ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER 8

by @hindatuauwal

Da azimansa yamiƙe yafita zuciyar shi na azalzalansa da son cika umarnin ta agareshi.



       *ZAINAB*



Zaune take ita kaɗai a falon. Tunda Khadija tazo tagaya mata abinda ke faruwa tai shiru zuciyar ta na suya, daƙyar ta iya daurewa ta kammala koyama Ramlat haddar da aka basu tacema yaran su tashi suje su kwanta.




Tai zaune tana tufka da warwara, ko amafarki bata taɓa hango Ahmed zai mata kishiya ba balle har ya wulakanta ta saboda yayi aureba. Tayi tinanin shirun da tayi shizai ceceta amma sai gashi komai na niman kwaɓe mata.




To kodai zata shirya ne taje gidansu Ahmed ɗin tagaya ma ƴan uwansa tunda mahaifinsa da mahaifiyar sa duk sun rasu, wa....



Ƙiii.....!!!



Sautin ƙofar ɗakin da aka turo aka shigo yakatse mata tinani.

Zainab ta ɗago kanta da sauri.

Ahmed ne. Ya shigo cikin ɗakin.

Fuskarsa babu annuri. Babu murmushi. Babu ko ɗan ƙaramin alamar tausayi.

Fuskarsa ta kasance fayau, kamar mutum wanda ya riga ya yanke hukunci tun kafin ya shigo ɗakin.


Saɓanin lokutan baya da take ganin soyayyar ta a zahiri kwance acikin idanuwansa data kuma kallonsa yanzu wani kallo yake mata na daban daya hargitsa mata tinani.


Zainab ta zuba masa ido. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri.

Me yake son faɗa?


Ta jefa ma kanta tambayar da babu mai bata amsa. Ta kasa cire idanunta daga gare shi.

Ahmed ya tsaya gabanta na ƴan daƙiƙu, sannan ya ce cikin sanyi:

“Khadija ta kawo min takarda. Ban ce mata komai ba saboda da ke nake son magana.”

Zainab ta ɗan gyara zamanta.

“Ahmed...”

Ya ɗaga hannu kaɗan, ya hana ta magana.

“Gaskiya, Zainab. Ba zan iya ɗaukar wani nauyi ba.”

Ta kalle shi cikin rashin fahimta.

“Nauyi?”

“Eh.”

Ya sauke numfashi ya cigaba“Na gaji. Ina buƙatar hutu daga komai. Daga wannan gidan, daga wannan rayuwar... daga ke... har ma daga yaran.”

Kalaman suka sauka a kunnenta kamar guduma.

Zainab ta yi shiru kamar ruwa yacinye ta.

Ahmed ya ci gaba.

“Na yi iya ƙoƙarina na tsawon shekaru. Amma yanzu bana son ƙara ci gaba da wannan rayuwar.”

Ya kalle ta kai tsaye.

“Daga yau, kada ki ƙara ɗora min wata damuwa ta kanki ko ta yaran nan.”

Zainab ta buɗe baki, amma takasa furta komai.

Ahmed ya ƙara da cewa:

“Kar ki kira ni idan yaran suna buƙatar wani abu. Kar ki turo su gare ni. Kar ki nemi in dawo domin wani abu. Ba na son a sake ɗaure ni da wannan gidan.”

Hannun Zainab suka fara rawa.

“Ahmed...”

“This Is my final decision”

Wannan kalmar ta kashe abin da ya rage mata na ƙarfin hali.

“Na yanke shawara cewa kowannenmu ya ci gaba da rayuwarsa yadda yake so. Ni bana son sake ɗaukar nauyin rayuwar ku.”

Ya ɗan dakata.

Sannan ya ƙara da kalmar da ta fi komai ciwo:
“Ki ɗauki yaran ki kula da su. Ni kuma ki ɗauka kamar ban taɓa zama mijinki ba.”

Zainab ta ji kamar an buɗe wani rami a cikin kirjinta.

Numfashinta ya tsaya..Idanuwanta suka cika da hawaye nan take.

“Ahmed... me kake nufi?” Muryarta ta fito a karye.

“Ka yi min adalci kenan?”

Ta kasa riƙe hawayen ta.

“Bayan duk sadaukarwar da na yi maka a rayuwa... bayan duk abin da na jure... bayan na ɗauki soyayyarka amatsayin mafakata arayuwa... bayan na tsaya tare da kai a lokacin da bakada komai... yanzu wannan ne abin da zaka biyani?”

Ahmed ya tsaya yana kallonta. Amma yanayin sa bai sauyaba, har yanzu yana nan akan bakansa.

Zainab ta share hawaye da bayan hannunta duk da wasu sabbine ke sake sirnano mata.

“Ka tuna lokacin da babu komai? Ka tuna lokacin da muka fara rayuwa? Ka tuna irin abubuwan da na bari saboda kai? Ka tuna sau nawa na yi shiru lokacin da zuciyata ke ciwo saboda bana son gidana ya rushe?”

Muryarta ta fara rawa sosai.

“Na haifan maka yara. Na raine su. Na kula da gidanka. Na yi maka haƙuri alokacin da bakada shi. Na yi maka uzuri a wurin kowa. A kwanakin nan kasan sau nawa na kwanta ina kuka saboda kada yarana suga raunin da nake ciki?”

Ta dafe kirjinta.

“Yanzu duk wannan... ya zama nauyi?”

Ahmed ya kalle ta ba tare da wani motsin tausayi ba.

“Wannan damuwar ki ce.”

Zainab ta tsaya cak.

“Ni dai daga yau kada ki ƙara tunkarata da damuwar ki, ko ta waɗannan yaran.”

Kalaman suka ratsa zuciyarta kamar ɗanyen ruwan dalma.

Ya juya ya fara tafiya zuwa ƙofa.

Zainab ta kalle shi cikin firgici.

“A’a... Ahmed!”

Ya buɗe ƙofar.

“Don Allah...”

Muryarta ta karye.

“Ka tsaya.”

Bai tsaya ba.

“Ahmed, don Allah ka saurare ni sau ɗaya kawai...”

Amma ya fita. Ƙofar ta rufe.

Ɗakin yai wani irin shiru mai ban tsoro.

Zainab ta tsaya tana kallon ƙofar, kamar har yanzu tana jiran ya dawo.

Kamar tana jiran ya buɗe ƙofar ya ce mata, “Yi haƙuri, Zainab. Ba haka nake nufi ba.”

Amma bai dawo ba.

Ƙafafunta suka kasa ɗaukar nauyinta. Ta zauna a hankali a ƙasa. Sai kawai wani kuka ya kubce mata.

Ba irin kukan da mutum yake yi domin neman a ji shi ba.

Kuka ne na mutumin da aka karya masa zuciya har ya kasa sanin inda zai fara tattara gutsurarren zuciyarsa.

Ta dafe bakinta domin kada yaran su ji. Amma hawayen suka ci gaba da gangarowa.

“Ya Allah...”

Ta furta cikin rawar murya.

“Me na yi?”

Ta kalli ƙofar.

“Me na yi maka har ka iya kallona haka?”

Ta runtse idanunta.

A cikin duhun idanuwanta, shekarun aurensu suka fara dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Komai ya dawo mata a lokaci guda.

“Na yi maka sadaukarwa...”

Ta ɗora hannunta a kirjinta.

“Na ba ka komai da nake da shi...Me yasa ka barni kamar ban taɓa zama wani abu a rayuwarka ba?”

Sai ta tuna da yaranta. Su ne kaɗai abinda yanzu suka rage mata aduniya.

Kalaman Ahmed suka sake dawo mata da ciwo mai zafi. 

“Ki ɗauki yaran ki kula da su.”

Ta kalli ƙofar ɗakin yaran hawayen ta naƙara ƙarfi wurin zuba.

“Yaran nan fa?” Ta furta cikin raɗaɗi. “Su ma naka ne, Ahmed...”

Ta girgiza kai.

“Ta yaya zan gaya musu cewa babansu ya daina ɗaukar nauyinsu? Baya buƙatar su acikin rayuwar sa?!!"

Kuka ya sake tasowa daga cikin zuciyarta.

Ta yi ƙoƙarin tashi, amma ƙafafunta suka kasa.

Ta koma ta jingina da gefen kujera.


Kamar zuciyar ta na dakon azo nan wurin ta ɗauketa ta watsa ta can wani lokaci mai girma

*

Mahaifinta ya ɗan yi shiru. Ya sauke idanunsa ƙasa, kamar yana ƙoƙarin tattara ragowar ƙarfin da ya rage masa. Lebɓensa suka motsa a hankali, amma kafin kalmar farko ta fito, ya ja dogon numfashi.

“Na rayu da mutane cikin tsantseni gaba ɗaya rayuwata… tsakanina da hukuma gaisuwa ce kawai. Inda ace wani ne ya kai ni wurin hukuma, abin ba zai min ciwo kamar yadda ya yi min yanzu ba…”

Muryarsa ta karye a kalmar ƙarshe.

Ya ɗaga idanunsa ya kalli Zainab. Wannan karon ba kallon uba yake yi wa ’yarsa ba… kallon mutum ne da ya ji an cire masa wani ɓangare na rayuwarsa.

“Saboda wanda na haifa da hannuna… wanda na raina da wahala… wanda na yi mata mafarkin ganin ranar da za ta zama farin cikin idona… ita ce ta kai ni wurin da ban taɓa tsammanin zan taka ba.”

Idanunsa suka cika da hawaye, amma ya ƙi bari su zubo. Sai ya yi murmushi mai ɗauke da zafi.

“Tunda kika zaɓi Ahmed a kaina, Zainab…”

Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, kamar kalmar da zai faɗa tana masa nauyi fiye da duk wata wahala da ya taɓa fuskanta.

“Ki sani… daga yau, ba ni da ’ya mai suna Zainab.”

Kalaman suka faɗo cikin ɗakin kamar wuƙa.

Zainab ta kafe shi da ido, numfashinta ya tsaya.

Amma mahaifinta bai sake kallonta ba. Ya juya fuskarsa gefe, yana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka tsere daga idanunsa.

Ta share hawayenta, ta daɗe tana kallon bayansa har ya ɓace daga ganinta, sannan ta ce a ranta:

“Zan tabbatar maka cewa zaɓin da na yi ba kuskure ba ne.”


*

Zainab ta runtse idanunta. Hawayenta suka ci gaba da zuba, a cikin zuciyarta, wata ƙaramar murya ta yi mata tambaya:

“Idan mace ta sadaukar da komai domin kare gidanta... shin wa zai kare ta idan gidan da kanta ta kare ya zama sanadin karayar zuciyarta?”



        *ALIYA*


Tsaye take a kitchen tana goge-goge. Ƙamshin tiraren Ustaz ne ya soma tsayawa akan iskar da take shaƙa, kusancin haibansa da kwarjinin sa suka cika kitchen din, buɗaɗɗiyar muryarsa mai taushi a kunnuwanta.



"Aliya sai nadawo."



"Ustaz....!!!"


Taja sunan a shagwaɓe. Idanuwan ta na narkewa da taɓara.



Yanayin fuskarsa bai can jaba a zahiri. Daga baɗini wani abu yatsirgamasa mai sanyi hakan ya sanya muryarsa fitowa da ƙwarin da baya jinsa ajikinsa.



"Karki soma Aliya students na can na jirana."



Idanuwanta ne suka ciko da ƙwalla.


Ƙafarsa yaɗaga daniyyar shiga kitchen din ya tallafo fuskar ta acikin tafukan hannayen sa. Sai zuciyar sa ta dakatar dashi.



"Gayamin mai kikeso"


Kai tagir giza mai alamar a'a. ƙwallan da suka ciko idanuwanta na saukowa saman fuskar ta. Harga Allah batason yatafi yabarta ita kadai agidannan.


Tsigar jikinsa ne yatashi. Idan har yaciga da kallon Aliya zai rasa control ɗinsa ta fannin da baya buƙata ayanzu, yajuya dasauri. 



Taku ɗaya...biyu...uku yaji muryanta abayansa tana kiransa da muryan nan tata mai rauni.



"Ustaz...!!!"


Juyowa yai yakalleta. Batai magana ba sai hannun ta da tai mai nunida yasunkuyo. Besan mai zatai masaba amma in duƙawar tasa zai sanyata farin ciki to shikenan.



Unexpected yaji soft lips ɗinta sun sauka akan goshinsa. Kamar wanda shock yakama haka yai. Murmushin ta daya haske fuskarsa da kalaman ta ya sanya sanyayyiyar murmushin da bai tsammata ba ya suɓuce mai.



"Good bye Zauji"



Tsayawa kawai yayi yana kallonta.



"Kadaina kallona haka cewa zakayi I love you and zanyi missing ɗinki sosai."



Be faɗaba sai murmushin nan nasa mai tsada daya sake wanke ta dashi. Yajuya yafice.