MATAR GIDA PAGE 72
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCIATION
P72
Bayan fitar Ɗalha daga ɓangaren Unaisa site ɗin Amirah ya shiga kasancewar girkinta ne yau bayan shigarsa ya tarar tuni yara sun yi bacci,hakan yasa ya wuce ɗakinsa bayan shigarsa ɗaki ne ya yi wanka ya shirya kansa cikin jallabiya maron colour daga haka ya fita zuwa kitchen inda ya haɗawa kansa tea hannunsa riƙe da kofi ya koma ɗaki,bayan komawarsa ɗaki kamputarsa ya dauka ya fara aiki,yana nan zaune yana aiki cikin kamputa misalin ƙarfe goma Amirah ta shigo ɗakin bakinta dauke da sallama,sanye take cikin wata doguwar rigar bacci kalar toka rigar ta tsaya mata iya gwiwa ta daura zani samar riga kanta sanye da hula, ba tare da ya kalle inda take ba ya amsa sallamar, waje Amirah ta samu ta zauna ta kafe Ɗalha da ido bata ce masa komai ba, bayan wasu ƴan mintina Ɗalha ya ɗago tare da mayar da dubansa gareta ganin yadda take kallonsa yasa ya ɓude idanunsa kaɗan ya ce ''hi lafiya irin wannan kallo haka'' shiru Amirah ta yi kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta sauke ajiyar zuciya har sannan idanun Ɗalha kanta ta ce ''mamaki ka ke bani'' mayar da dubansa ya yi kan kamputa kafin ya ce ''na me?" Amirah ta yi shiru tana nazarin yadda zata fidda masa magana can ta ce ''ka yi hakuri zan maka ƙatsalandan abinda ka yi ka bani mamaki sosai harda ban san dalilin ka na yin hakan ba amma sai nake ganin kamar baka yi mata adalci ba kamar baka kyauta mata ba'' Amirah bata gama rufe baki ba Ɗalha ya ce ''ita wa?" Amirah ta basa amsa a takaice ta ce ''Unaisa'' daga haka ta yi shiru tana jiran jin abinda Ɗalha zai ce ganin bai da niyyar cewa komai yasa Amirah faɗin ''yarinyar nan ta yi ciwo sosai'' shiru ta yi kafin ta ɗago idanunta a hankali ta kalle Ɗalha ta ga hankalinsa na kamputa dake gabansa shiru ta yi na wasu ƴan mintina kafin ta daura da ''a galabaice muka kaita asibiti,ta zauna asibiti har an sallameta ko sau ɗaya baka je ka duba ta ba,ko kiran waya,duk sanda na ce maka zan bata waya sai ka kashe waya me ta yi maka haka?'' tana kaiwa nan ta sake yin shiru tana kallonsa shi dai bai tanka ta ba wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta buɗe baki cikin kwantar da murya ta ce ''dan Allah in da akwai laifin da ta yi maka na roƙe ka ka yafe mata irin haka babu kyau a ce kana zama tare da mutum amma baka treating ɗinsa yadda ya kamata bai da ce ba bare kuma matarka sannan tana dauke da cikin ka jikinta'' ta ƙare magana cikin kwantar da murya a hankali Ɗalha ya mayar da dubansa gareta murya can ƙasa ya ce ''me yasa kowa ya tashi magana sai ya ce ciki na jikinta? Ita ce mace ta farko da fara daukar ciki a duniya?'' gyara zama ya yi kafin ya ce ke ma fa kin haihu sai nake ganin ba wani abu bane dan tana ciki'' ita dai Amirah mamakin Ɗalha ya cika zuciyarta fal gaba ɗaya ta rasa me zata ce masa kawai ta yi shiru tana kallonsa,hannusa ya kai ya dauki kofi ya yi siping tea kaɗan daga haka ya ajiye kofin,mayar da dubansa ya yi gareta a hankali ya kira sunanta yana kafeta da idanunsa amsa kiran tayi tana kallonsa kamar yadda shima ke kallonta,ajiyar zuciya ya sauki sai kuma ya yi shiru na wasu ƴan sakanni daga haka ya fara bata labarin zaman sa da Unaisa a Kano har izuwa yau bayan ya gama ne Amirah ta kallesa ta ce ''amma aiy ta fita daga kungiyar sannan ta mayar da mota me kuma ya rage?" hannu Ɗalha ya kai ya rufe kamputa da yake aiki daga haka ya miƙewa tsaye ya nufi gado yana shirin kwanciya, mayar da dubansa ga Amirah ya ce ''ban sani ba kawai bani son ganinta kusa da ni,l think l stop loving her'' daga haka ya kwanta tare da kashi side lamp dake daure kan bed site drower gyara kwanciya ya yi yana rufa jiki da bargo ya ce ''ni na kwanta'' shiru Amirah ta yi tana ƙarewa bayansa kallo can ta ce ''ya kamata ka yafe mata tun da ta baka hakuri and ta fita kungiya'' daga kwance Ɗalha ya bata amsa a takaice ya ce ''oky na ji zan yafe mata'' ya faɗa tare da rintsa idanunsa yana karanto addu'a bacci sanin kansa ne ba zai iya yafewa Unaisa ya cigaba da zama da ita ba ya amsa wa Amirah ne kawai dan bai son zancen,Amirah ta dauki a ƙallah mintina biyar zaune kafin daga bisani ta tashi ta kwance zanin jikinta daga haka ta hau gado tare da juyawa Ɗalha baya,kamar jira yake ta hau gado da wani irin sauri ya waigo tare ta janyota jikinsa,bayan sati biyu da sallamar Unaisa daga asibiti sosai ta samu lafiya yanzu tana iya cin komai sai dai cin abincinta ya rago ba kamar da ba,da ta fara cin abinci zata ji gaba ɗaya ya fita kanta sai dai bata amai,tun bayan da aka sallameta daga asibiti ko sau ɗaya bata kai kanta wajen Ɗalha ba duk yadda zata shiga yanayi sai ta daure ta yi ta murƙushe murƙushe a ɗaki ita kaɗai ko ta yi ta tsarki da ruwan ɗumi wasu lokuta kuma ta fita balcony bayan ɗakinta ta shaƙa iska,wani sa'ilin kuma ta shiga You tube ta yi kallon flims irin na ban tsoro haka horo flim bata cika chating a group ɗin matan gida ba yanzu,ba ƙaramin data take ƙonewa ba wajen kallo a You tube da ta gama aiyukan ta ta yi wanka ta ci abinci ta sha magunguna da aka bata a asibiti zata shiga You tube ta yi kallo sallah kaɗai ke tada ita ɓangaren ibada kowa babu laifi sallah baya wuce ta yanzu,sannan kowanne dare tana tashi sallah duk yadda ta kai ga bacci da zaran alarm ɗinta ya buga karfe uku zata farka ta yi nafilah raka'a biyu ta yi tilawar alkur'ani zuwa karfe huɗu sai ta koma ta yi kwanciyarta kasancewar bacci yana cika mata ido sosai sannan bata saba ba,karfe biyar da rabi daidai zata farka ta yi sallar asuba da ta idar zata yi azkar,bata komawa bacci sai karfe bakwai,a wajen Ɗalha kowa mamakin sauyin Unaisa yake yanzu sai ya dauki sama da kwanaki huɗu bai sata ido ba, har da bata gabansa amma ya kan jin mamakin sauyin halaiyarta a can ƙasan zuciyarsa kuma yana jin haushi yadda ta daina nuna damuwa kansa gani yake girman kai ta ke masa kuma zai yi maganinta,a ranar da ta cika sati biyu da sallamarta daga asibiti ranar a ɓangarenta Ɗalha ya ke,bayan tashinta da safe ta yi wanka ta yi duk abubuwan da ta saba daga haka ta nufi ɗakin Ɗalha bayan shigarta ɗakin ganin sa ta yi zaune kan kujera hannunsa riƙe da waya yana dannawa,tun shigowar ta Ɗalha ke binta da ido sai ya ga ta ƙara masa kyau fatarta ta ƙara haske sosai kafafuwanta sun ɗan kumbura kadan haka ma yatsun hannayenta,sanye take cikin wata ɓakar doguwar riga abaya kanta babu ɗan kwali yadda ta gyara sumarta har daukar ido yake ta yi parking sumar,a hankali ƙhamshin humra da ta shafa yake tashi ƙhamshin bai yi yawa ba sannan bai yi kaɗan ba,bayan ta shiga ɗaki ta rufe kofa kafin ta yi sallama ko kaɗan ba ta yi tunanin zai amsa sallamar ba ga mamakin ta sai ta ji ya amsa Unaisa da mamaki ya gama cika ta cikin zuciyarta ta ce ''ka sauko kenan'' a zahiri kuma ta gaishi cike da ladabi nan ma ya amsa taɓe baki Unaisa ta yi tare da mayar da dubanta garesa kamar yadda shima yake kallonta cikin kwantar da murya ta ce ''ina son zuwa gidan Mama'' har sannan idonsa kanta ya ce ''me ya sami Mama?" bata ji dadin tambayar ba amma sai ta danna zuciyarta ta ce ''babu komai kawai so nake na kai masu ziyara'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin a daƙeli ya ce ''ki kirata a waya ku gaisa'' shiru ta yi na wasu ƴan sakanni sai ta ce ''ka yi hakuri ina son zuwa ne'' kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ''shekenan Allah ya tsare hanya'' sosai ta ji dadin amsar da ya bata sai ta ce ''ameen nagode'' shiru bai ce komai ba yana danna wayarsa,Unaisa ta kallesa ta gyara zama cikin kwantar da murya ta ce ''asibiti da na kwanta sun yi min rijista antinatal sun bani magunguna sai ciki na shiga wata shidda zan koma sun kuma rubuta min scaning'' daga haka ta ja bakinta ta yi shiru tana jiran jin abinda zai ce ya dauki a ƙallah mintina uku kafin ya mayar da dubansa gareta ya ce ''allah ya kaimu'' Unaisa bata amsa ba jin ta yi shiru kuma bata fita ba yasa ya ɗago ya kalleta ya ce ''ya dai?" sosa kai Unaisa ta yi kafin a takaice ta ce ''kuɗin mota'' har sannan idanunsa kanta ya ce ''yanzu kike son zuwa'' gyada masa kai alamar eh,mayar da dubansa ya yi ga wayarsa ya ce ''ki shirya zan aji ki'' sosai ta ji daɗin hakan nan ta yi masa godiya daga haka ta fita daga ɗakin zuwa nata,bata wani ɓata lokaci ba ta shirya,bayan ta gama shirya wa ne ta yi zamar ta a parlour tana jiran fitowarsa ba a dau lokaci ba Ɗalha ya fito cikin shiri kallo ɗaya Unaisa ta masa ta dauki kai ta dauki wayarta ta fara danna,sanye yake ciki wata farar shadda ɗinkin zariyya sosai ya yi kyau idanunsa sanye da baƙar glass daga cikin glass yake kallonta gaba ɗaya ya ƙasa dauki idonsa daga gareta cike da kamala da ƙasaita yake tafiya ya ƙaraso inda take zaune,a daƙeli ya ce ''let's go'' a hankali ta mayar da wayarta jaka tare da miƙewa tsaye ta bi bayansa,tafiyar mintina ashirin da biyar ne daga gidan Ɗalha zuwa gidan Mama, the jurney was sileint tuƙi kawai Ɗalha yake fuska babu yabo babu fallasa har ya yi parking kofar gidan Mama bai tanka ta ba,tun fitarsu daga gida ta sa earpad ta kunna film a wayar tana kallo,bayan ya yi parking mota ne Unaisa ta kallesa ta ga ita yake kallo sunkuyar da kai ƙasa ta yi kafin ta ce ''nagode'' shiru ya yi bai ce komai ba buɗe kofar mota ta yi tana shirin fita daga motar ya yi magana kamar wanda aka wa dole ya ce ''karfe biyu zan zo na dauke ki'' ya faɗa ba tare da ya kalle inda take ba taɓe baki Unaisa ta yi kafin ta ce ''to Allah ya kaimu nagode''daga haka ta fita daga motar,ya bi bayanta da ido har sai da ta shiga gida,bayan shigar Unaisa gida da wasu mintina ya ja mota ya bar wajen,sallama dauki a bakinta ta shigo gidan Mama na zaune samar tafurma tana gyara wake yayin da Anty Aisha na can magudana tana wankin kayansu ita da Mama duk suka juyo tare da kallon kofa jin muryar Unaisa Mama ce ta fara amsa sallamar kafin Anty Aisha waje Unaisa ta samu gefen Mama ta zauna cike da girmamawa ta gaida Mama kafin ta fara kokarin tashi amma ta ƙasa Mama ta kalleta ta ce ''ina kuma za ki je?" a takaice ta bawa Mama amsa ta ce ''zan je na gaida Anty Aisha ne'' Anty Aisha dake zaune saman kujera ƴar tsuguno tana wankin kaya ta dauraye hannu tare da miƙewa tsaye ta ce ''yi zaman ki'' har inda Unaisa da Mama ke zaune ta ƙaraso suka gaida da Unaisa tana tambayar Unaisa karfin jiki shiru Unaisa ta yi bata amsa ba ita a dole kunya,da taimakon Unaisa Mama ta dafa farar shinkafa da mai Unaisa na zaune tana yankan salak Anty Aisha ta fita daga wanka bata dade da gama wankin ba mayar da dubanta ta yi ga Unaisa ta ce ''ki ka ce karfe biyu mijin ki zai zo daukan ki?" Unaisa ta ce ''eh'' Anty Aisha ta ajiye botiki da take riƙe da shi ta ce ''so nake ki yi min rakiya barka gidan wata ƙawata ta haihu shekaran jira'' Mama dake dakan yaji ta ce ''a'a Aisha ki yi tafiyar ki kar mijinta ya zo daukanta ya tarar bata nan ba zai ji dadi ba'' Anty Aisha ta ce ''haka ne'' misalin ƙarfe ɗaya da ƴan mintina Unaisa ce zaune ɗakin Mama daga gefenta Mama ce zaune tana tasbihi Unaisa na sanye da hijabi tana jan carbi da alama basu dade da idar da sallah ba,Unaisa ta shafe addu'a daga haka ta miƙe tsaye ta zauna bakin gado,bayan wasu ƴan mintina Mama ta shafe addu'a daga haka ta fita daga ɗakin bata dauki lokaci ba ta dawo hannunta riƙe da pleate ta zubawa Unaisa abinci kallon abinci Unaisa ta yi ta ji gaba ɗaya ya fita kanta amma bata cewa Mama komai ba waje Mama ta samu ta zauna,Unaisa kamar jira take Mama ta zauna nan ta gyara zama cikin kwantar da murya kanta ƙasa ta ce ''Mama daman ina son muyi wata magana ne" sosai Mama ke kallon Unaisa cike da ƙaguwa da son jin abinda Unaisa zata faɗa ta ce ''yi maganar ki ina jin ki'' shiru Unaisa ta yi na wasu ƴan sakanni tana tunanin ta inda zata fara can dai ta daure ta faɗawa Mama komai irin zaman da suke da Ɗalha bata ɓoyewa Mama komai ba,tun bayan rikicin mota da suka yi da Ɗalha ta faɗa wa Mama tun bayan wannan lokacin har izuwa yau zaman ta da Ɗalha babu dadi babu abinda bata faɗawa Mama ba a karshen zancen ta ce ''sai nake ganin na nemi saki tunda na fahimci baya sona baya kaunata baya son ganina ko kaɗan baya tausayina Mama'' ta kare magana cikin raunanniyar murya hawaye da take ta ƙokarin ɓoyewa tun ɗazu ya zuba daga idanunta hannu ta kai ta goge hawaye tana jan hanci,shiru Mama ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta sauki ajiyar zuciya tana shirin magana Anty Aisha ta shigo ɗakin bakinta dauke da sallama dawowarta kenan daga gidan barka,ganin Unaisa da Mama cikin wani yanayi yasa lokaci guda ta shiga damuwa ta samu waje ta zauna tare da mayar da dubanta ga Mama ta ce ''lafiya Mama me ke faruwa?" a hankali Mama ta mayar da dubanta ga Anty Aisha kamar baza ta yi magana ba sai kuma ta shiga bawa Anty Aisha labari kamar yadda Unaisa ta faɗa mata,tausayin Unaisa ne ya cika Anty Aisha can ta ce ''ki yi hakuri Unaisa amma saki ba ita ce mafita ba mutuwar aure musiba ce'' zuwa yanzu kuka kawai Unaisa ke yi sai dai marar sauti sai jan hanci take tana share hawaye lokaci guda idanunta sun yi ja sosai haka ma fuskarta
SHUUKRAN