ZAWARA.

CHAPTER 14.

by @1239900

ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️ 

PAGE 14.

Kamar yanda Samir ya yi wa Malam Sanda alƙawari haka ya zo cikin ƙanƙanin lokaci kan nan a hargitse. Tare da shi aka taimaka wa Hanifah ta shiga cikin motarsa Rabi da Nasibah na tsaye suna jera mata sannu. Ko ci kanku bai ce musu ba banda aikin kallon Nasibah dake sanye da riga da wando na bacci irin na gumamar nan da yake yi. 
Suna nan tsaye Malam Sanda da Kilishi suka fito a gurguje suka shiga motar Samir ya ja suka tafi asibitinsa. Komawar su Nasibah gida babu jimawa mijin Hanifah ya kira wayar Mama ya sanar da ita gashi nan zuwa,domin kuwa tun da Nasibah ta ji abun kunyar da Makaɗi ke shirin yi musu ta faki ido ta kira shi ta sanar da shi duk abinda yake faruwa. Sallama suka yi ya kashe waya Mama ta samu Nasibah ta rufe ta da faɗa. Baki ta tura ta shige ɗakinsu ta hau shirin makaranta dan bata son zama a cikin gidan Mama ta yi ta mata mita. A gurguje ta gama shiri ta fito sanye da uniform ɗinta a wanke a goge kamar ko da yaushe. Ko abun karyawa bata nema ba ta saka kai ta bar gidan tana fatan Allah Ya sa Hanifah ta haihu lafiya.

Ko a makaranta Nasibah bata da wani kuzari da walwala kamar ko da yaushe,daga malamai har ɗalibai kowa ya fahimci Nansy bata cikin yanayi na fara'a,dan haka kowa sai ya rabu da ita gudun kar mutum ya taka sawun ɓarawo a wajenta. Ana tashi ta samu Nawwarah da Nadiyah ta ce su yi mata rakiya zuwa asibitin Samir dan ta ga Yah Hanifah. Da ƙafa su Nasibah suka taka har zuwa asibitin Samir ɗin saboda rashin kuɗin abun hawa. Sai dai suna isa nurses ɗin wajen suka basu tabbacin babu jimawa aka sallami su Hanifah sakamakon ta haihu cikin ƙoshin lafiya. Lokaci Nasibah ta ɗaga kai ta kalla a jikin makeken agogon bangon dake manne a reception ɗin. Karfe uku da rabi na yamma Nasibah ta gani sai ta kama bakinta ta kulle tare da sakin wata ajiyar zuciya mai karfi. Da sauri su Nawwarah suka fita daga cikin asibitin suna faɗin.

"Yau idan muka je gida Nadiyah sai mun sha faɗa."

Nadiyah wadda take da mugun tsoron duka sai ta kalli Nasibah ta ce.

"Don Allah ki raka ni gidanmu ki faɗa wa Mommy inda muka je kar ta dake ni."

Kai kawai Nansy ta ɗaga musu suka ci gaba da tafiya a ƙafa har suka isa unguwarsu. Har gida Nansy ta kai su Nawwarah sannan ta sanar da iyayensu batun haihuwar Yah Hanifah,barka suka yi mata sannan suka yi musu faɗan da sun bari sai da suka dawo gida sannan suka je asibitin,gashi sun shiga lokacin islamiyya. Gaban Nasibah ne ya yanke ya faɗi da jin kalmar Islamiyyah. Tunanin Malam Luƙman ne ya ɗarsu mata a cikin zuciyarta. Tana fita sai ta kama hanyar makarantar islamiyyar tasu domin ta haɗu da Masoyin nata ta ji yanda suka ƙare da mahaifinta. A jigace ta isa makarantar tasu ta samu ɗalibai duk an shirshiga aji,makararru kuma na nan waje su na karatu a durƙushe a bakin ƙofar ajujuwansu. Kanta tsaye ta shiga cikin makaranta ba tare da ta damu da kallon uniform ɗinta da mutane suke yi ba. Ajinsu ta nufa domin ta yi wa Malam magana dan ya fito waje su tattauna. Sai dai tun kafin ta isa ajin ta jiyo muryar wani malamin yana karatu a madadin Malam Luƙman ɗinta. Tsayawa ta yi tana nazarin dalilin da ya hana Malam Luƙman zuwa makarantar. Tana nan tsaye ta ji muryar Mami maƙociyar su Malam Luƙman na yi mata magana. A hargitse Nansy ta juya ta ce.

"Asibiti kuma? Wanne irin asibiti? Lafiya ƙalau fa muka rabu da shi jiya. To me yake damunsa?"

Nan da nan kuka ya kwace wa Nansy,abunda babu wanda ya taɓa gani a tattare da ita kenan. Domin Nansy na da matuƙar dauriya da jure wahala saboda kada a ga gazawarta a raina ta. Cike da damuwa a saman fuskar Mami ta ce.

"Tun jiya da daddare da ya koma gida in ji Mamanmu yake kwance bashi da lafiya. Shine yau da suka ga abun ya yi yawa aka kira Yah Atiku ya kai su asibiti da motarsa, ɗazu da zan taho makaranta na ga sun dawo gida."

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Na shiga uku ni Nasibah."

Cikin sauri Nasibah ta juya ta fita daga makarantar ko hanya bata gani da kyau saboda hawaye da kukan da yake neman ya kayar da ita a wajen. Ga yunwa da ƙishirwa da suka kassara kuzarinta. A haka ta yi ta jefa ƙafa ta na tafiya cike da tashin hankali har ta isa gidan su Luƙman. Ta na zuwa ta tarar da gidan da mutane da yawa,wannan ya shiga wannan ya fita. Babu ɓata lokaci itama ta bi sahun matan dake shiga suna jimanta yanayin ciwon da suka samu labarin Luƙman ɗin yana fama da shi. Bayan Nasibah ta shiga cikin gidan sai ta samu jikin bangon ɗakin da ta ga mata na shiga suna gaishe da Maman Malam Luƙman suna yi mata jaje tare da addu'ar Allah Ya bashi lafiya. Hawaye take ta zubarwa kamar an kunna fanfo. Tana nan tsaye ta fara jin jiri na neman kayar da ita sai ta samu waje ta durƙusa tare da jefar da jakarta a wajen. A wannan lokacin ne Nasibah ta tuna da bata yi sallah ba,gashi ko gida bata je ba. Sai dai bata jin za ta iya yin ko ɗaya a ciki matsawar bata ga abincin ruhinta ba da halin da yake ciki. Tana nan tana tunani mahaifiyar Luƙman ta fito daga ɗaki ta tsaya a gabanta ta ce.

"Ke yarinya lafiya kika shigo gidan nan tun ɗazu kike ta kuka? Ko kina cikin ɗaliban wannan yaron ne?"

Da sauri Nasibah ta hau gyaɗa kai tana ƙoƙarin tsayar da hawayenta da suka gaza bata haɗin kai. Ido Ummi ta ƙanƙance tana bin Nasibah da kallo. Bayan wasu ƴan daƙiƙu sai ta haɗe fuskarta ta ce.

"Nasibah ko?"

Da sauri Nansy ta ɗaga kai ta kalli Ummi kafin ta yi saurin duƙar da kanta ƙasa tana ci gaba da zubar da ruwan hawaye. Murmushin takaici Ummi ta yi sannan ta ce.

"Taso mu je ki gansa kema. Ai bai kamata ki zauna anan kina kuka ba,kamata ya yi kema ki shiga ki ga halin da mahaifinki ya jefa min ɗana a ciki saboda son abun duniya."

Kai Nasibah ta sake sunne wa ƙasa tana jin dama bata zo ba. Sai dai kafin ta gama tunanin da ta ɗakko a cikin ranta ta ji an ja hannunta,babu ɓata lokaci jikinta ya bi umarnin ƙafafuwanta Ummi ta kaita har cikin ɗakinta inda Malam Luƙman yake a kwance hannunsa da robar karin ruwa a jiki. Baki Nansy ta damƙe wani sabon kuka na taso mata mai sauti. A cikin wannan halin Malam Luƙman ya buɗe idanuwansa ya kalli Nasibah. Wani irin kallo wanda ke nuni da tsantsar so da ƙaunar da yake yi mata. Itama kallonsa ta fara yi tana takawa zuwa wajensa a hankali tana shassheƙar kuka. Murmushi Malam Luƙman ya sakar mata tare da girgiza mata kai,cikin raunatacciyar murya ya ce mata.

"Ki dena irin wannan kukan Nasibah kada kema ki kamu da irin ciwon da nake fama da shi. Ina so da ni da ke mu ɗauki ƙaddara,mu yi haƙuri da junanmu,domin kuwa na fahimci matsawar ban fi mutumin da mahaifinki ya zaɓa miki arziƙi ba to fa ba zai taɓa yarda na aure ki ba."

Cikin kuka Nasibah ta ce.

"Me Baba ya ce maka ne jiya Mine?"

"I am not yours anymore Nasibah. Ya kamata ki gane hakan tun da wuri."

Malam Luƙman ya katse Nasibah cikin numfashi mai sarƙewa. Da sauri Nasibah ta durƙusa a gabansa ta ce.

"Don Allah kada ka sake faɗar haka Mine,zuciyata ba za ta iya jure rashinka ba a rayuwata. Ka sani ina son ka,ka yi min alƙawari ko bayan ka kammala karatu za ka jira na yi candy ka aure ni,a lokacin idan Baba ya ga ka yi kuɗi zai amince ka aure ni. Dan haka ina so ka kawar da duk wani tunani na ɓacin rai a cikin ranka game da koma menene Baba ya ce maka,ka mayar da hankalinka akan karatunka Please. Kai kaɗai nake son in aura Mine."

Idanuwa Malam Luƙman ya lumshe yana jiyo ƙamshin nasara da wani irin ƙwarin guiwa yana sake shigarsa. Kafin ya yi magana Ummi ta riga shi ta ce.

"Ah ah Nasibah kada ki ba shi ƙwarin guiwar da zai sake raunata zuciyarsa a nan gaba. Mahaifinki jiya ya yi masa iyaka da ke,duk da Luƙman bai sanar da mu abinda ya faru ba na tabbata ba ƙaramin abu mahaifinki zai yi masa ba ya haƙura da ke. Ni na haifi Luƙman na san irin zurfin cikinsa da girman soyayyar da yake yi miki. Dan haka ina so da ke da shi ku yi haƙuri da junanku,kada ku manta har yanzu kuna da sauran lokaci a rayuwarku;musamman ma ke da kike da ƙarancin shekaru,matsawar kuna cikin masu nisan kwana ba za ku rasa abokan rayuwar da za su so ku ba."

Cikin kuka Nasibah ta juya ta kalli Ummi wadda tausayin yaran ya cika mata zuciya ta ajiye makaman faɗan dake cikin ranta ta hau lallashi. Kasa cewa komai ta yi sai ta fita daga ɗakin da gudu ta nufi hanyar fita ko jakar ta bata tsaya ta ɗauka ba. Haka ta dinga haɗa hanya har ta isa gida. Shirun da ta ji gidan ya ɗauka ne kamar ba a yi haihuwa ba shi ya sanya ta tsagaita wa da kukan da take yi. Faihah ta gani zaune a bakin ƙofar ɗakinsu tana share hawayenta. Da sauri ta wuce ɗakinsu na ƴammata ta duba bata ga Yah Hanifah ba,sai ta wuce ɗakin Kilishi ta gansu zaune ita da su Rabi da Usman,da alama wata maganar suke yi da suka ganta suka yi shiru. Tsakar gidan ta koma ta shiga ɗakin Mamanta ta ganta zaune a bakin gado ta zabga tagumi. Wajen Faihah ta koma ta ce.

"Ke me ya faru na ga gidan haka kamar an yi mutuwa,ina Yah Hanifah da jaririnta?"

Kafin Faihah ta yi magana Kilishi ta fito tana ɗaure kanta da kallabi ta ce.

"Me kuwa ya faru banda halin mahaifin naki da ya saba yi a koda yaushe? Wannan yaron Samir na dawo da mu daga asibiti cike da kayan arziƙi Malam ya kirawo mijin Hanifah da ya gama ci wa mutunci a asibiti ya ce ya zo ya ɗauki matarsa su koma inda suka fito;saboda shi ba za a zauna masa a gida a cinye masa ɗan abinda zai ciyar da iyalinsa ba. Duk irin kuka da magiyar da Hanifah ta dinga yi wa bawan Allah'n nan bai haƙura ba sai da ya tattara mata kayanta ya sallame ta ta bi mijiinta. Yanzu don Allah in ba dan Nafi'u mutumin kirki bane ba ai tun abinda ya yi masa a asibiti sai ya yi silar macewar aurenta."

Ran Nasibah idan ya yi dubu ya ɓaci. Ba tare da ta ce komai ba ta shige ɗakin su ta zube a soson katifarta tana jin kamar ta yi ta kurma ihu. Sosai ƙirjinta ya yi mata nauyi,zuciyarta na zafi,ga ciwon kai wanda ta tabbata zama da yunwa da ƙishirwa ne ya jawo mata su. Lumshe rinnnun idanuwanta ta yi tana sauke numfashi da ƙyar. Tana nan kwance cikin mawuyacin hali ta ji muryar Mama na faɗin.

"Wato ke Nasibah kin rantse da Allah ni zan biki a matsayina na mahaifiyarki ba ke za ki yi min biyayya ba ko? Nan nan kika shiga har ɗakina ki ka fito ba tare da kin ce min ƙala ba. Daga ina kike tun safe sai yanzu kika ga damar dawowa gidan."

Shiru Nasibah ta yi domin bata jin za ta iya buɗe baki ta ce komai. Ganin haka sai Mama ta hasala ta ɗauki abinda Nasibah ta yi a matsayin raini da jin tashen balaga. Cikin zafin rai ta fita waje ta samo bulala ta dawo ta kulle ƙofa ta hau jibgar Nasibah wadda ke zaune kamar an dasa ta a wajen ko gezau bata yi ba. Tun Mama na dukanta tana magana har sai da ta gaji tana haki tana kallon Nasibah wadda wahala ta sanya ta zube wa a wajen a sume. Kilishi dake tsaye a bakin window tana kiran Mama sai ta fashe da kuka ta ce.

"Shikenan kin kashe ta Maryama kin ji daɗinki. Sai da na ce ki yi haƙuri ki ƙyale yarinyar nan ba ji take yi ba amma kika yi kunnen uwar shegu da ni. Za ki buɗe min ƙofar na shigo ko kuwa?"

Jikin Mama na rawa ta buɗe ƙofar ta yar da bulalar a wajen ta shige cikin ɗakinta. Sosai taurin kan Nasibah ke damun ta. Saboda gudun kada ta illata yarinyar ne ya sa take ƙyale ta tana abubuwan da ta ga dama. Gashi yanzu ta hasala ta ta yi mata dukan tsiya. A hankali ta buɗe labulen ɗakinta ta leƙa Kilishi dake rungume da Nasibah tana shafa mata ruwa a jikinta. Idanuwa Nasibah ta buɗe tana fitar da zazzafan numfashi ta ce.

"Me yasa...kika ƙwace....ni...a hannunta?...don Allah...ki barta ta kashe ni....na gaji da zama da  takaicin abubuwan....da...ake yi min....a gidan nan....Baba baya so na da Malam.... Luƙman....ya kore shi yanzu....haka bashi da lafiya...ni na fi so na mutu na huta da zafin da ƙirjina yake yi min Ummaaahh..."

Nasibah ta ƙarasa maganarta tana mai rushewa da wani irin kuka mai tsananin cin rai. Daga can ɗakin Mama itama kukan ta rushe da shi tana jin cewa sakacinta ne ya jawo ƴarta ta fara soyayya tun da ƙarancin shekarunta ba tare da ta farga ta yi wa tufkar hanci ba. Gashi yanzu tana ji tana gani ƴarta na neman kangare musu a cikin gidan..........

*Don Allah wai sakacin wanene yake jawo yara ƙanana su fara soyayya da ƙarancin shekaru a makaranta,wasu ma da Malaman makarantar. Shin akwai illa a soyayya da Malamai ko babu?*