15&16
by @nkds
❤️BA DARAJA!!!❤🔥
©® Nainarh KD♡
15–16
Ruk'ayya bata sake shiga cikin b'acin rai da takaici ba, sai da yamma ta yi gidan suna ya cika dank'am sannan Halima ta fara shige da fice cikin tsadaddun kaya na kece raini da ta zauna ta zuba basirar da Allah ya bata na d'inki ma kayan.
Abbas yana da yayyi mata da yawa kasancewar mahaifiyarsu ita ce mace ta uku wurin mahaifinsu shi ya sa yayyin nasu mata duk sun girme su sosai, domin wasu ma sai da suka yi aure sannan aka haifesu, to a cikin yayyin Abbas mata masu aure Anti Hajara tana da yarinyar da ta aurar, kuma suka kasance kusan sa'anni suke da Halima sannan suna shiri sosai shi ya sa lokacin da 'yar Anti Hajara wato Sayyada taji labarin haihuwar Ruk'ayya da kanta ta fidda kud'i ta sai musu atamfa 'yar ya yi kuma sabon fita wanda zasu saka ranar suna suyi anko, shi ya sa ita kuma Halima ta zauna ta baje basira wurin tsara had'add'en d'inki ma wannan atamfar ai kuwa zo ku gansu cikin wannan kaya musamman ma Halima da take da kyan jiki sai ku rantse ita ce mai jegon.
“Anti wai mene ne duk wannan yanzu ba zaki shirya ba, d'an hoton nan ma na tarihi aje ayi?.”
Jummai ke maganar cikin gundura da halin yayar tata, ji take kamar ta ta yi ta dukanta tsabar takaicinta da take kwasa tun daren jiya zuwa yau. Koma ta ce tun haihuwar domin yadda Ruk'ayya bata kauda ido a wasu abubuwan ita wallahi har kunya ma take Bata.
Ko kafin Ruk'ayya ta ce wani abu sai ga Sayyada ta shigo d'akin tana baza k'amshi cikin karad'i irin nata ta rik'e baki bayan ta ja ta tsaya a tsakiyar d'akin take fad'in.
“Mene ne haka nake gani ne Ruk'ayya mai jego guda ace ba gayu mu 'yan gayyan sod'i ma mun yi bare kuma ku masu abin, gaskiya Anti Rakiya ta Malam Abbas tashi kawai ki shirya muje ga mai hoto can Abbas ya turo.”
Duk irin taurin kai na Ruk'ayya sai da Sayyada ta saka ta shirya da dad'in baki da komai daga k'arshe ma ita ta yi ma ta makeup kuma ta yi kyau kasancewar ma fatarta mai haske ne.
“Haba wake tsayawa wani k'unci a lokacin farin ciki na yau kad'ai ai, saki jiki kawai kiyi abin da ya kamata, ki a aje komai a gefe.”
Cewar Sayyada lokacin da take yi ma ta kwalliyar.
Koda suka fito tsakar gidan wurin hoto lokacin da idon Ruk'ayya ya sauka akan Halima dake ta fama da jama'a ga Zainab sab'e a kafad'arta taci ado kamar ba gobe sai taji ranta ya sake b'aci sai taji ma kamar duk kod'a kyawunta da su Safiyya da Jummai keyi kamar muzantata suke, haka dai aka ci taro a ka gama zuwa lokacin kuwa Ruk'ayya ji take kamar ta yi bindiga tsabar bak'in ciki da hassada da ta sakama zuciyarta sai ya zama ranar da ta yi ma tanadi domin ta k'unsawa Halima bak'in ciki sai ya juye ita ce ta kwashi bak'in cikin ma'ishi, tabbas taso ace yadda ta fara da haifa wa Abbas d'a namiji to ya kasance Duniya ma ta shaida namiji ta haifa, ta yadda zata yi komai na kece raini kuma ya kasance harka na manya, sai gashi reshe ya juye da mujiya dama kuma hassada ga mai rabo taki, inda ace zata nutsu ta yi nazari zata fahimci ita Halima da bata saka hassada ko bak'in ciki ba ga yadda ta gudanar da komai cikin walwala da annashuwa duk da taron ba nata ba ne amma ta cinye.
**
Zaune yake ya kafa kujera a tsakar gidan ga wani uban kwalkuleto a hannunsa gefe guda yaransa ne zaune saman tabarma a nutse daga mazan har matan kowannensu d'auke da littafinsa a hannu, yayin da Halima ke ta shige da ficenta daga d'aki zuwa kicin da tsakar gidan.
“Wai Rakiya har yanzu bata dawo ba?”
Ya yi maganar yana duban Halima da ta fito daga d'aki rik'e da plate.
Ganin bata da niyyar kulasa ya sake cewa.
“Haba ayi mutum sam bashi da lissafi tun safe ka fita daga gida amma anyi magariba da issha'i mutum ba zai yi tunanin ya dawo ba, to daga yau an gama yawon arba'in d'in tun da ba farillah ba ne.”
Ita dai Halima tana jinsa yana ta sababi ko kanzil bata ce da shi ba, ita wallahi dariya ma yaso bata a ganinta mene ne nata a ciki da zai zo yana wannan maganganu ai sai ya bari wacce yakeyi domin ita ta dawo sai ya tare ta ba wai yazo yana yi ma ta ba.
“Gaskiya lamarin nan ba fita anya kuwa zan iya ci gaba kuwa gaba d'aya lissafi da burin da na d'aura akan noman nan da nayi sam bai tafi daidai ba.”
Abbas ya sake fad'a yana kuma latsa kwalkuleton hannunsa. Sai a lokacin Halima ta magantu da fad'in.
“Komai na Allah ne ka daure ka ci gaba wata rana zaka ci moriyar abin, shi dama komai na rayuwa d'an hak'uri ne, kuma ni sai nake ga ma abin da ka samu na amfanin gonar nan ai ba laifi.”
Ta k'are maganar lokacin da ta k'ari sa ta aje masa plate d'in abincinsa a gabansa da yake yana gida kuma bata gamar girkin da wuri ba shi ya sa maimakon a kula sai ta zuba masa a plate.
Sai da ya ce da ita Thank you yana k'arb'ar cokalin da take shirin aje masa sannan ya ce.
“Ba zaki gane lissafin ba, domin irin burin da naci akan noman nan da kuma yadda al'amarin ya kasance jikina fa ya yi sanyi ji nake kamar na aje noman nan a gefe na kama kasuwanci na kawai.”
Halima ta girgiza kai da sauri tana kuma 'yar dariya.
“Ni dai da zakabi shawarata da ka bar gonarka kuma ka ci gaba da noman a hankali wata rana zaka sama fiye da abin da kake buri domin komai d'an hak'uri ne kuma na lokaci ne.”
Shiru Abbas ya yi kamar mai nazari yayin da kafin ya nemo amsar bawa Halima sai ga Ruk'ayya ta shigo gidan da sallamarta sai duk suka mayar da dubansu kanta yaran suna yi ma ta sannu da dawowa cikin girmamawa kasancewar da haka mahaifiyarsu ta raini tarbiyyarsu.
“Sai yanzu muke ganin idonku?”
Cewar Abbas fuska ba rahama. Yayin da Halima ta mik'e tsaye bayan ta yi ma Ruk'ayyan sannu da dawowa ba dan halinta ba sai dan fita daga hakki. Tana ma jin yadda ta amsa ma ta kamar an yi ma ta dole sai dai ita Halima bata damu ba, domin ba ita ce gabanta ba ita wallahi da ma zata bata shawara ta d'auka, to da sai ta ce da ita tabi a sannu akan al'amarin Abbas domin indai shi ne sannu a hankali zai shayar da ita ruwan mamaki ta hanyar koyar da ita ilimin sanin wanene shi.
“Darling ke nan kai da zaka fara yi mana maraba da dawowa wannan uwar gajiya da muka kwaso shi ne kake wannan batu?”
Ruk'ayya ta yi maganar lokacin da ta aje jakar hannunta ta kuma cire hijjab d'in jikinta ta aje a gefe sannan ta kwanto goyon yaronta da ya ci suna Mahmoud tana d'aura wa Abbas a hannu tana neman kujera zata zauna. Da mamaki Abbas yake dubanta kafin ya bud'e baki ya ce.
“Keda zaki je ki kwantar da shi, kya mik'omin shi, naga ma bacci yake.”
Sai da ta turo d'an kwalli gaban goshi sannan ta bashi amsa da.
“Haba Darling ai baka shi nayi kaji d'uminsa shima yaji naka kafin naje na kwantar da shi kasan kwana biyun nan da bama samun zama gaba d'aya ba d'aukar sa kake yana jin d'uminka ba.”
‘Sabon salo kiran sallah da usur.’
Cewar Halima cikin zuciyarta ita abin ma dariya ya bata.
“Bana son maganar banza fa da'allah rik'e sa ki kai yaro d'aki da sanyin nan zaki wani bar yaro a waje salon ya kwashi mura. Ko suma wad'an nan da kika gani ai an yi musu shigar da sanyi ba zai musu illa ba ne ya sa kika gansu wajen.”
Takaicin kalamansa da dizgatan da ya yi ne ya sa ta fincike d'an daga hannunsa ta nufa d'aki fuuu kamar zata tashi sama.
“Ki fa bi dashi a hankali kinsan d'an naki ba kwari ya cika ba, kar ki ja ma mutane aiki a daren nan.”
Abbas ya fad'a shi da baya gani ya yi shiru.
Ita kam ko kula sa batayi ba.
“An fa baka shi ne domin ka saka mishi albarka, da ka sani baka mata haka ba, ai da ka bita da lalama.”
Halima da ke shimfid'a sallaya zatayi sallahr Issha'i da bata sama damar yi kan lokaci ba ta fad'a kuma ba tare da ta jira cewarsa ba ta fara sallahr ta.
“Hauwa'un Baba come here my girl, zoki bani labarin wannan da na ganku tare d'azu.”
Abbas ya yi maganar wa babbar 'yar Halima mai shekaru goma sha biyu zuwa sha uku. Take idanunta suka cicciko da kwalla ta mik'e kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta k'arisa daga gefensa ta rakub'e kamar wacce take jira ace kyat ta ruga da gudu. Abbas ne ya fara magana cikin yanayi bana nuna b'acin rai ba sai dai fuskarsa a tsare take sosai, daidai lokacin kuma Ruk'ayya ta dawo wurin ta zauna.
“Wanene wannan yaron da na ganku tare a tsaye a titi?”
Shiru Hauwa'u ta yi hawaye na shirin zubo ma ta, gyad'a kai Abbas ya yi sannan ya k'ara da fad'in.
“Idan aure kikeso ai sai kizo ki fad'a min kinga sai na dena kashe kud'ina a banza wurin karatunki, gwara nayi miki auren tun da haka kikeso koda tabarma na had'aki ai nayi k'ok'ari.”
Ya sake fad'a wannan karon tsumewar dake kan fuskarsa yafi na baya kuma a yanayin yadda ya yi maganar yana mai tabbatar ma ta da gaske yake.
Kuka ta fashe da shi sai dai ta kasa magana.
Tsawa Abbas ya daka ma ta da fad'in.
“Zaki bud'e baki kiyimin bayani ko zaki ci gaba da kukan ne har sai na dakko bulala?”
“Kkkkayi hak'uri Abba, dama dama fa cewa ya yi wai yana sona, kuma ni ni”
A fusace ya k'ara daka ma ta wata tsawar da tafi na farko da fad'in.
“Ke kuma me kika ce masa? Cewa kikayi kin amince?”
Cikin kuka ta ce.
“A'a ba haka ba ne cewa nayi ya yi hak'uri Abbana ya ce karatu zan yi.”
Ajiyar zuciya Abbas ya sauke yana kallonta.
“Kin kyauta yarinyar kirki ai nayi tunanin amsa masa kikayi da hakan ke nuni da aure kikeso kin ga da sai na cire ki a makarantar kawai ayi miki auren da kike buk'ata.”
Shiru ta yi kanta a k'asa yayin da shi kuma Abbas ya fara jan ta da fira cikin sakin fuska da raha dan ta saki jikinta kafin ya ce ta koma ta zauna taci abincinta.
“Haba Darling ka dinga bin yaran nan a sannu fa, ai ni sai nake ga abin ayi farin ciki ne yarinya da k'ananun shekarunta har ta fara tara samari hakan na nuni da farin jininsu gareta...”
“Dakata Rakiya wannan ba abin da ya shafe ki bane kuma da kike maganar nan me kike nufi ne? so kike na bar yarana sakaka ke nan babu kulawa ko me? Karki sake min irin wannan katsalandan d'in bana Buk'ata.”
Shiru Ruk'ayya ta yi duk da ba haka taso ba, amma a ci gaba da tafiyar a sannu a sannu dai...
Halima tana daga gefe da ta shimfid'a wata tabarmar tana yanka kasancewar tsakar gidan da hasken nepa taresu taso taji haushin abin da Ruk'ayya ta ce domin a ganinta da ta yi shiru da bakinta tun da ba sabgar da ya shafe ta bane kuma da yake tasan halin Abbas musamman akan yaransa shi ya sa bata ce komai ba.
Mik'e wa tsaye Ruk'ayya ta yi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ta shige d'aki daga ciki ta kwalawa Abbas kira kamar wani sa'an ta. Sai dai ga mamakin Halima a karo na farko ke nan Ruk'ayya ta yi ma Abbas irin wannan kira bai bar abin da yake yi ya tafi d'akinta cikin sassarfa da rawar jiki ba.
“Mene ya faru kike yi min kiran mafarauta cikin daren nan?”
Abbas ya tambaye ta lokacin da ta sake fitowa.
Mamaki ne ya bayyana a fuskarta da jin kalamansa sai kuma ta basar tare da k'ak'aro murmushi tana mik'a masa wata k'atuwar leda bak'a ta ce.
“Ah ba wani abu ba ne fa, dama na kira ka domin ka karb'a wannan tsarabar naka sannan nayi maka sai da safe ne. Ku ma kuzo ku karb'a ga naku.”
Ta k'are maganar tana kiran yaran tare da bawa kowannensu nasa tsarabar danginsu kayan mak'ulashe irin su Dubulan, cincin, donot da sauransu. Sannan ta bawa Halima nata ita ma ta yi godiya. Zuwa yanzu Halima ta fahimci sam Ruk'ayya bata da rowa tana da kyauta sam bata da mak'o ko kyashin bada abin hannunta sai dai matsalarta guda shi ne tafi so ya kasance ita ce ta yi kyautar ba wai Abbas ya yi ba koda wa 'ya'yansa ne.
“Iyye lallai Amaryata Rakiya tanaji dani wannan kayan dad'i haka duk ni d'aya.”
Abbas ya yi maganar cikin santi yana gutsirar donot har da wani lumshe ido yana kad'a kai, yaran kuwa mai zasu yi idan ba dariya ba, Halima ta d'an yi murmushi kawai ba ta ce komai ba.
Yayin da jin dad'i da nishad'i ya cika zuciyar Ruk'ayya ita fa tana masifar son ta yi abu a yabe ta, musanman ma idan ya kasance Abbas d'in ne ya yaba kuma a gaban Halima, wannan abu ba k'aramin faranta ma ta rai yake ba.
“Wai Halima ban ga kin bawa amaryata abincinta ba kodai har d'aki aka kai ma ta ne?”
Abbas ya sake fad'a yana mayar da dubansa ga Halima.
‘Huu'umm wato baka tuna cewa ba'a bawa matarka abinci ba sai da ta baka kayan dad'i.’
Cewar Halima a zuciyarta.
A fili kuma sai ta amsa masa da fad'in.
“Baka lura ba ne tun da ta dawo na bawa Saddiqa ta kai ma ta d'aki.”
“Yawwa Halima tah uwar gida a sarautar mata Allahu Akbar.”
Abbas ya yi maganar da kirari har da jinjina ma Halima hannunsa alamun girmamawa, wani murmushi kawai ta yi ba tare da ta tanka ba yayin da takaici ya hana Ruk'ayya da ta kasa komawa d'aki sukuni, duk da tana sane ba girkin ta bane.
Fira Abbas ya ci gaba da jan su su duka idan ya sako Halima ta tanka idan kuma bai sakota ba bata saka musu baki a haka har yaran suka yi bacci ta kaisu makwancinsu bayan ta tattare kayan da ta kammala yankawa, dare ya yi lokaci yaja amma Ruk'ayya tak'i komawa d'aki sai jan Abbas da zance take, Halima da ta ga haka sai ta yi musu sallama tana shirin shigewa d'aki ta rufo k'ofa domin ta lura da gayya Ruk'ayya ta yi.
“Ban gane kina yi min sai da safe ba?”
Abbas ya fad'a yana duban Halima sai kuma ya k'ara da.
“Ko dai kin manta yau d'in kece dani ne?”
“E to wai da gani nayi kuna fira kar na katse muku...”
“Zancen banza ma ke nan. Ke Rakiya Allah ya tashe mu lafiya sai da safe ki shafamin kan yaronki.”
A maimakon Ruk'ayya taji dad'in kalamansa na k'arshe sai ma taji wani takaici ne ya turnuk'e ta wai ta shafa masa kan d'anta. Qwafa kawai ta yi tana shigewa d'aki.
Haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa da Halima cikin gidan Abbas tare da Ruk'ayya wacce a kullum sabbin abubuwa take fito da su salo-salo gefe guda Halima bata tab'a biye ma ta idan ma taso yin wata kissar, sai dai abu d'aya da Halima bata yarda da shi ba shi ne aci zarafinta ko na 'ya'yanta sam bata d'aukar wargi a wannan b'angare. Kuma da yake abin da ya faru ya zama shi ne sanadin tafiya Khadija 'yar wurin Halima kwananta hamsin da takwas da k'onewa da man da ta yi Allah ya yi ma ta rasuwa a lokacin ba Halima da Abbas ba hatta ita kanta Ruk'ayya mutuwar yarinyar ta daketa duk da cewar duk tsayin kwanakin da ta d'auka tana jinyar k'unan Ruk'ayya bata tab'a bud'e baki ta yi ma ta sannu ba kuma Halima bata nuna hakan ya dameta ba sannan koda yarinyar ta rasu ta yi hak'uri ta karb'a k'addararta.
Gefe guda kuma tuni matan anguwa kowacce k'ok'arin shigewa jikin Halima take da masu yi domin Allah da ma wad'an da aka sin hakan ne a zuciyarsu.
Zaman na k'ara zama zama halin kowa yana ci gaba da bayyana yayin da tuni Halima dama wasu daga dangin Abbas har ma da makwafta sun gama fahimtar Ruk'ayya musamman ma dai Halima da suke zaune tare, ta fahimci Ruk'ayya tana da tsiya sosai da kuma saka abu a rai sai dai tana da kirki daidai ita, indai ba'a b'angaren kishi akan Abbas ba ne domin kam nan b'angaren koma mene ne zata iya aikatawa babu ruwanta, sannan Ruk'ayya bata da munafunci ko gulma indai ba ta biye son zuciya ba ko kuma idan ba'a kan Abbas ba, sannan abin hannunta bai rufe ma ta ido ba abu na gaba kuma tana da masifar son 'ya'ya a b'angaren kishi kuma tana masifar son ganin tana mulkar gidan Abbas yadda ranta ke so sai dai wannan ne ya ci tura har zuwa yanzu da take da kusan shekaru hud'u a gidan tuni ta yi haihuwa na biyu kuma da yake mace ta haifa yarinyar taci suna Bilkisu a lokacin da ta haihun ma da yake Halima tana da ciki sai dai bai tsufa ba watanni biyu da wasu kwanaki tsakani ita ma Halima ta haifa mace ita kuma taci suna Maryam ya zama yaranta hud'u ban da guda biyu da suka rasu wato Habib da Khadija. Yayin da Ruk'ayya take da biyu Mahmoud da Bilkisu, sai kuma sauran yaran Abbas da iyayensu basu gidan Sulaiman da suke kira da sule sai kuma Saddiqa.