MEET DR JANNAH
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
Ta jima zaune acikin motar nata qirar S-Class Maybach S680. Premises din qaton asibitin take bi da kallo yadda mutane suke zirga zirga kama daga patients da staffs. Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana bude motar tare daukar labcoat dinta dake nan a goge fara kal da ita sai qamshin turaren Lattafa ke tashi ajikinta mai sanyaya zuciya. Fitowa tayi tana gyara rolling din mayafin baqar abayar dake jikinta wanda ya fito da hasken fuskarta dake nan moderate ita ba wata fara ce ba haka ma a kyau she's moderate, gayunta kawai yasa akeyi mata kallon mai kyau. Wayarta qirar iPhone 17 pro max riqe a left hand dinta tare da jakarta ta fara takawa cikin clinic din da aka rubuta sunansa boldly NOVECARE CLINIC.
Tun a hanya staffs suke gaidata a matsayinta na babbar likita a asibitin.
She's Dr. JANNAH MUHAMMAD by name. She studied MBBS + MS/MCh at AIIMS Delhi. She's 29 years old. Just as her name implies, she's a surgeon with excellent qualifications.
Office dinta ta nufa kai tsaye wanda yake nan a gyare sai qamshin air freshener ke tashi ga wani sanyi dake busowa as a result of Aircon dake office din.
Jakarta ta ajje a table tana hanging labcoat dinta a hanger. Zama tayi tana jan files din patient data gani an tula mata akan desk dinta.
She just sighed. These past three months had been somehow hectic for her. She had overworked more than she usually did.
"Get well soon, CMO." Ta fada a hankali. The Director had told her to pause from checking the patient vitals she was reviewing.
Ajiye file din tayi tana daga kanta a hankali. "FA'IZ." Ta fada slowly da wani irin karyewa a muryarta. Dan tsaki tayi tana ture abinda zuciyarta ke kawo mata sai dai hayaniyar da taji a waje yasa ta miqewa ta nufi fita kai tsaye.
Qar yafi qarfi a reception don haka ta nufi waren, sai dai tana zuwa ta kusan sumar tsaye. Shine! Dr. FA'IZ ALIYYU ARDO, MS, MCh. A consultant surgeon and founder of Novecare Clinic. He named his clinic after NoveBuild for his brother Fu'ad. Yau kimanin wata uku kenan rabon daya zo asibitin as a result of rashin lafiya daya taba masa brain. Alzheimer's, yes Alzheimer's da aka ce har yanzu bai da magani. Then how come he's standing here looking relieved?
"Ba wannan ba Jannah, murna ya kamata kiyi Allah ya bawa masoyinki lafiya." Kanta ta gyada da sauri tana yadda da zuciyarta sai dai kuma masoyi da zuciyarta ta kirashi dashi ya bata haushi. Ita ba sonshi take yi ba, she's just respecting him as the medical director he was.
Hakan yasa tayi saurin dauke idonta akansa cike da basarwa ta tsaya daga nan inda taje ba tare da ta qarasa inda yake ba. Gaba daya staffs da workers duk gaisheshi sukeyi suna tayashi murnar jin sauqi, it seems like yana da kirki wa ma'aikatansa sosai. Jannah ce kawai ba tace qala ba as a result of fighting da zuciyarta da takeyi bata ankara ba sai jin muryarsa tayi a gefe da ita tare da wannan qamshin turaren nasa Baccarat Rouge 540 daya danne turaren kowa a waren.
"Dr. Jannah." Ajiyar zuciya ta sauke a boye, she missed his voice so much.
"Dr Fa'iz.... yk... how are you?" Duka a rarrabe tayi masa tambayar. Ba tare da yayi mata kallo na biyu ba ya amsa yana wucewa elevator don zuwa office din da yake nan sak CEO's office.
Wani iska ta taking in kamin ta nufi elevator din itama. Sai dai ta jima anan kamin ta shiga saboda bata so sam su hadu ko a hanya me. Tana kwabar zuciyarta sosai akan Fa'iz. Bawai yafi qarfinta bane the fact that shekararsu kusan daya ne yake mugun saka mata a ranta cewa she's no match for him. This is our culture, wannan banzar al'adar malam bahaushe ne.
10 good minutes ta bata kamin ta shiga elevator din aranta tana cewa "abin kunya ne wannan abinda zuciya na yake kimtsamin." Bata hadu dashi ba as she expected so da sauri ta nufi office dinta. Sai dai she's not lucky don ko minti 3 ba tayi ba saiga kira from Fa'iz's secretary wai yana son ganinta.
"Dole ma nayi resigning." Ta fada tana miqewa. Har zata fita sai ta dawo baya waren standing mirror dake nan can edge din office din nata ta tsaya tana sake gyara shigarta kamar dai ta manta da abinda da take kwabar kanta akai.
Sai da ta tabbatar tayi kyau kwalliyarta bai baci ba sannan ta dawo hayyacinta. Dungure kanta tayi tana cewa "Jannah you should get back to your senses. Fa'iz is not your match. You're age mates, besides, ke kadai kike haukanki." Sai ta gyada kanta tana cewa "Yah Allah what's wrong with me." Da sauri ta juya ta fita tana qarfafa kanta ta wuce office dinsa. Sai data tambayi secretary dinsa sannan ta shiga tana wani kame kanta as a classic woman she's.
Da sallama ta shiga office din nasa dake nan very neat, the atmosphere of the office itself is soothing, not to mention the one who owns the office. Jannah bata kalleshi ba sbd tana son maintaining her class.
Kallo daya Fa'iz yayi mata yana nuna mata kujerar dake opposite to him tace "bismillah." Zuwa tayi ta zauna tana iya qoqarinta wajen hana kanta kallonsa don tayi imanin kallonsa zai rusa mata dukkan wani shirinta na fadawa soyayyarsa ne.
Kai tsaye kallonta yayi yana tambayarta dukkan wani Information na schedule din surgeries din da zsuyi tare kamin yayi rashin lafiya. Full info ta bashi wanda ya gamsar dashi that ita tayi surgery din tare da help din sauran staffs. Ya yadda da ita don bata wasa da aikinta sam. Ba wani dogon lokaci suka dauka ba ya bata izinin tafiya ta miqe ta wuce kai tsaye tana jin kamar dai dagaske yaudarar kanta take yi.
Komai a bayyane yake, son Dr Fa'iz Aliyyu Ardo takeyi. Lokacin data koma office dinta a mugun sanyaye ta zauna akan sofa dake office din.
"Allahuma Yassir Wala Tu'assir." Ta fada asanyaye. Zuciyarta ba tayi shawara da ita ba. And that's one thing about love: love doesn't need permission to start.
"He's not my match. We're the same age. I can't love Fa'iz. I need to get over it. I need to get rid of all this....." Miqewa tayi kai tsaye ta duba schedule dinta. Abinda take dashi yau, babu surgery yau sai check ups da round da za tayi don haka ta miqe ta nufi office din Dr Cynthia ta fada mata she's not feeling okay and to cover her work before she went herself to explain to the receptionist and left.
Gida ta nufa kai tsaye, aranta tana jin she has to resign if she wants to end the love she has for Fa'iz. One thing she forgets is that love doesn't ask for permission when it starts, and you can't get rid of love until love itself leaves your heart. This is a long journey for Dr Jannah........
SUHAN'S POV
Tana fita already ta tarar da driver yana jiranta don yana da timetable dinta awurinsa. Saida ta gaidashi don Ammi ta mugun basu tarbiyyan girmama duk wanda yake gaba dasu koda kuwa a qasansu yake, hakan ya mugun jawo musu qauna daga ma'aikatansu.
Shiga tayi ba tare da ta jira y bude mata ba. Zama tayi tana daukar wayarta tana jin kamar ta kira Hamma Fu'ad. Sai dai tasan ba Lallai ya daga duba da yadda ya fita yana sauri dazu tasan yana office ma maybe.
Can sai ta dago kanta tana kallon hanya. "Me yasa nakejin Hamma Fu'ad fiye da yadda nakejin Hamma Fa'iz?" Tambayar da bata da amsarta kenan.
Koda suka kai makarantar bata jira Baba Sani ya bude mata motar ba ta sake ficewa tana yi masa sallama. A bakin department dinsu ta tarar da Aira, her friend.
Da sauri suka qarasa suna rungume junansu kamar sun wani dade basu hadu ba kamin suka wuce cikin department din suka nufi lecture hall dinsu.
Basu dade da zama ba lecturer din yazo ya musu 2hour lecture ya fita bayan ya basu group assignment. Fita Suhan da Aira su kayi don zuwa printing wasu papers na presentation da zasuyi next week.
"Hana, today you look happier. Is it because Hamma Fa'iz has recovered?"
Da sauri Suhan ta kalli Aira tana cewa "laaaa, kinga na manta ban fada mki ba, Hamma Faiz ya jima sauqi jiya da dare. He's back to his normal self. But do you know what's even more exciting?"
Kai Aira ta girgiza tana cewa "sai kin fada, Hana."
Ta qanqame hannun Aira tana cewa "Hamma F ya dawo jiya."
Idanu Aira ta waro waje tana cewa "really?"
"Yes, yes." Kallonta Aira tayi tana cewa "Hana, you're in love!"
Stiff haka Suhan tayi tana kallon Aira tana maimaita abinda Aira tace kamin taja tsaki tana cewa "you're not serious, Aira. How can I love Hamma F, abah?"
"This is just the fact, Hana. You love him, and you can ask someone else if you don't believe me."
Kai Suhan ta girgiza tana janta cikin cafe din tace "let's keep this aside. I'm too young for love. I'm 16 years old."
Aira ba tace komai ba ta rabu da ita. Amman wannan abu ne da yake afili. Suhana loves Fu'ad without even knowing what love itself is.
Ba wani dadewa suka yi ba suka gama abinda suke dashi, 3 lectures sukayi kamin kowa ya tafi gida. Basu sake zance akan Fu'ad ba duk da Suhan tana son yin zancensa. Bata da zance sai na Fu'ad. Komai Fu'ad, hirarta na Fu'ad ne many times.
Time din data koma gida ta tarar da Ammi kawai agida itama bata dade da dawowa ba, she's a lecturer at Base University Abuja.
Dakin Ammi ta fara wucewa ta tarar da Ammi zaune tana duba laptop dinta sanye da farin medicated eye glasses.
Ba tayi sallama ba ta shiga hakan yasa Ammi yi mata wani kallo. Baki ta turo gaba tana komawa baya tayi sallamar da wannan muryar nata dake sake tabbatae da yarintarta.
Amsawa Ammi tayi tana cigaba da abinda take yi. A kusa da Ammi ta zauna tana dora kanta a kafadar Ammin.
"Ammi, I'm tired."
"Go and shower, Suhana."
"Ammi, I'm hungry."
Yanzu kam kallonta Ammi tayi tana kallon Suhan tace "don't you know the way to the kitchen?"
Shagwabe fuskarta tayi tana cewa "Ammi manaaa..."
"Get up, Suhan."
"Ammi, did you hear what Aira said?"
Ammi bata kulata ba don tasan shirmensu ne don halin Aira da Suhan kusan iri daya ne banbancin kadan ne kamar yadda shekarunsu yake daya.
"Ammi, she even said I'm in love with Hamma F!"
Cak Ammi ta tsaya daga typing the exam questions she was working on.
Wani irin dagowa tayi tana sauke kallonta akan Suhan dake kallonta. Quruciyar Suhan din ta fara gani zahiri.
"Did you tell her you love Fu'ad?"
Da sauri ta girgiza kai tana cewa "noooo, Ammi."
"I warned you, Suhana. This should be the last time I'll hear talk like this. This should be the last time I'll hear you talk about Fu'ad, period."
Bata rai Suhan tayi zata sake magana Ammi ta daka mata tsawa tana cewa "find your way out of here, Suhan. Leave me alone."
Da sauri Suhan ta miqe tsaye tana fita don Ammi is strict and scolding her children is like Suhan is provoking her.
Suhan na fita Ammi ta ture system din dake gabanta tana dafe kanta.
"Yah Rabbi, make it easy for us... Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un."
Shiru tayi tama rasa wanne tunani za tayi. Suhan tana shirin ballo musu ruwa ne. Tana shirin son tono abinda yake a binne 29 years back. Wani abu da mutum hudu ne kawai suka sani. Wani abu da aka rufeshi a inda akayi shi. Yau fa Suhana tana shirin ruguje komai. Ta yadda da Abbinsu da yace zai mai da ita karatu abroad, let her go and stay with uncle Farouq, maybe she will forget her feelings.........
To be continued.......
#like
#comment
#share