ZAWARA.

CHAPTER 15.

by @1239900

ZAWARA.









NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ 







PAGE 15.








Da misalin ƙarfe 7:13pm Malam Sanda ya dawo gida. Ya na shiga gidan tun kafin ya kafe babur ɗinsa ya kalli Najlah da ta zo yi masa oyoyo ya ce.

"Ke ina Yayarki take ban ji motsinta ba?"

Juyawa Najlah ta yi ta kalli ƙofar ɗakin Kilishi inda Nasibah take a kwance kamar ruwa ta ce.

"Ta na ɗakin Ummah bata da lafiya. Baba ka san me? Mama ce ta daketa ta mutu,Ummah ta yi ta kuka ta kira Faihah ta ce ta bata ruwa, shine da Ummah ta shafa mata ruwan ta buɗe ido tana kuka."

Zuciyar Mama na lugude ta fito ta samu kan Najlah ta ƙoza ta tana hararta ta ce.

"To Suda sarkin zance,faɗi ba a tambaye ki ba,wuce ciki kafin na sumar da ke kema."

Ƙugu Makaɗi ya kama da hannu ɗaya,hannunsa ɗaya kuma ya dafe jikin babur ɗinsa yana kallon Mama ya ce.

"Af toh na ji,ita Nasibar kenan sumar da ita kika yi ko Maryama? Akan me za ki sumar min da yarinya? Laifin maita aka kama ta da shi ko na lalata?"

Shiru Mama ta yi ta durƙusa ta shimfiɗa masa tabarma,dan ta kula da fushin da Kilishi ke yi da ita ba zai bari ta fito ta kula da mai gidan nasu ba. Ta na gama shimfiɗa wa ta kalli ƙafar Makaɗi da har a wannan lokacin bai motsa daga inda yake ba,hakan na tabbatar mata da cewa bai dena kallonta ba,fuska a cure ta ce.


"An dawo lafiya?"

A hasale Makaɗi ya ce.

"Da masassara na dawo Maryama. Na ce da masassara na dawo. Za ki bani amsar tambaya ta ko sai ranmu ya haɗu gaba ɗaya ya ɓaci?"

Fuska a ɗaure Mama ta kalle shi ta ce.

"Kai ka san taurin kai da rashin jin Nasibah Malam,shine dan an hukunta ta kake yi min tsawa?"

"Hukunci? Hukuncin ne zai kai ki ga sumar min da yarinya?"

"Ni ban sumar da kowa ba."

Mama ta faɗa tana mai shige wa ɗakinta;domin zuciyarta ta kasa yin haƙuri ta bashi abincin da ta yi niyya. Ta na shiga ciki ta dafe ƙirjinta da ke yi mata lugude,a bakin gado ta zauna tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Makaɗi kuwa sai ya hau ƙwala wa Nasibah kira yana taku cikin sauri,a bakin ƙofar ɗakinsu ya tsaya ya ɗaga labule yana faɗin.

"Wai Nasibah bata ji na ne?"

Cikin kuka Nasibah da ta yunƙura da ƙyar ta fito daga ɗakin Kilishi ta ce.

"Baabaa."

Da sauri Malam Sanda ya juya idanuwansa suka sauka akan Nasibah dake jingine a jikin gini tana risgar kuka. A sukwane Malam Sanda ya isa gabanta ya kunna hasken wayarsa yana duba ta. Ganin shatin bulalai a jikin Nasibah sun kwanta sun yi jawur ne suka sanya shi sakin wayarsa a ƙasa yana salati. Ji ya yi kamar ya kurma ihu. Cikin ɓacin rai ya isa ɗakin Mama wadda ta yi saurin tayar da sallah ta yi sujjah. Malam Sanda na zuwa ya ga abinda take yi sai ya ce.

"Maryama idan shekara dubu za ki yi kina sallah,ni kuma zan shekara dubu da ɗaya ina jiran ki idar. Ba zaki dakar min yarinya ki ci bulus ba,a yau ba sai gobe ba za ki tattara ki tafi gidan iyayenki,ba zan ɗauki wannan sabon salon fushin rashin hankalin da kika fito min da shi a gidan nan ba. Ke Nasibah zo nan!"

Ƙafafuwan Nasibah na rawa ta fara tattaki zuwa wajen Malam Sanda. Sai dai kafin ta isa gabansa ta zube a wajen tana aman ruwan kunu da tuwon da Kilishi ta ɗura mata. Hankalin Malam Sanda ba ƙaramin tashi ya yi ba,kafin Kilishi da ta fito daga ɗakinta jin Nasibah na amai ta isa gaban Nasibah Malam Sanda ya riga ta. Tallabo Nasibah ya yi yana haki ya ce.

"Wai me ya faru a gidan ne da bana nan har aka yi yunƙurin hallaka min ƴa?"

"Yanda ka ganta nima haka na ganta Malam,kawai ka kama ta ka kai ta Kemis ɗin Ɗan Small ya bata maganin zazzaɓi da ciwon jiki."

A wannan ranar Makaɗi ko tuna wa da Samir bai yi ba ballantana ya nemi taimakonsa. A gaggauce ya sunkuya ya ɗauki Nasibah a hannu ya nufi ƙofar gida da ita. Su na fita suka ci karo da Usman ya dawo daga wajen abokansa. Da sauri ya isa gaban Makaɗi ya karɓi Nasibah ya goya ta yana faɗin.

"Baba ina za ka kai ta haka?"

"Mu je ka kai ta wajen Ɗan Small ya duba min ita."

Fankam-Fakam suke tafe kamar Makaɗi zai caki ƙasa da haƙoransa. Su na zuwa wajen Ɗan Small me Kemis suka ga zai rufe wajen saboda kiran sallah da ake yi,da sauri Makaɗi ya dakatar da shi ya roƙi arziƙi ya duba masa Nasibah. Magunguna ya bata Makaɗi ya cire kuɗin da ƙyar yana jin ciwon yin hakan a ransa ya bayar. A hanyar komawarsu gida ya bi ta shagon Isiya ya siya mata Fanta suka nufi gida yana faɗin.

"Ban kashi kuɗin banza ba Maryama,dan kuwa sai kin cake min kuɗin duk da kika sa na yi asara kan ki wuce gidanku."

Ransa a matuƙar ɓace suka koma gidan Nasibah na sake langwaɓewa tana sakin numfarfashin azaba.  A tabarmar da Makaɗi ke zama Usman ya kwantar da ita yana haki ya zube a gefenta yana lasar busassun laɓɓansa. Idonsa akan sanssanyar Fantar da Makaɗi ya siyo wa Nasibah ya ce.

"Ƙishirwa nake ji,ina ma mutum zai samu wani sassanyan ruwa ko lemo ya kora."

A hasale Makaɗi ya kalle shi ya danna masa harara,kai Usman ya sunne ƙasa ya miƙe tsaye ya bar wajen. Yana tashi Malam Sanda ya zauna tare da ƙwalawa Kilishi kira ya ce.

"Taho min da kofi da ɗan abincin nan mu ga ko za ta iya ci."

Daga ɗaki Kilishi ta amsa shi da "Toh Malam" sannan ta fito ta shiga madafa ta ɗakko abincinsa a babban faranti ta ajiye a gabansa tana tambayar jikin Nasibah. Ajiyar zuciya Malam Sanda ya sauke sannan ya cire hularsa da ta yi zufa ya ajiye a gefensa ya ce.

"Gata nan ki taimaka ki kular min da ita; tinda ita Maryama yanzu ta zama abinda ta zama."

"To Malam Allah Ya bata lafiya."

Nan fa suka tasa Nasibah a gaba da lallashi da lallami har ta samu ta sake cin tuwon kaɗan ta sha fantar,sannan ta sha maganin ta kwanta. Babu jimawa baccin wahala ya kwashe ta. A nan wajen Makaɗi ya zauna har ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Nasibah ya gani sanye da hijabi a zaune ta jingina da gini tana kuka hannuwanta a sama. Idanuwansa ne suka washe ya sake kallonta ya ce.

"Sannu ƴar Baba,yaushe kika tashi?"

Nasibah bata kula shi ba,kuma bata dena yin addu'o'in samun nasara akan mahaifin nata ba domin ya amince ta auri Malam Luƙman ɗinta. Buta Makaɗi ya ɗauka ya zaga banɗaki. Ko da ya fito sai ya tarar da wajen babu kowa,shima sai ya tattara komatsansa ya wuce ɗakin Kilishi ya kwanta.

A bangaren Nasibah kuwa bata sake rintsa wa ba saboda tsannanin tunani da ya cika mata zuciya. Sosai take jin tsana da haushin Samir a cikin ranta. Ana kiran sallar asuba bacci mai daɗi ya dinga sanɗar ta,kin bashi dama ta yi ta fita ta yi alwala ta koma ɗakin ta tayar da sallah. Ta na idarwa ta koma ta kwanta bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita.

A wannan ranar da safe haka Mama ta ƙaraci baiwa Makaɗi haƙuri da ban baki amma bai kula ta ba. Daga ƙarshe ma da zai fita sai ya kalli Kilishi ya ciro kuɗin cefane ya bata ya ce.

"Tinda na yi kora an ƙi bar min gidana to sai a yi ta zama,amma ba zan yarda a sake dafa min abinci ba a gidan nan,ke Kilishi ki yi girkin dare,sai na dawo."

Tagumi Mama ta zuba tare da sauke ajiyar zuciya. Kilishi kuwa sai ta hau mahaifa tana faɗin.

"Ba zai yiwu ba Malam, a gaskiya ni ba zan karɓi girkin kowa ba."

"Au kema nuna min za ki yi ban isa da ke ba? Rabi! Rabi ke zo nan."

Malam Sanda ya faɗa yana riƙe kan babur ɗinsa da kyau. Rabi dake ɗaki tana ninke kaya sai ta ajiye ta fito da sauri ta durƙusa a gaban Malam Sanda ta ce.

"Baba gani."

"Amshi nan ki siyo kayan miya ki yi girki,zan dawo da rana na duba jikin ƴar'uwarki idan ta farka."

"To Baba a dawo lafiya."

Ba tare da ya amsa ta ba ya buga babur ɗinsa tare da baɗe su da hayaƙi ya bar gidan. Kilishi ma ɗakinta ta nufa,dan itama fushi take yi da Mama,shi yasa gaisuwarta kawai ta amsa tun da suka tashi basu yi wata doguwar hira ba. Duk Mama sai ta ji ta tsangwami kanta,nadamar dukan Nasibah duk ta mamaye mata zuciya. Jiki a sanyaye ta faki idon Kilishi ta leƙa ɗakin da Nasibah ke kwance kamar ruwa. Ganin yanda jikinta ya yi ja shatin bulalai suka yi masa ƙawa sai jikinta ya sake yin sanyi. A nan take ta gasgata dukan da ta yi wa yarinyar ya yi yawa,amma kuma ai ita ce ta jawo saboda taurin kanta. Ɗakinta ta koma ta fito da nera ɗari uku ta ba wa Najlah ta ce ta siyo mata madara da milo. Da sauri Najlah ta bar gidan ta nufi shagon Isiya ta siyo ta kawo wa Mama. Ɗakin Kilishi Mama ta je ta miƙa mata kayan shayin da ruwan zafi a flask ta ce.

"Ummahnsu ga abun kari na kawo wa ƴar taki a bata,Allah Ya ƙara lafiya."

"Aje su nan."

Kilishi ta ce tana kawar da kai. Murmushi Mama ta yi ta ajiye a inda Kilishi ta nuna mata ta fita ta koma nata ɗakin. Ta labulen ɗakinta take ganin gilmawar kilishi tana ta hidima da Nasibah.

Haka Nasibah ta ɗauki tsawon kwana huɗu tana jinyar jiki da zuciyarta. Sai dai a zahiri kowa ya shaida ta warke babu zazzaɓi tabon dukan duk ya yi duhu ya fara ɓacewa. Amma a zuciyar Nasibah jinta take yi kamar wadda aka tattara wa dika damuwar duniya aka ɗora mata akanta. Gaba ɗaya ta rame ta ƙara haske. Babban takaicinta bai wuce yanda Makaɗi ya sanar da Samir ta yi fama da jinya ba,shi kuma sai ya saki bakin aljihu ya dinga siyayya yana kawo wa gidan. Duk zuwan da yake yi kuwa duk yanda Makaɗi zai kaɗa ya raya bata fita wajen Samir. 

Yau ma kamar sauran ranakun da suka gabata,Nasibah ta dawo daga makaranta,sai ta cire hijabinta ta shiga ɗakinsu ta ajiye jakarta ta shiga ɗakin Mama ta gaishe ta. Ganin yanda Nasibah ta rame sai hakan ya ɗaga hankalin Mama,amma da yake basu da shaƙuwar da za ta kira Nasibah ta tambaye ta abinda yake damunta sai ta yi shiru tana bin ƴar tata da kallo har ta fita riƙe da kayan da za ta sauya.

Nasibah na komawa ɗakinsu ta sauya kaya ta kwanta ko abinci bata nema ba. A hankali bacci mai daɗi ya fara ɗibanta a kan soson katifarta da ba shi da maraba da tabarma. Cikin baccinta ta dinga jin wani irin sassanyan ƙamshi mai daɗi yana shiga ƙofofin hancinta. A hankali ta juya ta kai kanta saitin inda ƙamshin ke fitowa. Idanuwanta da suka yi mata nauyi saboda bacci ta buɗe ta zuba su a kan kyakkyawar halittar dake tsaye a saman kanta yana ƙare mata kallo..........