NUFIN ALLAH

29

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Under team yota's amazing pen

Page 2️⃣9️⃣

Kan gadon ta faɗa suna shiga, ji take yi zuciyar ta na mata wani irin nauyi, ita tasan ba tunanin da zata yi, ba ma sai an kai da nisa ba dan harga allah bata jin son shi ko kaɗan 

Nabila kam dan tsabar murna sai adduo'i take yi da zubawa Allah kirari

Zama tayi kusa da Anisa akan gadon, ɗan dukan cinyarta tayi tace 
"mrs.faruq am suppose to see you happy naga kin wani koma gefe kodai duk tsabar shock din bakiyi expecting news din bane"

Banza ta mata takasa cewa komai, Jalila ce ta matso wajen ta tado ta zaune tace

"Pixie meya faru kodai ba kya son ya Faruq dinne"

Kallonta tayi a zuciyar ta tana mamakin wai ma tambayar ta take bata son shi hmmm

"Kema dai kin san baso nake ba, ya Umar fah, wallahi dan Abba ya mun nauyin ince mai a'a ne shi yasa"

Tayi maganar sai yanzu hawaye suka fara zubo mata, ta kwantar da kanta a kafaɗar jallila tana kuka 

Taya za ace wai ya Faruq itafa gani take kamar ba gaske ba ake kokarin wannan abun 

Nabila ce ta matso kusa da ƴaruwar tata tana lallaɓar ta ɗan duk a tunaninsu tana son shi, Dan ko ɗazu ma da suke mai da zancen jiya suna tunanin ko son junansu suke Amman ashe ba haka bane

Fareedah ma da da tayi getting hopes ɗinta up na auren Anisa da Faruq din sai taji duk ranta ba daɗi itama matsowa tayi kusa da ita tana lallashin ta

"Wai ya Umar fah, ke kin san yanda nike ganin shi kuwa kamar dodo wallahi, ba ga Amra ba daman ai ita tana son shi, nifa ya Faruq baya cikin kallan mazan da nike so gwara ya aura wadda take..."

Bata ƙarasa maganar tata ba fareedah ta matsa daga kusa da ita tana faɗin 

"Ya isa fah Anisa wannan ai cin fuska ne, anji bakya son shi Kuma kin faɗa ai ya wadatar basai kin kai ga ai bata shi a gabana ba kina cimun fuska" tana gama maganar tayi waje abunta dan ranta ya ɓaci sosai 

Tasan bata son shi Amman ai bata ringa wannan maganganun a gabanta ba tunda tasan waye shi a gurin ta

"Kin wuce limit sister baki kyauta ba tunda kin san yayanta ne be dace ki faɗa haka a gabanta ba" fadin Nabila 

"To ni mena ce da ba daidai ba, ai nima naga yaya na ne"

"Amman kema kin San ko yayan ki ne fah ita uwa daya uba ɗaya ba daɗi sister ace yanzu ne fah pookie...". 

"Karma ki fara sweet din nabilan zan ce haka akan shi" nabila ta katse Jalila tun kafin ta ƙarasa tana juya ido 

"Wallahi pookie Allah ya kyauta miki"
 
"Ameen, Amman sister ki bata hakuri dan ba daɗi"

"Toh" kawai ta ce ta juya musu baya tana gyara kwanciya a kan gadon ranta duk a jagule 

Fareedah ce ta dawo cikin ɗakin fuskarta kadaran kada han ta zauna kan 2 siter guda ɗaya dake ɗakin tana danna wayar ta bata tanka kowa cikin su ba

"Tofah ba mu muka kar zomon ba ratayar ma bata bamu ba ita ke rataya kayarta da zaki wani haɗe mana rai kina wani basar da mu"
 Faɗin Jalila 

"Barta ratayar ma an bamu ta yi kuguguwa ta fashe, tunda ai mu ba yayan mu bane iya ita kaɗaice me yayan" nabila ta faɗa tana hararar ta

"Kedai kika sani ai abun ne da kayan haushi ƴar rainin wayon can" 

ta faɗa tana hararar ƙeyar Anisa da ta juya musu baya kamar bacci ne ya ɗauke ta

Tana jin su Amman tayi musu shiru dan abinda ke ranta yafi surutan su

Jin kiran sallahn isha ne yasa ta mikewa taje tayi alwala tazo tayi sallah 

Kasa mikewa tayi daga kan dadduman saboda yanda ta ke jin jikinta a sanyaye duk ya mutu kawai sai ta kwanta a gurin tana maida numfashi a hankali 

"Pixie kidawo kan gadon ki kwanta" fadin nabila da itama ta idar da sallan ta matsa wa Jalila tayi
"To ina zuwa"

Bata ƙara cewa da ita komai ba dan tasan ita ƙadai tasan halin da zuciyarta ke ciki



______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺