WHEN EVERYONE LEAVES
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa.
Ko sake kallonsu Inna ba tayi ba ta sa kai ta wuce. Rabe da Sadin ma bin bayan Inna suka yi suna qarewa Mami da ta qanqame Nuri ajikinta da kallo.
"Wallahi ku tabbatar wani satin kun bar gidan nan na gaya muku. Audu dai na fidda ranshi. Allah ya jiqansa kawai." Ta daga murya daga waje tana sake jaddada musu kamin suka sa kai suka fita daga gidan.
For a moment duk shiru suka yi kamin Nuri ta dora kukan daga inda ta tsaya. Dama can Allah ne gatansu sai Abba, ynzu kam Allah kawai ne gatan nasu basu da wani madafa.
"Ina zamu je Mami? Me yasa Inna bata sonmu? 'ya'yan Abba ne fa mu? Anya tana son Abba kuwa?"
Mami bata iya amsa mata ba saboda yadda take faman kokawa da numfashinta. Tunanin Mami shine ina zasu je? Bata tabajin kadaici a rayuwarta da rashin dangi ba sai yau.
Ta taso rayuwarta ita kadai sai mijin dake sonta da yaranta. Mijin yau babu shi. "Ya Rabbi" ta fada aranta. Ashe dangi da 'yan uwa suna da dadi....ashe dangi da 'yan uwa suna da rana.... Yau ta tabbatar tayi babban rashi a rayuwarta. Gaba daya Mami sai taji kewar Ummanta na damunta. Kewar Innayo kakarta na dawo mata sabo. Yau da suna duniya tasan ba zata taba bangon da zata jingina ba. Zasu bata mafaka da kariya ita da yaranta.
"Su je ina wai" shine kadai abinda ke yawo akanta. Tasan Inna, farin sani ma kuwa sam bata da M daidai da sau daya gata da mugun son kanta. Ta tabbatar kudi taji bata dashi tayi wannan abun. Daman tabi abokan kasuwancin Abban duk ta amshe kudin Abban dake wurinsu ta cinye ita kadai wa ranta, ko shakka babu Zakiyya kam halin Inna ta koyo tsaf na son zuciya.
"Mami mene laifinki? Mene laifinki? Kawai saboda qaddarar da ba mu muka tsarowa kanmu ba?"
Da kyar Mami ta danni kanta tana cewa "is ok Nuriyya, karkiyi sabo please. Muyi haquri, Allah sees and is with us. Shine gatanmu...."
Da kyar Nuri ta danne kukan sai dai hawaye kam yaqi tsaya mata. Ita abinda yafi mata ciwo shine kakarsu ce Inna, wadda ta haifi Abbansu, itace take son jefa rayuwarsu cikin qunci. And this is just the beginning...........
JANNAH'S POV
Tun bayan data tura resignation letter take jiran jin kira from Fa'iz wai ko zai ce ta dawo sai dai ko sau daya. Daga Fa'iz babu kira sai su Dr Cynthia da Emanuel ke nemanta da bata haquri. It hurts her ta tuna cewa wanda tayi don shi ko nemanta baiyi. Bata gabanshi, bata cikin plans dinsa na rayuwa.
Ko da yake ita kadai daman ai take abinta. So cuta ne to Dr Jannah wanda baida magani. Da ace yana da magani babu abinda zai hanata neman maganin duk tsadarsa kuwa.
The only relieve da take samu shine miqa lamarinta da tai wa Allah. She's always praying, ta tashi da dare ta kai kukanta tasan dare lokacin amsan addu'a ne. Ko bama dare ba Allah maji roqon bawa ne.
Just like yadda Abba ya bata two weeks haka tayi qoqarin ta tsai da hankalinta akan wani Zaid dake sonta. Zai kirata zata dauka amman jin zancensa take kaman takura ko da yake to her that's what it is. Idan yace zaizo kam tayi ta bashi excuses kala-kala that's she's fully occupied bata da time din kanta.
Babu wanda ya fahimci ajiye aikinta tayi tace dasu kawai ta dauki hutu ne sai suka yarda tunda she's somehow workaholic bata gajiya sam da aikinta. Tana dakinta kusan ko yaushe tunani da soyayyar Fa'iz Ardo suna yi mata illa.
Just like everyday, yau ma tana zaune akan sofa dake dakin nata hannunta riqe da wayarta. Tana sanye cikin wani plain mustard palazzo da white chiffon top ta dora black scarf akanta qamshin lattafa yana tashi ajikinta mai sawa zuciya nustuwa.
Wayar nata take kallo, number din Fa'iz din ta shiga tana so ta kirashi, tana so ko sau daya taji muryarsa, tana so ta ganshi, tayi kewarshi, Ya ilahi.... slowly wani hawaye from nowhere kawai ya fara bin fuskarta. Bata taba sanin raguwa ce ita ba sai yau, sai yau data kasa jure son wani da namiji. Bama wannan ba, never in her life ko a imagination bata taba haskowa kanta zata so wani da bashi yake sonta ba, amman here she's, in love with wanda bai san tana yi ba.
"Ya Allah lamarina dukansa yana hannunka, Rabbi na roqeka ka ciremin Fa'iz daga raina...." Shiru tayi tama rasa me zata roqa akan Fa'iz. Ta lura the more take addu'a the more sonsa yana qaruwa aranta.
Kaman dai yanzu da zuciyarta ke azalzalarta akan jin muryarsa. Ta kasa daurewa tayi dialing number dinsa. With each ringing da wayar yake yanayi ne tare da zuciyar Jannah. She's praying Allah yasa ya dauka duk da ta sani sam Fa'iz baida wulaqanci. Sai dai kuma the thought of me za tace masa idan yayi picking ya tsaya mata arai. Da gaske bata da abinda za tace masa.
"Kawai muryarsa ya wadatar dani." Ta fada tana convincing kanta daidai Fa'iz yana amsa kiran. Jannah's heart skips at that moment, taji space din dakin yana mata kadan, kaman yadda taji nunfashinta yana son tsayawa na wucen gadi.
"Assalamu alaikum." Fa'iz said with his husky voice, akwai wani abu a muryarshi da yasa wani hawayen ya biyo fuskar Jannah, hawayen tausayin kanta.
"Assalamu alaikum." Ya sake fada jin shiru. Bin numbers dinsa da already ta haddace akanta take da kallo kamar dai ance mata Fa'iz din zai fito ta ciki. After series of sallama da Fa'iz yayi sai ya yanke kiran da taji kamar ya yanke da ranta ne.
"I love you Fa'iz." Ta fada da muryarta yana da yake yin rauni. "I love you Fa'iz with all my heart." Her voice is shaking. "I love you Fa'iz with all I have." Hatta muryarta yanzu rawa yake she then say "I love you with my soul Fa'iz." Tana ji kamar she's nothing without Fa'iz Aliyyu Ardo, kamar dai Fa'iz shine rayuwarta.
Ajiyar zuciya tayi Jin kamar muryarsa kawai da taji ya rage mata wannan kewar nashi kadan. Sai taji kamar walwalarta na kwana biyu yana dan dawowa kadan. His voice light up her mood haka nan.
Miqewa tayi tana share hawayen tare da murmushi tace "zuciyar Jannah..." Fita tayi downstairs tanajin wani kuzari tare da ita. A kitchen ta tarar da Mammansu, Mamma ta bita da kallo tana observing dinta. Ta dade da lura kaman she's not ok, ta saka mata ido ne taga iya gudun ruwanta na boye mata damuwarta. At the end tasan zata fada mata. Tasan Jannah ba yarinya bace.
NURI'S POV
The day was hectic to them, kaman dai bayan ranar da Abba ya barsu wannan shine worst day of there life....not knowing wannan mafari ne kawai. Daga Nuri har Mamin babu wani wanda yake da nutsuwa. Ita Mami damuwarta inda zasu nufa idan suka bar nan, ta zata matsalarta registration fee din Nuri ne kawai ashe more is coming. Sun haqura da kukan don sunsan ba magani bane.
Da yammar ne suka sake jin sabon bugun kofa. Nuri ta kasa fita ma kar taje Inna ce don bata san da me kuma ta dawo ba. Mami ce taje ta bude kofar. And it was Zara. Da murmushi Zara ta gaida Mami.
Itama Mamin da murmushin data arowa kanta ta amsawa Zaran. "Kwana biyu Zara."
"Wallahi Mami ayi haquri dani, amman gwara ni akan Friendy sam bata da zumunci."
"Idan nice ke ma zuciya zanyi ai Fadimatu, kullum ke kike nemanta ita bata nemanki."
Murmushi Zara tayi tana cewa "ina Mami, bazan iya fushi da Friendy ba Allah."
Tare suka shiga cikin parlourn da Mami. Nuri ta miqe da sauri tana boye damuwarta tayi welcoming Zara.
"Friendy idan ban nemeki ba ba zaki nemeni ba?"
Kai Nuri ta girgiza tana cewa "I'm very sorry best." Harararta Zara tayi kawai, zama suka yi suna sake gaisawa kamin Nuri ta kawowa Zara ruwa mai sanyi da zobo da kunun aya. Hirar makaranta kadan suka danyi wanda sam ba dadi yakewa Nuri ba.
"Finally Friendy we're leaving Kano!!" Another bombshell a rana daya. Hatta Mami da babu ruwanta da zancensu kallon Zara tayi.
"Ina zakuje Zara?" Nuri asked her kai tsaye.
"Transfer akayiwa Abba zuwa lagos."
"Harke za'a tafi kuma?"
"Yes Abba ya nemarmin transfer zuwa Unilag, wai kaina rawa yake bazanyi zaman hostel ba."
Kai kawai Nuri ta gyada, hawayen da take dannewa kar tayi ne taji ya dawo mata. Sai take jin kamar gradually wanda suke tare da ita suna barinta. It was Abba first, then Afif da yayi matuqar yi mata nisa and now it was Zara again, her best friend.
Mami ta kalla wadda tayi shiru sosai tana kallon Zara.
"Mummy zata shigo zuwa gobe idan ta samu time tayi mki sallama Mami."
"Da wuri haka?" Mami ta tambaya
"Wallahi Mami, abin ne dai kawai gashi nan."
"Allah ya sanya alkhairi Fadimatu."
"Aameen Mami."
Nuri dai tayi shiru kawai bata sake cewa komai ba.
"Friendy wallahi sai naji har na fara kewarki."
Kai Nuri ta gyada tana cewa "i donno ko zan samu wata qawar like you Zara."
Murmushi Zara tayi mata sosai tana cewa "wallahi ni nasan bazan samu kamar ke ba Nuriyya. You're a gem, so hard to find."
Rungume juna suka yi, Mami sai ta tashi kawai ta basu waje ta shige dakinta.
"Don Allah karki manta ni Friendy duk tsanani..."
Kai Nuri ta gyada mata da sauri tana cewa "i will not best, I will not In Sha Allah."
"I will not forget you too Friendy, I will not." Shiru sukayi for a moment kamin Zara ta sake cewa "so ya Afif?"
"No call or text from him."
"Haba, amman lafiya?"
"I'm praying so."
"Worry not kinsan sun fara lectures already, and karatunsa ba irin namu bane, maybe baya da time." Kai Nuri ta gyada tana jin anya biyayye zai iya zama occupied din da zai manta dasu, ita fa da Mami..... akwai matsala probably, but what could it be?
To be continued......
#like
#comment
#share