AASIYAH

13

by @mamuhgee

Aasiyah

Mamuhgee

13

Tinda Dr Binnah ya zauna a kan lafiyayyar kujeran palon da suke zaune suna kuka wiwiwi ya dago a natse da wani sanyi ya kallesu cikin kulawa da tausayawa dan sam baiji dadin ganinsu a tindaga sitirar jikinsu datake a mace har yanayinsu dan haka da rarrashinsu ya fara sbd kukansu dai ya kasa boyuwa kuka sukeyi na gaske na ganin duniyar da akwaita kenan suke can cikin masifar da batada sauki.

Nasiha ya fara yi musu mai kyau da sanyaya jiki sunata kuka wanda kukane da a duniyarsa bai taba sanin da wani zai iya yinsa ba dan ganin wata niima da Allah yayiwa wasu daga cikin bayinsa a duniya.

Lokaci ya dauka mai tsayi yana musu nasiha da magana cikeda kulawa kuma har lokacin kuka sukeyi idanuwansu sunyi jajir kafin ya fara musu tambayoyi gameda yaya suke yaya babansu da matakin da suke akai na karatu.

Hakuri da nuna nadama sukai sosai tareda qasqantar da kansu suka nuna masa sun tuba insha Allah bazasu sake kaucewa a hanya ba kuma su yanzu shine babansu dazasu so ya dorasu a hanya mai kyau madaidaiciya.

Dadin hakan yaji sosai tareda sake basu tabbacin insha Allah itama Maryam Binnah zata yafe musu bazata riqesu a raiba sam.

Kulawa ya nuna musu sosai tareda kokarin sakar musu fuska sbd yanason su dan sake dashi dan samun damar dorasu akan wani bangare na tarbiyar da suka rasa,

Dan lokacinsa ya basu sosai suka jima sosai a mansion din bar lokacin sallar azahar ya fito tareda su sukai sallah a masalaccin mansion din wanda tako ina sanyin ac ne kana sallah yana ratsaka tareda wani qamshi da haske kaman rana ce a cikinsa tsabar lantarki da ko qwarin haske baya tarawa.

Suna fitowa masallaci kai tsaye wani sabon makeken palon dayafi na farko suka ratsa suka isa Dining room wanda aka cika table din da kalolin abincin da suna shigowa masu aiki suka fara bubbudewa take idanuwan Jamilu suka ciko da hawayen wai yanzu duk wannan duniyar da Haj maryam binnah take ciki suna can a asare basu saniba sai yanzu.

Bulama ma ana cewa su zauna yana zaunawa akan jujeran yaji wani laushi ya ratsa mazaunansa aka fara bude luxury manyan warmers din dake jere sai kawai ya fasa kuka ahankali shima yana sunkuyar dakai sbd dai sun kasa dena kukan ganin daular dataci uban wadda suke buri da mafarki dama ji a rayuwa wai gata a hannun uwar data haifesu tana juyawa suna can asarar kwana da tashi cikin tinanin talauci.

Khamis ma dai jajir idanuwan suke har lokacin,

Fara saving nasu akai cikin nutsuwa wanda babu sautin komai daya kuma tashi saina cin abincin wanda sukeci a natse da sanyi da nuna daa da damuwa.

Sunada wani hali wanda kaman a cikin jininsu dayake daya yake wato ko basuyi magana ba ko kallan juna sunsan abinda ya kamata suyi a tare,

A kowace lokaci kuma kowane yanayi sunsan me zasuyi batareda ko kallan juna ba dan hakane komai nasu yake tafiya daidai a tsare da hadin kai dana baki sbd duniyarsu basusan komai da kowaba sai kansu wannan shine abinda Babansu ya tabbatarda ya saka a kwakwalwansu da tinaninsu da jininsu da zuciyarsu hakan ya saka su dukan duk ganimar dake gabansu basu saki jiki sunci ba hasalima kadan kadan sukaci sbd damuwa mai tsanani da nadamar datake bayyane a yanayinsu wanda ya qarawa Dr binnah tausayinsu sosai sbd harga Allah shi kam jinin maryam dinsa abin kaunane a garesa komai lalacewansa kuwa dan haka ya ringa jinsu kaman yayansa.

Miliyan daddaya aka bawa kowannensu cash ba baa acct ba tareda abinci kaya guda aka ce su tafi su siya yar sitirar sakawa ta kwana biyu kafin ya nemesu akan karatunsu da zasu koma daganan aka saka mota ta mayar dasu gida.

Tinda suka iso gidan kowannensu ya zauna suka saka kudin a gaba suna kallo jikin bulama har wata rawa yakeyi sbd jin yayi kaf duniya a yanzu babu burinsa irin Amsa suna Bulama Binnah.

Jamilu kuwa rigar jikinsa ya zare idanuwansa jajir yana hada wani irin zufa yana ambatar Haj maryam akai akai dan kuwa lokaci yayi da wlh ya shirya amsa sunan uwarsa a maimakon ubansa.

Khamis dai ajiyan zuciya ce take fito masa duk bayan mintina biyu idanuwansa a kafe kan kudin wainda duk yawansu da zamansu arzikin farko na rayuwarsu da basu taba riqewaba dan kaf asalin babansu dana mamansu a baya basu taba samun ko dubu dari biyarba a kammale bare miliyan daya.

Baba Ashiru dake kwance yunwa na neman dauke ransa ga azabar radadin ciwo dayake ji na kafafunsa dake fidda wasu ruwan azaba kallansu yayi a zare da kuma jin sanyin ganin kudin yace

"Ya banga kuna murna ba da samun wannan damin kudi haka gasunan dauri dauri???

Kunga ku fara bani abinci kafin yunwa ta tosar da numfashina"

Bulama ne ya kallesa da jajayen idanuwansa yace

"Baba a duniyar da ake ambatar ahalin BINNAH's kadai ta wuce ma a tsaya kallan wannan kudin,

BINNAH's sune asalin abinda muke nema Baba,

Sune asalin sunan danake son amsawa Baba,

Ayau nayi kukan rashin sanin sunan da mahaifiyata take amsawa wanda a yanzu kam ko zan rasa raina saina amsa wannan sunan dan cika maka burinka"

Wani kallo baban yayi masa da mamakin kalmarsa ta karshe tareda baqin ciki mai tsanani ga radadi da wani zugi dayake ji ya bude baki kaman zaiyo aman zuciyarsa sbd tsabar baqin cikin komai da kowa yace

"To kuma sunane da har abada bazaka taba amsawaba sedai sunan naka uban Ashiru wanda talauci ya saka matarsa soyasa da mangyada kaman alkali dan haka Binnah dai sedai kuci gaba da zuwa kai gaisuwa da samun irin wannan da aka baku yanzu.."

Khamis ne ya dago idanuwansa a lokaci daya tareda jamil dashi kansa bulaman suka kallesa gabaki dayansu sbd kalamansa batareda kowannensu yace komaiba.

Sauke numfashi bulama yayi kafin ya bude baki yace

"Zan tina maka da hakan wata rana Baba insha Allah"

Daga hakan ya miqe ya dauki nasa kudin ya shige daki.

Khamis ne ya miqe shima ya dauke nasa daurin kudin ya shige daki ya ajiye cikin kayansa ya fito ya fice.

Bai jima ba ya dawo da ledar take away na shinkafa da biya da kwai dafaffe da salak ya ajiye gaban baban ya cewa jamilu ya bude ya zube masa a plate ta miqa masa

Yana gama fadan hakan ya juya ya fice gidan gabaki daya.

Bulama ma wanka ya sake ya kuka ficewa.

Da tsananin baqin ciki baba yaci abincin yana masifar ko Nama babu jamilu dai baice komaiba daga baya shima fita yayi.

Babu wanda ya dawo a cikinsu sai dare kuma kowannensu da daurin ledar katuwar gasashiyar kasa suka zauna suka cinye tas suka sha lemu mai sanyi Baba Ashiru ma yau saida ya koshi da kaza.

Washe gari jamilu suka saka ya kai Baba asibiti sukuma suka tafi gidan baffa suna ci gaba da kamun kafa sai dare suka dawo lokacin Baba yayi baccin azabar dayasha dan kuwa dai kafa gurin wankinta ya kusan mutuwar da bame sauki ba.

***cikin kwana biyu da suka wuce rayuwarsu ta fara samun sauyi dan sitirar sakawansu da cimarsu ta sauya gabaki daya hakama a kowace daqiqa dake wucewa tsananin sonsu da kwallafa rai a BINNAH's dinsu qaruwa yakeyi yana qara wani irin karfi,

Sun kutsa sun tsananta sunci gaba da binciko tarihin BINNAH's da tarin arzikinsu wanda kullum sake shiga shock sukeyi da irin abubuwan dasuke sake tabbatarwa da asalin asalin BINNAH's dai arziki ne da daular da babu iyaka kuma batada ranar yankewa dan kuwa asalin asalin gadone na arzikin da kullum yake qaruwa da habbakar da hankalima baya dauka.

Sun rasa kowace tinani da buri da tattali sbd sun zama obsessed da sunan da dukiyar da ahalin da komai nasu dan haka da gasken gaske suka koma rayuwar baffa wanda ahankali ahankali ya karbi tubansu ya sake musu suna zuwa gidansa sosai sun shigesa yana sakar musu kudi amma dai sam ya kasa barinsu isa ga maryam dan haryanzu zuciyarsa bata taba nutsuwa da shigarsu rayuwar maryam dinsa ba badan komaiba aa sai dan shi yafison ya kular mata dasu da dukiyarsa.

Shi kansa Dr Binnah din basu sake ganinsa ba babu daman hakan dan kamarma ya kuma barin qasar amma dai suna nan sun kasa sun tsare suna jiransa da matarsa harma da yayansu wainda suke buqatan gani ido da ido,

Kadan kadan tafiyar dai tafara nisa yanzu har gidan Baffa suke kwana wanda anan dinma duniya ce mai zaman kanta dan kuwa kowa dakinsa daban ga Ac da wata irin cima mai kyau toilet kadai idan suka shiga kaman bazasu fito ba ba hayaniya koina shiru kawai kaci kasha ka kwanta kayi kallo ga wayoyin riqewa baffan ya saka ansiyo musu suna shiga media sosai anan suke sake sanin BINNAHs da irin power din dasuke riqe da ita.

Sunso tattarowa gabaki daya su dawo gidan baffan da zama amma sbd babansu sai baffa yaqi barin hakan wanda hakan shine yafara zama matsalar farko dake kokarin hanasu abinda suke so gashi shi baban ya yadda su tare gidan baffan sbd su samu isa ga maryam su cika burinsu kawai dai su samo masa mai kulawa dashi a ringa biyansa ya yadda da hakan.

Sun nunawa baffa hakan yace aa kada su yasar da babansu sbd sunason shiryawa da mahaifiyarsu gwara su kula dashi da kansu zaifi samun kulawa.

Duk yanda suka so suyiwa baffa dan su dawo gidansa kwata kwata sam bai yadda ba ga bangare daya ma ya kasa hadasu da maryam kota waya ne yaqi barinsu sake magana da Dr Binnah kota waya shima ya toshe kowace hanyar samun saduwarsu da Binnahs din dan haka sai kawai abubuwa suka fara musu zafi da fara kallansa a wata katangar dake kokarin shiga tsakaninsu da burin da bazasu taba qin barin ya cika ba.

#MAMUH

#BINNAH'S

#ASHIRUS

#AASIYAH

#THE TRAP

***

***