NURI

EVICTION NOTICE

by @saddiqahhh

NURI


By Saddiqa 


SUHAN'S POV.......

Yadda take saukowa cikin wata luxury Dubai abaya zaka dauka wata princess ce, she looks elegant sosai don ta ko'ina ta debo kyan iyayenta. SUHANA ALIYYU ARDO knn. Yarinyar dake at her 16 age take karantar architecture a Nile University Abuja. Hannunta yana riqe da wayarta qirar iPhone 17 pro max, kafarta sanye da flat shoe baqi qirar companyn Fendi. She looked elegant and classy.


Tayi kyau sosai a fuska amman sam babu wani walwala a tare da ita. She's somehow moody tun daga ranar da Abbie yace zata koma Germany da karatu and no one yayi convincing dinshi. Ta lura kaman Ammi tana goyon bayansa nema, kaman so suke tayi nesa dasu. She noticed it that.


Yau din ma Ammi ce tace ta shirya taje ta gaida Ummi don by next week In Sha Allah zata bar Nigeria, hakan yasa ta shirya da wuri don tana son zuwa wurin Ummi. Ummi over pampers her sosai fiye da Ammi, sam ba kwaba a lamarin Ummi, that's why take son zuwa. She loved being there.


Ammi ta tafi wurin aiki hakan yasa kawai wucewa tayi, driver ya kaita gidan Ummi. Da taje dinma bata sameta a parlournta na qasa ba hakan yasa ta wuce upstairs don Ummi ta basu access da komai nata. Tana sonsu kamar yaranta a zahiri, a badini kam tafi kowa tsanarsu! She was very close to her.


A zaune ta tarar da Ummi akan ottoman sofa tana typing a system, she's running her business a wani elegant and luxury boutique da ake kawo mata kaya from Dubai, China, Turkey and Qatar. The clothes are one of the best a kaf Abuja. Since she's the CEO ba ko yaushe take shiga ba. In fact ta bude boutique dinne don ya dauke hankalin mutane kar a saka mata ido, don boutique din bashi ke kawo mata kudi ba. Rituals group dinsu ke kawo mata wasu mahaukatan kudi na wuce misali. It was just a cover business.



Sallamar Suhan yasa Ummi ta dago kanta ta dubeta. Unlike ko yaushe da tana ganinta zata washe baki ta fara murmushin yaqe yau sai ta nemi murmushin sam ta rasa. Tana dubanta tana hango kamar da take da Aliyyu Ardo tsohon masoyinta! Sai taji wani abu ya tsaya mata a maqoshi, she has no reason da zaisa ba zata tsani Boddo ba. Ta kwace mata dukkan abinda ya kamata ace nata ne. She hated her deeply.



Suhan bata lura da kalar kallon da Ummi take yi mata ba, ta qarasa ta tsugunna har qasa tana gaidata. Da kyar ta hadiye abinda yaqi wuce mata, tana amsawa da kyar.


"Daughter na, how're you?" Suhan na gyara zama tace "Alhamdulillah Ummi."


"Kwana biyu baki zuwa ko Ummi tayi laifi ne."


Da sauri Suhan ta fara girgiza kai tana murmushin dake sake fidda kamarta da Abbie, tace "a'a Ummi, makaranta ne sai kuma pressure dinsu Ammi." Ta qarashe da muryar yarinta sosai.


"Me su Ammi suka yi?"


Ta marairaice tana cewa "Ummi plz talk to them... Abbie was planning to send me abroad on no reason....."


Ummi was shocked don tana da plan akan Suhan, ammn a fuskarta sam ba zaka ga hakan ba, sai mamaki data daurama fuskar nata.


"Abroad? On what reason baby?"

"There's no concrete reason Ummina."

Ummi sighed and said "ok, I will talk to Ammi then...kwantar da hankalinki kinji baby girl." Murmushi Suhan tayi tana miqewa ta zauna a gefe da Ummi tana cewa "Ummi yau baki zuwa office ne."


Kai Ummi ta gyada tana kwala kirawa maids dinta tana cewa su kawowa baby drinks da small chops while ita kuma wayarta ta jawo tayi dialing number Ammi dake zaune a nata office din tana marking script din test da dalibanta sukayi, She was a university lecturer.


Ringing farko Ammi ta amsa ganin Addarta ke kira. Sallama Ummi tayi tana tambayar Ammi lafiyarta. Murmushi Ammi tayi tana jin son Addarta yana qaruwa aranta. The way Ummi ke treating dinta kmn wata baby hakan yake sa taji kaman har yanzu Innarsu na nan. She felt cared for.


"Boddo am are you there?" Da sauri Ammi ta gyada kai tana cewa "eh Adda ya aiki?"


"Alhamdulillah Boddo. Baby tazo yanzu..."


"Ni nace tazo Adda, kwana biyu naga bata zuwa..." Tabe baki Ummi tayi yadda Suhan ba zata gane ba tace "tayimin wani zance that you guys are planning on sending her abroad... which kind of thought is that? Wa take dashi abroad da zata zauna dashi? Don't forget she's a female, she must be with her Mahram.."


Kai Ammi ta gyada kaman tana gaban Ummi ne tace "Adda there's a reason, concrete reason Adda."

"What's the reason Boddo?"

"Adda your daughter besides you loves FU'AD!!!!". Firgita Ummi tayi tana juyawa ta kalli Suhan dake scrolling a system din Ummi, hankalinta sam bai warensu.


Miqewa Ummi tayi da sauri tana wucewa bedroom dinta tace "repeat what you've just said Boddo am?"


"She loves him?"


"Shi wa?"


"Fu'ad!"


"Ya ilahi." Sai duk suka yi shiru, ita Ummi ba son da Suhan kewa Fu'ad dinne damuwarta ba, sam. Wannan bai dameta ba ko kadan. Kawai ita bata so a samu tangarda akan plans dinta ne sam. Tana da wani babban tanadi da zai quntatawa Boddo har illa Masha Allah. Don haka sam ba zata so wani abu da zai bi ta wannan plan din ba. She had her own agenda.

"Then me kuke jira bata tafi ba har yanzu?"

"Next week In Sha Allah Adda."

"Allah ya kaimu, I will convince her then." Da haka suka yi sallama. Ummi ta fara safa da marwa a dakin nata tana juya wayarta.

"Duk da haka bazan barki haka ba Boddo. Zan fara shayar dake baqin cikin tun yanzu. Kamar yadda na tsara I will destroy you and your family Boddo!!!!"


Number din Azzam tayi dialing, sai daya kusan katsewa yayi picking yana dauka ta fara da zaginsa "don ub*nka kana ina?"

Hade rai yayi yana cewa "ina office mana."

Tsaki Ummi tayi tana cewa "then Ka shirya yau zakayi min aikina?"

Kaman bai San wanne aiki bane yace "wanne aiki Ummi?"

"Our plan on Suhan!!"

Ya tabe baki yana girgiza kai, a yanzu yana da abinda yafi masa wannan abinda Ummi ke son yi don haka yace "I'm out, banyi, ki samu wani." Yana fadin haka ya kashe wayar yana turata gefe da tsaki yace "kina son ganin bayan 'yar uwarki just like yadda nake son ganin bayan danki da kike so! Ban sa kowa yayi min aikina ba, kema you can do it yourself." He refused.

Bin wayar da kallo Ummi tayi. Like irin "Mu'azzam ya kashemin waya, hell."


Kasa fitowa tayi gaba daya. She just has 2 days da Bonefather ya bata acikin week. What if bata basu jinin da suke so ba? Ihu tayi tana wurgi da wayarta don she can't even imagine the kind of loss da zatayi. Gumi ta fara yi tun yanzu kamin ta miqe taje tana duba wayarta, taga ya fashe tas ba zai sake moruwa ba. She wants to force Azzam yayi mata aikinta, if not zai ga bacin ranta. She was angry and scared.


Fita tayi tana daidata kanta ta nufi wurin Suhan da ta shiga videos dinta data tura a system din Ummi ta fara kallo abinta, idan tana gidan Ummi tana jinta kamar agida ne harma fiye. She felt safe at her house sosai.


At that time Ummi feels like kaman ta dauki wuqar dake gefen Suhan na cin abinci ta caka mata a wuya, sai dai sam ba yanzu. Ranar da burinta zai cika yana nan tafe. Ranar da zata ga Boddo cikin madawwamin qunci da bala'i! She was planning revenge.


NURI'S POV.


Suna zaune ita da Mami agaban fridge din Mami suna jera kunun aya da zobon da suka yi tare, suna dan taba hira. Kagansu sam ba zaka ce uwa da 'yarta bane, sunfi kama da Yaya da Qanwa ne. They looked like sisters.


"Mami har yanzu biyayye bai kira ba, even WhatsApp call."


"Zai kira Nuriyya, da yana nan da tuni kuna fada. Yanzu da baya nan kin isheni gaba daya." Ba wai itama Mamin bata damu bane, ta damu da Jin Afif din, shiru sai dai ba zata nunawa Nuri ba sam. Yaci ace by now ko yaya ne sunji daga gareshi since it was two weeks yanzu, amman babu kira babu saqo ko daya daga gareshi. She was worried but didn’t show it.

Knocking qofarsu da akayi yasa Nuri miqewa taje ta bude, ganin Inna yasa ta dakata tana bin Innar da kallo.

"Ko an haramta min shiga gidan dana ne?"


Kai Nuri ta girgiza da sauri tana cewa "Allah ya huci zuciyar Inna." Matsa mata tayi sai a sannan ta lura da wasu magidanta guda biyu Innar take tare. Wucewa tayi da sauri don ko dankwali babu akanta, da yake sam Allah bai saka mata son hula ko dankwali ba, gata da uban gashi irin na asalin fulani mai laushi sosai da baqi.


Tana shiga parlour ta sami hula irin Chantilly dinnan ta cusa gashin nata acikin tana janta har goshi. Mami ta miqe tsaye tana kallon Inna dake qarewa gidan kallo ta tsakar gida kamin ta shigo cikin parlourn tana cewa "bismillah Rabe shigo."

Da sauri Mami ta zira hijab dinta tana daidata kanta tace "sannu Inna."

Bata kalli Mami ba bare amsa mata tace "ya kuka gidan Sadi?"

Rabe da Sadi sai qarewa gida kallo suke suna gyada kai kamin Sadi yace "gida fa yayi Laure sosai ma kuwa."

Kai Inna ta gyada tana cewa "to nawa zaku siya yanzu da kuka ganshi?"

Rabe ya qarewa Mami kallo yana cewa "amman naga da mutane fa Laure."

Kallon Mami tayi tana dauke kai tace "af kuma Rabe. Gida fa na dana ne ina da gadonsa. Kudine bani dashi shi yasa ku siya ku bani kudina malam." Rabe da Sadi suka bi juna da kallo.

Mami bata san sanda tace "Inna idan kika siyar ina zamu zauna."

Ba tare da ta kalli Mami ba tace "sai ku bi duniya dama can ne asali."

"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un." Mami ta fada da sauri, Nuri kam tuni taji hawaye ya taru a idonta, da sauri ta koma kusa da Mami tana naniqeta da sauri.

Rabe dai yana sake qarewa Mami da Nuri kallo yace "Laure gida kam yayi mana sosai ma kuwa, kizo muje mu tsadance Sadi ya baki kudin, sannan akwai sabuwar magana fa." Ya fada yana sake qarewa Mami da Nuri kallo kaman yanda Sadi yake binsu da kallo.

"Inna ta kalli Mami tana cewa "ke ku fara tattara tsummokaranku, zuwa qarshen sati zaku bar musu gida."

"Ina takardun gidan?" Sadi ya tambayi Inna.

"Takardun gidan ai suna wurina Sadi, Audu ni yake bawa ajiyar abubuwa masu muhimmanci."


Kai Nuri ta girgiza, hawaye yana fara bin fuskarta tace "kiyiwa Allah Inna karki tashemu agidan nan. Bamu da wurin zama sama dashi."

"Ke tafi can, kibi uwarki, nace ku shiga duniya ko?"


Kai Nuri ta girgiza, za tayi magana Mami ta riqeta tana durqusawa gaban Inna ta hade hannuyenta duka biyun tace "don girman Allah Inna ki rufamana asiri kaman yadda Allah ya rufa miki asiri, ki bar mana gidan nan?"

Tsaki tayi tana cewa "Kai Sadi ku muje, raina baci yake idan ina kallon wannan jinin marasa asalin."

Kuka Nuri ta fashe dashi sosai tana rungume Mamii dake kuka sosai yau agabanta. Ya tabbata yau sunyi rashi, sunyi rashin mai sonsu Abba. Basu da madafa da jigo bayan shi. Idan Inna ta koresu ina zasu je? Me suke dashi ko wa suke dashi da zai taimakesu.....(Ni kuwa nace Allah)

To be continued......

#like
#comment
#share