Page 15
By
*Ummu Fadeela*
*Arewapen: ummufadeela01*
Page 15
*KANO*
Halima: tunda nabi bayan Baba na shiga gida nake kuka tamkar raina zai yi bankwana da gangar jikina. Babu wanda yace mini ci kanki a tsakanin Ummata da Baba. Ko wannensu ya shige dakinsa sun rufe da sakata. Zaune nake jikin bangon dakina na hade kai da guiwa. Tun ina kuka har karfina ya gaza na koma sheshsheka. A hankali na ja jiki da rarrafe na isa ƙofar ɗakin Umma.
Kuka ya dade da cin karfina, bani da sauran kuzari, na bude kasalalliyar muryata da ta dishe da kuka nace. "Ummata domin Allah ki bude kofa ki saurare ni. A duniya kece mutum ta farko da nake da yakinin cewa zata fahimce ni. Idan har kika rufe idanu kika gaza fahimta,kuma kika hana mini wannan damar da zan yi miki bayani, ina zan saka kaina Ummah. Idan kika gaza fahimtata waye nake dashi da zai fahimce ni a wannan duniyar Ummah. Kasa ya rufe idanun Anty Ikleema balle in tunkareta ta bani kafadar yin kuka! Ki fito dan Allah Ummah, muje ki tayani bawa Baba hakuri. Kuma inyi masa alkawarin bazan kara janyo muku magana ba Ummataaaah!"
Naja ajiyar zuciya. kukan da yafi na farko karfi yana kufce mini. Na dora kaina jikin ƙofar ɗakin ina rera kuka mai ciwon da wanda ya taba shiga kwatankwacin halin da nake ciki yanzu ne kawai zai fahimci kuncin da zuciyata take ciki.
Kamar a mafarki naji an zare sakatar ƙofar ta ciki, Umma ta bude kofar fuskarta babu alamun wasa, tana kallona ta nuna hanya. "Halima wuce ki koma inda kika fito, kafin in sauya miki kamanni da duka."
Da sauri na mike jikina yana rawa na fada jikin Umma ina kara sautin kukana, "Umma ki saurareni, ki bani listening ear kamar yadda kika saba Ummah."
Ummah bata da zabi face karbata, ta rungume ni tsam a jikinta, har a kirjina nake jiyo yadda bugun zuciyarta ke bugawa fiye da kima. Ta lumshe idanunta kam a hankali tace, "wannan ce jarabarwarmu Halima, amma meyasa kike kara tsaurara mana shi?" Na rumtse Ido da karfi ina rage sautin kukana Nace, "Na daina Ummah, na daina wallahi Allah ke nan, wannan ma ba laifi na bane. Kawai taimaka mini yayi daga masu yunkurin saceni."
Na dade ina yiwa Ummah bayanin da ta gamsu. Ummah tana da hangen nesa, tana yiwa mutum adalci a cikin dukkan al'amura. Itace dai a kanta ta rasa wannan adalcin a wajan mutanen dake zagaye da ita. Kuma wannan adalcin nasha alwashin samo mata. Ina da burin inganta rayuwarsu da Ikon Allah.
Ummah ta girgiza kai tana kallon cikin idanuna, ta kama hannuna duka biyu ta rike. Ta sassauta murya tace. "Halima ni na haifeki, kuma ni uwace. duk da banyi rainon yaya da yawa ba, amma tabbas ina amsa sunan uwa. Na san duk wani motsinki, daga yanayin tafiyarki na san har yanzu kina tare da mutuncinki baki tambadar a titi ba. Amma wannan rashin kunyar da rashin jin maganar da kikeyi shi nake so ki daina."
Dr Tareeq yana zaune a kan kujerar ofishin dpo na division din da aka kaisa, bayan umarnin da Yaya Faruk ya bayar na aje a rufeshi. Abubuwa da dama sun daure masa kai a kan lamarin yarinyar. Bata da iyayene a gidan. Gashi daga ginin gidan alama ya nuna they're well doing, meyasa suke dukanta haka?. Wannan image din na yadda ake dukanta tana kuka da bada hakuri yaki barin hoton kwakwalwarsa. Kuma ya gaza fahimtar me tayi har ta cancanci wannan hukuncin. Kamata yayi family dinta suyi murna ne ta dawo ba yanke hukunci ba.
"Ina ruwanka da lamarinta Tareeq, baka fi 3days da saninta ba, kasan asalin rayuwarta ne? Wani sashi na zuciyarsa ta tunatar dashi. Dr Tareeq ya dafe goshinsa da hannu daya a fili ya furta, "damn it! I caused her all this"
Dai-dai shigowar DPO cikin ofishin yana tura babban tumbinsa. Da sauri yayi saluting Dr Tareeq, har jikinsa yana rawa yace, "ranka ya dade kayi hakuri, yarana basu da masaniyar kai waye da bazasu taba gangancin taba ka ba. Su wadanda suka bada umarnin kamaka ma basu san kai waye bane na tabbata. Ayi hakuri yallabai. Yanzu zan hadaka da jami'anmu su rakaka har gida.
Dr Tareeq da surutun mutumin ke kara dagula mishi lissafi ya daga hannu alamar dakatarwa. Sai kuma ya mike gently ya bar ofishin, dan isowar dpo din kawai yake jira dama. motarsa ya shiga ya bata wuta. Amma duk wani dakika hoton Halima ne ke gilmawa ta cikin hoton zuciyarsa ana dukanta.
*Some hour's early*
Bayan isowar su Dr Tareeq police station din, ya bukaci zai yi waya. Ya zauna a kan dogon bencin dake reception din. Bugu daya wayar yayi aka dauka. Daddy dake zaune a gaban laptop duk da kasancewar sassafe ne yace, "Hello Tareeq, how are?" Tareeq ya dan rankwafo kansa kadan tace, "Dad I had a little issue with police, they've arrested me".
Daddy ya zaro idanunsa lokaci daya ya mike, calmly yace, "Tareeq sukayi arresting dinka for what reason" lumshe idanu Tareeq yayi ya bude, a hankali yace "Iam so exhausted Dad, ina son inje in huta zan maka bayanin komai it's not a big deal" Daddy ya yanke wayar da sauri. Dr Tareeq ya jingina kansa da bangon wajan gami da harde hannayensa duka a kirjinsa.
Da sassarfa Daddy ya shiga bangaren Dangana, ya sameta kwance a kan gadonta.
"Dangana ta mike tana hamma Bayan ya tada ita. "Da ido tayi masa tambayar ya akayi, ganin tashin hankalin dake rubuce saman fuskarsa.
"Dangana Tareeq yana hannun police yanzu ya kirani." Ta gama bude idanunta da sauri tace, "a kan me" Daddy ya sanar da ita yadda sukayi da Tareeq. Dangana ta dage kafada tana yamutsa fuska tace, "Fine"
Daddy ya fusata yace, "fine as how? Yaro yana cikin masifa kina cewa fine"
Dangana tace, "haaannn yau naga abunda ya isheni. Ba kai ya kiraba, ohk sai kaje ka fitar dashi ai". Daddy yace, "You're wicked Dangana" da sauri ta daga masa hannu tace, "kai ka koya mini wickedness din Mr Olamide" Tareeq kuma ya san kai zaka fara taimakonsa shiyasa ya kiraka first bai kirani ba. So go help your son."
Daddy yace, "Amma ai danki ne kema." Dangana tace, "point of correction, yaronka dai." Yace, da Alex ne da yanzu kin fita da kanki" tayi murmushi tace. "Ko kai baka jiba, Alex kace. Wancan kuma Tareeq, daga sunan kasan akwai bambanci, look Olamide, wannan rayuwar ka zaba mana, plsss mu tafi a yadda muka faro shi." Daga haka ta juya masa baya ta kwanta. Daddy yayi kwafa a fusace ya bar dakin.
Yana fita Dangana ta mike. Waya ta lalubo tayi kira. Cikin nutsuwa tace, "Police mess with my son in Kano. I want him to be free right now, sannan a tabbatar da an hukunta duk wanda yake da sa hannu wajan kama shi yadda ya kamata.
Daga daya bangaren aka amsa da "as you said your excellency "
Cikin minti goma aka gano division da Tareeq yake, a take aka bada umarnin sakinsa.
Lokacinda Dr Tareeq ya iso gida, wanka yayi sosai ya shirya cikin suit nashi army green. A tsattsaye ya hada cornflakes a bowl ya zuba madara mai yawa don already yayi lattin zuwa school yau. Zama yayi yana sha amma rabin hankalinsa yana kan tunanin Halima. Tambayar kansa yake, ko me takeyi yanzu"
Wayarsa tayi kara ya dauka, ganin sunan Daddy yana yawo a kan screen din ya zari tissue hadi da goge bakinsa yayi picking call din. Daddy yace, "Tareeq ka dawo gida?" Ya gyada kai da fadin, "yes Dad"
Dad ya sauke ajiyar zuciya yace, "Tareeq bana son wannan aikin naka, kawai ka dage ne. Kana da komai a nan Lagos, kana rayuwa cikin aminci just a sudden ka kirkiro wannan aikin na karantarwa Tareeq, a hakan ma kuma arewa. Tareeq I don't believe with those northerners. Gashi tun ba'aje ko Ina ba ka fara samun matsala da police. Plss Son ka dawo ka cigaba da harkokin ka a nan."
Tareeq ya sauke ajiyar zuciya with respect yace, "Iam sorry Dad, I prefer staying here, ina jin dadin rayuwata a nan. And karantarwa nakeyi, course mai girma da zai taimaki matasa da kasa baki daya. Nafi bukatar in zama independent bawai dependent ba. Komai da kake fada akwai a Lagos ai duk ni da kai mun san waye ya mallakesu."
Daddy yayi shiru yana gyada kai, a ranshi yana jin takaicin yadda Dangana ta raba mishi kan zuriyarsa. Yace, "But you have your own Son, kana da komai kaima." Tareeq ya dafe goshinsa yace, "Daddy" daddy yayi shiru, sai kuma yace , "to shikenan, tunda kana farin ciki a can. Zuwa yaushe ne contract din zai kare"
"In 5months to come Daddy" daddy yace "fine, ka kira mahaifiyarka yanzu ka gaisheta".
Tareeq ya lumshe idanunsa ya bude murya kasa kasa yace, "it is necessary Dad? Wani abu ya soki zuciyar Daddy yace, "Yes my son. Call her right now, and your brother, shima bai da lafiya. Ka kirashi".
Koda Tareeq ya yanke wayar, lambar Mother ya lalubo kamar yadda suke kiranta, ya dade yana kallon lambar kafin ya danna Kiran. Bai yi tunanin zata dauka ba, yaji ta kama.
"Morning Mother." Dangana ta amsa a takaice "Morning ya kake"
"Ina lafiya Mother"
"Good" ta fada, sai kuma dukkansu sukayi shiru. Kusan minti biyu bata ce ba shima bai ce ba. Kafin a hankali yace, "sai anjima Mother".
Kafin ya yanke ta katse shi a zafafe, "wato ubanka ya koya maka yadda zaka cigaba da mantawa dani ko. To koma ina zakaje ni Dangana nice nan na haifeka. Ka shiga matsala baka kirani ba amma shi ka kirashi. To ni din dai da ka raina ni nasa aka sakeka."
Da sauri yace, Iam sorry mother i don't mean...." Ta katseshi da fadin, "sorry for your self " ta yanke wayarta.
Ya sauke wayar yana dan murmushi kadan yace, "she can't change" layin Alex ya kira.
A hankali ya fito daga bathroom din yana sanye da farar bathrobe. Fatarsa mai kyau tana sheki ya tsaya gaban mirror. Thick wavy hair dinsa ya fara gyarawa zuwa kan dan karamin gemunsa na yan gayu. Yayi shafe shafensa as usual kafin ya taka zuwa cikin closet nashi.
Wasu kyawawan dark charcoal-grey three-piece luxury suit na kamfanin Brioni ya fitar, bayan ya sanya inners ya saka kayan wanda ya zauna masa sosai tamkar dan shi kadai akayi su. Ya makala black silk tie mai kyau.
Ya bude mazubin takalmansa. Cikin daruruwan takalma dake jere a wajan tamkar kamfani, ya dauko wasu black polished Oxford leather shoes na kamfanin John Lobb, masu sheƙi sosai.
Ya daura agogon Patek Philippe Nautilus a tsintsiyar hannunsa silver colour. Ya sa silver cross chain ɗinsa na Diamond a wuyansa da ƙaramin diamond silver earring a kunnensa daya, ya fesa turaren Creed Aventus perfume, black sunglasses dinsa ya saka dai dai lokacinda wayarsa kirar Vertu da ba kowa yake mallaka ba tayi ringing. Brother mie. Shine sunan dake yawo saman screen din. Ya dauki wayar yana magana a hankali ya bar bangarensa.
A stair case ya hadu da Mother, tana shirye tsaf cikin shirin fita office as Deputy governor she is. Kaya ne na alfarma a jikinta da tarin gwala gwalai. Dan rankwafawa yayi kadan kasancewar ya fita tsawo sosai, ya yi mata kiss a goshinta. Ta shafa kansa tace, "God bless you my dear, kayi kyau sosai."
Ya langabe kai yace, "Amen Mother, ina zakije da sassafe haka" tace, "muna da meeting da Mr governor da sauran cabinet, so I have to go early" ta sumbaci hannunsa tace, "bari ubangiji ya kare mini kai a cikin sunan yesu".
Koda Mother ta wuce a tsattsaye yasha black tea da zuma a ciki. Daddy da Mom ma gaisuwan sama-sama ya musu ya bar gidan bisa rakiyar securities dinsa.
Duk inda ya wuce cikin company din ma'aikata kasa sukeyi da kansu suna miko gaisuwa, kowa yana tsoron kada yayi laifi a koresa. Mrs Hannah secretary dinsa ta dafe kirji tana sauke ajiyar zuciya lokacinda ya wuce ba tare da ya amsa gaisuwar da take yi masa ba. Ta dan dakata tsawon 5minutes da shigansa office din kafin ta mike ta shiga hannunta rike da tab wanda akayi scheduling aiyukansa na ranar.
Kafin ta fara gabatar masa da schedules din aka bude kofar glass na office din, dukkansu suka juya suna kallon mai shigowa.