NACINA YA JAWO MINI..

Chapter 21

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*








NACINA YA JAWO MINI...



021

Waro idanu tayi waje,idan ta kalli Umman Sa'eeda sai ta kalli Sa'eeda don tabbatar da abinda zuciyarta take rayawa game dasu,ai tuni Dr Nabila jikinta ya fara rawa tana kallon kowaccansu ,lokaci guda ta ɗauko wayarta,dailing numban mijinta tayi,shi kuma a lokacin yana gab da shiga jirgi,da mamaki ya kalli wayar,lafiya kuwa take kiransa yanzu duka-duka yaushe suka gama wayan,picking call ɗin yayi  da cewa


"Hello darling hope lafiya kike kirana at this moment"

Dr.Nabila da duk ta ruɗe ta ce mishi

"Abban Twins kazo asibitin nan yanzu don Allah"

Cikin mamaki yace

"Bangane nazo asibiti yanzu ba,bayan kinsan tafiya zanyi kuma mai muhimmanci..."

Katseshi tayi da cewa

"Ba tada muhimmanci yanzu Abban twins,na roƙeta kazo kaga abinda nagani da idona,wallahi ƙwalƙwalwata ta rikice bata bani haɗin kai,don Allah ka fasa tafiyan sai gobe ka tafi,plsssss"

"Ok yanzu wani asibiti kuke saina kira driver ya kawoni"

Sanar masa da sunan asibitin tayi tare da numban ɗakin,sai ya kira drivansa a waya,da mamaki drivansa yayi picking wayan don shi a tunaninsa mai gidansa ya daɗe a sararin samaniya,babu ɓata lokaci driver yazo ya ɗauki Abban twins a Airport zuwa asibitin.Bayan sun isa asibitin,sai ya fito tare da nufar female ward na asibitin, direct numban ɗakin da Dr. Nabila ta sanar masa can ya nufa.


Shiga ɗakin yayi da sallama,cak! ya tsaya yana kallon Sa'eeda wacca take facing ƙofar ɗakin,kallon ƙurilla yake ma Sa'eeda babu ko ƙyafta ido,itama kallonsa take cike da mamaki ganin mai kama sak da Ummanta,haske ne kawai bambamcinsu,suna a wannan yanayin ne sukaji tari mai ƙarfi,da sauri kowa yakai duban wurin gadon,Umman Sa'eeda ce ta farka haɗi da tari saboda ƙirjinta zafi yake mata tare da azababban ciwon kai,da sauri kowa ya nufa gadon haɗi dayi mata sannu,Abban twins ne yakai dubansa ga Umman Sa'eeda, lokaci guda ƙirjinsa ya bada Darrammmm!!! Ganin kamarsu ta ɓaci,tabbas wannan ce Hussainarshi,tabbas ita ce Hussainarshi,cikin murya mai sanyi haɗi da tsoro Abban Twins ya kira Umman Sa'eeda

"Hussaina"

Umman Sa'eeda dake cikin tsananin ciwo ta waiwaya daƙyar inda aka kira sunanta,zaro idanu tayi waje ganin mai kama da ita sak! Hannu na rawa Umman Sa'eeda take nuna Abban Twins tana cewa


"Hhassann Hassannn kaine ba'a mafarki ba,kaine! Kaine,ku cemin ba mafarki nake ba,Hassan ɗina ne ya dawo gareni,mama kullun cikin cewa take zamu haɗu,zamu haɗuuuu.......?

Fashewa Umman Sa'eeda tayi da matsananci kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai sauraronta,da Sauri Abban Twins ya iso gunta tare da riƙo hannunta wanda ba'asa canular ba,shima kukan ya fara ganin ƴar uwar wacca yake mutuwar so da ƙauna,babu ranar da zatazo mishi ta wuce ba tare da yayi tunanin ƴar uwarsa da mamansa ba,kullum tunani yake a wani hali suke? Wani irin rayuwa sukeyi?  A ina suke? Me suke ci? Me suke sha? Wani irin muhalli suke a ciki,me,me tambayoyi bila adadin yake ma kansa a kullum. Saboda zuciyar ta kasa yarda sun mutu,kullum zuciyarsa ce masa take suna nan lokacin huɗuwarsu ne baiyi ba.Cikin kuka Abban Twins ya fara magana wanda ba kowa ke jin abinda yake faɗa ba

" Mmmama fa,tana ina itaaa"

Wani sabon kuka Umman Sa'eeda ta fashe dashi tuno da Mamanta tare da wahalhalun da suka sha a baya,girgiza kai Umman Sa'eeda take tana kuka,ga raɗaɗin ciwo da duk ilahirin jikin yake gashi yanzu an tuno mata da rayuwarsu ta baya.Babu wanda a cikin ɗakin bai zubda hawaye ba saboda yadda suke kuka zai tabbatar maka sunyi kewar juna domin jini ba wata bane,tun daga kan Dr. Nabila,Iman tare da uwar gayya Sa'eeda kuka suke sosai saboda tausayin da ya shigesu,baka jin  maganar kowa a cikinsu saidai shassheƙa haɗi da jan majina.

Suna a wannan yanayin ne saiga Likita ya shigo ɗakin tare da nurse,turus yayi a tsakiyar ɗakin ganin yadda kowa yake zubda ƙwalla shi a tunaninshi ko patient ɗinsa ne ta rasu,amma daya ƙara kallon gadon mara lafiyar sai ya ga itama kukan take sosai,fuskar likitan ne ta sauya,cikin ɓacin rai ya fara magana

"Haba don Allah, wani irin abu ne haka,ku da zaku kwantar mata hankali amma ku kuke ƙara saka kuka da  damuwa,please kuje waje ku zauna tana buƙatar hutu yanzu sannan inaso na ƙara dubata"

Babu musu kowa ya fita har Abban Twins wanda ji yake idan ya fita wani abu zai iya samun ƴar uwarsa,a kujerun dake a receptionist suka zauna,cikin ɗumbin farin ciki Dr. Nabila ta fara kiran ƴan uwansu da abokan arziƙi kama daga wa'inda suke a Kebbi,Kano,Abuja,har wa'inda suke a ƙasashan waje duk ta kira ta sanar musu da ganin su Umman Sa'eeda da tayi.koda aka sanar ma Momin Sadam akan bayyanarsu Umman Sa'eeda ai a rikice tare da ɗumbin farin ciki  tace gata nan zuwa yau ɗin nan ba sai gobe ba.

Kiran daddyn Sadam tayi a waya tana sanar mishi da anga su Hussaina amma tana asibiti dasu Hassan da matarsa,shima farin ciki yayi sosai,kasancewar baya ƙasar da dashi za'a je amma yana dawowa zuwa jibi zai shigo Kadunan,kamar yadda Dr. Nabila taiyi ta sanar ma ƴan uwansu bayyanarsu Umman Sa'eeda haka itama Momin Sadam tayi harda abokan arziƙi,hatta yaranta duk suma ta sanar musu.Koda Dr. Nabila ta sanar ma mahaifinta kuka ya fashe dashi,yana cewa akaishi kun ƴar uwarsa,shidai akaishi gun ƴar uwarsa,haƙuri akaita bashi akan ita ƴar uwar tashi ta rasu,ɗiyarta ce Hussaina da ƴarta aka gansu,duk da haka hankalinsa yaƙi kwanciya wai shi ko yaranta ne sai an kaishi ya gansu,kunsan tsofaffi da kafiya,da ƙyar aka shawo kansa da dubara akan gobe za'a kawoshi wurinsu,da wannan bayanin tsoho mai ran ƙarfi hankalinsa ya kwanta.

Kasancewar da safe lamarin ya afku,Momin Sa'eeda sai wurin 5:18pm na yamma ta iso Kaduna tare da motoci har Uku masu kare lafiyarta,direct asibitin suka nufa da jiniya,koda suka iso asibitin, Momin Sadam bata jira an buɗe mata ƙofa ba,ta fito da kanta tana sauri haɗi ta sassarfa ta wuce female ward har ɗakin da aka kwantar dasu Umman Sa'eeda tare da bodygaurd har uku,a ƙofar ɗakin bodygaurd ɗin suka tsaya ita kuma ta shiga ciki da sallama,amsa mata sallamar ƴan ɗakin sukayi,cike da murna Dr. Nabila ta rungume favourite Auntynta,itama Momin Sadam ƙara rugumeta tayi sosai,sai a sannan ne Momin Sadam da hangi Sa'eeda wacca take a raƙube kusa da Ummanta a kan gado,sakin Dr. Nabila tayi tana nuna Sa'eeda tare da cewa

"Amma daga gani ko ba'a faɗa ba wannan ce ƴar Hussaina ko"

Murmushi Dr.Nabila tayi tana cewa

"Tabbas kuwa,sunanta Sa'eeda "

"Maa shaa Allah, tabarakallah,zo nan my gorgeous daughter "

Sauka Sa'eeda tayi daga kan gadon ta tako har inda Momin Sadam take tana ɗan murmushi,russunawa tayi zata gaisheta,Momin Sadam tayi saurin riƙota haɗi da rungumeta tsamm! A jikinta,ɗagota tayi tana cewa

"Maa shaa Allah, wannan kama haka,ai sai nace ɗiyar Hassan ce"

Dariya Dr. Nabila tayi sannan tace

"Bake kaɗai ba Aunty wallahi farkon ganin da nama Sa'eeda saida gabana yayi mugun faɗuwa,saboda tsantsar kamar da suke da Abban Twins, kasa haƙuri nayi na tambayi sunanta da garin da mahaifinta yake,da ta cemin ita ƴar Kaduna ce,sai kawai na basar,kinsan kusan kullum saina ma Abban Twins maganar Sa'eeda, dayake Allah bai ƙaddara a lokacin zance ta kaini wurin mahaifiyarta ba,sai yanzu da Allah ya nufa da haɗuwa mu ta hanyar accident"

"Ikon Allah kenan,ita Hussaina bacci take kenan"

"Eh wallahi, Abban Twins ma bai daɗe da fita ba saig....."

"Assalamu Alaikum"

Juyawa sukayi dukkaninsu tare da amsa mashi sallama, Momin Sadam ce da murmushi take cewa

"Ɗan halak kaƙi ambato,yanzu muke maganarka sai kuma gaka"

Murmushi Abban Twins yayi duk da ransa a ɓace yake tun sanda shida Sa'eeda sukaje gidansu Sa'eeda da niyyar sanarma Abbansu Sa'eeda halin da Umman Sa'eeda take a ciki wanda saida suka kusa yin faɗa da Abban Sa'eeda kasancewar ba'a hayyacinsa yake ba


*WAIWAYE*


-------lokacin da likita ya ce masu Sa'eeda su fito domin Umman Sa'eeda ta samu hutu,Abban Twins ne ya cema Sa'eeda tazo suje gidansu su ɗauko kayayyankin da Umman Sa'eeda zata buƙata sannan sai su sanar ma mahaifinta rashin lafiyar Ummanta,babu musu ta bishi suka tafi,ita ce a gaban mota tare da driver,shi kuma yana mazaunin baya,nunama driver hanya take har suka iso  ƙofar gidansu,bayan sun sauka daga motan,Abban Twins sai dube-dube yake yana ƙarema gidan kallo,a zuciyarsa yana cewa 'Yanzu haka Hussaina kike rayuwa a wannan kurkukun gidan,ya Salam!!! Farin cikinki yazo Hussaina keda ƴarki da izinin Allah, farin cikin da kika gaza samu tun kina yarinya,shi yanzu zaki samu,zan samar muku da farin ciki dawwamamme in shaa Allah, lokaci yayi na ɗaukar fansa!!! Tabbas lokacin bayyanarmu ga dangin mahaifinmu tare da ƙwatar hakƙinmu yazo!!! ' Yana wannan tunanin ne Sa'eeda ta katse mishi tunani da cewa

"Uncle gáma Abbana can ma a majalisarsu basai an kira shi ba"

Hannunta take nuna inda Abbanta yake zauna a majalisar layin kasancewar yau baije kasuwa ba,inda hannunta yake nunawa nan Uncle Hassan yakai dubansa ga mutanan wurin,ce mata yayi tazo suje ta nuna mai Abban nata ,babu musu ta bisa har majalisar inda su Abban Sa'eeda suke zaune,sallama yayi musu haɗi da yima kowannansu musabiha sannan ya ƙara da cewa

"Don Allah Abban Sa'eeda nake nema"

Abban Sa'eeda da tunda ya hango Sa'eeda annurin fuskarsa ta ɗauke gabaki ɗaya ya fara mishi magana da faɗa wanda har ƴan majalisar saida sukayi mamaki wasu harda riƙe baki

"Ba Abban Sa'eeda ba saidai uban Abban Sa'eeda!!!  Ni banda wata ɗiya Sa'eeda saidai daga,Musa,Nusaiba,Zaliha da Iklima amma bansan wata Sa'eeda ba"

Wani a ƴan majalisar ya kasa haƙuri ya ce

"Haba Sule yanzu ƴartaka Sa'eeda kake cewa baka santa ba,wai ina hankalinta yaje ne Sule,mai ya shiga ƙwaƙwalwarka ne,haba! "

Shima wani daga cikin ƴan majalisar ya ƙara da cewa

"A gaskiya wannan halin da kake nunawa ƴarka tare da mahaifiyarta ba daidai bane wallahi, yanzu kalla fa kuka take "

Nuna Sa'eeda yayi wacca tun sanda Abbanta ya ce ita ba ƴarshi bace ta fara kuka, cigaba da maganar yayi

"Yanzu kaji ɗadi da tozarta ƴarka ta cikinka da kayi a gaban kowa tare da baƙonka wanda bakasan mai yazo wurinka dashi ba Sule,yanzu kayi abinda ya dace kenan Sule"

Ƴan majalisar ne sukai mishi caaaa!!! Akan abinda ya faɗa ba daidai bane,shi kuma Uncle Hassan ido ya zubama Abban Sa'eeda ko magana ya kasa jin wannan irin tozarci haɗi da ɓatanci daya jefi ƴarsa dashi,hakan ya nuna Hussaina ba jin daɗin zaman auran take ba ita da ƴarta,shi kuma Abban Sa'eeda ko a jikinshi,duk maganar da zasuyi saidai ya taɓe baki irin Oho dai ku kuka sani.Cikin murya mai nuna ɓacin rai da damuwa Uncle Hassan ya fara magana wanda kowa a wurin saida yayi mamaki banda Abban Sa'eeda kasancewar baya cikin hayyacinsa,cewa yayi

"Naji abinda ka ce,sannan daga yau Hussaina da Sa'eeda sumbar gidanka da zama,bancin ƙaddarar da  tasame mu,wallah da baka isa ka tsaya  ɗaya daga cikin jerin da Hussaina ya cancanta ta aura ba,domin tun daga kallon kurkukun gidanka na tabbata ba mutumin arziƙi bane,kuma ilai sai gashi ko faɗa maka abinda yake tafe dani baka tsaya kaji ba,ka fara nuna min halin ɗan akuya! Well daman nazo sanar maka da Hussaina tayi accident wanda kuma shi ne mafarin haduwanta da asalin ahalinta wato ƴan uwanta da ni ɗin nan "

Nuna kansa yayi sannan ya ƙara da cewa

"Ni ne Hassan ɗinta,yanzu banda ta cewa saboda Hussainata tana asibiti, amma kasani duk randa ta ce ta gaji da zaman aure dakai to ka tabbata rabuwarku tazo kenan,yanzu ma kaci darajar Hussainata ne da kuma ƴarka wacca ka tozarta if not da nasa a ɗaureka a gidan kaso ɗaurin rai da rai,amma ka kula nan gaba domin ba'a shiga gobar Hassan Sani Mai Gado a zauna lafiya koma uban waye"

Taɓe baki Abban Sa'eeda yayi tare da cewa

"Oho dai,can ta matse muku a matse-matsin hammata,ku tafi can ku ƙarata,shikenan na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda,Mtwss! Aikin bazan! "

Uncle Hassan bai sake bi takan zantuttukan Abban Sa'eeda ba yaja hannun Sa'eeda suka tafi wacca har a lokacin  kuka takeyi sosai gwanin ban tausayi,cikin ɓacin rai ya ce ta shiga ciki ta ɗauko duka credentials ɗinta dana Ummanta banda kayansu ta fito yana jiranta,haka Sa'eeda ta shiga gidan da sallama amma shiru alamun ba kowa duk da koda akwai mutane ba amsa mata sallamar za'ayi ba koda yake yanzu idan Jummalo ko Iklima suna waje sukan amsa musa sallama ita da Ummanta, kasancewar akwai extra key a hannunta dashi ta buɗe ɗakin haɗi ta fito da duk abinsu mai amfani banda kaya,ɗan akwati ƙarami ta fito dashi waje,tana niyyar kulle ɗakin saigasu Umma Kande da Maman Jummalo amma ita Maman Jummalo akwai niƙaf a fuskarta kasancewar yanzu da niƙaf take yawo,tsayawa sukayi baki buɗe suna kallon Sa'eeda, murmushi ta musu tare da cewa

"To Umma Kande da Maman Jummalo a yayyafe,domin yau zamu bar muku gidanku nida Ummanta, wanda kuka gani a waje shi ne Uncle Hassan wato abokin haihuwar Ummina nazo tare dashi ne domin ɗaukan muhimman abubuwanmu,wata ƙila bazamu sake haɗuwa ba sai a *DARRUS-SALAM* mu yafi juna,nasan Ummana ta daɗe da yafe muku......."

Bata ƙarasa maganar ba taji horn ɗin mota alamun ana jiranta,da sauri ta ɗau ɗan akwatinsu tare da yi musu sallama sai wataran tana murmushi ta fita,na mujiya kowaccansu ta bita dashi tare da taɓe baki irin ko ajikinsu ɗin nan.Umma Kande ta ce

"A tafi can a ƙarata,mundai yada ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda,yanzu zamu baje mu ɓararraje abinmu"

Maman Jummalo dai bata ce komai ba,ta wuce ɗakinta tare da buɗewa ta shiga ciki,ita kuma uwar gayyar saida ta ƙara fita waje don ganin ƙwaƙwaf saboda tun ɓullowarsu layin motar take walƙiya a tunaninsu ko ƴaƴan ne wata tayi sabon kamu.(Su Umma Kande badai gulma da ganin ƙwaƙwaf,to tafaru ta ƙare,sai abi wani sarkin domin Su Sa'eeda sun muku nisa😂😂😂🙃🙃🙃)

Koda Sa'eeda ta fito,samun Uncle ɗinta tayi a cikin mota,wannan karon a baya ta zauna,driver yaja musu motan,umarni Uncle Hassan ya bada akan su wuce supermarket zasuyi siyayya,cikin ladabi ya amsama mai gidan nasa duk da yaga alamu kamar amɓata masa rai,direct suka nufi wani haɗadɗan supermarket na gani na faɗa,cema Sa'eeda yayi tafito,babu musu ta fita tare da bin bayansa suka nufi cikin supermarket ɗin.Wooow!!! Kawai zan iya cewa domin babu abinda zaka gaza samu a wannan ƙayataccan supermarket wanda sai wa'inda sukaci suka tadá sannan suke zuwa shopping a cikinsa,suna shiga Uncle Hassan ya cema Sa'eeda ta zaɓa musu duk abinda suke bukatar tun daga kan kayan wasa,cosmetics,da dai sauransu,haka ta fara ɗiban musu kayan kaɗan-kaɗan,Uncle Hassan daya ga Sa'eeda shirme takeyi kawai ya fara jidar kaya kamar za'a buɗe wani sabon shago,haka suka gama shopping,su kuma ma'aikanta supermarket ɗin suna biye dasu niƙi-niƙi da kayan har wurin biyan kuɗi,direct ya ciro ATM card ɗin ya bada bayan an sanar masa maƙudan kuɗin da kayan sukaci amma ko ajikinsa hasalima ce musu yayi suyi sauri suna ɓata mishi lokaci,daskarewa Sa'eeda tayi tun sanda aka faɗi maƙudan kuɗin kayan,ita a tunanin zaice a rage kayan sunyi kuɗi dayawa amma ko ajikinsa haka ya cire ATM card ɗinsa ya biya.Fitowa sukayi daga supermarket ɗin tare da ma'aikanta wa'inda suka fito musu da kayan zuwa boot ɗin motar,driver ne ya taimaka suka saka kayan complete sannan yaja musu motar,nan ma ƙara tambayar mai gidansa yayi cike da girmamawa akan ina suka dosa,ce masa yayi plazan da Dr. Nabila take kai ɗinkunanta zai kaisu,haka ya jasu zuwa plazan,nan ma basu ɓata lokaci ba aka gwada Sa'eeda tare da bata kayan da suka siya daga supermarket domim a ɗinka masu , kasancewar Umman Sa'eeda baza'a iya gwadata ba,saidai estimation Sa'eeda tama telan da zai musu ɗinkin,nan ma Uncle Hassan tranfer ɗin maƙudan kuɗin da za'a musu ɗinki ita da Ummanta yayi,sai suka wuce direct zuwa asibiti. Wannan kenan----




*Cikin labari*


Zama ya samu yayi tare dayiwa Momin Sadam sannu da zuwa,sai ya ce

"Nifa ina tunanin zansa ayi ma Hussaina Visa sai mu wuce da ita can Germany a dubata don gaskiya bana tunanin likitocin nan sun ƙware sosai "

"Wannan tunani ne mai kyau,amma mai zai hana ayi mata Visar India kaga sai mu tafi tare wurin likitan da yake dubani nida Alhaji kaga yafi sauƙi tunda kai  course zai kaika Germany ba jinya ba,koya kace" cewar Momin Sadam tana murmushi

"Haba ai duk ɗaya ne,bara na kira can immagration office insa ayi mata International passport ,sai ku wuce jibi amma inso samu ne gobe saisu ku wucd,don ƙila  gobe zan wuce Germany dama ƙaddarar haɗuwa da ƴar uwata ce tasa na jin kirta tafiyar"

"Ok,bara na sanar ma Daddyn Sadam yasan da tafiya tamu kaga sai shima yázo can ɗin dama ya ce immediately yana dawowa zaizo nan"

"Ok toh ba matsala ai"

Shiru ɗakin yayi kowa na zancen zuci,can Dr. Nabila ta katse shirun da cewa

"Kai! Shida ta kusa bara na kira larai taje ita da driver su ɗaukosu Afnan daga school"

"Iyayan rigima ba,tana nan dai da halinta da ƙin mutane ko"

"A'a Aunty ai duk wannan rashin son mutanan duk ta daina yanzu"

"Hmmm Allah yasa dai"

Dariya sukayi sai sannan Dr. Nabila ta tambayi Sa'eeda ina Friend ɗinta take,sanar mata tayi ai tun sanda zasu je ita da Uncle Hassan gidansu tayi mata sallama.

Haka suka zauna har kusan 8:00pm wanda sallah ce take tashinsu suyi shi kuma Uncle Hassan sai ya tafi masallaci.Sai wurin 9:12pm na dare Dr. Nabila da Sa'eeda haɗi da Uncle Hassan da yaransu suka wuce gida tare da barin Momin Sadam a asibiti bayan mai aikinsu Dr. Nabila ta aiko musu abinci tare da yaran.

A ranar Uncle Hassan ya sanar ma abokinsa wanda babba ne a offishin Immigration akan maganar International passport tare da yi musu Visa zuwa India,abunka da kuɗi nan da nan Visa ta fito washe gari,haka sukayi ta shirye-shiryan tafiya zuwa India, kasancewar Sa'eeda har yanzu basuyi hutu ba yasa bada ita za'a tafi ba sai bayan exams zasu wuce Kebbi ita da Dr. Nabila domin za'a shiryama su Umman Sa'eeda ƙyataccan liyafar murnar dawowansu cikin ahalinsu.

Washe gari Jirginsu Umman Sa'eeda tare da Momin Sadam ya lula sararin samaniya zuwa ƙasar India,sai daga baya jirginsu Uncle Hassan wato Abban Twins ya ɗaga zuwa Germany.Wannan kenan.


            @@@@ @@@@@@@@@


A ɓangaren  *LOVE BIRDS*  🕊️🕊️ wato Sauban da Maryam kuwa abubuwa ƙara rincaɓe musu yayi,domin ranar da Maryam ta dawo gidan ranar wannan lamarin ya afku,kasancewar Maryam ta suma sanda Sauban ya kaita asibiti, sanda kuma ta farfaɗo shi kuma lokacin yaje ɗauko musu kayan da zasu buƙata a asibitin, da ihu haɗi da kururuwa ta farka tana cewa

"Wallahi baka isa ba Sauban!!! Bazan zauna da kishiya ba Sauban!!! Ni kaɗai ce matarka ta duniya da lahira Sauban!!! Babu wata macan da ta isa ta raɓeka Saubannn!!! "

Da ƙarfi take maganar tare da fizge canular da aka saka mata a hannu,jini na zuba amma bata bi takan jinin ba tayo hanyar waje,wata nurse tazo wucewa ta ƙofar taji wannan surutan da sauri ta kirawo wasu nurses ɗin don su duba kodai mahaukaciya ce aka kawo musu, da sauri suka shiga cikin ɗakin,koda suka shiga ita kuma Maryam tanada niyyar fita sai suka kusa cin karo da wata nurse,jiki da rawa idanu sunyi ja sosai Maryam ta cema wata nurse wacca take suka da ita

"Ɗan aramin wayarki don Allah nayi kira yanzu zan baki"

A tsora ce nurse ɗin ta miƙa ma Maryam wayar,domin duk wanda yaga Maryam a wannan yanayin dole ya tsorata saboda zakayi tunanin mahaukaciya ce,ganin gashinta duk a birkice yake,ga idanunta duk sunyi ja,kayan jikinta a yage suke saboda damban da sukaci da Sauban.Amsar wayan tayi haɗi da saka numban wayar mominta ta kira,wayar na ringing amma ba'a ɗauka ba,saida ta kira kusan sau hudu kana a akayi picking,sallama acan aka mata,bata amsamata sallama bata fashe da kuka,su dai nurses ɗin suna kallon ikon Allah

"Mom! Mom! Mom Sauban ya cuceni! Kishiya zaimin Mom!  ƴar uwarsa zai aura Mom!,har dukana yayi daga dawowana yanzu ma ankwantar dani a asibiti Mom"

Cikin tashin hankali Momin Maryam ta tambayi wani asibiti ne aka kwantar da ita,saida  Maryam ta tambayi sunan asibitin haɗi da numban ɗakin sannan ta sanar mata,cike da ɓacin rai Momin Maryam ta kashe wayar tare da nemo numban Hajiya Laraba wato babbar yayarsu tare da sanar mata abinda ya faru da Maryam harda dukan da Sauban yama Maryam ɗin,ita ma rai ɓace ta ce ina ne asibitin da aka kwantar da ita,sanar mata tayi sanna ta katse kiran haɗi da miƙewa ta nufi bedroom ɗinta don shiryawa,tana cikin shiri saiga Daddyn Maryam ya shigo gidan da sallama, amsa masa tayi,bata bari ya zauna ba ta sanar masa da abinda ke faruwa da Maryam shima hankalinsa ya tashi matuƙa ainun jin tilon  ƴarsa na a asibitin saboda duka,to ma wani irin duka ne Sauban ya mata da har saida aka haɗa da asibiti.Ce mata yayi ta shirya su wuce asibitin dashi don zama baigansa ba.haka suka ɗunguma zuwa asibitin.

A ɓangaren Hajiya Laraba kiran Mahaifiyar Sauban tayi tare da zazzaga mata masifa akan dukan da ɗanta yayima Maryam, kasancewar Momin Sauban itama ba kwanwar lasa bacd,hayayyaƙo mata tayi itama da masifa,faɗan kaci uwaka kaci ubanka Hajiya Laraba da Momin Sauban sukayi,katse kiran Momin Sauban tayi tare da saurin nemo namban Sauban,bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga kiran,cikin  girmamawa Sauban ya fara gaisheta,bata amsa masa ba sai jefo masa tambayar bazata da tayi,tana cewa

"Me Maryam tayi ka duketa  harda zuwa asibiti Sauban"

Bai ɓoye mata komai akan abinda ya faru,tun daga dawowarta,da fashe-fashan da tayi da haukan da tayi masa,bai cire komai ba ya sanar mata.Shiru tayi sai can ta tambayi yanzu yana ina,ce mata yayi yana gida yazo ɗaukan kayan da zasu buƙata,a nan ta ce masa karya kuskura ƙafarsa ta taka zuwa asibiti domin idan yaje akwai matsala babba,cikin mamaki Sauban ya tambayi Momin akan wace irin matsala ce haka,faɗa masa tayi faɗan da sukayi da Hajiya Laraba wato Auntyn Maryam sannan tasan definitely iyayenta zasuzo asibitin yanzu tare da ita kanta Hajiya Larabar,don haka kawai yabar zuwa asibitin yanzu ya bari sai gobe idan ta dawo daga Zaria sai suje tare,amsa mata yayi da to sannan sukayi sallama,kwanciyarsa yayi a bedroom ɗinsa tare buɗe shafukan tunaninsa wanda shi kansa baisan wanne ya dace ya fara ɗauka ba,a gaskiya kwanan nan baya samun natsuwa tare da kwanciyar hankali,gashi komai nasa taɓarɓarewa yake anya Maryam bata shigo gidanshi da *farar ƙafa* ba kuwa,domin har a wurin aikinsa sai a hankali yanzu,yadda yake samun kuɗi ada yanzu baya samu sosai.Haka dai Sauban yayita tunaninsa daya gama wannan tunanin sai ya koma kan wancan har bacci ɓarawo ya sacesa.

A ɓangarensu Maryam da iyayenta kamar Momin Sauban ta sani,jiran Sauban  suke don su tugumesa akan irin wannan dukan dayama Maryam, shiru-shiru babu Sauban babu alamunsa,haka suka gaji suka wuce gida bayan ambar Hajiya Laraba da jinyar Maryam.

Washe gari saiga Momin Sauban ta dayo gidan da safe kasancewar duk hankalinta ya dawo gida domin taga abinda ke faruwa.Ko zama batayi ba suka shirya ita da Sauban suka nufi asibitin,a can suka iske iyayen Maryam ɗin sunzo suma duba ta *Wuta iya Wuta* domin wani sabon yaƙin duniya🌍🌍🌍 na huɗu ya kaure a asibitin, faɗa iya faɗa anyi harda ƙannan Sauban tare da yayyinsa saida sukazo domin Momin Sauban kiran kowannansu tayi a waya tare da sanar musu abinda ke faruwa,babu ɓata lokaci dukkaninsu suka hallara a asibitin, danginsu Maryam  ma suma sunzo,asibitin kacamewa yayi da hayaniya sosai wanda a ƙarshe ma'aikatan asibitin suka koresu waje tare da sallamar Maryam ɗin,a nan Daddyn Maryam ya ce sai Sauban ys saki Maryam don bazata zauna da kishiya ba,amma buɗar bakin Momin Sauban ta ce ai shida Maryam mutu ka raba takalmin kaza ko bayan ranta babu shi babu sakin Maryam badai sunce danginsu basa zama da kishiya ba to akan Maryam zasu ɗau darasin zama da kishiya ko sunƙi ko sunso,kuma a shirye suke koda ƙuliya manta sabo ne suka kaisu  babu gudu babu ja da baya.Haka iyayen Maryam suka wuce da Maryam gidansu.

Ita kuma Momin Sauban ta sanar ma ƙanwarta akan ta faɗama mijinta a saka ranar Sauban da khairat nan kusa ta fasa sai khairat ɗin ta dawo ƙasar,domin sai ta tabbatar ma Hajiya Labara da duk ilahirin danginsu ita ba kanwar lasa bace,ita buhun ƙaya ce tafi ƙarfin danna,sannan duk wanda taci tuwo da ita ya tabbata miya yasha domin wasan yanzu za'a fara.

Kamar yadda Momin Sauban ta umurta a saka ranar Sauban da Khairat nan kusa haka mahaifin Khairat yayi kasancewar shi dama tuntuni yaso ayi auran a huta amma akace sai khairat ɗin ta dawo.Wannan kenan.


         @@@@@@@@@@@@


A ɓangaren su Umma Kande da Maman Jummalo duniya ta fara musu juyin waina,musamman Maman Jummalo domin yanzu ta rame tayi baƙi sosai,kullum cikin ciwo take,ga shegen kwaɗayi da takeyi yanzu,tun sanda cikinta ya fara girma ta daina yawo  babu niƙaf,kullum cikin saka niƙaf take kamar wata matar liman idan zata fita.


Yauma zaune suke a ƙofar ɗakinsu Sa'eeda kasancewar tunda Sa'eeda tayi musu sallama ƙofar ɗakinsu ya koma wurin shan iskarsu,Umma Kande ce  ta kasa haƙuri ganin yadda ƙawarta ta koma gwanin ban tausayi,cikin sanyin murya Umma Kande ta fara magana


"Ƙawas anya ba komawa wurin boka Sankeru zamuyi ba,ko za'a samu wata mafitar gane da cikin nan? "


Maman Jummalo ce ta mata wani mugun kallo  tare da cewa.............