Page 4
Salim cikin tashin hankali ya lalubo wata number a wayarsa ya danna kira. Wayar ta yi ring... ring... ring... har ta gama ba a dauka ba.
Ya sake dannawa. Hannunsa na rawa.
A karo na biyu, kafin ta gama ringing na uku, an dauki wayar.
Cikin tashin hankali, muryarsa na rawa, Salim yace
"Hamma Jameel! Dan Allah... Dan Allah ka kira wayan Hamma Muhammad! Bashi da lafiya! Dan Allah Hamma Jameel!"
A daya bangaren, Jameel yayi tsam! Saboda basu dadin da rabuwa ba shida MD din. Yau sunyi meeting akan company har dare, meeting mai zafi akan sabon contract na Rolls Royce 50 da za'a kai Saudi. MD din ya fita daga meeting din fuska a hade, saboda abubuwa da suka faru wajan meeting,
Jameel yace, "Salim kana lafiya kuwa? Mai ya faru da MD din? Ka natsu kamin magana. Muna cikin waya Hamma Jameel..."
"Naji yana fadin kanshi... da alama kan na mishi ciwo sosai... Dan Allah ka kira shi..."
Jameel ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune a gidansa.
"Okay shikenan, zan kira shi yanzu. Ince dai kuna lafiya?"
Samun kanshi Salim yayi da fadin, "Lafiya lau muke Hamma Jameel."
Daga haka Salim ya yanke wayar.
Bangaren Jameel kuwa, ya kira wayan MD din. Ya kira har ya gaji amma be dauki wayan ba. Wayar na ringing, amma Hamma Muhammad be dauka ba., yana rike da kansa a saman sofa.
Hakan yasa Jameel bai jira ba. Ya dauke makulan motarsa ta Mercedes G-Wagon Brabus, ya nufi company kai tsaye. Security din dake kasa sun ga motarsa suka bude gate da gudu.
Sai da ya saka wani kati kafin ya bude kofan ya saka kai cikin office din
Zaune ya hango shi saman sofa. Ya jingina bayansa da sofan, hannuwanshi duka biyu dafe da kansa. Gashin kansa ya hargitse, suit dinsa ya jiki da zufa. Agogon Patek Philippe din dake hannunsa na haskawa.
Cikin sauri ya karasa gare shi, yana fadin cikin turanci:
"Lion! What is happening? Baka da lafiya ne?"
Ya kare maganan yana zama kusa dashi.
Kusan minti uku kafin MD ya dago kanshi. Idanuwan nan nashi gaba daya yayi jajur kamar garwashi, kamar mutum ya kwana uku baya bacci. Ya sauke idanuwan shi akan Jameel. Gaba daya jijiyoyin kanshi sun mike, sun fito a wuyansa da goshinsa.
Amma duk da haka bece komai ba.
Cikin sauri Jameel ya karasa gaban desk din da yake bayan shi, ya bude drawer, ya dauko maganin ciwon kai na musamman da likitan MD din ya ba shi, maganin da ake ba shi idan stress ya kama shi sosai.
Balla yayi kafin ya karasa wajan fridge din office din, ya dauko goran ruwa mara sanyi, ya tsiyaya a cup.
Kafin ya karasa kusa dashi ya mika mishi. Hannu ya mika, Hamma Muhammad ya karba cup din.. Jameel ya saka mishi maganin a baki kafin yasha ruwa tas ya shanye. Kafin ya dire kofin.
Ganin haka yasa Jameel ya kama shi, ya taimaka masa ya mike, ya nufi cikin bedroom din dake office din, bedroom din da ya gaji da haduwa, wanda ba kowa ne ya san akwai shi ba, sai shi da MD din.
Ya taimaka mishi ya kwanta a kan gadon. Ya ja mishi blanket mai taushi na cashmere ya rufa mishi. Kofan ya rufe mishi a hankali kafin ya koma falo.
Yana mamakin menene ya samu MD din haka., wanda rabon da yaga haka tun wasu watanni baya da suka wuce, wanda ba irin tambayan da bai mishi ba akan menene ya faru amma har yanzu bece mishi komai ba.
To wai me yake faruwa da aminin nashi haka... Gaba daya yana jin ba dadin a ranshi. Amma koma menene, zuwa anjima sai ya magantu, ko dan saboda lafiyan shi.
Jameel ya zauna a kujera, ya rike kansa.
---
GWARAM ESTATE - PART DIN MOMMY
A Gwaram Estate, cikin gidan alfarma mai hawa uku, part din Mommy
Daddyn yara zaune yake a kan kujera, kansa a kasa. Ya rame kwarai da gaske. Idanunsa sun fada ciki.
Mommy ta karaso, ta zauna kusa da shi cikin atamfa glitter purple, tana da manyan fulawuyi a jikinta, an mata dinkin A shape doguwar riga. Kanta tayi daurin dankwali mai sauki. Kwata kwata ba zaka taba gane halin da take ciki ba,
"Daddyn yara, dan Allah na roke ka kazo ka zauna ka samu ka karya. Wai baka ganin yanda duk ka rame? Bana son wannan raman naka."
Ta kasara maganan tana kai hannayenta cikin nashi, tana hadin su waje daya.
Idanuwan shi ya dago, wanda suke lumshewa irin na Jazzeelah tas, yana mai sauke su akan Mommy, wace ke zaune a bakin gado,
Ya kauda kanshi, yana tunanin irin juriya da kawaici da take dashi.
Kafin yace, "Bazan iya ci ba, Rangida. Na kasa gane meyake faruwa damu. Shin ina Ummin Baba ta samo ciki dake jikinta? Rangida na kasa gane ko mai. Gaba daya na rasa tunanin da zanyi. Wai Jazzeelah na da ciki?
Sake matsa hannun nasu tayi, kafin cikin sanyi tace, "Jarabawa ne, Daddyn yara. Allah shi kadai yasan gaskiya. Yanzu dai kayi hakuri, kace abinci. Komai zai wuce."
Ganin ta damu yasa yace, "Ki bani ruwan shayi kawai, ya isa Rangida."
Ya kare maganan da murmushi, wanda ke dauke da abubuwa masu yawa - damuwa, kunya, da kuma tsoron abin da mutane za su ce.
---
*WASHAGARI - PART DIN HAJJA KAKA - 6:00AM*
Tsaye take a gaban madubin da yake jikin toilet din bayinta, zuba ma kanta idanuwa take.
Wasu irin zafafan hawaye suna sauka daga idanuwan ta.
Jazzeelah.
Ta kasa yarda da wannan abu. Wai itace take da ciki harna tsawon wata biyar? To wai dama mutum yana samun ciki haka kawai?
Wasu hawayen ne ya sake zubowa. Ta kasa gane ko mai ji take, kamar mafarki take yi. Wani sa'in tana jin kamar ta kashe kanta, kowa ya huta. Kowa baya sonta yanzu. Kowa ya tsane ta. Kowa baya son ganin ta.
"Ya Allah!" ta fada cikin kuka.
Sake kallon kanta tayi, yanda gaba daya ta canza. Farin da tayi harya fara bata, tsuro ya fara fitowa a fuskarta. To ko dai jininta ya kare ne? Ga wani irin cika da kirjinta yayi, ga jikinta tana jin ya mata nauyi.
Ko wani hali Mommy take ciki zuwa yanzu? Wani irin kuka taji ya taso mata, tuna cewa ko dai zuwa yanzu Mommy ta tsene mata. Zuwa yanzu basan da wani bakin zata fada musu cewa ita bata taba yin zina ba, saboda tafi kowa kyamarta, kafin taji ana magana.
Ta sake saurin goge idanuwanta, tana bude kofan toilet din.
Abidah ta gani cikin tashin hankali, tana fadin da sauri, idanunta a bude:
"Jazzeelah! Hamma Muhammad ya dawo! Hamma Muhammad ya dawo daga China! Yanzu nan ya sauka
Wani irin zabura Jazzeelah tayi, tana jan baya.
Nan take cikinta yayi wani irin murdawa mai tsanani! Wani ciwo mai kama da mashi ya soke ta a mararta!
San taji wani abu na bin kafafunta, mai zafi...
Idanunta ta kai kasa tare da Abidah da ta kai hannu ta rikota, ganin irin zaburan da tayi.
Idanuwan su biyu ya sauka akan jinin daya biyo kafafunta.
Jini. Jini mai yawa. Ja-jajir.
Jinin da ke fitowa daga jikinta yana malala a kasa.
Abidah ta fashe da wani irin ihu mai tsanani wanda ya girgiza gidan gaba daya!
"Hajja Kaka! Mommy! Ku zo! Jazzeelah! Jinin... Jini...!!!"
Masu bukatar a musu tallah zaku iya tuntubana ta wannan number 👉*** MRS CLASSY WRITE nagode🙏