BAYA TA HAIHU

16

by @rabiattu0444

*BAYA TA HAIHU*
16
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72

Ummu Maher (Mrs green)🍀


*AREWA WRITTER'S ASSOCIATION*


*🗣️Kar ki wuce ba tare da kin karanta ba Please👏🏻 domin na tabbatar da kuma watarana za ki zama kamar Ummufadeel da ga shirye sai ki fara siyarwa👏🏻🗣️💃🏼*

*_UMMUFADEEL!_*
_*UMMUFADEEL!!*_
 FOODMART🍊🍋🍎🍏🥦🥬🥑🥝🥥🍇🍓🍒🍌🥔
*UMMUFADEEL*
*Ƴar Jos💃🏼*
*UMMUFADEEL*
_Gidan sauƙi_
*Ummu fadeel me gidan gonar kayan marmari kowanne iri, da nau'ikan kayan tsirrai ko wanne iri, tana bayarwa akan sari*

*_SHIGA GROUP DOMIN GANIN KOMI DA IDONKA_*
***

*1_Citta ɗanya🫚 buhu ko bucket*
*2_Kaninfari kwano ko buhu*
*3_Cinnamon*
*4_Kimba*
*5_Masoro*
*6_Rosemerry*
*7_Tafarnuwa*
*8_Amla*
*9_Habbatussauda*
*10_Man kwakwa*
*11_Zaituun*
 Da dukkan nau'ikan kayan ƙamshi na gida da na waje, dukkaninsu za ku same su cikin sauƙi da kuma rahusa gami da aminci, trust and thrusted.
_______________
*_Kar ku ga Ummu Maher ta fiye faɗin sunan, ku tambaye ni menene? Tabbas Ummufadeel ta shahara a fannin kawo muku kayan tsirrai, da kayan lambu, nau'in su Fruits, vegetables, ko wani nau'in kayan fruit da na lambu tana kawowa, kamar su;_*
*Strawberry🍓*
*Roseberry🍒*
*Inibi🍇*
*Ayaba🍌*
*Fiya🥑*
*Kwasha kwasha🥝🥝*
*Apple 🍎🍏*
*Mango🥭*
*Plum*🍑
*Cocumber🥒*
*Latas🥬*
*Cornflower*
*Doya🥔*
*Dankalin turawa*
*Dukkaninsu tana siyarwa a raha da kuma rahusa, ku dai ku hanzarta ku neme ta akan lambarta kamar haka ****
*_Idan na ce zan jero muku za mu daɗe ba tare da na gama ba, sannan tana siyar da na'uikan tsirrai kusan rabi da kwatansu tana siyarwa cikin aminci da kuma rahusa, tana siyar da danƙwala-danƙwalan doya, dankalin turawa, dankalin Hausa, makani._*



_MERO_


Na zaro idanuna waje ina kallonsa cike da mamaki, a karo na biyu n ce"don Allah Hammana ka faɗa min me ka gani a Wayar? Sannan na ce ka bani wayar ka ƙi ka bani don girman Allah ka faɗa min? Ko dai mutuwa aka yi ne ko dai Baffana ne ya rasu?.

Sai a lokacin ya waigo ya kalle ni cike da tausayina domin ina hango hakana cikin kyakkyawan idanunsa, sai gabana ya ƙara faɗuwa sosai saboda a tunani ko maganar da na faɗa ta karshe ce ta auku ai kuwa tuni na fara gunjin Kuka. Da sauri na tare ni gami da cewa haba abar ƙaunata, ka da kiyi kuka mana ba abin da kike zata bane wata ƴar matsala ce amma zan war warware ta in sha Allah ke dai kawai ki dinga taya mijinki da addu'a domin kuwa ina cikin ruɗu  ni dai addu'arki ma kaɗai ta wadace ni, bana so Kuka don Allah".

Sai a lokacin na yi shiru inason kin damuwarsa, amma sai ya nuna min ai ba ta shafe ni ba bin da yafi kawai na yi masa addu'ar kamar yadda ya ce.
Ina ji ina gani ya fi ce da mutuƙar sauri saboda haya ganin gabansa sosai  saurin d yake yi kawai ya isa gidan Hafsah, yau idan ya kama Hafsah sai ya kai ta lahira domin ba zai barta a cikin duniya ba, ta ɓata masa mutunci ba shi a ganinsa duk masifar da yake ciki Hafsah ce ta sanya shi domin a baya yana cikin ƙoshin lafiya babu abin da yake damunsa, tun d karfa Hafsah ta shigo rayuwarsa shi kenan komi ya canza har gwara ma a dawo masa da talaucinsa akan a barshi a cikin wannan chakwakiyar masifar wacce bai san ranar da za ta mutu ba, idan ya kashe ta da ruwan sanyi sai ta ƙara bulbuluwa tamkar dai ya sanya mata boom.
Haka ya dinga wannan tunanin har ya isa gidan Hafsah, kai tsaye ya shige gidan kamar dai yadda yake yi da babu izini ko neman yardar matar gidan kawai faɗawa yake, saboda tashin hankalin da yake ciki idonsa bai kawo masa motocin gidan sun ƙaru ba haka ya shige yana cewa Allah ubangiji yasa babu kowa a gidan Allah yau dai sai ya kashe Hafsah saboda wata irin mahaukaciyar tsana yake mata wacce ba tada misali wacce ko a tarihi bai taɓa jin irin tsanar da ya yiwa Hafsah ba.


Sai dai me? Yana shi ga gidan ya hango Hamza zaune kan kujerar treaseeter yana kurɓar shayi a kofi, a take gabansa ya yi wani mummunan faɗuwa zuciyarsa ta shiga cikin mummunan ɗimuwa da tunani, amma tabbas har shigo to fa babu tunanin komawa tun da dai Ali ya ga Ali sun haɗu ido-ido wannan shi ne abin da ake cewa flash eyes wato fitilar ido ko kuma haɗuwar ido, sannan ya yi matuƙar kaɗuwa da kuma firgita, saboda haka sai ya yi saurin wayancewa ya ce"Masha Allah dama ance min ka dawo ne na zo mu gaisa domin kwata-kwata ba a ganinka".
Daga bayansa Hamzah ya ji maganar saboda ya juyo domin ya ga waye, ganin Habibu a tsaye cike da mamaki ya ce"to ikon Allah ban fa faɗawa kowa na zo ba".
D sauri Habibu ya ce" wani ɗan unguwarmu ne ya ganka a Airport shi ne sai ya faɗa min, shi ne na zo na ganka to nan gidan ma ban sani ba matata ce ta kwatanta min".
Sai da ya ji wani abu akansa kamar dirar mikiya, saboda har yanzu Mero tana cikin tarihin first Love ɗinsa bai taɓa jin ɗigon son wata ɗiya mace in ba  Mero ba da ita ya fara kuma ya rufe da ita, da sauri ya furta inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, domin ya tuna a yanzu ita matar aure ce bai kamata ya yi tunaninta ba kama ta ya yi ma ya manta da babinta amma ya kasa hakan, koma menene shi dai yasan dolensa ya dage da addu'ah domin har yanzu Hafsah ba ta samu gurbi a cikin zuciyarsa ba da ita kanta Hafsah tasan yana mata kallon ita namiji ce da ko kusa da shi ba ta zo ba.

Cike da fargabar da yake ji ya daure, ya yi ta maza ya ja ɗamara da ɗanba ya samu waje ya zauna yana yi wa Hamzah ta hanya hira ce ta ɓarke a tsakaninsu amman fa Allah² Habibu yake ya bar gidan saboda matsananciyar kunyar Hamzah yake yi wanda suka haɗa kai shi da matarsa suka ci amanarsa.

Suna cikin hirar ta su ne ma Hafsah ta fara saukowa daga benen da yake manne a falon wanda ya gaji da haɗuwa haka take saukowa a hankali, kana ganin fuskarta kasan sam ba tada nutsuwa sosai gabanta ya fara bugawa hango Habibu da ta yi tsumu² a falonsu suna ta ɓaɓɓaka dariya tamkar dai babu wata alaƙa tsakaninsu, murza idonta ta fara yi wanda ya kumbura sosai domin jiya kwana ta yi tana kuka a ɗakinta ta rasa mafita sannan Billy da take ɗan ɗauke mata kewa ta kirata ta faɗa mata mijinta ya dawo shi yasa ma ba ta so ba.

Da ɗan sauri ta ƙarasa saukowa cike da mamaki, tana faɗin a'Allah yasa dai ba zuwa ya yi ya tona min asiri ba tuno tare suka yi laifin sai yasa a zuciyarta ba zai zo domin tona miki asiri ba, ya zo ne kawai domin ya tsoratata amma ba don ya tona mata asiri ba.

Tana ƙarasowa kallon Habibu ya koma kanta, tuni ya shiga yi mata kallon tsana yana mata kallon maci amana bututu tabbas sai ya ɗauki mummunan mataki akan ta domin ba zai juri a bata masa suna ba.
Da ƙer ta samu ta zauna suka gaisa sama² saboda ƙirjinta da yake bugawa sosai ba shiri ta tashi ta koma ɗakinta kai tsaye ta sanya sakatar ɗakin ta shige ban ɗaki wani yunƙurin amai ya tunkaro ta ga zuciyarka cike da ƙunci da kuma danasanin bin shawarar ƙawarta, tuni ta shiga tsinewa Billy domin duk ita ce ta ƙara rurawa abin wuta da ta same ta a mai yi mata nasiha da yanzu wata ƙila ba ta aikata, lallai Billy ba ta zamo ƙawa tagari ba.


Haka dai rayuwarta ta koma kullum cikin kuka da kuma zullumi tana tuna yadda ta ci amanar ƙanwarta yanzu ba fata take ba ta yaya za ayi ra nemi yafiyar Mero ta tabbatar da tabbas ko ita ce sarkin marasa kunyar duniya ba ta isa ta tunkari Mero da wannan mummunar maganar ba. Ko abinci yanzu Hafsah ba ta ci, kula da lamari ta yasa Hamzah ƙara kusanto Hafsah domin ya ji meye damuwarta, amma kai tsaye sai ta ce masa babu komi.


A haka ne ya fara bibiyar rayuwarta domin yasan me yake damunta, tun da matarsa ce kuma yana da haƙƙin duk wani abu musamman abin da zai cutar ta da ita dolensa ya kare ta ko da kuwa ba ya sonta hakan ba zai sa ya cigaba d wulaƙantata ba sannan Allah zai yi fushi da shi domin babu ruwan Allah da ai auren dole aka musu ya zamar masa dole kula da ita, musamman ma da yaga Hafsah ɗin duk ta tsangwami kanta ta rame ta ƙanjame duk sai yake tunanin ko abubuwan da ya yi mata sune suka yi coursing ɗin matsalar, da ga haka ya fara shiga ɗakin Hafsah yana son gyara laifin da ya yi kafin ya koma sannan yana son ya koyawa zuciyarsa don Hafsah domin yana ganin hakan shi kaɗai abin da ya dace ya yi, duk da zuciyarsa har yanzu ta ƙi karɓar Hafsah bai san meye hakan ba.

Wannan shiga ɗakin Hafsah ɗin da ya fara sai ya kawo wata babbar matsala wacce ita ce mabuɗin tonuwar asirin Habibu da kuma Hafsah, wato abin da ya faru shi ne.

Ranar da daddare ya shirya, ya shirya tsaf domin tunkarar matarsa da aure domin ko a baya da baya kusantarta zuciyarsa taƙi yarda ya bawa Hafsah kansa duk da yana a matsayin mijinta, sai yanzu ne shi da kansa ya matsu yana muradi, kuma yana so, domin bai taɓa ba, sannan yana zumuɗi. A haka ya shirya ya tafi ɗakin Hafsah sai dai ya ga ashe har barci ɓarawo ya ɗauke domin ɗazu² ya hango ta ta shiga ɗakinta mintina ƙalilan kuma ashe har ta yi barci, haka ya shigo ɗakin a hankali yana kallon Hafsah tuni idanuwansa suka rufe ta ji baya ganin komi.


A haka dai zuciyarsa ta ayyanasa masa muradinsa, bai san lokacin da ya fara addu'a ba tana barci ta dinga karɓar saƙo tunaninta mafarkin da ta saba yi ne da wani yana mu'amalarta to yanzu ma ta ɗauka haka ne shi ne ta bada kai bori ya hau.


Tuni Hamzah ya yi cilli da Hafsah, ya ji wata irin muguwar tsanarta ya ji dama bai taɓa saninta, tuni wannan mummunar tsanar da yake mata ta dawo sabuwa dal a cikin dari sai ta dawo dubu, ya dinga kallonta a ƙyama ce domin shi a tunaninsu in ba mantawa ya yi ba ai Hafsah budurwa ce ba bazawara ba, amma kuma ya zai same ta a matsayin on virgin.

Jin irin wani wahalataccen maruka har biyu ya yi sanadin tashin ta daga nannauyan mafarkin biyan buƙatarta, ta wari idanuwa waje ganin Hamza a gabanta yana mata kallon tsaf da tsaf, da kuma kallon tsantsar tsana tuni ta kalli jikinta ta ga yadda take ai sai ta sanya wani irin ihu domin tasan Hamzah yasan komi.


Hamzah kuwa cike da tsanarta ya nuna ta da yatsa ya ce"wallahi tallahi Hafsah kin cuci iyayenki sannan kin cuci kanki tabbas ina tubarwa Allah dana aure ki, tur da halinki na auri mazinaciya da kai na tabbas na ƙara tsanarki Hafsah amma ki sani tabbas sai kin ɗanɗana baƙin cikin da kika sanya min, wallahi Hafsah sai kin yi danasanin aikata zina a rayuwarki".


Da mugun sauri Hafsah ta taso ta tsugunna a ƙasa ta riƙe ƙafafunsa tana ce wa"don Allah da manzonsa kayi haƙuri ka da ka tona min asiri saannan kuma wallahi wannan abin da ya faru dani ba laifina bane don girman Allah ka yafe mun na yi nadama wallahi".

Tuni tsanarta ta ƙara fusgota bai san lokacin da ya haɗa ta da garu ba, ya shaƙe ta sosai tuni idanuwanta suka firfito ta fara ganin duhu², cikin fushi ya fara magana"wallahi Hafsah a yadda nake ji kamar na kashe ki saboda ƙarya ne kici ba da gangan kika yi ba, shekarar ki nawa yanzu a duniya shekara 20 ɗin shi ne har kin san ki bi namiji ya biya miki buƙatarki, baƙin ciki na ma ɗaya dana auri fasiƙa marar tsoron Allah irin ki, sannan ki sani ba zan zauna dake a matsayin mata ba, tun da dama bana son ki amma ki sani dole a wannan lokacin ki faɗawa Ammi komi domin ba za ki yi shiru ki cuce ni ba bazan cigaba da zama da mazinaciya ba".


Tuni ya sake ta ta faɗa can gefen gado tana numfafarshi, tamkar dai wacce ta farfaɗo daga dogon suma haka ta daɗe a wajen tana kuka da kuma danasanin aikata laifin da ta yi, tabbas rayuwarta ta afka kogin nadama.
Shi a tunanin Hamzah ma kafin ta yi aure ne ta bawa wani kanta, bai kawo da aurenta domin da yasan da aurensa take zina tabbas zai iya kashe ta ma kowa ya huta. A mugun gigice ta tashi ta lalubo lambar Billy a haukace tana kuka tana rufe bakinta saboda kukan ma ba ya fitowa sosai sai sauti da kuma haɗiyar zuciya.



Sai da ta yiwa Billy kira biyu sannan ta ɗaga tana ce wa"mutuniyar ko har ogan ya koma n..."

Jin gunjin kukan Hafsah ta yi, irin kukan nan na baƙin ciki tamkar dai irin kukan nan da aka ce mahaifiyar ka ko mahaifinka sun mutu, tuni Billy ta turo sabon babyn da ta samu ta ce"Hafsah kuka kike fa me kuma ya faru?.

Hafsah tana kukan ta ce"na shiga uku Billy asirina ya tonu wallahi Hamzah ya gane ina bin maza domin yau yazo kusantata ya gani komi tabbas Billy mutuwa zan yi saboda baƙin ciki".
Billy ta ce"kin ga yi shiru, na faɗa kiki sirri ɗaya da za kiyi, yanzu dai kiyi shiru ki saurari zuciyarki cewar ba a yi miki adalci ba Hamzah ya zalunce ki, a lokacin da kike buƙatar namiji a kusa da ke sannan yana ji yana gani ya wofantar dake, sannan a yanzu zuciyarki ta bushe ta irin wanda aka yiwa rashin adalci, sannan ku tunkari matsalar ki gyara jikinki kiyi wanka har kici abinci, ya ga kin saki jikinki sannan sai ki same sa kice masa in har ya ɗauki matakin sakinki ke kuma za ki faɗawa duniya zaluntar ki da yayi ya barki har tsawon wata 7 ba tare da ya kusance ki ba, sannan ma a yanzu zarginki yake yi saboda ba ya sonki idan kika faɗa masa haka zai barki a gidansa, sannan bayan haka dole harkar nan a haɗa ta da malamai a rufe musu ba ki, sannan abar ma cikin a barshi a matsayin ɗan Hamza ne kuma kin ga dole ne ya karɓi cikin tun da an gama da shi an juyar masa d kwanta".

Tuni Hafsah ta rufta ga shawarar ƙawarta, ta ji zuciyarta ta yi sanyi tsaf tamkar ma babu wata matsala da ta faru , maimakon ya faɗawa Ubangiji ya ƙara shiryar da ita a a kawai sai ta faɗa ga mummunar shawarar ƙawarta.







***
Mrsgreen ce.