BA DARAJA

13&14

by @nkds

❤️BA DARAJA!!!❤‍🔥

©® Nainarh KD⁂𝓝𝓴𝓭'𝓼❦♡




13–14


*
SA'ADA...

Da hanzari ta mik'e tsaye daga kan kujerar da take tana fama da saka allura a keke lokacin da ta lura Rabi'u ya faki idonta zai bar gidan bayan kuma yana sane basu da komai na sarrafawa a gidan.

“Baban Samira ka manta ne zaka fita bayan baka bani komai ba, gashi ina ta fama da kai akan kud'in matar can mai shinkafa kullum sai ta aiko fa dan Allah ka daure a biyata kud'inta.”

Ta k'ari sa maganar da tun jiya take maimaita masa amma ya yi kunnen uwar shegu da ita bayan kuma shi ya ce ta karb'a bashin shinkafar bashi da kud'i a lokacin gashi har yau da ake cike kusan sati biyu da karb'an tana ta fama ya'ki ya biya ita kuma bata da kud'i da ta biya matar musamman ma yadda ta addabeta da aike ba dare ba rana domin ita gani take ai Sa'ada ce ta cinye kud'in ba wai Rabi'u ne ya hana ba.

“Haba Sa'ada yanzu kin rantse dai sai kin tona min asiri Duniya ta zageni ban da haka wannan wani irin tijara ne zaki tsareni a tsakar gida da wannan kalaman naki na banza.”

Sororo ta yi tana dubansa da d'unbin mamaki, ko da yake dai ya ci ace zuwa yanzu ta dena mamakin halayen Rabi'u domin babu wanda bata sani ba abin da ya fi haka ma zai aikata ta kasa gane wani irin miji ta aura ji take kamar ta d'an yi nadamar aurensa musamman a yanzu da munanan halayensa suka bayyana kamar dai tayi garajen hak'uri ne duba da halin matsi da take a hannun matar mahaifinta ya sa lokacin da Rabi'u ya nema aurenta ta yi saurin amince masa ba tare da tsaya ta fahimci wanene shi ba.

“Ina magana kin wani kafeni da ido...”

Maganarsa ce ta dawo da ita daga d'an tunanin da ta fara.

Ta sauke ajiyar zuciya cikin sassauta murya ta ce.

“Kayi hak'uri ba burina na b'ata maka ko kuma yunk'urin tona maka asiri ba kawai nayi maka tuni ne...”

“To ki rik'e abin ki ba'a so kuma ni banda kud'i wannan ita ke nan min...”

Ya yi maganar yana ciro wata gudan d'ari biyu da ta ji duniya ya wurga ma ta a tsawace ya ci gaba.

“Ban da rashin arziki ma irin naki Sa'ada ace har sai kin dinga d'aga min hankali akan kud'in cefane bayan kina sane bani da kud'i ina amfanin sana'ar da kike idan ba zaki tallafa min ba lokacin da bani da shi haba jama'a wasu matan dai indai ta halinsu za'a bi to fa ba zasu tab'a shiga aljanna ba ko kin manta Allah da kansa ya ce mace tabi miji ta yi masa biyayya domin aljannarta yana k'ark'ashin k'afarsa ne sai ya d'aga sannan zata shige saboda haka wallahi ki bini a sannu muddin kina so ki gama da duniya lafiya ehee.”

Tun da ya ci gaba da sababin Sa'ada ta saki baki tana kallo da saurarensa cikin tsananin mamaki na kalaman dake fitowa daga bakinsa sai ta jinjina kai tana k'ok'arin ganin ta tuna inda ta yi masa ba daidai ba a wannan lamari da har yake maganar idan tana son gamawa da Duniya lafiya.

“Rabi'u ni ba jahila ba ce koda ka ganni haka yanzu mene ne ya kawo batun gamawa da duniya lafiya dan kawai na tambayeka kud'in cefane abin da yake hakki ne a kanka kuma da kake maganar ina sana'a bana tausaya maka naga ai kaine nauyina yake hakki akanka kuma sannan idan ka manta na tuna maka duk irin jarin da ake bani a baya domin nayi sana'a kai kake cinye kud'in amma ban tab'a k'orafi akai ba amma shi ne zaka dinga fad'an irin wannan kalaman gaskiya ya kamata ka sake nazari dai domin wannan hanyar da ka d'auka mana a zaman aure ba mai b'ullewa ba ce...”
Kafin ta sauke numfashi Rabi'u da ya k'ari sa wurin yana sakin huci ya kifa ma ta mari masifa na cin sa yake fad'in.

“Lallai ma Sa'ada ashe har nayi lalacewan da zaki dinga fad'a min irin wad'annan maganganun har ki kirani da jahili saboda kin rainani.”

Kallonsa take da mamaki hannayenta dafe da kuncinta cikin k'unar rai ta ce.

“Baban Samira me ya yi zafi dan kawai na fad'a maka gaskiya kuma ni dai da bakina ban kiraka da jahili ba sai dai...”
Saurin datse kalaman bakinta ta yi tana ja da baya sakamakon ganin yadda ya tunkaro ta yana nad'e hannu da shirin kai ma ta duka kamar zai yi dambe da namiji sa'ansa.

“Ina ce baki da kunya ai da kin tsaya wallahi sai nayi k'asa-k'asa dake a wurin nan shashashar banza kawai mara tausayin miji ni wallahi nayi nadamar aurenki ma da na san haka kike da na ban yi kuskuren aurenki.”

Jin kalaman dake fitowa daga bakinsa maimakon Sa'ada ta yi masa shiru har ya yi ya gama amma sai taji ta kasa ganin yadda yake d'aura ma ta laifin da yake nasa ne k'iri-k'iri.

“Ai ni ce zan ce nayi kuskure da na aureka domin ban san haka kake ba Rabi'u kuma ka ci gaba da halinka karka fasa Allah yana ji kuma ya na gani muddin baka sauke nauyin hakkina dake kanka ba wallahi wutar...”

Bai bari ta k'ari sa ba ya d'aga hannu da niyyar sake kifa ma ta wani marin sai dai kukan da yayayyiyar 'yarsu Samira keyi wacce hayaniyarsu ya tasa da kuma sallamar da ake kwad'awa a k'ofar gidan ne ya sa shi sauke hannunsa yana jan qwafa tare da ficewa daga gidan kamar zai tashi sama yayin da Sa'ada ta sauke ajiyar zuciya tana k'ari sawa wurin yarinyar dake kuka ta fara lallashi.

GIDAN ABBAS...

A fusace ta mik'e tsaye tsabar yadda ranta ya b'aci zuciyarta ta fara tafarfasa ya sa taji ba zata iya jurar ci gaba da sauraren kalamansa ba cikin tsananin b'acin rai muryarta a sama da hayagaga ta fara magana.

“Wani irin wulak'anci kake nema kayi min ne Abbas me kake nufi da kalamanka? cewa fa kake nayi hak'uri, haka mukayi da kai, wannan ai cin zarafi ne da cin fuska na haifa maka d'a sukutum kuma ka zo min da wannan kalaman naka na banza da wofi ai Wallahi ba zata sab'u ba duk inda kud'i suke ma ka nemo kawai kayi min ragon suna dan ba zaka ja min abin gori ba wallahi.”

Da tsananin mamaki Abbas yake dubanta ganin yadda take nema ta yi masa tijara sai yaji ransa ya soma b'aci amma sai ya daure cikin sassauta murya ya ce.

“Rakiya ki zauna mana mu yi magana ta fahimta ki kuma saurareni ba wai nufi na...”

“Dakata Abbas ba fa zan tab'a sauraranka ba indai ba rago naka ka siyomin ba, haba a'ina aka tab'a haka ma? to gaskiya ba zata sab'u ba, ba kuma zan lamunci wannan cin fuskar da kake kokarin yi min ba haba.”

Ta k'are maganar tana mai ficewa tsakar gidan ba tare da ta saurara abin da yake fad'a ba.

Ta fara zage-zage tana fad'in ba'a isa a tauye ma ta hakkinta ba wallahi.


“Wai Rakiya ina hankali da tunanin ki ya tafi ne yanzu a kan 'yar wannan maganar zaki nema ki tara min jama'a sai kace akanki aka fara rashin yin hakika a haihuwar fari.”

A fusace ta dubesa cikin d'aga murya ta ce.

“Wallahi Abbas ka bani mamaki ina son da kake nuna kana min ace hakika ta gagara a haihuwar fari, kuma da kake maganar a kaina aka fara rashin yin hakika ai duk macen da ta yarda aka ki yi ma ta ita taso.”

“Ah ah ah wai meke faruwa ne tun ina a band'aki nake jiyo hayaniya? Ke kuma Rukayyatu mene ne abin da ya fito dake tsakar gida kina d'anyen jego kuma kike d'aga murya baki ko tsoron dare?”

Mama Tsahare da ta yi gaggawan fitowa daga band'aki da jin hayaniya ta fad'a tana k'are musu kallo su duka.

Sai da Abbas ya duba saitin d'akin Halima dake rufe kamar ya san ita ma ta farka saboda hayaniyar tasu sannan ya ce.

“Mama ba wani abu ba ne fa bata fahimce ni ba ne. Rakiya ki kwantar da hankali kiji abin da zan fad'a miki mana...”

“Wallahi ba zan kwantar ba haba Abbas me zaka ce min idan na saurareka, bayan ka gama wulak'anta ni.”

“Ke da'allah zakuyimin bayanin abin da yake faruwa ne ko kuwa?”

Mama Tsahare ta k'ara fad'a cikin rud'ani.
Abbas ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa sai dai ko kafin ya sama zarafin magana Ruk'ayya ta riga da fad'in.

“Ki jiye min wani son zuciya irin na d'anki cewa fa yake ba zai yi min hakika ba bayan kuma ba haka mukayi da shi ba.”

Mamaki da rud'ani ya sa Mama Tsahare ta kasa gane mene ne ma ma'anar kalmar hakika.

“Nifa kin k'ara jefani ne a duhu ban gane inda kalamanki suka dosa ba.”

Cikin k'ara kufula Ruk'ayya ta ce.

“Ai dama ba zaki gane ba tun da dama kina goyon bayan d'an ki to wallahi ba'a isa ba indai sunana Ruk'ayya sai an yankama d'ana rago kamar sauran 'ya'ya.”

Sai da taji kalamanta na k'arshe sannan Mama Tsahare ta gane inda zancen ya dosa da mamaki ta sake ware idanu tana dubansu su duka kafin ta sauke ajiyar zuciya tana neman yawun bakinta domin mamaki ma ya sa ta rasa ta ina zata fara.

“Anti mene ne haka kike yi ne Dan Allah ki kwantar da hankali abi komai a sannu.”

Cewar K'anwar Ruk'ayya wato Jummai da ta zo domin kwana kasancewar ana gobe suna ne.

Wani banzan kallo ta yi ma ta tana fad'in ta rufe ma ta baki tun da ba da ita take ba.

Masifar Ruk'ayya ya sa 'yan tsirarun 'yan uwanta da na Abbas da zasu kwana a gidan kasancewar gobe sa suna duk suka tashi suna mamakin halinta ganin yadda take tijara akan ance ba zata sama ragon suna ba.

Ita ma Mama Tsahare duk tsiyarta da ta ga haukar Ruk'ayya yafi k'arfinta ya sa ta fara neman sulhu ta dube Abbas da ya yi tsuru cikin damuwa.

“Idan baka da kud'in yi ma ta ragon ne ko bashi sai naci a samu ayi ma ta kasan ba dad'i abin ace haihuwar fari ba'a yima mutum yanka ba.”

Gyara kwanciyarta Halima ta yi tana kuma saurara taji amsar da Abbas zai bayar gefe guda tana mamakin hali irin na Mama Tsahare sai dai taso bata dariya ganin yadda da farko taso tabi bayan d'anta amma ganin haukar Ruk'ayya mai lasisi ba zata bar kowa ya sarara ba ya sa ta sakko.

“Ni ba zan ci bashin kowa ba Mama kuma tun da ita bata san mutunci ba ta ci gaba da haukar nata, ragon ne ba zan yanka ba kuma bi bayan ma da nace zan ma ta na fasa tun da ba tsoronta nake ba ta yi duk abin da take ganin ya yi ma ta.”

Yana gama fad'ar hakan ya sa kai ya koma d'aki cike da takaicin halin Ruk'ayya na rashin hak'uri gefe guda yana mamakin kansa da ya yi shakkan Halima akan abin da ta ce zata aikata muddin ya siya ragon, a zahirin gaskiya ba wai bashi da kud'in yima ma Ruk'ayya hakika bane to amma kalaman Halima yake dubawa.

“Aikin banza mata duk subi su hana mutum sukuni.”

Ya fad'a cikin takaici yana juya kwanciya a ransa kuma yake tabbatar da ba tsoron kalaman Halima ne ya sa bai siya ragon ba kawai dan a zauna lafiya ne.


Ita kuwa Ruk'ayya da ta gama kufula da abin da Abbas ya yi ma ta tasha alwashi iri-iri kuma bata dena tijarar ba har sai da k'anwarta ta jata d'aki da kyar nan ma bata dena mita ba domin abin ba k'aramin haushi ya bata ba ta ya ma za'a ce da girmanta ana ganin girmanta amma Abbas ya ma ta wulak'anci har haka yanzu me zata ce ma Kawayenta da ta gama cika musu baki? A daren ranar dai haka ta kwana cikin k'unci da takaicin abin da Abbas ya yi ma ta kuma ta yi alwashin bai yi a banza ba dole sai ta nema wata hanyar da zata fanshe takaicin da ya k'unsa ma ta.

Washegari ma haka aka tashi da hidimar suna sai dai abin ba wani armashi domin ita kanta mai jegon b'acin ran da take ciki bai bari ta yi shigar kece raini da ta yi niyya da kuma kirkirar taron suna na bada labari ba ko dan fitan kunyan Kawaye.