HER ORDER
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
Yana gama amsa wayar Abie ya nufi part dinsu kai tsaye. Ko lura da Azzam baiyi ba kanshi tsaye ya wuce dakinsa. Anan ya qare sauran yinin nasa yana research akan ciwon dake damun Fa'iz. With all the research da yayi ya kuma sake yi abu daya yake samu, that Alzheimer's lead to memory loss and there's no cure. Abin yana sake daure masa kai sosai especially daya kalli abinda yake jawo Alzheimer's din is not related to abinda aka ce ya jawowa Fa'iz. A severe fever is not it's symptoms. Then what could it be?
Maghrib ne ya fitar dashi daga gidan zuwa nearby mosque din dake nan gaban gidansu kadan. Bai dawo ba sai da akayi Isha sannan. A bakin gate ya hadu da Azzam da shima dawowarsa kenan.
Kallo daya Fu'ad yayi masa ya dauke kansa yana murmushi kadan. Azzam ya kureshi da kallo ganin yadda hasken wajen ya mugun haska Fu'ad din. Wani baqin ciki yazo ya tokare masa wuya, is like kyan Fu'ad shine main abinda yafi tsayawa Azzam din arai. Bafa wai shima bai da kyau ba, yana da nashi kyan though kalar fatarshi daya da Ummi wato dark skin.
"Azzam." Yaji muryarsa mai amo at the same time yana da sanyi yana kiransa. Hadiye duk abinda yake ransa yayi yana cewa "yes Hamma daga ina?"
Da hannu ya nuna masa masallacin without saying any word yana shiga cikin gidan walking majestically. Da harara Azzam ya bishi da ita yana take masa baya. Yanzu da yake bayansa sai ya samu kansa da qarewa yadda Fu'ad din yake tafiya. Wani irin tafiya yake cike da charisma, the way yake tafiya kaman ya hada jini da saurata haka da wani izza da shi kansa Fu'ad din bai san yana yi ba, although an sha fada masa idan yana abubuwansa kamar wani dan sarauta kamar komai nasa da izza haka.
"I promise I will ruin your life Fu'ad. Ban taba tsanar abu irin tsanar da nayi maka ba." Har wani daci yake ji a maqogaronsa. Wannan pure hatred din da yake masa kaman ya wuce kima har yana jin kamar ya daba masa wuqa ya mutu kowa ya huta.
Fu'ad din bai san yanayi ba. Bawan Allah hankalinsa da tunaninsa are stuck with his pal. Part din Ummi da Azzam yaga Fu'ad ya nufa yasa shi kuma ya canza hanya daga zuwa can ya koma nasu part din. Yasan lokacin dinner yayi to amman idan yana kallon Fu'ad baisan ko zai iya cin abincin ba. Bai san me yasa yaji kamar tsanar ninkuwa tayi akan da ba, don yanzu yafi jinta kuma bai jin zai iya dannewa.
Fu'ad kai tsaye daya shiga part din Ummi bai ganta ba sai ya nufi upstairs acan ma bata parlour kawai sai ya wuce bedroom dinta. Kamin ya shiga sai da yayi knocking saboda privacy. Still shiru yaji ganin ya dade sosai sai ya shiga kawai yana yin sallama. Nan ma bata nan sai kawai ya wuce ciki ya zauna agefen gadon Ummi yana rufe idonsa saboda qamshin da yake tashi a bedroom din na turaren wuta irin na 'yan Maiduguri. Ummi na son kamshi sosai just like him.
Wayarsa ya ciro a aljihu ya fara dannawa daga baya ma zamewa yayi ya kwanta akan royal bed din Ummin as daman ya saba yin haka, many times especially da rana a dakinta yake yin bacci idan yana nan. Bai wani jima yana danna wayar ba ya ajiye kawai yana saman dakin.
Ya jima a haka sosai kamin ya dauke idonsa ya juya fuskarsa mai cike da haiba zuwa order side of the room. Ahankali idonsa ya sauka kan wani clayed pot 'yar qarama mai ado sosai, daga nesa ma you can't say it was clayed saboda irin design dake jikinta. Da ido ya qure tukunyan qasan yana mamakin me yake yi a wajen don shi kadai ne a ajiye a wajen. A yadda yasan Ummi bata son shirgi sam a rayuwarta, komai nata is in order. Dakinta very simple haka yake sai dai an zuba dukiya irin mara hayaniyar nan.
Miqewa tsaye yayi zai fita sai dai bai san meye yake jan hankalinsa towards wannan pot din ba. Har ya nufi hanyar fita a dakin ya juya ya koma inda take ya tsugunna yana sake binta da kallo.
Lokaci daya yaji kansa ya wani buga har sai daya kai hannunsa ya dafe kan nasa. Miqewa yayi tsaye amman yaji kaman jiri yana dibansa kaman zai fadi hakan yasa yayi saurin kai hannunsa bango ya dafa yana loosing balance dinsa kadan kafarshi ya buge wannan pot din ya fadi qasa a take ta fashe.
Fashewarta yayi daidai da dawowar Fu'ad hayyacinsa at the same time wayarsa dake aljihunsa ya fara ringing. Wayar ya dauka yana tsugunnawa zai tattarrewa Ummi barnar da yayi mata. Amsa wayar yayi ganin Ammi ce ke kira.
"Assalamu alaikum Ammi."
Da wani irin sauri Ammi ta amsa tana cewa dashi "Fu'ad Fa'iz is back to his senses!"
__________________
RITUALS'S POV
Wani irin katon daki ne da yake nan paint dinsa gaba daya ja ne, komai na dakin ja ne hatta da launin fitila dake dakin was red. Bama iya wannan ba mutanen dake dakin sun saka red clothes ne dukansu mazansu da matansu. Sun yi da'ira ne gaba dayansu wani baqin abu da aka shafe da ja a tsakiyarsu. They're enchanting some words known to them.
"A dakata." Wani mutum da yake nan babba fuskarshi babu kyan gani sam gashi baqi ga ya shafa red abu a fuskar nasa, he was the head a wurin...
"ZUHRA." Ya faɗa da wani irin murya da bai da dadin saurare sam. Da sauri Zuhra ta daga kanta tana kallon mutumin jikinta yana rawa ta amsa da "yyyess Bonefather....."
"Wannan dan naki ya lalata komai. Ya lalata mki aiki." Jikinta yana rawa zata miqe tsaye Bonefather ya daka mata tsawa "you're breaking the rule already and you want to stand up, you want to ruin your life."
Rawar da jikin Zuhra yakeyi karuwa yayi sosai akan na da tana jin wani mugun tashin hankali.
"Danki ya lalata mana aiki kamar kin lalata mana aiki ne. Kisan abinda muke da buqata ai. Muna buqatar ki bamu jini. Kinsan wanne jinin muke buqata babu wani bayani, get lost." Da tsawa sosai ya kareshe hakan yasa a firgice Zuhra ta miqe jikinta yana wani irin rawa sosai ta fita. Wani irin gumi ne sosai yake bin jinkinta.
Tana fita ta zare red kimono data daura akan kayan jikinta ta fita daga wurin kai tsaye ta shiga motarta ta fara driving.
Ita ba sacrifice din da zata bayar ne damuwarta ba. Damuwarta aikin ta daya lalace. Wai me yasa bad luck yake bin rayuwarta ne? Tayi ma kanta tambaya. Zuwa yanzu duk wanda suke tare da ita ta tsanesu idan ka cire mutum daya. Duk da tana sonsa amman yasha bata mata duk wani abinda ta tsara.
Wani huci ta fitar a bakinta tana bugun steering motar da hannunta da qarfi ta furta "damn you BODDO. Rayuwana duk ya baci a dalilinki. Na tsaneki tsana mafi muni. I must shatter your life dake da yaranki duka sai na dandana muku baqin ciki. Well ina tayaki murnar dawowar FA'IZ cikin hayyacinsa. You ruin everything FU'AD, amman qanwarku SUHANA will pay for it, zan shayar da BONEFATHER jininta, just like yadda na shayar da jinin 'yayan yayarku SAFA, this is my prize to you guys......" Wani irin speed ta sawa motarta tafiyar da zatayi one hour tayi shi a 30 minutes. Motarta na shiga street dinsu na Fu'ad yana fita da wani mahaukacin gudu.
Wani irin burki tayi wanda da ace akwai wani a bayanta babu abinda zai hana su bugu. Da kallo tabi motar Fu'ad tana jin sabon wutar tsanar Boddo na ruruwa aranta. Ahankali taja motar zuwa gida. Ko parking batayi daidai ba ta fita daidai Azzam yana fitowa daga part dinsu ya bita da kallo ganin yadda take tafiya da wani irin sauri yasan ba daidai ba don haka ya bita a baya.
Bedroom dinta kai tsaye ta nufa da sauri, turus ta tsaya ganin wannan tukunyar qasar a fashe a qasa. Hannunta ta dunqule da karfi tana dannar zuciyarta. Dafe kanta tayi kamin ta wuce waren mirror ta zubar da komai dake dakin da ihu tace "you ruin everything Fu'ad......"
Azzam ne ya shigo da sauri sai dai ya tsaya daga baqin kofa yana jin tana cewa Fu'ad ya lalata komai. Da kallo yabi dakin kamin ya wuce cikin dakin zuwa inda Ummi take tsaye idonta jajawur. Hannunta ya riqo yana juyo da ita "Ummi me Fu'ad yayi mki?"
Da wani irin kallo tabi Azzam, sai kawai hawaye masu mugun zafi suka sauko mata a ido. "Azzam I loose again, is like duk lokacin da nayi niyyar daukar fansa akan Boddo sai komai ya rushe. Bad luck ke bina MU'AZZAM"
Janta yayi suka zauna agefen gado hannunsa yana riqe da nata. Dayan hannunsa ya kai yana goge hawayenta ya kalli hannun nasa da hawayen Ummi yake kai "Duk saboda su hawayenki yake zuba Ummi?"
Kallonsa tayi tana cewa "Mu'azzam you will not get it. Wannan duk ya samo asali daga Boddo ne. Komai da nake so Boddo ke samunsa ciki harda ALIYYU ARDO mutumin da nake masifar so!!!!!"
Baki Azzam ya tabe aranshi yana cewa "kamar dai yadda komai da nake so danki da kika fi sone yake samu."
Miqewa Ummi tayi ta fara zagaye dakin "zan shayar da Boddo baqin cikin da yafi wanda tasha akan ciwon Fa'iz!"
Miqewa Azzam yayi yana kallon Ummi yace "how Ummi? Kin sani baki da sa'a akanta fa."
Tas! Ummi ta dauke Azzam da wani irin jahilin mari tana nuna shi da yatsa tace "never call rashin sa'a for me Mu'azzam. Kar ka sake. Ina da sa'a, kuma zanyi sa'a sannan zan cigaba da samun sa'a har zuwa sanda zanga bayan Boddo."
Dafe inda Ummi ta mareshi yayi yana yi mata wani irin kallo "you slapped me Ummi?"
"Zaka rama ne MU'AZ?" Wani irin huci yake yi kawai yana girgiza kai bai ce komai ba yasa kai zai wuce ya fita Ummi ta dakatar dashi tana cewa "ina zakaje Mu'az bayan kaine wanda zaka yi min wannan aikin?"
Kallon rashin fahimta ya bita dashi ba tare da yace komai ba ya kureta da kallo.
"You will be the one to complete this mission Mu'az."
Kansa ya nuna yana cewa "ni kuma." Tace "yes Mu'az."
Tsaiwarsa ya gyara yana cewa "amman dai kinsan bana cikin wannan banzar harkar taki ko Ummi?" Harara ta zabga masa tana cewa "you must do it Mu'az ko kana so ko baka so"
Juyawa yayi zai fita yana yin tsaki kasa kasa. Sai daya bude kofa zai fita Ummi tace "ina burinka nason fin FU'AD kudi yake?" Cak ya tsaya daga fitar yana juyowa ya sauke idonsa akan Ummi "taya kika san wannan?"
"Taya bazan san burin DANA ba Mu'az? Ina burinka na son zama famous yake? Duka suna ina?"
Qasa yayi da kanshi aranshi yana ayyana taya Ummi ta fahimci yana hassada wa dan uwansa.
"I promise zan cika maka wannan burin zaka fi Fu'ad kudi." Da sauri Azzam ya kalli Ummi, ta gyada masa kai tana cewa "na tabbatar maka muddin kayi abinda nace."
"Karki kuma sakani aikata laifi irin na waccan karan! Karki kuma saka rayuwata a hadari Ummi!"
"Wannan yafi waccan sauqi Mu'az, wannan ba rai zaka dauka ba!"
Kallonta yayi yana cewa "then what is it again Ummi?"
"Rape!!!!"
Da mamaki ya maimata rape din da Ummi tace.
"Yes I want you to Rape SUHANA!!!!!!!!"
"SUHANA Ummi?"
To be continued.........
#like
#comment
#share