NURI

PEACE IN CHAOS

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa



Kai kawai Nuri ta gyada ma Zara dake kallonta. Sun dade tare don anan Zara tayi Maghrib kamin tayiwa Mami sallama ta tafi. Tafiyar Zara yasa gidan ya sake yin shiru. Nuri sai ta rasa wanne kalar tunani ma za tayi. Ba labari daga Afif, Zara za tayi nisa da ita, and now ga wani sabon tashin hankalin da Inna ke shirin saka su ciki ko tace ta ma saka sun, don agabansu dai akayi cinikin gidan da suke ciki

Tana zaune a parlour don anan suka yi sallah ita da Zara. Ranar ko tilawar data sabayi ma ba tayi ba kawai tana nan zaune Mami ta fito daga dakinta, ta bita da kallon tsaf tana cewa "Nuriyya?"

Da sauri ta kalli Mami tana amsawa da "na'am Mami."

"What are you thinking? You’re just staring off into space like that?" 

Kai ta girgizawa Mami kawai bata iya cewa komai ba. Agefe da ita Mami ta zauna tana riqo hannunta.

"Na sha fada mki cewa no condition is permanent ko? Allah is with us Nuri, Allah will never let us down, so karki takurawa zuciyarki da tunani kinji."

Kai ta gyada tana cewa "Mami ni tunanin biyayye kawai nkyi ba tunanin Inna ba."

Ajiyar zuciya Mami ta sauke tana cewa "Afif is no more a child, he can take care of himself, let's pray for him uhmmm." Rungume Mami Nuri tayi tanayin luf ajikinta, wani peace taji yana shigarta daga rungume Mami kawai da tayi, that motherly bond felt like a shelter.

Kanta Mami ta shafa aranta tana jin for Nuri, zata qarfafa kanta wa yarinyarta da bata da juriya. Tun dazu take faman ture damuwar Inna, bata son saka pressure wa kanta. 

Kiran Isha yasa duk suka miqe suka je suka yo alwala anan parlor suka yi sallar bayan sun idar Mami tace da Nuri taje ta dauko kayan data wanke su yi guga tunda ga wata nan. Tunda suka fara gugar basu suka gama ba sai around 9 don kayan nasu ne duka kuma suna da yawa. Suna gamawa suka ci abincin dare ba wani mai yawa ba don ji suka yi kaman basu da appetite sam, Inna ta kwashe appetite din nasu.

Daren kai tsaye idan muka ce Nuri ce tayi bacci ba muyi karya ba. Mami bata iya yin bacci ba. Sleep just wouldn’t come for her at all. Sam baccin ma baizo mata ba, tana jin kamar rayuwar da Inna ke shirin jefasu yafi qarfin bacci. The thought of idan ta koresu daga gidan ina zasu nufa ya kasa barin kanta. Idan tace haya zata kama da kudin wurinta nawa kudin ma yake bai wuce 50k ba gaba daya ga shi dama yanzu abinci awo suke yi don basu da yawa shi yasa wannan bai daga mata hankali. Makarantar Nuri ta fado mata a rai. Nan da three weeks gaba daya zasu koma, though ta san zasu iya barin registration dinsu har zuwa one month after resumption. Dole ta ture batun makarantar Nuri agefe tana dasa sabon tunanin inda zasu samu mafaka. Ba zata so Nuri tayi kalar rayuwar camp din da tayi ba. Rayuwa ce akeyi kara zube babu wani tsari da dokoki sai zallar son kai da son zuciya, kamar dabobbi. Nuri ta taso cikin gatan Abbanta, mahaifin da yake qoqari waren farantawa iyalinsa. Miqewa tayi kawai ta fada bathroom din dake dakinta ta dauro alwala tazo ta tayar da nafila ko zata samu nutsuwar zuciya.

FU'AD'S POV 

He was exhausted. It had been a long day, and he worked non-stop at the company. Wani contract suka samu daga ministan tsare tsare. Shi da Ahad, his PA, spent the whole day organizing every detail of the contract. Saboda haka they had to postpone the trip to the construction site in Kano that had already started. Har bayan 5pm suna zaune planning how everything would work. Anan sukayi Maghrib before each going their separate way, with Ahad saying he’d come to his house later to finish the rest.

Yana shiga motar ya cire tie dinsa tare da suit ya ajje agefe yana relaxing bayansa sosai ya lumshe idanunsa yana cewa "wipe down the windows." Don fresh air yake so yanzu ya dade acikin Aircon. Ko bayan da suka je gida ya dade acikin motar ya kasa fita kawai gajiya yake ji, ba fa wani zirga zirga yayi ba amman yadda ya takure brain dinsa da tsare tsare yasa yakejin ya gaji. A karshe dai dole haka ya fita yana daukar wayarsa kawai ya bar sauran abubuwansa cikin motar.

Part din Ummi ya wuce duk da gajiyar da yake ji ajikinsa. Ahankali yayi sallama da muryarsa daya koma very low yana tafiya a mugun hankali wanda kana gani zaka ce iyayi ne ko kuma ka zata wani basarake ne, da wani irin charisma haka yake tafiyar.

A zaune ya tarar da Abie da Ummi, dukda agajiye yake amman ganin Abie ya sakashi dawowar normal yana sakin fuskarsa sosai.

"Abie." Ya kirashi da wani irin calm voice yana nufar inda yake. Azzam dake zaune a qasa yana danna waya yayi wa Fu'ad wani kallo da niyyar dauke kansa sai dai ina, shigar Fu'ad was elegant, everything about him screamed luxury, everything was super expensive. Wannan kyansan mai sanyi ya dakeshi da kyau, sai yaga kamar Fu'ad yana qara kyau ne with each passing days, fuskarsa kamar yana zuwa spa kullum, beard dinsa dake nan baqiqqirin yana shining din gyara shi yafi daukar hankalinsa. Abin da yafi damun Azzam shine yadda ya lura Fu'ad din agajiye yake amman kyansa yana nan bai ragu ba sai daduwa da yayi. Ya sake karewa shigarsa kyau data tsole masa ido ya dauke kai yana basarwa. Shi kansa Azzam dake zaune bawai kayansa basu da tsada bane, shi kansa komai na jikinsa masu tsada ne, kawai dai Fu'ad ya mugun tsole masa ido ne, yana mugun so yaga komai nasu iri dayane ko yama fi Fu'ad din.

Da murmushi Abie yabi Fu'ad da kallo, yayi kewar wannan dan nasa sosai, bai tabbatar da hakan ba sai daya ganshi yanzun. A qasa kusa dashi Fu'ad ya tsugunna yana cewa "Abie barka da dare." Sumar kan Fu'ad mai yawa da santsi Abie ya dafa yana cewa "Alhamdulillah dan albarka, ya aiki?"

"Alhamdulillah Abie ya hanya, ashe yau zaka dawo ban sani ba dana ajiye aikina na daukoka ai." Kai Abie ya girgiza masa yana cewa "nasan idan kana gari aiki yana maka yawa a office ai."

Ummi dake kallonsu cike da so Fu'ad ya kalla yana cewa "afwan Ummi barka da dare." Harar wasa Ummi tayi masa tana cewa "sai daka gama gaisar da babanka ka ganni kenan Hayaty?" Kai ya girgizawa Ummi da sauri yana marairaice mata fuska kamar bashi ne wannan boss din na NoveBuild ba. "Kiyi mini Afwa Ummina, na kwana biyu banga Abie ba shi yasa."

"Nayi maka Hayaty." Murmushi yayi mai kyau yana cewa "Allah ya qara muku lafiya my worlds." Da murmushi duk suka amsa masa. 

"Hamma barka da dare." Kallonsa Fu'ad yayi yana amsawa tare da cewa "how's your work?" 

"Alhamdulillah Hamma."

"Get ready zakaje ayi maka interview Azzam. Make sure you pass. You know we don’t take anyone without passing, no matter who it is!!!"

Kai Abie ya gyada cike da burgewa yake kallon Fu'ad yana cewa "this is good son, Allah yayi albarka. Daman na gaji da ganin Azzam din yana zuwa waccan companyn, taurin kai ne dashi."

Fuska ya bata zaiyi magana Ummi ta katseshi saying "don't utter a word against their words. They've said the fact." 

Ransa yaji yana shirin baci, wato duk abinda Fu'ad yake so agidan kawai shi akeyi, amman fa inji Azzam ba inji ni ba😀. 

Shiru yayi zuciyarsa yana tafasa ta ciki amman a fili sai ya rausayar da kansa yana cewa "duk yadda kukayi....." Bai qarashe ba sai a zuciyarsa da "ba daidai bane." 

Miqewa Fu'ad yayi yana cewa "Lemme go and shower. I need to wash this stress off."

"Ka gaji Hayaty da yawa yanayinka duk ya nuna, Allah ma yasa ka ci abinci." 

Kai ya gyada mata yana cewa "naci Ummi yayi dadi." Don indai yana gari ita ke aika masa da lunch.

"A fito lafiya son." Abie ya fada. Miqewa Azzam yayi kamin Fu'ad ya fita ya rigashi ficewa fuuuu, ya lura Fu'ad yana shigowa suka manta dashi (kuji dorawa kai damuwa🤔) 

Binsa a baya Fu'ad yayi sai dai shi cike da wannan nustuwar da a komai sai ta bayyana kanta ko bai bayyana ba. Wucewa bedroom dinsa yayi babu bata lokaci ya fada bathroom ya sakarwa kansa ruwan dumi don jikinsa yana buqatarsa and yasan Ahad zaizo bada jimawa ba. Ko kamin ya fito anyi kiran Isha hakan yasan ya fito sanye da bathrobe baqa data mugun fito da hasken da Allah ya hore masa, mai daukar ido. Hannunsa daya da towel yana tsane sumarsa baqa data jiqe ta kwanta har zuwa kusa da idonsa. Gaban mirror ya nufa ya dauko lotions dinsa masu tsada ya fara bin jikinsa dashi ahankali kamar wata mace, yana tattala jikinsa sosai. Haka ya shirya cikin t-shirt sky blue na companyn Prada da jeans deep blue ya feshe jikinsa da Amouage Oud ya zura black loafers na kamfanin givenchy ya fita zuwa masallaci. Bayan an idar yayi addu'arsa sannan ya miqe ya nufo gida a qafa don babu nisa daga nan, ga wata yunwa dake damunsa.

Part din Ummi ya sake nufa inda ya tarar da Abie da Ummi a dinning, Ummi na serving dinsa. Shima zama yayi yana sake gaidasu kamar basu gaisa ba dazu. Ummi da kanta tayi serving dinsa yayi bismillah ya fara cin abincin daya mugun yi masa dadi.

Kamin ya gama sai ga kiran Ahad, yasan ya iso tunda ya kirashi don haka kawai ya zari tissue ya goge bakinsa yana miqewa.

"Ina zaka je Hayaty?"

"Ummi Ahad ne yake jirana." Kai ta girgiza tana cewa "aikin baiyi yawa ba Hayaty throughout yau abu daya za kayi kenan."

"Ummi it's urgent that's why. We need to finalize this tonight."

"Allah ya bada sa'a son." Abie ya fada Ummi tana amsawa ya sa kai ya fita. Ahad na ganin fitowarsa ya fito daga nashi motar qirar SUV. Part dinsu Fu'ad suka nufa a tare bayan sun gaisa. A anan parlour suka baje da aiki har zuwa 10 sannan suka gama. Fu'ad ya kira Ummi yace aiko musu da abinci ya bawa Ahad, da yace ma ba zaici ba Fu'ad din yayi masa wani duban sai kaci kuwa yana dauke kai. Ahad din girmi Fu'ad amman duk suna girmamashi a matsayinsa na boss dinsu......

AZZAM'S POV 

Yana shiga dakinsa yayi wurgi da wayarsa kan gado making sure it didn’t fall 😀. Zuwa yayi ya dafe mudubi yana kallon kansa da kyau.

"What did I lack? Why is Fu'ad ahead of me?" Ya fada yana bin jikinsa da kallo sosai, yaga banbanci kam sosai na halitta dake tsakaninsu. Fu'ad ko baida kyau jikinsa a gine yake with abs and muscle from exercise da yake kanyi everyday, while Azzam malalaci ne bai yin wani abin motsa jiki. 

Tsaki yayi ya juya ya koma ya zauna kan gadonsa yana daukar wayarsa yayi dialing wata number duk kuwa da cewa yana jin kiran sallahr isha da akeyi amman baima da niyyar miqewa number din da ba'a daga ba yake ta dialing.

Yaji yana son kawai ayita a wuce wurin kawai. Zai yi aiki a NoveBuild only and only if Fu'ad baya nan, baya nan ba wai yayi tafiya wani garin ba, a'a baya nan baya duniya! ko baya nan unconscious ko wani ciwon dai da zai hanashi moruwa.

Har ya fidda rai ba za'a daga kiran ba yaji anyi picking. 

"Bad ina ka ajiye wayar ne?"

Wani murya mara dadi ya amsa daga daya side din yana cewa "kasan dai lokacin shaqatawa nane yanzu ko Mu'az."

"My ass, na manta. Kai wani aiki nake so kayi min"

"Wanne aiki ne wannan?"

"Yes fuskar wani nake so ayiwa dameji gaba daya, destroy it with all means." Yanajin kamar ya fara ta haka kamin akai lokacin da zaiga bayansa.

"Mu'az ban gane ba?"

"Are you deaf bad, I want you to use acid on his face that's all!!!!!!!"

To be continued..........

#like
#comment
#share