KACIBIS😂
INUWAR ƘADDARA 🖤
Book 1
Page 4✍️
Meelah Bazata
Yana shiga cikin gidan nasu, kamar yadda ya so Ammah ba ta nan, ta riga ta fita, hakan kuwa ya yi masa yadda yake so.
Ƙofar gate ɗin ya kulle da ƙarfi, sannan ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon harabar gidan.
Bangaren Iya, bangaren Kawu Manu, bangaren Baba Auwal, sai bangaren Autan Iya Jafaru.
Bangaren Ammah yana can gefe ne, sai kuma wani part wanda ya fi kowanne girma da kyau a cikin gidan.
Akwai wasu sauran part guda biyu.
Shiru.
Idan Ammah tana nan, ko da ya yi ƙoƙarin shiga ɗakinsa sai ta fara tambayar shi ina ya je, me ya yi, ya dawo daga makaranta lafiya ko a'a.
Amma yau ya samu dama.
Ya ɗaga hannunsa ya duba agogon da ke ɗaure a wuyansa.
11:07 AM.
Rooman kuma za ta dawo ne ƙarfe 12:00 pm.
Rocky kuwa yana tsaye bakin ƙofa, wani kallo Madugu ya yi masa tare da yin wata alama da hannunsa wanda Rocky ya san mai uban gidan nasa yake nufi.
Kamar mutum haka Rocky yake kallon mai gidan nasa, take ya yi wani irin tuma da ihu wanda sai da gidan gaba ɗaya ya ɗauka.
Mutanen gidan kuwa suna ɗakunan su suka ji wannan sanarwa ta Madugu daga bakin Rocky, sun san me yake nufi, wanda in suka ƙara bata lokaci sun san mai zai biyo baya.
Rocky kuwa yana sanarwar da uban gidan nasa ya saka shi ya koma gefe ya zauna ya ɗan sunkuyar da kai.
Wani bangaren daban ya nufa, yana zuwa wani ɗaki ne ya buɗe wasu kalan manyan karnuka na ga ya buɗe, suna ta haniniya, a kalla za su kai su biyar, karnuka ne kala da kala, ɗakinsu daban yake a cikin gidan.
Karnukan sa dama su shida ne, Rocky shine na hannun damansa, wanda da yawan lokaci idan zai fita yake tafiya da shi, sauran kuma suna gida ne sai lokacin aiki wataran yake fita da su.
Yana buɗe su suka wani karkada jiki suka tsugunna alamar gaisuwa, hannu ya ɗaga musu sannan suka biyo bayansa.
Haushin su ne kawai ya cika gidan yayin da duk wani wanda ke gidan jikinsa ya ɗau rawa, musamman Iya wacce tasan itama da nata laifin a gurin wannan tambadadden kamar yadda suke kiransa.
Harabar gidan ya nemi kujerar ya zauna ya daura ƙafa ɗaya akan ɗaya yana kallon ko ina babu alamar mutunci, kana ganinsa kaga cikakken mara mutunci.
Aikuwa matar Baba Auwal ce ta fara fitowa tana kuka wiwi, zani yana kwancewa tana ɗaurawa, tace:
"Dan soyayyar ka da mahaifiyar ka, ka yi hakuri, ban san sanda suka aikata ba, ni bana gidan ma wallahi, ka tambaya kuma ka ji."
Tana faɗa tana kuka sosai da sosai.
Wata irin harara da ya zafga mata yasa ta ja bakinta ta yi shiru, domin ba ta manta hukuncin da ya yi mata kwanaki da ta yiwa Ammah rashin mutunci, cikin ɗakinta ya biya ya haɗa ta da Karen sa guda ɗaya, Viper, sai da ya yi mata cizo fiye da biyar, ta fi wata ɗaya ba ta gama warke ba.
"Malama koma gefe," ya faɗa cikin muryarsa irin ta tantirai.
Aikuwa jiki na rawa ta koma gefe.
Kawu Manu dama ya ɗan fita siyo abu, matar sa Allah-Allah take karya dawo, kiran wayarka take, amma wayar ya bar ta a gida tunda ba nisa zai yi ba.
Duk mutanen gidan sun fito, da yake masu zuwa makaranta duk sun tafi, sauran iyayen ne kawai.
Ita kuma matar Kawu Jafaru dama babu ruwanta, hakan yasa ko fitowa ba ta yi ba, mijinta dama matafiyine kuma baya garin ma, ita kuma duk da Madugu ko kallonta ba ya yi, amma tana mutunta Ammah sosai haka kuma Rooman, har ɗakinta tana shiga kuma tana ɗakko yaranta, ba ruwanta da Madugu bare ta je tana zaginsa a makota tana tsine masa, ita dai addu'arta kawai Allah ya shirya sa ya sa ya daina wannan harkar.
Shi kuwa Madugu yana zaune yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, wanda yake nema ma babu shi aciki, dama a yau case ɗinsa da Kawu Manu ne da kuma Iya.
Kowa ya yi shiru.
Babu wanda ya iya ɗaga ido ya kalle shi, domin babu wanda yake da wannan zarrar.
Alawiyya, yarinyar Kawu Auwal ce, ta yi zaraf jiki na rawa, ƙirƙira na kufcewa, tace:
"Wallahi tallahi Yaya Madugu babu ruwanmu, jiyane Iya da Kawu Manu suka je ɗakin Ammah suka dinga zaginta wai ta haifowa duniya masifa, amma wallahi mu muna ɗaki ma ba mu fito ba, Kawu Manu ne ya yi ta zaginta yana zagin Rooman har yace ma wai aure zasu nata ba zasu bari ta lalace kamar kai ba...."
Ai ba ta rufe baki ba, Iya wacce take gefe itama a ƙasa aduke ta lalaiyo wani ashar tana faɗin:
"Amma wannan yarinya Allah ya tsine miki albarka, ni Iya naga sharri ganin ido na, yanzu ke Alawiyya kanin ubanki kike yi wa sharri irin haka, ni kakar ki wacce ta haifi ubanki kike haɗa mu da bala'i...."
Kuka Iya take sosai da sosai tana zagin Alawiyya, itama Alawiyya cikin rashin tarbiyar take faɗin ai gaskiya ta faɗa ba ta yi ƙarya ba.
Daga kansa ya yi yana kallonsu, ganin yadda kowa ya sa gwiwarsa a ƙasa, shi kuwa yana zaune saman kujera kamar wani sarkinsu.
“Na tambaye ku ina shi Manun yake?”
Babu wanda ya amsa, shiru, domin ba kowa bane ma zai iya yin magana.
Sai matar Baba Auwal ce ta ɗan matsa gaba kaɗan tace:
“Yana… yana.....”
Madugu ya jefa mata wani kallo alamar gargadi yace:
“Na tambaye ki ne? Kika ƙara magana ɗaya anan daga yanzu har nan da kwana uku ba za ki sake furta komai ba, dan sai na yanke miki bakin.”
Ai nan take ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da sa hannu ta damƙe bakin nata, domin kaɗan daga aikinsa ne wannan.
Wani irin shiru ya sake mamaye harabar gidan, babu wani mai iya dogon motsi, ga karnukan sunata zagaye kowa suna kiran umarni Madugu.
Babu abinda yake tashi sai kukan Iya a gurin, a zuciyarta tana ƙara tsine masa, gashi kuma ba za ta iya buɗe baki yanzu ta yi magana ba, amma ace duk girmanta gaban Yaya da sirikai wannan mara mutuncin yasa ta sa gwiwa a ƙasa, tasan uwar sa ba ta nan domin ita kaɗai ta isa ta hana sa a duk duniya.
Tsawa ya daka mai ƙarfi yana miƙewa tsaye, aikuwa take karnukan suma suka daka nasu ihun tare da haushi.
“Iya zan miki kashedi na ƙarshe akan Ammah, duk ranar da kika sake kwatankwacin abinda kika yi in ba sai na sāraki ban shege nake, sai na yi gunduwa-gunduwa da namanki sannan na ba karnuka su cinye, ki gaya wa sauran yaranki kar su wuce iyakarsu, Madugu bai san na gida ba, suk san wani ɗan wahala ya sake shiga gonata to ki shirya jinya ko kuma ki shirya kai wa kiyama domin lahira za ta yi sabon bako.”
Madugu yana zuwa nan ya ɗaga hannu ya shafa gemunsa a hankali, sannan ya kalli sauran ya ci gaba.
“Kun san dalilin da yasa na kira ku nan gaba ɗaya ko?”
Kowa ya yi shiru, babu wanda yayi magana.
Ƙara daure fuskar sa yayi tamau, domin Madugu baya dariya, haka murmushin sa Ammah ce kawai ko Rooman suke ganinsa a duniya.
“Abinda ban sani ba shi ne, me ya sa kuka yi tunanin ba zan sani ba, ko kuwa kun yi tunanin idan bana nan za ku yi duk abinda kuke so ne?”
Babu wanda ya ce komai dai har yanzu.
“Ku duka ku ji ni sosai, duk wanda ya ƙara kallon part din Ammah, ko da da harara ne, to ya tabbatar idanuwansa zasu daina aiki a wannan ranar, Ammah ita ce duniyata, don haka ki kiyaye.”
Muryarsa sam ba ta da ƙarfi sosai, amma ta isa ta sa kowa ya nutsu, domin amonta kaɗai abinda saurara ne da kuma tsoro.
“Gidan nan ba kasuwa ba ne. Ba gurin da kowa zai yi abinda yake so ba ne, Madugu sarki ne don haka dole kowa ya saurari umarni na.”
Ya kalli matar Baba Auwal wacce har zuwa lokacin tana riƙe da bakinta kam, domin ita dai tana da cutar magana, bakinta baya iya yin shiru, haka idan taji magana jikinta har rawa yake, hankalinta baya kwanciya har sai ta faɗa, hakan yasa duk wata gulma unguwar to tana ciki.
“Musamman ku, munafukai wanda bakinku baya shiru, in kika sake shiga gonata za ki ga yadda zanyi da ke, dan na lura ba ki bukatar ƙarasa tsufanki da ƙafafunki.”
Ta sunkuyar da kai, har zuwa lokacin dai ba ta saki bakin nata ba, domin yace inta sake magana sai ya yanke bakin.
“Idan na sake jin wani abu ya faru, ba zan zauna ina tambayar wa ya fara ba, ko kuma wiya aikata gaba ɗaya zan hukunta kowane.”
Ya juya ya kalli matar Kawu Manu yace:
“Ina mijinki yake?”
Aikuwa take jikinta ya ƙara ɗaukar rawa domin duk abinda yake yi ita ce wacce take zugashi.
Cikin in'ina ta fara magana.
“Ya... ya... fita.... ya yi.. tafiya..”
Wani banzan kallo ya jefa musu sannan ya kalli karnukan yace:
“Duk wanda ya tashi daga nan ki yi kaca-kaca da manasa! Ki kuma daga nan har lokacin sallah wani in ya isa ya mike..”
Yana faɗa ya saka kai ya nufi hanyar ƙofa tare da Rocky a bayansa.
Kuka suka sake saki, domin kuwa Iya ita fitsari ma take ji, kuma ta san yanzu bata da damar tashi a gurin kamar yadda ya faɗa.
Madugu yana kaiwa kusa da ƙofar gate ɗin Kawu, yana saƙo kai zai shigo gidan.
Kacibis kenan😂, aikuwa wani irin birki da Kawu Manu ya ja yana komawa baya da azabar gudu ne yasa Alawiyya ta kyalkyale da wata irin dariya duk da halin da suke ciki gaba ɗaya, Iya kuka kuka ta fashe da shi, somin tasan Allah ne kawai zai kwaci Manu a hannun Madugu yau.
Juyawar da Kawu Manu yayi ne yasa Madugu ya kalli Rocky yace:
“Get him.”
Aikuwa da wani irin gudu Rocky ya bi bayan kawai Manu, wanda ya ruga da azabar gudu, bai san yana da gudu haka ba sai ranar, aikuwa yana gudu Rocky yana binsa, yayin da ya cika unguwar da ihu da neman ɗauki.
Duk wanda ma yake ko ya ga Madugu a ƙofar gidan nasu ga Baba Manu na gudu, Karen Madugu na binsa, kowa juyawa yake ya ɓoye.
Masu tir da tsinuwa ne aibata sa a kan abinda yayiwa kanin uban nasa, kuma babu damar magana a gabansa.
Ko rabin layin Kawu Manu bai yi ba ya sare da gudun da yake yi, domin Rocky ya kawo masa wani mummunan cizo wanda har sai da ya saki fitsari a wandon sa tare da faɗuwa ƙasa, kansa Rocky yayi zai sake damƙa masa haƙoransa masu azabar kaifi da dafi, Kawu Manu ya riƙa ya sadakar yau ƙarshensa ya zo, ya tabbatar da kiyama ta tsaya tun yau, sai dai muryar Rooman da ta ratsa gurin yasa shi ma Rocky ya tsaya daga aikata abinda yayi niyya.
“Rockyyy!” Rooman ta faɗa cikin tsawa, aikuwa ya tsaya yana zazzaro harshe, kallon sa tayi tace masa:
“Mu tafi.”
Aikuwa binta yayi tinkis-tinkis.
Leenah wacce ta yadda jakarta ƙasa ta saka kuka saboda ganin Rocky da tayi, ta ma kasa gudu domin kuwa tana bala'in tsoron wannan bakin azzalumin Karen.
Yanzu aka tashesu daga makaranta suka fito domin komawa gida.
Shine sukaga Rocky yana bin wani da gudu, kuma sun san Madugu ne ya saka sa, tun anan gurin jikin Leenah ya fara rawa, ita kuma Rooman sauri take ta matsa domin ganin waye, amma tana zuwa taga Kawu Manu.
Tasan akan abinda ya musu jiya ne Madugu yake masa wannan hukuncin, danne zuciyarta kawai tayi ta hana Rocky aikata abinda aka saka sa.
Kawu Manu yana kwance ya jika jikinsa da fitsari, yayin da inda Karen ya cijesa yake ta zubar da jini.