NURI

I WILL RUIN YOUR LIFE

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa





Yau kwana hudu uku da zuwan Hjy Inna, bata sake dawowa ba tun ranar. Duk da sunsan shirun Inna ba alheri bane sam sai dai hakan yafi musu, bata sake zuwa daga musu hankali ba dukda hankalin nasu dama a tashe yake.


Suna tsakar gida Mami tana hada kayan zobonta while Nuri na gyara zogale zasu yi miyarsa ne. 


"Nuriyya kinsan me nake tunani idan har dagaske Innarku take zata saida gidan nan?"

Baki Nuri ta turo gaba tana cewa "nidai Allah Mami ki dena cewa Innarmu, Innar Abba ce kawai."



Mami bata kulata ba tayi kamar ba taji abinda tace ba tana fadin "I'm thinking zan saida wasu abubuwan na kayan dakinmu Nuriyya!"

Da sauri Nuri ta dago tana kallon Mami idanunta widely opened "for real Mami? ke da baki son sai da kayan amfani."


"Ya zanyi Nuriyya? Ina da kudin da zan kama mana wani gidan ne? Ko ina da wani kadara da zan saida ne?"


Jiki a sanyaye Nuri ta girgiza kanta tana cewa "duk yadda kika yi Mami daidai ne?" Muryarta yana breaking sosai kamar za tayi kuka.


"Don't cry for me anan, idan kukan kike sonyi tashi ki wuce dakinki sai kiyi da kyau." Ta fada tana hade rai don harga Allah kukan Nuri ya fara isarta duk da suna cikin halin da dole sai anyi kukan amman ya kamata ace Nuri ta kori dauriya.



Da sauri Nuri ta share hawayen daya biyo fuskarta tana cewa "I'm sorry Mami " dauke kai Mami tayi daga kallon Nuri tana cigaba da aikinta. Amman tana ji kamar hakan shine mafita, sam bata son tashin hankalin Inna ko sau daya. 

Ta gama tabbatar da Innar bata sonta kuma ba zata taba sonta ba, da tana saka ran wata rana zata sota amman ynzu ta gama sarewa da lamarin Innar. Bata sonta bata son jininta duk da kasancewarsu jinin danta kuwa.



Idan ta duba rayuwarta sai taji kamar qaddararta ce rasa jigon rayuwarta right from her parent. Jarabawa kala kala, tana yawan yin addu'ar Allah kada ya jarrabi yaranta da kalar nata qaddarar, Allah y sauqaqa musu qaddararsu.



Miqewa Nuri tayi da zogalen dake hannunta ta shiga kitchen don qarasa girkin da takeyi ta bar Mami ita kadai tana shirya zobonta.



Da kallo Mami tabi Nuri tana girgiza kai, bata san me yasa take ji ajikinta kamar da sauran jarabawa agaba ba. Wannan yana yawan karya mata nutsuwa. Ajiyar zuciya tayi tana fatan Allah ya dubesu. 


Afif ne ya fado mata rai, ya kamata ace by now ya nemesu. Two weeks da tafiyarsa amman shiru kakeji babu wani labari daga gareshi. Is like wayarsa is useless baida amfanin komai, tunda sun kirashi baya shiga at all. 


Tana so taji daga gareshi, tana so taji halin da yake ciki a matsayinta na uwa, uwar da takejin duk duniya su biyu kawai take dasu. Sune sanyin idaniyarta, rayuwarta a taqaice.



Ta dade da fara zuba zobon a roba kamin Nuri ta gama girkinta tazo ta fara tayata in no time suka gama suka je suka zubasu a cikin freezer.



Zama Nuri tayi tana daukar wayarta dake nan kan centre table. Missed calls from Khaleel ta gani. Ji tayi kaman tayi tsaki tana questioning kanta wanne irin dan naci ne Khaleel din. Idan itace wata take yi mata haka tana jin zuciya za tayi. Bama wannan ba soyayyar gaba dayanta bata burgeta sam, haushi take bata ita da meyi.



Sake kiranta yayi kaman yasan zancensa take yi azuciyarta, ita fa sam lokacinsa ne bata dashi. Tana da matsalolin da suke gabanta. She needs to focus on her future and the trials ahead ba soyayya ba, ba Khaleel ba, ba kowanne namiji ba! In short, maza gaba dayansu basa gabanta a yanzu.



Har kiran ya katse bata dauka ba, zata ajiye wayar wani ya sake shigowa.


"Pick that call Nuri." Tun kamin ta dago ta kalli Mami ta turo baki gaba tana karya wuya tace "number ce Mami, ni bansan waye ba?"



"Yaushe kika fara karya Nuriyya?"


Bakin ta sake turowa gaba tana tuna Mami knows them ciki da bai. Duk lokacin da suka yi karya ko suke cikin damuwa tana ganewa ko basu fada ba, kaman tana reading mind dinsu, that's why Nuri ke yawan cewa Mami is the best mother ever da mutum zai samu. She plays the exact role a mother supposed to. 




Miqewa Nuri tayi ta nufi dakinta tana picking call din Khaleel din da ta gama bashi suna headache, he never shows up sai suna cikin damuwa.


Shiru tayi bayan tayi picking din yau ko sallama ba tayi masa ba kawai tayi shiru. Shima a daya side din jin shirun sai yayi sallama. Bata da wulaqanci amman Khaleel is provoking her, tanajin kamar ta surfa masa masifa, the only problem is bata ma iya fadan ba bare tayi. She regrets me yasa bata engaging kanta cikin mutane har ta iya fada. Kamar she's an introvert haka ko yaushe bata son shiga cikin mutane that's why take nan sam bata da wani wayon arziqi, gata miskila ce idan taso.



"Ranki ya dade" ya fada yana gyara zamansa from the other side.



"Uhmmm" kawai tace dashi bata jin zata ma iya amsa masa, ko kuma miskilancin nata ya motsa akansa ne, oho.



"How're you dear?"



"Well." Tayi masa reply with short answer ne ko zai gane she's not in the mood amman sam kamar kansa yana cikin kwali haka.



"Kwana biyu, sam ba kya nemana Nuri, you never check on me idan kika jini shiru."


"Nasan lafiya." Ta fada masa kai tsaye tana hararar wayar nata kamar itace Khaleel din.



"I missed you."



"Uhmmm."



"Plz Nuri, ko sau daya ki bani dama nazo na ganki plz, ina kewar ganinki."



"Request not accepted." Ta amsa masa kai tsaye don ba wani boye boye kuma.


"Don...."


Da sauri ta katseshi kar yayi mata magiyar da zai saka ta yadda da buqatarsa na zuwa inda take.


"Khaleel I'm doing something right now, can we talk some other time?"


Shiru yayi yana jin tausayin zuciyarsa data kasa haqura da Nuri.


"Ok then as you wished." Yau Kam bata jira ya kashe wayar ba tayi saurin kashewa ta dannawa nunber dinsa block don ya kaita maqura kuma. A halin da suke ciki ba halin soyayya bane.




AZZAM'S POV 




"Are you ok Azzam? Kasan me kake cewa kuwa, I should use an acid a fuskar wani, are you this rough daman?"



"Damn you bad, are you in or not, if ba za kayi ba akwai mutane da yawa, duniyar nan da fadi take."



"Is ok, I'll do it, but kasan is very risky, how much will you pay?"



"Kudi ba matsala bane bad."


"A'a fa, kasan a kan kudi ni babu abinda bazan yi ba, rai ne kawai bazan kashe ba!!!!"



Shiru Azzam yayi for a moment, wani guilty conscience from nowhere yana rufeshi, bad babu irin bad deals din da baya yi, duk wani mugun harka yana yi amman banda kisa. Me yasa all of a sudden sai yake jin kamar bad din ma ya fishi hankali haka? Ture duka wannan tunanin yayi daga ransa yana cewa "Zan saka maka 1M."


"To hell with you and your 1M, kaga duk sanda ka shirya you can call." Yana fadin haka ya kashe Kiran.


Da sauri Azzam ya duba wayarsa yaga dagaske bad ya kashe masa waya ne. "1M yayi kadan ne?" Ya tambayi kansa.


Da sauri ya girgiza kansa yana cewa "no, haba ai nayi kokari ma, 1M fa." Mugun mammako ne dashi duk wani abu da zai fitar da kudinsa da yawa baya so. 


Tsaki yayi yana jin kamar ya haqura da deal din sai dai ina. Zuciyarsa tana hasko masa Fu'ad, yana jin kamar idan Fu'ad yana duniya, tauraruwarsa tana haskawa kamar ba zai taba nasara ba. Kamar ya kulle masa kofofin nasara haka a rayuwarsa haka yake ji. 



Sake kiran bad yayi Allah ya taimakeshi ya daga. Kai tsaye Azzam yace dashi "what's your pay?"



"10M idan zakayi idan ba zakayi ba shi kenan."



Miqewa tsaye yayi da sauri tana cewa "what? Kasan nawa kake cewa kuwa bad? 10M! A ina zan samo kudin?"


"Your brother owns the top construction company within Africa."


"Kai ba'a cin kudinsa a banza."


"Mu'azzam kai kasan wannan. All I know is my pay is 10M babu ragi sai ma qari idan 
naso don samun acid dinma sai da dabaru."




Ajiyar zuciya Azzam ya sauke yana tunanin ina zai samu har 10M don kudin account dinsa gaba daya bai haura 3M ba. 



"If you're ready you can call." Bad ya sake katse kiran for the second time.


Jefa wayar kan gadonsa yayi yana riqe kugu, "why on earth zanso Fu'ad? Maybe da babu shi da yanzu nine mai NoveBuild, da babu shi da yanzu nine favourite din Ummi, da babu shi da yanzu duniya ta sanni. "I hate you brother with all my heart."



Bathroom ya fada kawai yana jin zafi azuciya tsabar hassadar dake cinsa. Ya kasa gane kamar hassadar da yake yiwa Fu'ad din yake sake sawa ko yaushe Fu'ad din yake a samansa just like yadda yake a samansa agidan.



"I will ruin your life." Ya fadi kalmar nan yafi a kirga. Tunanin inda zai samo kudin ya farayi, yasan ko hauka yake bazai samu a wurin Ummi ba sam, don bata bayarwa sai da dalili biyu, ko zata mora ko za tayi don ta burge that's all amman bayan nan kudin Ummi baya tabuwa. Abie kam yasha amsar kudi a wurinsa da sunan business alhalin kudin a club da mata duk suke tafiya, yasan abie din zai iya sake bashi idan yayi sa'a. Fu'ad dama bai gabansa tsabar bai son Fu'ad din abu indai nasa ne baya so. Zai mori dukiyar Fu'ad ne bayan ya gama lalata masa rayuwarsa, yana ji ajikinsa kamar duk wannan fadi tashin da Fu'ad yakeyi shi yake tarawa dukiyar. Irin Fu'ad mai tarawa shi mai mora dinnan. Yana zaune wani yana yi masa labour, kamar dai he will reap what Fu'ad sow.






NURI POV 



Bata fita tana gama wayar ba sai data dan bata lokaci saboda Mami, Mami can easily understand what she does. Gyaran kayanta ta tsira data bata wardrobe dinta, ta zauna duk ta ninke su ta sake jerasu suka yi tsaf sannan ta fita.




Shiru ta tarar da Mami zaune akan kujera tayi tagumi, kamar she's lost in her thoughts. Bata taba ganin Mami in such state ba. Mami nada dauriya sosai, she never shows what's going on her mind ko da wasa amman yau ga Mami lost in whatever she's thinking.



Qarasawa warenta tayi ahankali ta zauna a qasa ta zuba tagumin itama tana kallon Mami, ga dai Mami tana kallonta amman she's not with her.



"Mami." Ta kirata da wannan muryar nata da yake da mugun sanyi, very melodious. Mami bata jita ba sai da ta sake kiranta sau uku ana ukun sannan taji.


Da sauri Mami ta cire hannunta tana gyara dankwalinta daya zame ya bayyana wannan sassalkar doguwar baqar sumar da Nuri ta gado.



"Ke lafiya kike min wannan kallon?"


Kai Nuri ta girgiza tana cewa "Mami tunanin me kike yi?"


"Ba tunani nake ba Nuriyya."



"Shi kike yi Mami, na dade a nan fa baki san nazo ba. Inna ce ko?"


Kai Mami ta girgiza tana cewa "sam ba tunanin da nke yi"



"It has to do with Inna nasan Mami."



"Afif Nuri, biyayyenki Nuriyya, shi nake tunawa."



Kamar Mami ta tabo inda yake ma Nuri ciwo don haka tayi raurau da idanu zata fara hawaye Mami ta dungure mata kai tana cewa "ke mace ce fa ke? Komai kuka, wanda ya dace da wanda bai dace ba." 



Hawayen daya biyo fuskarta tayi saurin sharewa tana kallon Mami dake harararta.



"Da ana saida hawaye hala da sai kinfi kowa ciniki, don naki arha ne dashi."


"Mami I'm missing biyayyena so much I missed fadan da muke yi, i missed tsokanata da yake yi, I missed everything about Afif Mami...........(Ko nima nayi missing Afif gaskiya😭)



To be continued.......



#like
#comment
#share