17
*BAYA TA HAIHU*
17
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72
Ummu Maher (Mrs green)🍀
*AREWA WRITTER'S ASSOCIATION*
*My channel*
***
*🗣️Kar ki wuce ba tare da kin karanta ba Please👏🏻 domin na tabbatar da kuma watarana za ki zama kamar Ummufadeel da ga shirye sai ki fara siyarwa👏🏻🗣️💃🏼*
*_UMMUFADEEL!_*
_*UMMUFADEEL!!*_
FOODMART🍊🍋🍎🍏🥦🥬🥑🥝🥥🍇🍓🍒🍌🥔
*UMMUFADEEL*
*Ƴar Jos💃🏼*
*UMMUFADEEL*
_Gidan sauƙi_
*Ummu fadeel me gidan gonar kayan marmari kowanne iri, da nau'ikan kayan tsirrai ko wanne iri, tana bayarwa akan sari*
*_SHIGA GROUP DOMIN GANIN KOMI DA IDONKA_*
***
*1_Citta ɗanya🫚 buhu ko bucket*
*2_Kaninfari kwano ko buhu*
*3_Cinnamon*
*4_Kimba*
*5_Masoro*
*6_Rosemerry*
*7_Tafarnuwa*
*8_Amla*
*9_Habbatussauda*
*10_Man kwakwa*
*11_Zaituun*
Da dukkan nau'ikan kayan ƙamshi na gida da na waje, dukkaninsu za ku same su cikin sauƙi da kuma rahusa gami da aminci, trust and thrusted.
_______________
*_Kar ku ga Ummu Maher ta fiye faɗin sunan, ku tambaye ni menene? Tabbas Ummufadeel ta shahara a fannin kawo muku kayan tsirrai, da kayan lambu, nau'in su Fruits, vegetables, ko wani nau'in kayan fruit da na lambu tana kawowa, kamar su;_*
*Strawberry🍓*
*Roseberry🍒*
*Inibi🍇*
*Ayaba🍌*
*Fiya🥑*
*Kwasha kwasha🥝🥝*
*Apple 🍎🍏*
*Mango🥭*
*Plum*🍑
*Cocumber🥒*
*Latas🥬*
*Cornflower*
*Doya🥔*
*Dankalin turawa*
*Dukkaninsu tana siyarwa a raha da kuma rahusa, ku dai ku hanzarta ku neme ta akan lambarta kamar haka ****
*_Idan na ce zan jero muku za mu daɗe ba tare da na gama ba, sannan tana siyar da nau'ikan tsirrai kusan rabi da kwatansu tana siyarwa cikin aminci da kuma rahusa, tana siyar da danƙwala-danƙwalan doya, dankalin turawa, dankalin Hausa, makani._*
_HAFSAH_
Tun da ta Billy ta ba ta wannan mummunar shawarar sai ta tashi ta ja numfashi, gami da dafe ƙirjinta wanda yake mata ciwo saboda har yanzu zuciyarta tana mata ciwo kawai yaƙi da ita take yi, musamman ma da Billy ta bata shawara.
Ko da ta yi wanka ta yi fitowar ta falo, tamkar dai ba ta yi wani laifi ba ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ɗakko lemo me sanyi a cikin fridge ta fara sha tana wani rufe ido. A lokacin ne Hamza ya fito cikin shirinsa tsaf zai tafi gidan Amminsa ya faɗa mata komi, kana ganin idanuwansa kasan ya sha kuka har ya ƙoshi. Ganinta yasa ya ƙara tsanarta, amma kuma sai ya yi turus yana mamaki ita da zai ganta cikin nadama kawai kuma sai ya same ta a zaune ta wani ɗora ƙafa ƙan ƙafa tana shan lemon tamkar na gidan uban ta cikin gadara, sannan da ya fito ko kallonsa ma ba ta yi ba ta cigaba da abin da take tana wani hira hanci ba kunya ba tsoron Allah, shi a tunaninsu tun da ta yi abin kunya za ta dinga ɓoye kanta ma a ɗaki amma sai ga ta a falo cike da gadara, sannan ya yi mamaki sosai biyo bayan yadda kawunsa ya tashi tsaye akan yaransa ya basu tarbiyya ba za ka taɓa tunanin hakan daga gare su ba, sai ga shi Hafsah ta lalata tarbiyyar ta ba tare da kowa yasan ga yadda take ba tun da ta ɓoye halinta.
Ba ta ce masa ƙala ba, haka ya sanya kansa ya fice daga gidan yana Allah wadai da halin Hafsah, ka yi abun kunya sannan ko a jikinta shi sai yanzu ne ma yake tambayar kansa anya kuwa ba ta daɗe bama a harkar yawo? To idan ba ɗan bariki ba waye zai yi abu kuma ya zo daga baya ya nuna tamkar bai yi ba? Shi dai yasan wannan mummunan hali ne wanda ƴan bariki suke yi, da ire_iren waɗannan tunanin ya ƙarasa gidansu.
A bakin parking space ya hango ƙanwarsa baby tana zance, gabansa ya bada ras_ras saboda shi a ganinsa kamar matarsa ma tsohon saurayinta ne ya lalata tun da dai yasan ba yawo take ba. Cike da fushi ya ƙarasa har in da su Babu suke, cike da gadara ya ce"ke Baby uban waye ya baki damar yin zance? Ko an sanar dani kina da saurayi ne?.
Da sauri ta juyo cike da tsoronsa kan ta a sunkuya na yara waɗanda suka jiƙo da tarbiyya, sannan ta ce"uhum uhum uhum dama...dama... Ammi ta san shi ɗan ƙawarta ne".
Shi kuwa Hafiz da sauri ya tsugunna yana gaida surukin na sa yayan budurwarsa cike da tarbiyya da kuma kunya.
Sai kuma Hamzah ya ɗan ji kunya sai ya ce" to idan kun gama zancen ka zo ka same ni za muyi magana domin ba zan yarda babu wata magana ku dinga tsayuwa ba". Ya amsa cikin ladabi da to, shi kuma Hamzah ya shige gidan cikin tashin hankali domin zuciyarsa ciwo take ta yadda aka yi ya raini mazinaciya a gidansa da kuɗinsa saboda a wannan watanni bakwai zuwa takwas ɗin duk wata abin da yake tura mata dubu ɗari takwas yake saka mata domin ko a lokacin yasan bai mata adalci ba sannan yasan ko ba komi za ta yiwa iyayenta tun da yasan ba su da ƙarfi sannan za ta siye ɗan wani kayan maƙulashe saboda haka ya tabbatar da cewa kuɗin zai ishe ta, ashe bai san ko iyayen na ta haka bata taimakawa balle ta taimakawa wani.
A falon farko y samu Ammi, tana karatun Alqur'ani sanye take da gilas fari ƙal ba ka hango komi sai kyawawan idonta domin Ammi tana daya daga cikin irin matan nan kyawawa masu capacity, farar bafulatana mai farar aniya.
Ba ta amsa masa sallamarsa ba saboda tana karatu ne, shima da ga haka sai ya zauna domin ya jira ta ya matsu ta faɗa mata zai saki Hafsah ko zuciyarsa ta huta.
Sai da ta ƙarasa surar ba ki ɗaya ta ajje Alqur'anin tana mai yin addu'ah, shima taya ta addu'ar ya yi suka shafa sannan ta alkinta alqur'anin a wata babbar dirowa me kyau wacce take jikin kusa da dining area ɗinsu.
Ta dawo ta zauna cike da ƴar damuwa ta ce"Babana lafiya kuwa na yanka a cikin damuwa? Ga idanuwanka nan ma ana ganinsu ansan kasha kuka? Me ya faru haka?.
Cikin murya marar sauti ya ce"Ammi ke kika bani ƙwarin gwuiwar auren ƴar ɗan uwanki Hafsah, don Allah ki bani dama na saki Hafsah don Allah".
Ammi ta yi saurin kallonsa cikin fushin da bai taba gani akan fuskarta ba cikin fushi ta ce"haba Hamza ka haukace ne? Ta yaya zan ba dama ka yi saki? Idan kai ba ka da hankali to ni ina dashi saboda haka ban baka dama ba ban kuma aminta ba, kuma bana son ma nasan abin da ya haɗaku kuma wallahi idan kaje ka yi gaban kanka na rantse da Allah ban yafe ba".
Tana faɗar hakan ta tashi ta bashi waje tana huci, jikinsa ya yi matuƙar sanyi tunaninsa ma shi yanzu ka da yawan jininta ya motsa don ɗan ɓacin rai kaɗan ne yake janyo mata shi, da ya sani ma bai faɗa mata ba sai kawai ta ji ya sake ta ɗin domin shi dai wallahi ba zai zauna ya saka ido a cuce sa ba, amma gudun ka da ya yi gabansa kansa ya sa dolensa ya haƙura ya zo gare ta, sannan yasan idan da ya yi gaban kansa da ya tabbatar da Ammi sai ta yi gagarumin fushi da shi domin yasan yadda take ƙaunar ƴan uwanta, yadda take ƙaunarsu ko kanta ba ta so kamar haka musamman ma Baffansu Mero wanda ya kasance abokin shawarar ta a kullum, sannan tana yawan bashi labarin lokacin da shi Hamzah yana ƙarami ta fuskanci ƙalubalen aure a gidan mijinta Baban Hamza ɗin, shi Baffansu Mero shi yake kula da duk wani al'amarinta tun daga kan abinci har kan sutura da kuɗin magani, har Hamzah ta girma bai daina hidima da su ba har Allah ya yiwa Baban Hamzah rasuwa bai taɓa gazawa ba, saboda shi baban Hamza mutun ne me aure-aure da ya ɗan samu ɗan kuɗi sai ya saki wata ya auri wata sannan babu abinci a gidansa, ita ma Ammin Hamzah ya ƙi sakinta ne saboda ya ce ita ce dama asalin matar da yake so, amma duk da haka bai daina aurensa ba to da Allah yasa Baffansu Mero me son ƙanwarsa ne sai yake ta kula da ita har ta haifi Baby bayan wasu shekaru da suka shuɗe har ana tunanin ma ta daina haihuwa ne domin sai da Hamza ya yi shekara 13 sannan ta yi masa ƙanwa Baby, wanda a yanzu shi yana da shekara 35 ita kuma baby tana da 22 domin duk ta girmi su Hafsah.
Sai da ya daɗe a wajen kamar ba zai tashi ba, sannan daga baya ya wuce wani restuarenta ya ci abinci ya daɗe ma a wajen sannan ne ta tashi ya koma gida zuciyarsa duk babu daɗi.
Ko kafin ya koma gida, tuni Hafsah ta kira Billy ta shaida mata ya fita amma tana so ta faɗa mata duk inda wannan malamin yake ta je za ta tura mata kuɗi ta karɓo mata asirin da za a rufewa Hamza baki da ido ya ma manta duk wani abin da ya faru ya karɓi ɗan da ba na shi ba, domin ita ba ta son zubarwa domin har yanzu tana jin haushi da baƙin ciki da Mero take da cikin Habibu, har yau har gobe Habibu ne muradinta abin sonta saboda haka take ta haife cikin ta dinga kallon ɗan a matsayin allon Fuskar Habibu, sannan ta ce wa Billy a haɗa har da Habibu ya daina mata taurin kai.
Billy kuwa da gudu ta ce ta turo kuɗin yanzu za ta shi ta tafi saboda ana samun layi sosai, tuni Hafsah ta tura mata zunzurutun kuɗi har dubu ɗari biyu Billy ta yi godiya ta yi wanka ta tafi.
Tana gama wayar Hamzah ya shigo, ko kallo bai ishe ta ba ta cigaba da kallo a tv ta ɗauki remote tana canja tasha cike da wani irin yauƙi wanda ita kanta bata ma san tana da shi, ga wani irin farin cikin da take ji za ta mallake Hamzah sai yadda ta yi da shi da shi da dukiyar ta sa, sannan ba iya dukiyarsa za ta raba shi da shi ba har da mahaifiyarsa ma domin tana ɗaya daga cikin mutanen da suka tsaya mata a zuciya domin tana ganin yadda yake yi wa mahaifiyarsa abu kan jiki kan ƙarfi saboda haka idan ta raba su shi kenan ita kaɗai ce za ta ji kuɗinsa sai ɗan shege dan Habibu.
_BILLY_
Tana ta murnar tsuntsu daga sama gasasshe ta wuce gidan malam Hassan me sittin, ta samu layi sosai a gidan mata kuwa tamkar ba za su ƙare ba rabi da kwatansu duk sun zo ne akan a haukata kishiyarsu ko a raba ta da duniyar, ko dai a raba su da mijin Billy ta dinga dariya domin tana jin duk hirar da matan suke yi, ta kalle su tsaf babu wata me suturar arziƙi dukkaninsu sai a hankali sannan har ma wai suke wannan asirin, ita a tuni ta asiri ai sai wanda ya ƙoshi tuni ta kalli wata mata a wajen ta ce"ke baiwar Allah ya ake yi kuma kuke samun kuɗin?.
Sai kuwa ta ce maza muke bi mana, da yake ma ina da ƙaramin goyi to babbar ƴata nake barwa ƴar na yi tafiyata hotel-hot el anan ne muke samun wannan kuɗaɗan duk da kika gani tun da su mazajen na mu sun kasa kula damu, a saboda haka sai muke samun masu kula damu duk namiji ɗaya yana iya bamu kuɗi dubu hamsin, saboda suma ai biyan buƙatarsu suke samu saboda ba ta inda Allah ya ce ayi abun suke ba ta dubura suke yi, kin ga kuwa ai ba kowa ne zai yadda ba, sannan su kuma kishiyoyin mu sai mu asirce su ba su isa wuce komi ba shi yasa muke cin karen mu babu babbaka".
Duk irin iskancin Billy ba ta taɓa rashin imani irin na waɗannan mata ba, ka ajje dan ka ke shan mama ka yi tafiyarki? Haba gaskiya dai abin ya tsoratar da ita duk da haka ba ta za ta rage abin da take ba da layi ya zo kanta ta shi ta shiga.
Tana shiga Malam Hassan ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya ce"Hahaha mutuniyar kin kasa haƙuri ko? Sai da kika biyo ni har nan? Ai da kin bari mun haɗu a hotel wallahi sai mun yi sati acan".
Ta murmusa tana mamakin mutumin matansa da huɗu, har da yara waɗanda ya aurar mata da maza amma duk matansa basu ishe sa ba ga shi da kashewa mata kuɗi kamar mahaukaci, matansa na gida kuwa da kuɗinsu suke ciyar da kansu ko yaransu su ciyar da su. Kuma yana noma sosai amma kuɗin sai dai ya ƙare wurin matan banza. Amma yadda kasan ɗan akuya haka yake sam ba ruwansa da abin da yake yi maimakon barnarsa ta ragu tun da ya aurar a a sai ma gaba da take yi.
Billy ta ce"yauwa ƙawata ce ta aiko ni wajen ka daga baya ma yi maganar sai ka faɗa min wajen da zamu haɗu tun da dai kasan ba ka da matsala dani duk inda kace inje ai dole na je tun da da kuɗaɗenka ai da rabi ka".
Suka ƙyalƙyale da dariya, sannan Billy ta faɗa masa komi sannan ya ce"to ba matsala amma aiki na gaba dole ne ta zo tun da akwai aikin da za a mata a jikinta".
Nan da nan ya haɗa komi, ya cewa Billy za a yi aiki sosai sannan ta kai mata wannan maganin a binne a ƙofar ɗakin Hamza, sannan shima Habibun asan yadda za a yi ya ci wannan abincin shi kenan sai yadda ta yi dasu. Billy ta raba kuɗin da Hafsah ta bata tun a gida domin tasan saurayinta ne zai mata aikin ba tsada ta bashi dubu ɗari sannan ta ce"to amma dai ai ka bani ko dubu hamsin ce".
Ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya ce"Bilkisu ke kin san wannan aikin don dai kawai kece amma wallahi ba don haka ba na rantse da Allah wannan aikin ko dubu ɗari biyu ba zan amsa ba, domin sai an je rafi an samo wani kifi me suna jajaye an sanya layu a bakinsa dana shi wancan Habibun dana Hamzah kin ga shi ne za ta mallakesu har abadan".
Haka Billy ta ƙyalesa ta tawo.
Da wuri Billy ta dawo, kai tsaye ta kira ta gami da cewa "na dawo daga wajen Malam amma ya ce zuwa na gaba dole ne kizo yanzu ma saboda aikin amergency ne shi yasa amma fa ya ce muddin aka yi aikin nan babu kuskure wallahi Habibu da Hamza sun zama na ki..."
Mrsgreen ce.