RABO DA KADDARAFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

RABO DA KADDARA

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

--- ⚜️ *RABO DA KADDARA | AREWA PEN* ⚜️ ✍️ Marubuciya: MRS CLASSY WRITE 📖 Labari mai taba zuciya | Tausayi | Kaddara *DOKOKIN PAGE DIN NAN:* 🚫 Ba'a yin zagi a comment 🚫 Ba'a satar labari ba tare da izini ba 🚫 Ba'a tura link na *** ba ✅ Ku yi LIKE, COMMENT, SHARE don karfaf...

More from @mrsclassywrite

Sample · Page 1

⚜️ *RABO DA KADDARA* ⚜️_Marubuciya: MRS CLASSY WRITE__Page 1_Wani irin karan mari ne yake tashi a cikin falon, har sai da kunnuwan kowa suka yi ruri.Duk falon ya dauki wani irin shiru mai ban tsoro. Shiru da zaka ji bugun zuciyar kowa. Sai karar AC kadai ne yake tashi a hankali, tare da shekarar kukkan da take kokarin boye wa a tsakiyar makoshinta.Fatima ta dafe kuncinta da hannunta daya. Idanunta sun ciko da hawaye, amma ta ki barin su su zubo. A gabanta, Baba ne a tsaye. Fuskar sa ta hade, idanunsa sun yi ja-jawur kamar saboda tsananin bacin rai ya cinye zuciyarsa."Dan ubanki!" Ya sake daka mata wata tsawar. Muryarsa na rawa. "Nace miki cikin uban waye a jikinki yanzu Fatima? Da abin da kike so ki saka min kenan ko tukuicin da zaki bani kenan?"Kalmomin nasa kamar wukake ne a zuciyar Fatima. Jikinta na rawa.Ta kasa magana. Harshenta ya makale. Wani irin tari mai tsanani ne ya taso mata daga kirji, tana kokarin tari amma hawaye ne ke fitowa maimakon sauti.A gefe, Salim ne ya mike cikin sauri. Amma tsoro ya bayyana a fuskarsa. Ya nufi Baba, ya kama hannunsa."Baba, dan Allah kayi hakuri. Dan Allah. Idan kun bi ta a hankali zata yi magana. Dan Allah Baba..."Baba bai kalle shi ba. Ya ture hannun Salim din.A can tsakiyar gefen falo, a kan kujera mai laushi, Mommy ce zaune. Tana kallon kasa, hannunta na wasa da zane. Ita ma ta kasa magana.Amma Abidah... Abidah da take zaune a kasa kusa da Mommy, ita ce ta kasa jurewa.Cikin wani irin sauri, ta mike. Kuka ne ya kwace mata, kuka mai cin zuciya, kuka na tausayi da takaici. Ta nufi Fatima, ta rungume ta da karfi a jikinta. Ta damke ta kamar zata kare ta daga duniyar da ke son ta cinye ta."Fatima..." Ta fashe da kuka. "Kada ki yi shiru, dan Allah ki yi magana. Me ke faruwa dake? Waye yayi miki haka?"Fatima ta jingina kanta a kafadar Abidah. A wannan lokacin ne duk hawayen da ta boye suka sauko. Ta fashe da wani irin kuka, kukan da ya girgiza falon. Kuka ne na mace daya tilo da ta rasa mafaka. Kuka ne na tsoro, na kunya, da nadama.Kanta a kasa tace, "Bansan cikin nan na waye ba..."Kowa a falon ya tsaya cak. Saboda jin abinda ta fada.Baba ya ja da baya kamar an harbe shi. Mommy ta dafe kirji.Yaya Bilal! Ya kasa jurewa,Wanda tun dazu yake hade rai a kofar falo, ya shigo cikin falon da wani irin gudu. Idanunsa sunyi jajir, jijiyoyin wuyansa sun tashi saboda bacin rai."Me kika ce? Baki san na waye ba?!" Ya daka mata tsawa, muryarsa na rawa. "Kin zama karuwa kenan a cikin gidanmu? Kin bata mana suna? To yau sai jikin ki ya gaya miki!"Kafin kowa ya ankara, hannunsa ya nufi wandon da yake jikinsa. Ya cire belt din fata mai kauri da yake daure da shi."Bilal! Kada ka aikata!" Salim ya yi ihu yana kokarin kamashi, amma Bilal ya tureshi da karfi har ya fadi a kan kujera.Ya daga belt din sama."Yau sai kin mutu ko kin fadi ga...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium1
02

Page 2

Premium
Updated 3 hours agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play