RU'UYAA (The dreams we never lived)

27. ... Gentle man Khalil...🖊️

by @autum17

27. ... Gentle man Khalil...🖊️



Da wani irin chilly voice kamar ƙanƙara yace '' what has my breathing got to do with you?" yawu na haɗiye ban yi tsammanin wannan tambayar daga gare shi ba...'' get out! kada ki ƙara shigo min ɗaki!" sauka yayi daga sama na..sai lokacin sanyin Ac ya bugo min...amma bai kashe zafin da jikina ya ɗauka ba...da sauri na sauka daga gadon na nufi hanyar fita

'' Ke!" Ya kira da rainin wayo tsayawa nayi nima ina tafasa nace '' k ta cikin ABCD?" shima dai sai da ya gama laguda ta shine zai wani dinga cin magani,ɗan iska kawai!

Ƙanƙantar da idonshi yayi akaina...murya ba wasa yace '' don't ever...kada ki ƙara shiga harkata...and don't try to get close to me!" 

'' oh...da farko ai na ɗauka kai kurma ne!me zanyi dakai? Mutum kullum cikin haɗe fuska kamar hadari...Hmph!" Da ƙarfi na bugo ƙofar ina ƙunƙuni kuma naji haushin kaina...da har naji tausayin shi ashe baida mutunci..'' and don't try to get close to me...me zanyi da tsoho kamar shi!" haushinsa sai ƙara ruruwa yake a zuciya ta..samun farzan nayi tsaye ya tokare ƙafa ɗaya a baya hannun shi cikin aljihu yana kallona da ido masu duhu

'' so...da gaske ne ke budurwar shi ce?"yake kallona sama da ƙasa baki tsuke Juya idona nayi '' meyasa ƙwayar idonka yake ja? Ko dai kai ma vampire ne?!" 

Na tambaya a maimakon amsa tashi tambayar 

'' answer the darn question I asked!" yayi maganar da rashin haƙuri yana hararata 

matsawa nesa dashi nayi '' damar abun banyi kama da Google ba!" na bashi amsa kafin na sheƙa da gudu ganin yana shirin damƙo ni



Bin bayan Abeedah yayi da kallo... idonshi suka ƙanƙance, '' You look like her....kina kama da ita sosai!" yayi maganar yana jinjina kai hannun sa cikin aljihu,lokaci guda kwanar bakin shi tayi sama murmushin mugunta ya wanzu a fuskarshi...
 

'' Perfect!" Ya furta da poisonous voice sannan yabar hall way...


Ɗakin Diyaam na tafi na ganta tana ƙoƙarin kama sumarta amma abun yaci tura fuskarta tayi ja '' Oh Abeedah..zoki taya ni...'' ƙarasawa nayi na karɓi tsinken daga hannun ta nayi tsagu kafin na fara kitsawa '' wai ya kuke samun dogon gashine?"

'' haka gashina yake..kona aske sai ya ƙara tsawo!" Na zaro ido aske gashi tab ɗi jam...

'' Abeedah kin taɓa son wani...? Wanda kike addu'ar samu kuna tare a koda yaushe amma duk da haka yay miki nisa?" 

Leƙa fuskarta nayi jin tambayar data jefomin '' wani kike sone?" girgiza kanta tayi amma nidai ban yarda ba '' ko Romo kike so?"

Dariya ta saki harda hawaye tace '' shi ina mashi kallon yaya ne kawai...ban taɓa jin hakan game dashi ba!"

Na gyaɗa kaina '' ni ban taɓa soyayya ba...ban ma san yanda ake jiba...amma ina so inyi experiencing karayar zuciya!"

Da sauri ta juyo tana bina da kallon ' baki da hankali'

Nayi dariya nace '' na san abinda kike tunani amma da gaske nake...ina so in san yanda ake ji idan mutum ya rabu da masoyin shi!" Na sake maimaitawa

'' Allah ya maki magani!'' 

'' Ameen...''

Bayan na fito daga ɗakin Diyaam sashen muna koma na ɗauko wayata na kira Jay d muna ta hira..daga nan na kira su Mama..na kwanta ina tunani...duk da yace in fita daga harkar shi ji nayi ina so in ƙara tsoma kaina a harkar tashi dan in bashi haushi...zai gane baya da wayo...


Bayan sallar la'asar nida su Fauziyya muna kitchen muna aikin jidar abinci kusan kala shida da masu girki suka dafa muna kaiwa a parlorn baƙi...wasu maza ne su biyar suka zo daga gani ƙawayen su Khalil ne...

suna hira tsakaninsu.. Romo ya hakimce a kujerar shi shi kaɗai riƙe da littafin drawing ɗinshi duk hirarrakin da ake bai ko ɗago ba kamar babu shi a wurin naji kamar in kwarara mashi juice ɗin dake hannuna

ashe da rabon wani daban zanyi ma wanka da juice...sanda muka shigo wurin dariya suke akan wani abu da ɗaya daga cikin maxan ya faɗa Fauziyya gaba sai wata yarinya tsakani nice ta ƙarshen shigowa....

Kun dai san Fauziyya yanda take yauƙi tana botsare botsare..ba ƙaramin kunya ta bani ba...duk cikin ma'aikatan ni kaɗai ce kesa hijabi...

Shigowar mu wurin yasa sunyi ƙasa da dariyar su suka kafe muda ido... particularly wani wanda yafi sauran baƙi naji idon shi akaina ɗagowa nayi daga juice ɗin dana tsare da ido gudun kada ya zuba dan an cika cups ɗin har baki idona ya sauka a cikin jajayen nashi...yana da kyau amma nidai mummuna ne a idona


'' Sassannun ku ina yini!" Fauziyya ta gaishe su da yauƙi '' lafiya lau'' suka amsa da fara'a


'' Biatris tana ta neman ka Rom...'' ɗaya daga cikin maxan ya ɗaura hannun shi a kafaɗar Romo

'' in mata me?" Ya tambaya batareda ya ɗago daga abinda yake ba '' well sonka take kasani fa...'' bai amsa ba ya cigaba da harkar shi

'' We have Romeo among us...'' wani daban ya faɗa

Khalil yace '' who is not Romantic!'' duka suka saka dariya...gayen nan dai har yanzu Idon shi na akaina sanda idon mu ya haɗu ya lashe baki kamar maye... tuni naji na kama da wuta...


Fauziyya take zuƙunne a gabansu tana zuba masu abincin..nida ɗayar yarinyar munja mun tsaya gefe

Sai juya idona nake...su wa'yannan mutanen basu san su Dena kallon mutum ba

'' I.B,wannan kyakkyawar mai idon mage fa?" Wani daban ya nuna ni da wani banzan murmushi a fuskar shi... murmushin Khalil ya ragu

'' Nope Auwal..kitten is off limits!''

'' shegen kaya...kace kanka kaima reservation!" Sauran suka sa dariya 

'' Allah yasa mutum ya sarƙe da abinci!" Na ɗauka cikin raina nayi maganar..sai da naga kowa ya dawo da kallon shi akaina nayi tsuru tsuru da ido


'' ke Abeedah baki da manners ko gaishe su bakiyi ba kuma kina musu mugun fata!" Fauziyya ce tayi maganar tana maƙe murya...

'' bulo aka ɗaura maki a maƙoshi ne? Naji kina magana kamar akuyar da aka shaƙe!" Fuskar ta tayi ja da fushi..na juya idona ita tasani..

Bayan ta gama iya yinta ta miƙe nida ɗayar yarinyar dake riƙe da wannan shrimps ɗin muka matsa gaba...tana tura masu suna ɗiba ni kuma ina miƙa masu juice

Da Romo na fara dan shi yafi kusa kusa...ƙin karɓa yayi kuma bai ko kalle niba,sai dana kalli mutanen wurin naga hankalin su baya kai na,na karkatar da tray ɗin ina so in zuba mashi juice a jiki ,da wabi irin murya that could freeze an entire town yace 


'' idan koda ɗigo ɗaya ya sauka akai na,sai ma maki tsirara a wurin nan!" yayi maganar hankali kwance kamar ba abun banza ya faɗa ba 

"Subhanallahi!!!!" na faɗa da ƙarfi haɗe da ja baya,juice ɗin yayi gaba zai zube,ƙafa ta ta daku da table ɗin dake wurin,kowa ya dawo da idonshi kaina na kusa faɗuwa har na Runtse ido naji saukar hannu a ƙugu na,kafin ƙamshin turaren Khalil ya cika hancina 

zuciyata na tsananin bugu na buɗe idona suka sauka cikin na Khalil dake kallona da kulawa, hannu na a kafaɗarshi, kamar daga ni sai shine a wurin...duk wani surutu da abinda mutanen wurin ke faɗa yayi nesa da kunne na as I got lost in his hazel eyes

''You'kay?'' ya sake tambaya a karo na ba adadi, da sauri na sake shi kunya tasa na kasa ɗago kaina,idon mutanen wurin sai yawo yake a kaina

suna maganganun da bana ji saboda yanda kaina ya fara ɗaukar zafi,haka ma ƙasan idona,sai na ɗago na kalli Khalil idon mu ya haɗu,ban san meya faru ba kawai na fara hawaye kafin nasa hannuna na tare fuskata ina kuka sosai 

'' hey.. it's okay..'' ya faɗa gently yana matsowa kusa, da sauri naja baya zan bar wurin,wani irin azababben ciwon dayasa nayi losing balance zan faɗi naji ya ratsani 

a karo na biyu naji hannunsa zagaye da cikina ya riƙo ni gam kafin in kai ƙasa 

'' i got you...'' ya ɗago ni sannan ya riƙe kafaɗuna muka fara barin wurin,har lokacin ban dena kuka ba sai haƙuri yake bani,ina tafe ina ɗingishi wai harda tambaya ko ya ɗauke Ni...ina hauka ne? Su Seraphina su cinye ni ɗanya

sashen shi muka wuce ya zaunar dani a ɗaya daga cikin kujerun dake parlorn ya wuce ɗakin shi sai gashi ya dawo da wani ointment,ya durƙusa gabana ya riƙo ƙafar

'' ina ke ciwo?" kasa amsawa nayi sai sheshsheƙar kuka da nake kamar zan shiɗe,hawaye na ɗiga a hannunsa,

 a nutse ya ɗago ya kalle ni,ya riƙon fuskata yana share min hawayen '' ki dena kuka kin ji,idan ciwon yayi tsanani zan iya kai ki asibiti..'' da sauri na girgiza kaina,

sannan na nuna mashi inda ke ciwon,cike da kulawa ya shafa ointment ɗin yana tausa wurin,duk da zafin da nake ji na hana kaina ihu,sai kuma na kafe shi da ido 


he looked so perfect, wannan shine gentleman ba ɗan iskan Roman ɗin nan ba... mtche*** mugun banza 


ina wannan tunanin ya ɗago,idon mu ya sake haɗuwa, zuciya ta tafara bugu da ƙarfi,sai lokacin ma na lura da yanda muke kusa kusa sosai,for some seconds babu wanda ya ɗauke nashi

sai kuma lokaci guda muka kauda kawunan mu gefe


'' uhm, kina jin yunwa?" ya tambaya tare da miƙewa,na girgiza kaina..sai ya gyaɗa kanshi,ya kai ƙofar fita daga sashen,nabi bayan shi da kallo sai kuma ya dawo ya kunna min TV 

'' you can wait here till you get better!" yayi maganar yana kallo na, nayi ƙasa da kaina dan wani irin nauyin shi nake ji haka kawai...





 da ƙarfe biyar muka taru a wurin swimming pool muna tsame ganyayyakin da suka faɗa ciki...aikin yayi min daɗi Fauziyya take harara ta a kaikaice ban ankara ba ta jefani cikin swimming pool ɗin amma kafin in faɗa sai dana jawota mu biyun muka faɗa tare...

Sauran suke bin mu da kallo...a mamakin mu sai gani mukayi suma sun afko ciki..daga aiki muka ɓuge da wasa... Diyaam tazo ta taya mu aiki na jawota muka shiga watsa ma juna ruwa babu wanda ke nutsewa cikin mu kenan dukan mu yan ruwa ne....

'' meyake faruwa anan?!" Su Seraphina ne suka iso wurin ɗaure da wasu ƙyallaye a ƙugu da breziya Innalillahi wa inna ilaihi raji'una kamar wasu kafurai...

Da gudu muka fara fita daga swimming pool ɗin kamar kifaye ruwa na tsiyaya daga jikin mu


Ƙin bari mu koma cikin gida sukayi wai mu tsaya nan sai mun bushe kuma fa akwai sanyi....babu wanda ya lura da akwai hadari cikin mu aka tsuge da ruwa suka wuce ciki suka barmu tsaye a waje

Yaran nan mugaye ne na ƙarshe...wasun mu kamar zasu suma... Mukhtar ne ya buɗe wurin da wata mai aiki maƙale a jikinshi suna abinda suke...da sauri na runtse idona na rufe ma Waleeda da DIYAAM nasu ...

Sauran ma they were shocked

'' kubar wurin nan!" Ya faɗa cike da rashin kunya da gudu muka dinga wucewa ciki wasu daga cikin ma'aikatan muryoyinsu da ɗaci nidai ina ruwa na....

Sashen mu muka wuce muna dariya na samu Mama Asabe kwance tana bacci a karo na farko salin alin na canja kaya na zauna ina rawar sanyi...da ƙarfe tara muna babban gida a kitchen nida Diyaam muna wanke wanken daya ƙi ƙarewa tsabar yawa... Heedayah ce ta bamu wannan a matsayin punishment...

'' yaran nan mugaye ne...'' na faɗa ina wanke wani ƙaton plate daya girmi hannu na

Romo ne ya shigo kitchen ɗin DIYAAM ta gaishe shi ya gyaɗa kanshi kawai,take na tuna abinda ya faɗa a parlon nan idan ka ganshi kamar na Allah ashe iskanci ne cike da cikin shi, ɗauke idona nayi daga kallon shi

wani cupboard ƙarami ya nufa ya zaro makulli daga aljihun shi ya buɗe ya ɗauki wani abu a cikin leda kamar lipton ya zuba ruwan zafi ya tsoma ciki ya koma can gefe wurin ɗauko cokali

Cup ɗin kawai na matsar daga inda ya ajiye ina share wurin .yana zuwa ya ɗauki cup ya zubar da Lipton ɗin simply saboda na taɓa....nabi shi da kallon mamaki ya sake haɗa wani yayi gaba

''baya so ana taɓa mashi abu musamman abinci ko sha...'' 

'' kaji min wani rainin wayo...'' daga nan na ƙudiri aniyar koya mashi hankali wallahi


Ranar juma'a da daddare mun aikatu ƙaton hall ɗin nan da muka share kwanakin baya muka koma muna laƙa ƙananan globes masu haske kalala...sai wasu manya manyan speaku da aka samu gogewa suma aka kai a can...abubuwan ciye ciye wa'yanda bazasu lalace ba da sauran su...ranar sai ƙarfe ɗaya mukayi bacci

Washegari muka tashi da wuri muka cigaba daga inda muka tsaya su Seraphina ansha kwalliya kamar Disney princesses...sauran ma sun ɗau ado na kece raini amma matasan kaɗai suke abinsu su Hajiyoyin na sashen su babu wacce ta leƙo


Samarin ma ba ƙarya da ƙarfe goma party ya kankama harda caterers akayi hayarin bayan wa'yanda ke dafa abinci a gida... ma'aikata sai nan da can muke bamu da lokacin hutu sai lokacin salla gida ya karaɗe da waƙe waƙe...

Cikin hall ɗin kuwa mata da maza ne ake ci ana sha ana raye raye da wasanni..suma wa'yanda aka gayyato party'n ya'yan wasu ƙwari ne a gwamnati sai jiji da kai...

Wurin ƙarfe huɗu na tafi kitchen aka turani ɗakin Mukhtar da drinks...tunda naji sunan shi Nasan ba Alkhairi zan tarar ba,ai kuwa dana shiga ban gan shiba sai da na ajiye plates ɗin zan juyo aka rungume ni ta baya ... ihu na saki yayi sauri toshe baki na ya jefani saman gado yayi tsalle zai faɗo sama na... bedside lamp na kwaɗa mashi ya faɗi gefe 


Jiki na ɓari nayi ƙofa yana biye dani a baya...

'' ba zaki tsaya ba...ki tsaya nace!" Inaaaa ban ko jishiba sai dana fita daga gidan gaba ɗaya...na isa wurin motoci na shige cikin wata baƙar mota dake buɗe na ɓoye a baya jikina na tsuma...idan fa aka Kore Ni? 

' sai ki koma gida,kina da Mama!' zuciya ta taban amsa...hawaye ne suka ciko idona dana tuna abinda Mama ta faɗa


Bada daɗewa ba naji anbuɗe gaban motar an shiga..tsoro ya hanani ɗagowa a tunani Mukhtar ne ya biyo ni...ji nayi an tada motar kafin aka ƙara gaba...gabana ya shiga faɗuwa...motar waye na shiga


Kuma da gudu ake tuƙa motar Innalillahi ni Abeedahtuwo...da ƙyar na ɗago daga duƙen da nake a baya inga ko waye...gabana ya faɗi da ƙamshin Romo ya daki hancina idona ya haɗu da ƙeyarshi

ƙasa na sake yi da kaina zuciya tana dukan tara tara...bayan tafiya mai tsawo motar ta tsaya...ɗagowa nayi naga munkawo cikin wani wuri kamar daji mai ɗauke da fulawowi...fita yayi ya zagayo ya buɗe bayan motar idon mu ya haɗu...bai nuna alamun mamaki ko akasin haka ba, abubuwan painting shi dake baya ya ɗauka yabarni a wurin...

Da sauri na buɗe ƙofa nabi bayanshi...haɗuwar wurin ya tafi da zuciya ta dama kuma ƙarfe huɗu da rabi tayi a lokacin....i couldn't believe he brought us to a meadow...duk yanda zan faɗi tsaruwar wurin bazai faɗu... ƙarƙashin wata bishiya mai ƙarancin hasken rana ya ajiye abubuwan shi,saye yake da farar riga da baƙin wando a karo na farko ya haɗa wata color daban da baƙi


hair clip ya ciro daga aljihun shi ya tattare gashin shi ya ajiye abubuwan drawing ɗinshi ya shiga aiki....

Bai yimin magana ba,bai kalli inda nake ba nima na share shi kawai...ina wasa tsakanin fulawowin na manta da abinda ya faru tsakanina Mukhtar....


Bishiyar da yake a ƙarƙashi nake zagayewa da ɗan gudu gudu ina dariya...ga sassanyan iska dake kaɗawa ƙamshin furanni na tashi na ɗauka ƙarya ne idan ana nunawa a fim yanda suke shaƙar fulawa wai tana da ƙamshi sai yanzu na tabbatar ba ƙarya bane da gaske ne....


Ƙila ya manta dani ko sau ɗaya bai kalli inda nake ba... ciyayi da fulawa na kwasa a hannuna na watsa sama '' yeyyyy!!!!!" Na saki ƙara da nishaɗi..sai dai naji idanu akaina kamar zasu huda ni da sauri najuyo naga yana kallona kamar ya mangare ni


Kallon drawing ɗinshi nayi naga ashe ciyayin dana watsa sama sun sauka akan painting ɗin


'' oh! Yi haƙuri...'' matsowa nayi kusa ina cire hakukuwan amma painting ɗin ya ɓaci sosai ƙirjin shi sai sama da ƙasa yake


'' Uhmm,ba wannan setting ɗin ka zana ba,idan ciyayi sun faɗa sama...ai duk cikin yanayin ne ko?" Na kalli hannu na daya ɓaci da kala naja baya da murmushin rashin gaskiya sai kuma na kwasa da gudu ina dariya sosai...


Sabon page ya buɗe ya fara wani drawing ɗin daban ni kuma na cigaba da wasa nesa dashi...harda cire takalmi ƙasan wurin da taushi..kwantawa nayi ina mulmula..can na miƙe jin gurnanin wani abu kafin shuke shuken dake wurin suka fara motsi kamar wani gagarumin abu zai fito

'' Ahhh!!!!!" Na saki ihu tareda yasar da hijabina gefe wani ƙaton ƙadangare ne yayi supa ya haye min saman kai


Ba burki nayo cikin Romo daya bayarda duk hankalin shi wurin zanen shi...jin ihuna yasa ya juyo nikam sai kakkaɓe kaina nake ido rufe nayo cikin shi nida shi mukayi baya baya muka faɗi,cikin painting ɗin daya sha wahala kafin ya samu ya fito...idona ya sauka cikin nashi dake ɗauke da matsanancin fushi tureni yayi daga jikinshi ya tashi zaune da sauri 


Sakin baki yayi daya fahimci ashe kwance yake saman painting ɗin bayan rigarshi ya ɓaci da kala.. painting ɗin ya dame


'' LORD GIVE THE PATIENCE!!!" Ya furta da ƙarfi...nafara ja baya...ya miƙe tsaye yana goga haƙoranshi ya nuna ni '' You!..." He was speechless sai hura hanci yaki jikinshi na rawa..na rakuɓe wuri guda duk kunya ta kamani

Gaba yayi yabarni a wurin da sauri na ɗauki hijabina nasa bayan na kakkaɓe nabi bayanshi..ba takalmi...sai tafiya yake da sauri har lokacin temper ɗin shi yaƙi ya sauka...

 Muna ta tafiya cikin daji cikin shiru...'' yanzu fa idan akwai namun daji a wurin nan?" Na faɗa ina kallon ko ina 

'' ko akwai kura?" Nayi tambayar ina kallon gefen shi

'' kasan hanya kuwa?" Na daɗa jefo tambayar bayan wani lokaci

'' idan fa dare yayi? Idan fa namun daji suka cinye mu? Idan fa muka ɓace? Idan fa aka fara ruwa?...'' riƙe kumatuna nayi idona sun kasa tsayuwa wuri guda..sai tafiya muke gashi dare na ƙara yi

Can naji kukan wani abu kamar kura

Hannun shi na damƙa a tsorace...ƙwace hannun shi yake ƙoƙarin yi na ƙara damƙe shi...'' tsoro nake ji...''

'' idan fa bamu...''


'' One more word and I will chew your lips and spit them on the ground!!!" Daga ƙarshe dai ya fashe, tohhh kun dai gani na faɗa maku mutumin nan tantiri ne,wai zai cinye min baki kai!... 

da sauri na rufe bakina,ina kallon shi ido waje,ya kamata inyi nesa da mutumin nan tunda ba mutumin arziƙi bane,sai kawai na jinjina kaina 

amma ban saki hannun nashi ba...dajin tsit babu abinda ke tashi sai kukan tsuntsaye duhu kuma ya fara sauka....

🍁🍁: baki sake shiba bakince zakiyi nesa dashi ba?

Abeedah: cikin dajin zanyi nesa dashi inje ina? nasan hanya ne?😡

🍁🍁:🤭

 

Bayan wani lokaci na sake jin motsi cikin bishiyoyi kafin wani abu mai jajayen ido ya fito daga wurin....ido waje banko tsaya naga menene ba na saki ihu nayi tsalle na haye shi fuska ta ɓoye a gefen wuyanshi, hannuna dafe da idon shi 

'' ROMAN!!!!!!"


***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️