022
by @oumfatima33
*MEERAH*
*022*
Washe gari gidanmu ya tashi da shirye-shiryen tarbar su Ya Sultan, gaba ɗaya Momy ta hana kanta huta wa sai da ta tabbatar an tanadar musu duk abinda zasu buƙata. Ƙarfe 10 na safiya aka ce jirginsu zai sauka, don haka zuwa 9 da rabi mutanen gidanmu sun gama shirya wa.
A dai-dai wannan lokacin tashi na daga bacci kenan ina ƙoƙarin sauka a saman gadon kira ya shigo cikin waya ta, a hankali na juya idanuna na sauke su a saman wayar dake ajiye a saman bed side drawer.
Ganin Nawaz ne mai kiran yasa kyakykyawan murmushi ya bayyana a saman fuskata. Sai da kiran ya katse wani ya sake shigowa sannan na ɗauka da sallama.
"Ba dai na tashe ki a bacci bane?." Nawaz ya faɗa lokacin da na ɗauki wayar, ɗan ƙaramin murmushi na saki sannan nace.
"A'a, na riga na tashi daman."
"Masha Allah, ina fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya?." Nawaz ya faɗa daga can ɓangaren.
"Ina lafiya, ina fatan kai ma haka." Na faɗa a hankali da muryar baccin da bai gama saki na sosai ba.
"Ina lafiya." Nawaz ya faɗa sannan ya ɗora da cewa.
"Bari na bar ki samu shirya, dama kawai daddaɗar muryarki nake son ji kafin na wuce Studio, don yinin yau ya kasance daddaɗa a gare ni."
Murmushi na saki zuciyata cike da farin ciki.
Duk lokacin da Nawaz ya nuna min irin tsananin ƙaunar da yake yi min na kan ji kaina ta musamman sosai, har nake jin cewa ni ɗin mai sa'a ce sosai a soyayya.
Domin kuwa yanda Nawaz ya raini zuciyata da wata irin soyayya mai ɗauke da tsananin kulawa, abin ba ƙaramin kama zuciyata ya yi ba. Hakan ya sa nake jin cewar duk duniya shi kaɗai ya can-cance ni.
"Masoyiya! Kina jina kuwa?." Ya yi min tambayar cikin taushin lafazi. Ajiyar zuciya na sauke nace.
"Ina jin ka masoyi."
"Zan tafi to." Ya faɗa tamkar mai jiran umarni daga gare ni. Murmushi na saki ina jin shauƙi irin wanda mutanen da suka tsunduma cikin soyayya kaɗai suke tan-tance yanayin.
"Allah ya tsare min kai, ya kai ka lafiya, ya dawo min da kai lafiya. Allah ya sadaka da dukkan alkairan dake cikin wannan ranar, ya yi maka tsari da dukkanin wani sharrin dake cikin ta." Nayi masa addu'ar da na saba yi masa kullum idan zai fita.
A ɓangaren Nawaz tun da ta fara magana ya lumshe ido yana jin daɗi da wata irin natsuwa dake saukar masa. Allah ya baiwa Meerah baiwar iya magana da saka mutum farin ciki, duk da ƙarancin shekarunta. Don duka shekarun nata basu ƙarasa cika sha tara ba.
Amma sai dai tana da wani irin wayo da baiwar iya sarrafa magana, tana da matuƙar shiga rai sosai duk wanda ya yi mu'amala da ita sai yaji yana sonta. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ta kammala addu'ar yace.
"Allah ya maki albarka masoyiya, ina roƙon Allah ya mallaka min ke."
"Ameen ya Allah." Na bashi amsa sannan na ɗora da cewa.
"Ka tafi wurin aikinka nima yanzu zan tashi na shirya, yau su Ya Sultan zasu dawo." Har ga Allah sai da zuciyar Nawaz ta motsa a cikin ƙirjinsa jin cewar su Ya Sultan zasu dawo, ba a kan kowa ba kuma zuciyar tasa ta buga sai a kan Ajmal. Domin shi kaɗai ne mutumin dake kayar masa da gaba a cikin ahalin Meerah.
"Masoyi kana jina kuwa?." Na yi masa tambayar jin ya yi shiru. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"Ina jin ki masoyiya, kije ki shirya, Allah ya dawo da su lafiya." Ya yi maganar yanayinsa na ƙara yin sanyi a kan sanyinsa da na sani. Ban wani tsaya tunani a kai ba nace masa.
"Okay baye, I love you."
"I love you too." Ya faɗa sannan ya ajiye wayar, ajiyar zuciya na sauke fuskata ɗauke da murmushi. Ina ɗagowa naga Momy tsaye a bakin ƙofar wacce ban san lokacin da ta shigo ba.
Tsare ta na yi da kallo zuciyata cike da tunanin cewar taji maganar mu da Nawaz ko bata jini ba. Baki na buɗe zan yi mata magana ta riga ni da cewa.
"Ki yi sauri ki shirya ki fito lokaci na ƙure wa."
"Okay Momy." Na faɗa, daga haka ta juya ta fice daga ɗakin. Idanu na lumshe ina sauke ajiyar zuciya da tunanin cewa bata jini ba kawai, da wannan tunanin na sauka a gadon ina nufar bayi.
Baki na fara wanke wa sannan na yi wanka na fito daga bayin, ban tsaya ɓata lokaci ba na shirya cikin gaggawa kasancewar na san Momy na jira na. Tsaf na fito shirye cikin Abaya Black color ina tashin daddaɗan ƙamshi.
Samu na yi su Ya Maheer duk sun fito don haka muka shiga Motoci muka wuce airport cike da farin cikin dawowar Yayun namu, musamman Ya Sultan wanda na yi matuƙar kewar sa.
Bamu daɗe a airport ba jirginsu ya sauka, don haka muka tarbe su cike da farin ciki. Ya Sultan na fara hango wa don haka na tafi da gudu na rungume sa ina faɗin.
"Oyoyo my Yaya, I miss you!." Na yi maganar cike da farin cikin ganinsa, kamar an ce in kalli bayansa sai idona a cikin na Ya Ajmal wanda ya yi matuƙar sauya wa a idanuna. Wani irin kyau naga ya ƙara mai cike da kwarjini.
Jikinsa ya ƙara buɗe wa sosai fiye da yanda na san shi a baya, chocolate skin ɗinsa ta ƙara kwanciya tana sheƙin dake nuna tsananin hutu da jin daɗi. Masha Allah kyawu da kwarjini kam Allah ya hore wa Ya Ajmal, don duk inda ake neman cikakken Namiji mai cikar kamala to ya kai.
'Bar shi dai da baƙin ran tsiya da iya takurawa mutane.' na furta a ƙasan zuciyata ina ɗauke kaina daga kallon seconds ɗin da na yi masa, wanda a cikin su na banbance sauyin da ya samu.
**** A ɓangaren Ajmal shima kamar yanda ta yi mamakin sauyawar da ya yi, haka shima ya yi matuƙar mamakin irin girman da ta ƙara, kallo yake ƙare mata cike da tsanaki inda ya tabbatar da cewa wannan ba Meerah ɗin da ya bari bace a ƴan shekarun da suka wuce.
Wannan Meerah ɗin cikakkiyar budurwa ce a yanzu mai ɗauke da wani irin kyau mai matuƙar sanyi da fizgar hankali, ta ƙara girma sosai a idanunsa wanda har hakan yaso ba shi mamaki. Kasancewar tunda suka tafi basu dawo gida ba sai da suka kammala.
Sai dai su Dady suna zuwa su duba su, Momy ma ta taɓa zuwa sai dai bata tafi da Meerah ba kasancewar tana makaranta ita ma a lokacin. Sannan ko waya sai dai ya ji tana yi ita da Sultan, don basu da shaƙuwar da zata ɗauki waya ta kira sa.
Shima kuma koda ya kira Momy sai dai kawai ya tambayi lafiyarta shike nan baya tambayar a bata su gaisa.
Wannan yasa girman nata ya bashi mamaki sosai, muryar Sultan ce ta dawo da shi daga wannan zancen zucin da yake yi. Inda ya ji yana cewa.
"Wai Autar Momy ce wannan ta girma haka ta zama ƴanmatan gaske?." Ya ƙare maganar cike da mamakin girman nata. Shagwaɓe fuska na yi jin maganar da ya faɗa nace.
"Yaya mana! Kenan da ni ba ƴanmatan gaske bace?." Na yi maganar ina taɓe fuska.
"Ana nan dai da halin." Ajmal ya furta ƙasa-ƙasa sosai wanda babu wanda yaji abinda ya faɗa ɗin. Sultan kuwa dariya ya yi yace.
"Da gaske Auta girman naki ya bani mamaki, yo ni na zaci zan zo in samu Autar yanda na barta ashe tayi tsawon ƙafa. To Allah yasa tsarabar da nayo maki suyi maki."
"Ai Ya Sultan yarinyar nan ta dage dole sai ta kamo mu tsayi." Aryan ya faɗa cike da raha. Duk dariya aka yi daga haka aka shiga gaisawa, inda hankalin Momy gaba ɗaya yana kan Ajmal ne tana masa magana cike da kulawa.
Da haka muka tattara muka wuce gida cike da farin ciki.
*****
Bayan mun isa gida ɓangarensu suka nufa don su samu su yi wanka su shirya, su Ya Maheer kuwa Palon Momy suka zauna. Ni da Bintu kuma muka shiga shirya table.
Ba'a jima sosai ba su Ya Sultan suka shigo duk sun yi wanka sun sauya kaya. Kai tsaye dining suka nufa Ya Sultan yana faɗin.
"Me aka shirya mana haka daddaɗan ƙamshi yake kai min ziyara a hanci tun kafin na ƙara so?." Murmushi na saki nace.
"Ai Yaya wannan ɗin duk aikin Hajiya Meerah ne."
"Sannu uwar ƴan son kai, sai a zaci ke kaɗai kika shiga Kitchen ɗin kika shirya komai." Ya Aryan ya faɗa yana harara ta. Baki na tura gaba nace.
"Ai dai komai idea ɗina ne." Dariya su Momy ke yiwa drama ɗinmu Ni da Aryan, don baya iya shiru sai ya tanka min tamkar wata sa'ar sa.
Gaba ɗaya muka hallara a dining muka ci abinci, ina manne da Ya Sultan ina faman masa surutu yana biye min. Ya Ajmal kuwa tun gaisuwar da nayi masa babu abinda ya ƙara haɗa ni da shi. Sai dai idan mun haɗa ido ya harare ni ni kuma in tura masa baki gaba.
"Dady yana City kenan?." Ya Sultan ya tambaya lokacin da yake kammala cin abincin nasa.
"Eh sai weekend zai dawo ai." Jawad ya bashi amsa, hira muka ɗan taɓa bayan kammala cin abincin har aka kira sallar Azahar sannan muka tashi. Maza suka fita Masallaci mu kuma muka haye sama, bayan an taso masallaci su Yaya Sultan ɓangarensu suka wuce domin huta wa.
Nima bedroom ɗina na shige na ƙule muna waya da Nawaz wanda yake rero min wasu daɗaɗan baitukan da ya rera yau a Studio.
"Kin san me masoyiya?." Ya tambaya cike da shauƙin soyayya.
"Sai ka faɗa." Na bashi amsa ina ƙara lafe wa a saman gadon. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"Lokacin da nake rera waƙar nan fuskarki zuciyata take hango wa, gaɓa ɗaya kalaman dake cikin waƙar naki ne kuma don ke na yi su. Ina fatan wannan ma zata birge ki." Ya ƙare maganar cikin sanyin yanayinsa wanda yake birge ni.
Gyara kwanciya nayi ina janyo Tedy bear ɗina na rungume shi da kyau nace.
"Duk wasu kalamai da zasu fito daga bakinka karɓaɓɓu ne a wurina masoyi. Yanzu dai ɗan rera min waƙar tawa naji." Nayi maganar cike da shauƙin soyayya. Ƙaran murɗa ƙofar da aka yi aka shigo da sallama ne ya saka ni ajiye wayar bayan na katse kiran.
"Momy." Na ambaci sunanta a hankali ganin tana tsaye ta kafe ni da ido. Ƙaraso wa tayi ta zauna kusa dani tana fuskanta ta da kyau tace.
"Da waye kike waya Ameerah? Yaushe ne kika fara soyayya har tayi nisa haka ba tare da jin sanar min ba?." Ta yi min tambayar fuskarta babu alamar wasa.
"Momy?." Na faɗa da yanayin shagwaɓa ina son ta bar zancen.
"Bana son wasa Ameerah, ki faɗa min gaskiya don ɗazu ma na shigo na same ki kina waya, yanzu ma haka. Da waye kike waya? A ina kika san shi?." Ta yi min tambayoyin babu alamar wasa.
Ganin ta riga ta kama ni babu yanda zan yi in kauce, sannan ko ba komai ma Gara na bayyana mata soyayyata da Nawaz tunda ina son sa da gaske. Sannan kuma shima yana sona da gaske, aure muke burin yi babu buƙatar ci gaba da ɓoye wa.
Wannan tunanin da na yi ne ya saka ni faɗa mata gaskiya, na sanar da ita cewa Nawaz ne muke waya da shi. Sannan kuma muna son junanmu.
Shiru Momy tayi tana sauraren bayanin da nake yi mata kai tsaye babu wani ɓoye ɓoye na sanar mata cewar ina son Nawaz, kuma shi nake so a aura min.
Sai da na kammala bayani na sannan ta fuskance ni da kyau tace.
"Yaushe hakan ta faru? Ina nufin yaushe ne kuka fara soyayyar?." Duk da cewa na ɗan ji kunyar tambayar amma haka na daure na bata amsa domin kuwa da gaske nake yi.
"Momy nima kaina ban san yaushe hakan ta fara a tsakanin mu ba, amma dai ranar da muka yi graduation ne ranar da ya sanar min cewar yana sona. Nima kuma na amince da hakan." Na bata amsa ina kallon ƙasa. Ajiyar zuciya mai nauyi Momy ta sauke sannan tace.
"Ba zan ce kar ki so Nawaz ba Ameerah domin kuwa shi ɗin mutumin kirki ne, sannan kuma bashi da wani abin da za'a ƙisa. Sai dai abinda nake so ki sani shi ne, har yanzu ke ɗin yarinya ce ƙarama. A halin yanzu ba soyayya ce ta kama ce ki ba. Abinda ya kamata shine ki natsu ki mayar da hankalin a kan karatun da zaki fara wanda shine burin Mahaifinki."
Dakata wa tayi ta sauke numfashi sannan taci gaba da cewa.
"Abu na biyu shine, bana tunanin cewar Mahaifinki zai amincewa da wannan zaɓin naki, don ba wannan burin yaci a kan ki ba. Saboda haka ki mayar da hankali a kan abinda zai amfane ki, shi aure lokaci ne idan Allah ya ƙaddara Nawaz Mijinki ne idan lokaci ya yi sai ki ga kin aure sa ba tare da wata matsala ba." Ta ƙare maganar tana kallona da fatan na fahimci abinda take son fahimtar dani ɗin.......
Barka da dare da fatan mun yi hutun ƙarshen mako lafiya?.
Oum Fatima