15
by @mamuhgee
Aasiyah
Mamuhgee
15
Fizge fizge ya fara jamilu na jin hakan jikinsa ya tsananta rawa yayi saurin saki pilon ya zame zai fadi khamis ya saka qafa ya dannesa saiti da gurin hancin nasa batareda ya sake hannuwansa daya riqeba sbd kada fizge fizgensa yabar alaman da zata nuna yayi fizge fizgen kafin fitar ransa.
Bulama ne ya bude baki qasa qasa yana matsowa yace
"Ka dafe da kyau fa kada kafarka ta toshe ba daidaiba"
Jamilu da jikinsa ke rawa zufa ne ya tsinke masa yana kallo har ran Baban ya fita daga jikinsa.
Bulama ma zufan yakeyi yana kallo yanajin kaman khamis bai cika aikin da kyau ba.
Janye pilon khamis yayi batareda yace komaiba bai kuma sake duba Baban ba sbd yasan ya riga ya tafi kenan dan haka kai tsaye waje yayi ya tsaya tsakar gidan ya shaqi wani iska idonsa na cikowa da hawayen daya maida ya shanye abinda kawai ya koma dakinsu ya kwanta.
Jamilu ma sauri ya fice hawaye na sauko masa jikinsa na rawa har lokaci yana fitowa dakinsu kawai ya fada shima ya kwanta da yana dunqulewa guri daya.
Bulama ne ya tsaya ya gyara kwanciyan Baban ya rufesa ya hana komai nuna akwai abinda ya faru cikin daren kafin shima jiki na rawa yaje ya kwanta.
Asuba nayi suka fara doka salati da ambatar sunan Baban wanda ya daka maqocinsu kuma abokin Baban ji ya shigo gidan da sauri anan kuwa ya tadda Baba Ashiru dai lokaci yayi take jamilu ya fasa kuka yana ambatar sunan baban jikinsa na rawa bulama ma bakinsa ya hau yana sambatun yaya zasuyi babu Baba wlh bazai iya rayuwa babu babansa ba.
Khamis ma rungume baban yayi yana kiran sunansa take suka saka Malan shehu kukan tausayinsu dana rashin amininsa yafara hawaye yana basa hakuri da kokarin rarrashinsu sbd tabbas suna cikin tsaka mai wuya ba uwa ba uba duk da sun zama matasa amma akwai tashin hankali.
Koda gari ya waye rasuwar Baba Ashiru ta yadu a anguwan harma da Baffa wanda Jamilu ya kira ya sanarwa.
Jin yanda suke kuka cikin tashin hankali da nuna tsananin baqin ciki da damuwa ya sanya Baffa jin zuciyarsa tayi laushi akansu tareda tausayinsu sbd dai Ashiru ya lalata rayuwarsu kuma gashi yanzu ya bar duniya yabarsu a cikinta zasusha wahalar wasu daga cikin halayensu daya koya musu.
Anyi janazah da komai anyi zaman gaisuwa har yamma ana zaune kofar gida sai ga baffa yazo gaisuwan da motarsa data ringa daukan idanuwan mutane tareda driver dinsa da Lawal.
Suna ganin Baffa kukansu ya dawo sabo damuwansu ta tsananta suka sake zama abin tausayinda kowa a gurin saida ya ringa fadan irin kauna dake tsakaninsu da mahaifinsu da irin halinda suka shiga tin asubar.
Tinda safiyar tayi babu wanda ko ruwa yasha a cikinsu dan hakane bakinsu ya bushe maqoshinsu ya bushe sunyi wani irin abin tausayi da taba zuciya.
Baffa ne yayi musu nasiha sosai kafin ya tafi da tausayinsu.
Da daddare bayan sun shige fitowa jamilu yayi yaje ya siyo musu abinci mai lafiya suka rufe gida suka zauna sukaci babu cewa komai sbd dai har lokacin zuciya bata samu abinda takeso ba dan haka da sauran lokaci a farin cikinsu.
Washe gari ma anyi zaman gaisuwa har tsawon kwana uku kafin aka watse daga nan sai suka koma gidan baffa suke wuni sai dare su dawo gida wani lokacin ma acan suke kwana,
Baffa tausayinsu yakeji sosai yanzu sbd damuwa tayi musu yawa ko abinci basa ci sosai daga karshe ma rashin lafiya bulama ya kwana hakama jamilu khamis nata kulawa dasu shima ya koma gwanin tausayi.
Zuciyar imani ta baffa da kallansu a matsayin jinin maryam dinsa sai ya karaya sosai ya sakasu tattaro suka rufe gidan babansu suka dawo gidansa gabaki daya yace ya karbesu har mutuwansa insha Allah.
Wannan shine matakin farko na nasararsu ta cimma burinsu dan kuwa dawowansu gidan baffa ya saka wata sabuwar duniya bude musu,
Alh Daddy ma yaxo gidan ya musu gaisuwa kuma ya sake tattauna sosai da baffa dasu akan karatunsu da yanzu zasu iya tafiya Cyprus suyi nan ma wani farin cikin ya rifesu sbd komawansu can na nufin zama tareda Haj maryam acan dan haka murna ta qume su sbd ran Babansu dai ya zama fansar cikar burinsu dan haka baba ai zaiyi farin ciki ko a lahira.
Ana fara shirye shiryen tafiyarsu Alh Daddy ya sakar musu wasu irin kudi sosai dan yin nasu shirye shiryen duk da baa buqatan suyi wani siyayya duk da saman sitira ce kawai da abubuwan buqatansu na kullum.
A daidai wannan lokacin ne Haj maryam ta san cewa sun dawo rayuwar mahaifinta sbd baa sanar da ita komaiba baffa ya boye mata bai taba barin ta hadu dasu ba sbd harga Allah bayason haduwan tasu amma tinda Dr ya riga ya yanke shawarar kaisu qasar dasuke dan karatu dole ya bari suka hadu amma dai duk da hakan baa gidansu zasu zauna ba a nasu apartment dayake kusa da inda zasuyi karatu ne.
Wani lokaci mutum yana gudu daga abu ne saboda yana tunanin musiba ne alhali kuwa yana gudu ne daga abin da zai zama alherinsa,
Wani lokaci kuma...
mutum yana buɗe ƙofa da kansa yana tunanin baƙon da yake shigowa zai kawo masa farin ciki ko alkhairi kokuma hadin kai da zama daya alhali bai san cewa abin da zai shigo da shi shine farkon rikicin da zai iya rusa rayuwarsa dana kusa dashiba kamar yadda Hausawa ke cewa:
"Ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare." lokacin ne mutum zai gane wanda ya zo masa da zuciya ɗaya, da wanda ya zo masa da zuciyar duniya.
Haj maryam tashiga shock na ganinsu sedai bata nuna hakanba sbd Allah ya riga ya cire mata su a cikin ranta bata taba tsammanin sake ganinsuba a rayuwarta sbd tasan bazasu taba nemanta ba hakama itama bazata namesu ba tinda sune suka zabi cireta a rayuwarsu.
Da farko ma tana shigowa palon Baffanta tana tareda Aliyu wanda yake biye da ita tana kallansu bata ganesu suka gaidata ta amsa a natse babu komai sbd bata dauka sune dinba ta qarasa gurin baffa ta xauna tana gaidasa yana amsawa yana miqawa Aliyi hannu da sakewa sosai a fuskansa da kulawa mai yawa yace
"Gadanga 'dan gidan Amminsa kana lafiya ko??
Murmushi Aliyu yayi yana zaunawa kusa da baffan yana cewa
"Ammi nace ni kadai"
Dariya baffan yayi yana basa amsa.
Su khamis gabaki dayansu mutuwar zaune ce sukai kowace gabar jikinsu na sakewa da rushewa idanuwansu na sauyawa gavaki dayansu musamman jamilu datafi kauna kasancewansa autanta a baya data nunawa kauna sosai.
Tabbas wannan haj maryam binnah ce ba maryam mahaifiyarsu ba,
Wannan matar datake da iko da dama ce damar da zata iya dama kowace rayuwa a hannunta,
Securities dinta ne suka shigo a jere da suka gaida Baffa da girmamawa tareda ficewa suka koma harabar gidan.
Idanuwansu jajir sukai matiqar yi take jikinsu su dukan yafara rawa musamman khamis wanda yaji duniyarsa ta tsaya cak sbd ta tabbata su marayun gaske ne dan kuwa a macen dayake gani gabansa bazata taba karbansu a matsayin 'yayan da kowace uwa take bawa yayantaba,
Sunyi sake,sunyi ganganci kuma sunyi asarar wannan uwar rasawan har abada dan a yanxu sedai a matsayin tausayawa zata karbesu babu wanna zazzafar kaunar ta uwa.
Jamilu kuwa hawayene suka gangaro masa ya rufe idanuwansa yana fasa wani irin kukan daya kasa boyuwa yana sunkuyar da kansa qasa..
Bulama da zufansa ke qaruwa shima idanuwansa na cikowa da hawayen ambatar sunanta yayi da "MAMA"
Cak ta tsaya daga maganar datake kokarin yiwa baffa tana kasa juyowa har saida ya kuka ambatarta kukan jamilu na ratsa kunnuwanta zuwa kirjinta ta juyo da wani irin mamaki da slow ta sauke idanuwanta akan jamilu wanda ya dago shima ya ambaci sunanta muryansa na rawa.
Bulama ta kalla ta dawo da kallanta akan khamis tukuna ta juyo da sauri ta kalli baffa wanda ya sauke numfashi yana gyada mata kai ahankali tareda jin jikinsa na sake mutuwa.
Gabaki dayansu su ukun rarrafowa sukai a tare suna sake kuka mai tsananin ratsa zuciya suna ambatar sunanta da wata irin nadama da bayyanarda baqin cikin halayensu da sukai nadama.
Kasa motsawa tayi ta kafe baffa da ido wanda ya fara jero mata bayanin komai da komai tin farkon zuwansu da rasuwar Babansu da matakin da ake kai yansu na Dr binnah ya gama musu komai na tafiya makaranta.
Sake kallansu tayi sunata kuka da neman gafararta kaman zasu shide da baqin cikin rayuwarsu.
Miqewa tayi kokarin yi jamilu ya riqe kafafunta yana sake qasqantar da kansa da rokonta yafiya ko zasu samu duniya tayi musu daidai harma da lahira.
Aliyu dayake kallan abinda yake faruwa shima miqewa yayi yana riqeta yace
"Ammi kiyi hakuri ki yafe musu sunata kuka fa"
Kallansa tayi da idanuwanta da sukai jajir zuciyarta na wani irin nauyin datake jin inama basu dawo gareta ba amma kuma sai tinawa da a yanxu iyakacinta dasu ido ne ba wata alaqar saita sauke ajiyan zuciya tareda juyowa ta kalli baffa wanda ya bude baki yace tayi hakuri ta yafe musu din insha Allah komai ya wuce tinda yanzu suna kokarin bawa kansu tarbiya mai kyau.
Wannan ne sanadin da 'yaya uku sika dawo rayuwar mahaifiyarsu wadda ta yafe musu ta amsa tubansu ta bar komai ya wuce amma bata buqatarsu a rayuwarta sam tabarwa baffa su har abada.
Farin ciki suka shiga mai tsananin da basu taba jinsa ba dan haka duniya ta dawo musu sabuwa aka fara shirin tafiya wanda ya riga yayi nisa dan har a waya yanzu suna kiranta da Alh Daddy su gaidasu kuma suna zuwa can gidan sosai duk da haryanzu basu samu komawa binnahs ba amma a hakanma sunsan sun cimma wani babban nasarar kafin gaba.
Duk ranar da suke cikin gidan haj Maryam binnah wani sabon abu suke ganowa,Wani sabon abin mamakin da baya qarewa,wata sabuwar kofar arzikin da baida iyaka,
Wata sabuwar hanya ta rayuwar da basu taba saniba,
Su kalli yadda ma'aikata suke girmama Dr Binnah kaman zaa fadi a masa sujjada,kaman zaa cire rai a basa,
Su kalli yadda mutane ke tsayawa idan ya shigo,
Su kalli yadda kalma ɗaya daga bakinsa take iya canza komai,
Su kalli yanda ake bawa aliyu so da kauna da kulawa tareda tattalin da ko rijiyar zinari bata kaisa ba,
abin ya fara wuce mamaki garesu
Ya zama sha'awa,Sai sha'awar ta koma ƙishirwa,Sai ƙishirwa ta koma son mallaka.
Kuma son mallaka idan ya yi wa zuciya katutu bata tambayar halal da haram.
Tafiyarsu bulama karatu Cyprus ta kammala ana kokarin tafiyar ne Baffa zuciyarsa ta kasa nustuwa sam hankalinsa ya tashi bayajin daidai dan haka ya kira maryam gidansa taxo suka zauna ya kalleta a natse bayan ta zauna kusa da shi.
Ya daɗe yana kallonta kafin yace
"Maryam"
"Na’am Baffa"
"Kin tabbata kin san abin da kike yi?"
Shiru tayi jikinta na sanyi kafin tace
"Akan me baffa"
"Yaran nan"
Shiru ta kuma yi.
lokaci baffan ya kuma dan dauka shika kafin ya ci gaba
“Na san su 'ya'yanki ne,
Na san zuciyar uwa ba ta iya rufe ƙofa ga kuma ke kina kallonsu da idon uwa Ni kuma ina kallonsu da idon mutumin da ya ga yadda rayuwa take canza mutane,
Bance ki kuje su ba amma inason ki kiyaye sosai,ki kula sosai,ki saka ido akansu sosai sbd zuciyata ta kasa sukuni da samun nutsuwa"
Ajiyan zuciya ta sauke itama kafin ta dago ta kalli baffan tace
"Baffa tinda zuciyarta ta kasa nutsuwa inaga gwara abarsu anan to kawai"
"Tabbas nima zanfi son hakan maryam gaskia,a hakura abarsu dan Allah ki fahimtar da Dr abarsu kawai ni xan dauki nauyin komai nasu"
Hakan taji itama yafi mata dan haka tace
"Yau yanada baqi daga qasar turkey dan haka zuwa gobe insha Allah idan ya samu nutsuwa sosai zan sanar masa"
Cikeda farin cikin shawaran da suka yanke da samun nutsuwa akanta sukai sallama ta bar gidan.
Bulama da jamilu ne akai komai akan kunnuwansu dan daman sun jima da fahimtar rashin nutsuwan baffa da tafiyarsu shiyasa zuwanta ya kasa basu nustuwa saida suka ji komai dan haka hankalinsu yayi mugun tashi.
Jikinsu har wata tsima yakeyi suka tattauna zancen a tsakanin su ukun wanda take suka yanke shawarar bazasu taba barin haj maryam tayi magana da Dr binnah ba zuwa goben zasu tabbatarda bata samu nustuwan hakan ba bayan haka ma rashin baffa shine zai barta da rashin zabin daya wuce tafiya dasu tinda basuda kowa kaf a qasar.
Tsakar dare baffa yana tashi shan ruwa dan haka ake kai masa ruwa dakinsa duk dare.
Sune suke kai masa wani lokacin kuka lawal,
Yau lawal ne yakai masa ruwan ya fice.
Asubar fari lawal dinne ya shiga dakin dan sanar da baffa lokacin asuba kamar kullum sedai yana shiga baffa ya riga ya amsa kiran ubangijinsa babu ciwon komai haka kawai gawa ya tadda yana kwancensa lafiya kalau a rufe kaman a kira sunansa ya amsa.
Tashin hankali lawal ya shiga ya fito da sauri yana ihun kiransu take kowa ya fito hankali tashe da rawar jiki.
Mummunan tashin hankalin da binnahs suka tashi dashi a ranar shine na rasuwar baffa wanda ta girgiza duniyar haj maryam binnah wadda a yanxu daga mijinta sai yayanta kadai takeda.
Rasuwar baffa ta saka su khamis shiga wani halin dayake bayyanarda duniyarsu ta tsaya cak dan kuwa kalar tausayi da taba zuciya suka koma wanda dole haj maryam tabar Dr Binnah daukansu suka tattara suka koma Cyprus dasu wanda hakan ya basu damar saka kafa a cikin burinsu daya fara cika daga ranar.
#MAMUH
#AASIYAH
LAST FREE PAGE
AASIYAH
Mamuhgee
1k regular
5k vip
***
***