana da muryarsa cikin yanayi na kashedi ya ce.
“Wai Halima wani irin hali ne kike k'ok'arin fito da shi ne, tun da ta bada hak'uri kuma ba da gangar ta yi ba tsautsayi ne ba shikenan ba a kyale magana ta wuce...”
“Hmmm ai a wajenka ne magana zata wuce amma ni ba zan tab'a mantawa ba kuma na riga da na kai k'ara ga mahaliccinmu ni da ku duka.”
Ya bud'e baki zai yi magana ihun Ruk'ayya ya karad'e gidan tana kwala masa kira.
A gaggauce ya nufa d'akin nata yayin da Halima ta bishi da kallo zuciyarta nayi ma ta zafi.
“Mamma kiyi hak'uri...”
Juyawa ta yi tana duban Hauwa'u dake rakub'e kuma ta yi maganar cikin kuka.
“Ki dena bani hak'uri kinji domin ba laifinki bane.”
Cikin kuka yarinyar ta ce.
“Laifina ne Mamma, da ace nayi sauri na k'ara ma ta fanken kafin Mommi ta fito da duk hakan bai faru ba.”
Da yake tun Ruk'ayya bata rufe wata a gidan ba ta saka ma yaran dokar kiranta da Mommi domin da farko Anty suke ce ma ta ita kuma ta ce basu isa ba sai dai kamar yadda suke kiran mahaifiyarsu da Mamma ita ma su kirata da Mommi.
“Karki damu kinji ki dena kuka dama Allah ya nufa hakan zai faru da ita tun fil'azal yanzu dai ku duka kuyi ma ta fatan samun sauk'i.”
Ta k'ari sa maganar tana duban sauran yaran su duka.
Shirya wa ta yi tsaf ba tare da b'ata lokaci ba domin kai yarinyar asibiti domin ta lura idan ta tsaya jira har sai Abbas ya fito wata k'ila sai dai su kai gawar yarinyar asibiti.
“Halima ina kuma zakije.”
Juyawa ta yi tana mai jin kamar ta kifa masa mari jin irin tambayar da ya yi ma ta amma sai ta daure ta ce.
“Asibiti...”
Dafe kansa ya yi sai kuma ya yi saurin dubanta a d'an rikice ya ce.
“Rakiya fa nak'uda take yi wannan abin da ya faru ya tado ma ta nak'uda Dan Allah kizo ki tsaya a wurinta in yaso ni sai na kai ita Khadijan asibiti.”
Wani irin kallo ta yi masa tana shirin bud'e baki ta bashi amsa da. “Abbas ke nan kana bani mamaki wallahi Matar da ta k'ona min 'ya ce kake maganar na dakata daga kai yarinyar asibiti saboda tana nak'uda ko? Kai bakaji kunyar kanka ba?”
Sai kuma ta cije baki tana had'iye kalamanta lokacin da idanunta ya sauka akan yaran da suka yi musu tsuru kamar sun sama TV.
Daga k'arshe sallamar Mama Tsahare shi ne ya kawo k'arshen d'an shirun da ya ratsa tsakani. Dama ziyara ta kawo musu sai kuma ta tarar da k'adamin da ake ciki, daga k'arshe dai ita ce ta tsaya wurin Ruk'ayya dake nak'uda yayin da ta tilasta wa Abbas kai Halima da yarinyar zuwa asibiti.
BAYAN KWANA BIYAR.
“Sannu Khadija Allah ya k'ara lafiya. Ai abin ma ya yi ma ta da kyau an gode Allah k'unar wuta ai masifa ce amma da yake bata da k'an jiki, gashi ya yi sauk'i sosai bakya ce kwana biyar ke nan ba.”
Cewar Zuwaira tana duban yarinyar dake kwance sannan ta mayar da akalan dubanta ga Halima dake zaune daga kan kujerar d'inki tana dubansu.
“Ai ni ban san da wannan al'amari ba sai jiya da na dawo kin san na fad'a miki zamu tafi anguwa to sai jiya muka dawo ban shiga gida ba, na biya ta gidan Yaya Abu take sanar min da abin da ya faru amma garin ya ya hakan ta kasance ne Halima?”
Halima ta d'an sauke ajiyar zuciya ta ce.
“Bata sanar da ba bani a gidan dawowarmu gidan ke nan a ranar muka tarar da abin da ya faru bayan nayi abin da zan iya ne aka kaita asibiti.”
“E ta fad'a min wannan amma ina mamakin yadda za'ai yarinyar nan ta fad'a cikin kaskon mai har ga k'one ga Matar can a wurin amma bata iya tsinana komai ba.”
Zuwaira ta fad'a cikin yanayinta na fad'a fad'a. Halima ta d'an yi murmushi jin sunan da Zuwaira ta kira Ruk'ayya da shi dama tun sanda ta fara ganinta ta ce ita kam bata yi ma ta ba.
“Yaya Zuwaira tsautsayi ne kawai da baya wuce ranar sa.”
Shiru kawai Zuwaira ta yi badan ta gamsu ba da yake dukkaninsu ne suka zo gidan duk da sauran sun zo a baya sun duba mai k'unar amma kasancewar Zuwaira da bata sama zuwa ba zata zo shi ya sa duk suka taho tare.
Suna zaune suna d'an fira sai ga Ruk'ayya da ta dawo daga wanka zata shige d'aki amma idanunta naga d'akin Halima da yake d'akunan nasu a jere suke, ai kuwa idanun Zuwaira ya sauka akan na Ruk'ayya wani kallo mai had'e da harara ta aika ma ta tana sake tamke fuska k'aramar k'anwarsu Azima da ta lura da komai ta yi dariya cikin tsokana ta ce.
“Ya dai Yaya Zuwaira ko zamuje ne muyi ma ta barka kin san fa ya kamata ki shiga kiyi ma ta Barka tun da kin zo gidan.”
“Saura uwar barkan zan yi ma ta kinji ko ku ma kuma wallahi baku isa kun shiga da sunan ma ta Barka ba ai duk wanda ya nema a zauna lafiya sai a zauna amma idan mutum bai nema haka ba sai a bishi duk ta inda ya b'ullo.”
Wahida ta yi 'yar dariya tana fad'in.
“Yoo na nawa kuma Matar Ibrahim ai tuni aikin gama ya gama domin tun ranar da muka zo dubiya Yaya Abu ta ce bamu isa ba sai mun shiga mun yi ma ta Barka da samun kai.”
Cikin mamaki Zuwaira ta ce.
“Da gaske?”
“Kwarai kuwa.”
Suka bata amsa.
Shiru ta yi sai dai ba haka taso sai dai batajin da wanda ya isa ya saka ta shiga ta yi ma Matar can wani abu wai shi Barka.
Suna a haka sai ga Abbas ya dawo gidan Halima batayi mamaki ba domin tun bayan haihuwar da yau kwanaki hud'u ke nan a rana ya shigo gidan fiye da sau biyar, bayan ya gaisa da su Yaya Abu kuma sun yi halin nasu shi da Hadiza na tsokanar juna yayin da Azima ke kare ma Abbas sauran sunayi musu dariya, sannan Abbas ya wuce zuwa d'akinsa Halima tabishi.
A karo na biyu ke nan da ya sake kallon ta yana kuma sauke ajiyar zuciya tare da nazarin ta inda zai fara.
“Kamar da magana a bakinka gashi ka tsareni nan ina da bak'i fa.”
Halima ta fad'a cikin gundura yanayin domin tun bayan abin da ya faru wancan ranar zuwa yau da ace ta biye masa da ira-iren abubuwan son zuciya da yake yi da kullum sai an ji kansu, domin bayan haihuwar da Ruk'ayya ta yi so ya yi ya d'aura ma ta d'awainiyar kula da mai jego bayan kuma ga mai k'una tana fama da ita, kai tsaye kuwa ta nuna masa ba zai yiwu ba, shi ne ya d'auki fushi sannan ya kira yayarsa da suke uba da mijinta ya rasu tazo ta zauna wa Ruk'ayya d'in yayin da kullum a gidan Mama Tsahare take wuni zuwa dare ta koma gidan autanta inda take zaune, bai tashi neman sulhu daga fushin nasa ba sai ana gobe za'ayi barka da yake namiji Ruk'ayyan ta haifa, nan d'in ma ya sakko ne saboda yana so ya shawo kanta akan abincin 'yan Barka da za'ayi da kuma sauran abubuwa da ya kamata nan d'in ma ba dan halinsa ko na Ruk'ayyan ya sa Halima ta yi ba sai dan Allah kuma duk da tana lura da yawan abubuwan da yake kai ma Ruk'ayya bata tab'a nuna damuwarta ba duk da ranta ya b'aci da yadda kaji uku ya bayar aka yankawa mai jego amma ita da yaranta bai iya basu ko k'ashi ba duk da hakan bai zama dole ba amma ko ba komai kyautata wa ai tana da dad'i, kuma abin da ya k'ara bata haushi shi ne na yadda duk abin da take yi amma sannu bare na gode baya tab'a had'a ta da Ruk'ayya, ranar da aka yi Barka ma da ace ta biye ma 'yan uwan Ruk'ayya da suke yada habaici a gidan tabbas da sun bar abin kunya.
Ta nisa tana mai d'aura jaririyarta a kafad'a bayan ta gama bata mama, Zainab ya saka ma yarinyar da yayyinta suka saka ma ta Ummita kuma ake kiranta da hakan. Da yake Zainab d'in sunan k'anwar mahaifin shi Abbas d'in ne shi ya sa ta ce yaran suke kiranta da hakan duk da shi Abbas ya saka sunan ne bisa ra'ayi ne ba dan komai ba, dan kuwa shi bashi da ra'ayin sakama yaransa sunan iyayensa ko na Matarsa domin tun Halima tana naci akan ya taimaka ya saka ko sunan Mahaifiyarta ne da ta rasu amma yak'i har ta hak'ura ta kuma zuba masa ido.
“Dama ba wani abu ba ne fa ce hak'uri da zan baki tabbas nayi niyyar yi miki rago na hakika lokacin da kika haifi Zainab amma rashin kud'i ya hana sakamakon lokacin ban gama watstsake wa daga hidimar biki ba, kuma a yanzu kinga Ruk'ayya haihuwar fari ta yi bai dace ace ba'ayi ma ta ragon suna ba kuma a gaskiya bani da kud'in siyan raguna biyu saboda haka Halima kiyi hak'uri ita nayi ma ta.”
Ya kai maganar nasa yana d'ago idanunsa domin yaga yanayin da Haliman ke ciki.
Ita kuwa tun da ya soma maganar ta zuba masa idanu tana duba babu ko giftawa har sai da taji ya kai aya nan ma bata sama zarafin magana ba sakamakon abin da ya tsaya ma ta a mak'oshi.
“Halima kina jina kuwa?”
Ya sake fad'a ganin kamar bata fahimtar abin da ya ke cewa.
“Hmmm Abbas naji ka fa, naji duk abin da ka fad'a ina lalubo amsar da ya kamata na baka ne domin na lura ka riga da ka yanke hukunci ba Shawara kake nema a wurina ba.”
Ta fad'a tana murmushin takaici.
“Ban gane ba.”
“Ai dama ba zaka gane ba Abbas ka riga fa da ka yanke hukunci kawai kayi abin da kake ganin yayi maka nima zan bi umarnin zuciyata ta hanyar aikata abin da nake ganin shi ne daidai.”
Ta fad'a tana sab'a 'yarta a kafad'a ta mik'e tsaye.
“Koma ki zauna Halima bamu gama maganar ba ai, ki sanar da ni abin da kike nufi da kalamanki?”
Abbas ya fad'a yana tsare ta da ido.
Dubansa ta yi daga tsayen da take sannan ta ce.
“Wallahi Abbas muddin ka siya ragon nan da sunan yima Ruk'ayya hakika bayan ni baka sauke nawa nauyin dake rataye akanka ba wallahi wallahi kaji na rantse sai na bari an gama suyar naman da komai sannan zan bulbula masa fetur nasa ashana kowa ya rasa!”