023
by @oumfatima33
*MEERAH*
*023*
Wani irin kallo nake yiwa Momy tunda ta fara magana har ta kammala, ji nake jikina yana yin sanyi a kan kalaman da ta furta. Dogon Nazari na shiga a kan kalaman nata ina fassara su dai-dai da tunanina.
Tunda na fara soyayyata gaba gaɗi nake yinta, koda wasa ban taɓa tsayawa na duba matsayin dake tsakanina da Nawaz ba.
Bare nayi tunanin cewa wani ƙalubale zai iya biyo wa bayan soyayyar tamu ba, sai dai kalaman Momy a yanzu sun fara haska min abubuwan da ban taɓa tsaya wa na duba su ba.
Amma sai dai ni a wurina wannan ɗin ba zai iya zama abinda zai shiga tsakanina da Nawaz ba, a ganina tunda ina son sa yana sona komai mai sauƙi ne.
Momy kuwa ganin nayi nisa a cikin tunani ya saka ta dafa kafaɗata tace.
"Ina fatan kin fahimci abinda na faɗa maki?." Ban iya bata amsa ba sai kai na gyaɗa mata. Kaina ta shafa tace.
"Da kyau, ki kwanta ki huta kafin la'asar." Tana kammala faɗa ta miƙe ta fice a ɗakin zuciyarta cike da saƙe saƙe a kan ƴar tata.
*******
Bayan fitar Momy kasa yin baccin na yi kamar yanda ta buƙata, maimakon hakan sai tunanuka da suka shiga yi min kai-kawo a cikin zuciyata. Idan na fahimta dai-dai Momy na son sanar da ni cewa Dady ba zai karɓi Nawaz a matsayin Mijina ba.
"To amma saboda me?." Na yi wa kaina tambayar ina tashi zaune daga kwanciyar da nake.
"Saboda bambancin matsayin dake tsakanin ahalinku mana." Zuciyata ta bani amsar tambayar da na yi wa kaina.
"Koma dai miye ni dai ina son sa a hakan, kuma na san cewa Dady ba zai taɓa hana ni abinda nake so ba. Domin kuwa duk abinda na nema a wurinsa yana bani shi, na san ba zai ƙi yi min wannan ba." Na faɗa ina koma wa na kwanta don bawa kai na ƙwarin gwuiwa.
Tattara komai na yi na ajiye a gefe da tunanin cewa babu abinda zai hana mu mallakar juna. Kiran Zeezee da ya shigo min ne ya saka ni manta wa da komai na ɗaga kiran nata.
"Bestiena kuma amaryar Nawaz Baffa." Zeezee ta faɗa lokacin da na yi mata sallama. Sunan da take kirana da shi kenan in taso tsokana ta. Don tunda na sanar mata cewa soyayya muke yi da Nawaz ta saka min sunan.
Bana manta lokacin da nake tunanin cewa ko dai Bestie tana son Nawaz ne so na gaske ba wai fans ɗin sa kawai ba, na taɓa tambayarta hakan a lokacin da aka yi birthday party ɗinta wanda a nan ne muka fara ganin Nawaz ɗin.
Amsar da ta bani cewar kawai dai tana son sa a matsayin best mawaƙinta ce ta sauya wan can tunanin da nake yi, don haka koda yace yana sona kai tsaye na amince masa. Ita ce ta fara zargin cewa son juna muke nida Nawaz, saboda ganin kusancin dake tsakanin mu.
Sun saba sosai ita ma don suna gaisawa idan ya kira ni muna tare, sannan yana mutunta ta a matsayin babbar fans ɗin sa, wacce ya samu alkairi sosai ta dalilinta.
Magana muka yi da ita sosai a waya tana sanar min cewar Dad ɗinta yace a abroad zata yi jami'a, da zarar result ɗin mu ya fito zata wuce.
Shine take roƙona na yiwa Dady magana a sama mana admission a makaranta ɗaya mu tafi tare don bata son a raba mu, dariya na yi sannan nace.
"Bestie ai ko Dady ya amince na san wannan azababben Ya Ajmal ɗin ba zai taɓa bari na fita waje na yi karatu ba. Kuma nima dai a nawa ɓangaren gaskiya bana son tafiya wata ƙasar yanzu." Na faɗa lokacin da ta gama roƙo na.
"Iye! Wato saboda kin fara soyayya shi yasa bakya son tafiya ki bar masoyinki ko?." Zeezee ta faɗa tana riƙe baki cike da mamaki. Domin kuwa ta san a da burinmu kenan idan muka kammala Secondary School mu fita waje karatu.
Maganar Zeezee gaskiya ce don har cikin raina soyayyar Nawaz ita ce ta sauya min ra'ayi, har nake jin ba zan iya yin nisa da shi na tafi wata ƙasar na bar shi ba.
"Ba zaki gane bane Bestie, ke dai ayi sha'ani kawai. Amma fa kema bana son rabuwa dake gaskiya, saboda haka ki haƙura kawai mu yi karatun mu a nan." Na faɗa ina son jin ta bakinta.
"To Allah ya sa Dady ya amince da hakan." Zeezee ta faɗa sannan ta ɗora da cewa.
"Yauwa Haneef ya kira ni yace min bakya ɗaga kiransa, yana cikin damuwa sosai a kan ki Bestie Please ki ɗan ji tsusayinsa ko wayarsa ki riƙa amsa wa mana." Tsoki naja ace.
"Yaron nan bashi da hankali Bestie. Wai ni Haneef zai kalla yace yana so, Haneef fa Class mate ɗinmu Bestie, to nayi soyayya da Haneef in ce nayi soyayya da wa kenan?." Na faɗa cikin ɓacin rai.
"Ban ce ki yi soyayya da shi ba, amma dai ki daure ki riƙa kula sa tunda ko ba komai friend ɗin mu ne." Cewar Zeezee.
"Shike nan naji to, yanzu dai bacci zan yi sai anjima." Na faɗa ina kashe wayata na zame ba kwanta, ban jima da kwanciya ba bacci ya ɗauke ni.
*Ajmal....*
A ɓangaren Ajmal kuwa tunda suka koma ɓangarensu ya kwanta yake bacci don ya yi matuƙar gajiya, bai farka ba sai da aka kira sallar la'asar sannan ya tashi ya yi alwala. Yana fito wa ya haɗu da Sultan shima ya fito daga nasa bedroom ɗin.
Haɗuwa suka yi suka tafi masallaci, bayan an idar da salla suka fito tare da su Jawad da suka haɗu da su a can. Koda suka ƙarasa gidan kowa ɓangarensa ya nufa.
Ajmal bedroom ɗinsa ya nufa, yana zuwa kuma laptop ɗinsa ya ɗauka ya shiga duba sababbin tsare-tsaren Company ɗin sa na kansa da zai fara aiki ba da jima wa ba. Don yace baya son yin aiki a cikin Companies ɗin su Dady, nasa kasuwancin yake son buɗewa da ban kuma su Dady sun bashi goyon baya a kan hakan.
Saɓanin Sultan da zai karɓi ragamar kulawa da Kasuwancin Dady, saboda da rashin lokaci da bashi da shi dalilin harkokinsa na siyasa. Shima Ajmal ɗin yana bayar da gudummawa sosai a Companies ɗin iyayen nasu tun ma kafin ya kammala degree ɗinsa na farko.
Kasancewar Allah ya masa baiwar tafiyar da kasuwanci da fito da sabbin tsaruka, waɗan da idan aka yi amfani dasu ake ganin ci gaba sosai. Yanzu ma ba wai ya ajiye aikin gaba ɗaya bane, a'a kawai dai yana son kafa nasa Kasuwancin na kansa.
Katafaren Company da za'a riƙa shigo da ko wane kalar furniture's daga ko wacce ƙasa yake ƙoƙarin buɗewa, sannan da kayan electronics komai da komai. Ya jima yana wannan shirin hakan ya sa zuwa yanzu Alhamdulillah komai ya kammala sai buɗe wa da fara aiki kai tsaye.
Ya yi nisa sosai a cikin duba sabbin kayan da zasu shigo da su daga ƙasar Turqish, don bayan ya ɗan huta na kwana biyu zai wuce Turqish ɗin a kan batun shigowa da kayan. Sallamar Sultan ce ta saka shi ɗago wa daga aikin da yake yi ɗin yana kallon sa.
"Ni zan wuce na sabunta soyayyata, ko zaka raka ni ne?." Sultan ya faɗa yana tsare sa da ido. Baki Ajmal ya taɓe yace.
"Sai ka dawo, Allah ya bada sa'a ɗan soyayya."
"Please Man yau dai ka daure ka raka ni mana, kaga baka taɓa zuwa kun gaisa kai da My Amani ba fa." Sultan ya faɗa cikin rarrashi.
"Allah ya kiyaye hanya, ka gaishe ta idan kaje." Ajmal ya faɗa a taƙaice yana mayar da hankalinsa kan duba sample ɗin kayan da aka turo masa.
"Shike nan tunda ba zaka je ba." Sultan ya faɗa yana ficewa a ɗakin, kai tsaye motsrsa ya nufa ya shiga ya yi mata key ya fice a gidan.
****** Ajmal kuwa bayan fitar Sultan sanyi jikinsa ya yi sosai, saboda ya fahimci tamkar ya yi fushi ne. Har ga Allah shi kuma baya son abinda zai ɓata wa ɗan'uwansa rai saboda yana matuƙar son sa, sai dai shi wannan shirmen zuwa zancen baya cikin tsarin sa gaskiya.
Ajiyar zuciya ya sauke a zuciyarsa yana raya cewar zai daure ya raka shi zancen nan wata rana ko zai wanke kansa.
Kiran da ya shigo wayarsa ne ya saka shi kallon wayar don ganin mai kiran, sunan Mamy da ya gani ne ya saka shi lumshe ido har sai da kiran ya katse sannan ya kirata back.
"Barka da wannan lokacin Mamy, fatan kina lafiya?." Ya faɗa bayan sallamar da ya mata ta amsa murya a cunkushe.
"Kana ina ne?." Ta jefo masa tambaya maimakon amsa gaisuwar da ya yi mata.
"Ina Kano ne Mamy a can flights ɗinmu ya sauka." Ya bata amsa cike da girmamawa.
Wani irin ɓacin rai taji jin cewar yana Kano, bayan tsawon lokacin da ya ɗauka baya nan. Yanzu da ya tashi dawo wa shine ya kasa wuce wa gida kai tsaye ya tafi Kano. Kasa danne kanta ta yi sai da tace.
"Yanzu Ajmal ace ina Mahaifiyarka har ka dawo ƙasar nan bayan tsawon lokacin da baka nan, amma ka kasa taho wa inda nake ka wuce wurin Uwar wani kai taka uwar ko oho!." Ta ƙare maganar cikin tsananin ɓacin rai.
"Ki yi haƙuri Mamy ba haka bane in sha Allah gobe da safe zan taho, dama da naga mun sauka a nan ɗin kuma gida ne, shi yasa na bari in ɗan huta yau gobe sai na taho." Ya yi maganar cikin kwantar da murya sosai.
Kashe waya kawai Mamy ta yi cike da takaici ba tare da ta sake cewa komai ba. Lumshe ido kawai ya yi yana fatan ganin ranar da Mamy zata fahimce sa.
Ya jima a haka sannan ya buɗe ido ya ɗauki waya ya kira Momy, sallama tayi masa cikin kamilar muryarta. Gaishe ta ya yi ta amsa masa da kulawa tace.
"Son kana buƙatar wani abu ne?."
"Eh Momy, Meerah ta haɗo Coffee ta kawo min." Ya bata amsa cike da ladabi.
"Okay yanzu zata kawo maka, lafiya kake kuwa Son?." Momy ta yi masa tambayar jin muryarsa a ƙasa sosai.
"Ba wani damuwa bace Momy, kaina ne yake ɗan min ciwo, da na sha Coffee ɗin zan sha Paracetamol." Ya faɗa cikin son kwantar mata da hankali.
"To Allah ya sauwaƙe, amma idan ciwon kan bai sauka ba ka yi magana a kira Doctor yazo ya duba ka." Momy ta faɗa da kulawa sosai.
"Okay Momy." Ya bata amsa sannan suka ajiye wayar.
Da kanta ta shiga Kitchen ta haɗa masa Coffee ɗin don ta san bai cika saka masu aiki su yi masa abinda zai ci ko zai sha ba. Sai da ta kammala haɗa komai sannan ta kira Meerah dake ɗakinta, don yau babu Islamiyya.
*******
Lokacin da Momy ta kira ni ina kwance ina kallon wani American Film wanda Ya Aryan ya tura min jiya, ajiye IPad ɗin na yi na miƙe na sauka ƙasa don amsa kiran.
A tsaye na same ta riƙe da farantin da ta ɗora Mug ɗin da ta zuba Coffee ɗin a ciki.
"Gani Momy." Na faɗa lokacin da na ƙara sa kusa da ita, kayan hannunta ta miƙo min tace.
"Kije ki kai wa Yayanku yana ɓangarensu." Mayafin abayar dake ɗaure a kaina na kwance na yafa shi da kyau sannan na amshi kayan na fice ba tare da tambayar wane Yayan namu ba, saboda na san wanda keda azabar shan Coffee ɗin.
Kai tsaye ɓangarensu na nufa ina ƙun-ƙuni a zuciyata cewar 'mutum sai iyayin tsiya da son saka mutane aiki. In Banda ɗora wa kai ko miye na shan wani Coffee da yanmar nan.' na ƙare zancen zucin nawa lokacin da na isa ƙofar part ɗin nasu shida Ya Sultan.
Tsayawa na yi na ajiye kayan dake hannuna sannan na samu damar dannan doorbell, na kwashe kusan mintuna biyar tsaye a wurin sannan ya taso ya buɗe min. Zuwa lokacin na gama kai wa wuya da wulaƙancinsa, don na san sarai yana jina ya manna min.
Yana buɗe wa kuma ya juya ya koma abinda ba tare da ya min magana ba. Baki na tura gaba sannan na tsuguna na ɗauki kayan na bi bayansa zuciya fal takaicinsa.
Kwance na same sa saman Couch yana faman danna waya.
"Aikin kenan." Na faɗa ƙasa-ƙasa lokacin da nake ƙaraso wa kusa da shi. Ɗago wa ya yi ya zuba min waɗan nan idanun nasa masu ladabtar da ni koda ban shirya hakan ba kuwa.
Yanda ya tsare ni da idon ya saka tsoro ya kamani da tunanin ko yaji abinda na faɗa ɗin.
Sai da ya gama shan ƙamshinsa sannan yace.......
*Oum Fatima*