THE FIRST CALL FROM GERMANY
by @saddiqahhh
NURI
By saddiqa
AFIF'S POV
Zaune yake a Library din makarantar yana duba wani text book. Gaba daya attention dinsa yana kan littafin da yake duba wani abu da aka basu assignment ne. Shi kadai ne a edge din wurin hakan yasa wurin yake nan shiru babu wani hayaniya sam. For almost 30 minutes, yana zaune yana tara points da ya samu ya zauna duk yayi jotting a wani qaramin littafi.
Bayan ya gama ya miqe ya maida littafin yana juyowa zai tafi. Ya canza sosai fiye da yadda ya baro gida. Daman fari ne ammn ya qara wani hasken anan sakamakon weather din garin da yake da dadi sannan daban da namu. Sai dai a fuska ya fada sakamakon ba wani abincin kirki yake iya ci ba don bai saba da abincinsu ba, yafi cin junk foods. Sai few times da ya siyo kayan girki yayi da kansa don ya iya girkin sanda yake gida yana tayasu Nuri.
Fitarshi ba dadewa ya hadu da Zachariah abokinsa. Ba wai yana sakar masa fuska ba kawai Zach din yana mugun son Afif ne shi yasa yake yawan shisshige masa. Tun Afif yana basar dashi har ya fara kulashi kadan kadan. Tun da Afif din yazo Munich gaba daya ya sauya. Ya koma so silent kamar ba shine wanda yake takurawa kowa agida ba. Ko Zach din ba wani magana suke ba don zai iya zaman fin awa ba tare da ya kulashi ba.
Yayi loosing wayarsa ne ranar da yazo Germany, bai san a ina ta fadi ba ya dai fito daga cab din daya kawoshi apartment din daya kama ya tarar babu wayar. Hankalinsa ya tashi sosai don bai san yadda zaiyi ba kuma, yana son communicating dasu Mami amman babu waya. Haka dole ya haqura ya kwana ranar babu waya da niyyar washegari zai bincika inda ake saida wayar.
Da ya bincika washegarin sai yaga kudin warensa ba zai sai masa waya ba tunda zaiyi amfani dasu a sauran harkar makaranta da abinci. Don haka ya yanke shawarar ko aiki zai fara nema. Bai fara neman aikin ba sai bayan da ya fahimci yadda garin yake tukunna and he was a little bit busy with lectures..
Sai after one week dinnan ya fara neman aiki da kyar ya samu wani cafe ya samu da kyar da taimakon Zach. Zach din da kansa ya roqa masa aikin suka bashi. Hakan yasa yake dan kula Zach din tun baya sakewa dashi har ya fara sakewa dashi. Daga baya da suka dan saba shhine har suka gane makaranta daya ma suke yi kawai suna different department ne sannan Zach yana aji biyu ne while Afif yana daya.
"How far? I've been looking for you Afif. Where have you been?"
Library din kawai Afif ya nuna masa da hannu yana shirin wucesa zach din ya take masa baya yana cewa "You're so annoying Afif. I feel like punching you."
Juyowa Afif din yayi ya masa kallo daya kawai ya sauke kansa yana cewa "Go ahead and do it, Zach." Murmushi Zach yayi yana daidaita tafiyarsu suka jera tare. Wurin sai da waya suka nufa don Zach din dama ya tambaya inda ake samun wayar shine yace zai rakashi.
Cab suka tsare suka hau suna yi masa bayanin inda zai kaisu. Afif was silent while Zach yana bashi labarin yadda akayi expelling wani student last year. Har suka karasa Afif was silent sai da Zach din ya gaji ne yayi masa shiru yana harararsa, sai a sannan Afif yayi masa murmushi yana cewa "If I'm annoying, then what are you, Zach?"
Fita Zach yayi without responding to him, shi ya biya kudin cab din suka karasa mall din da ake saida wayoyi na different types. Daidai kudinsa Afif ya dauka bayan yayi signing wasu takardu na shaidar siya sannan suka fito already ya riga da ya sai SIM card. Apartment dinsu suka koma don a same apartment suke zama. Kawai Allah ya hada jininsu irin sosai dinnan. Suna zuwa Afif ya shiga toilet dake nan parlour ya daura alwala don it's already Zuhr time.
Ya fito ya shimfida sallayarsa dake can corner edge din dakin ya tayar da sallah while Zach ya kwanta yana danna waya. Har Afif ya idar da sallar Zach yana kwance yana danna wayarsa don yana game ne. Miqewa Afif yayi yazo zai dauka wayar ya saka a caji ya tarar Zach ya riga da ya saka masa.
Murmushi kawai yayi, Zachariah yana da kirki sosai that's why Afif yake kulashi sannan yana da mugun kai don shi zallar civil engineering yake yi and he's assisting Afif sometimes.
Zama yayi yana kallon Zach yace "What are you eating, Zach?"
Hankalinsa yana kan wayarsa yace "I'm full for now Afif. Maybe later."
Kai Afif din ya gyada yana miqewa tsaye yaji anyi knocking musu kofa. Fasa nufar kitchen yayi ya juya yaje ya bude kofa. Akan wata farar baturiya dake nan kamar zabiya idon Afif ya sauka. Lokaci daya ya kankance idanu yana mata wani kallo more like harara.
"Hi, handsome."
"What brought you here Alissa?"
"I've come all the way here to see you, handsome. Can we talk, please?"
Yanzu kam harararta yayi yana cewa "I don't have time for you Alissa. Who gave you my address?"
"It was your friend, Zach."
Kai ya gyada yana cewa "Okay, bye." Ya fada yana rufe kofar ya juya a fusace ya koma ciki. Kai tsaye wurin Zach ya nufa yana zuwa ya fisge wayar Zach din yana cewa "Why the hell did you give that girl my address, Zach?"
A fusace shima Zach din ya miqe yana fisgar wayarsa yace "Fuck you Afif. I'm tired of all this drama. I'm not like you. Why should they be using me as a stepping stone?"
"Fuck you too, Zachariah. This should be the last time, wallahi."
"I will still give your address to whoever asks for it."
"Then I will cut ties with you."
"To hell with you and your ties." Ya fada yana komawa ya kwanta abinsa ko ajikinsa. Basu dade da haduwa ba amman sun saba irin wannan fadan daman. Ko wacce rana sai sunyi fada indai akan mata ne. Afif din yana da farin jinin mata sosai don kowa acikin department dinsu dama outside there department suna crushing akansa while shi kuma Zach bai son takura that's why yake bawa duk wadda ta nema address dinsa. A addininsu Zach da al'adarsu hakan ba komai bane while Afif hakan is totally haram a nasu addinin da al'ada, ko bama wannan ba, karatu shine abinda ya kawoshi Munich ba 'yan mata ba.
Kitchen ya wuce yana cewa "I'll chase you out of here if you do it again." Banza Zach yayi masa kaman baiji abinda yace ba. Shima bai sake kulashi ba ya fara hada ingredients din dafa noodles don shine very simple musamman yanzu da yake jin yunwa. It only takes him 10 minutes ya kammala yayi serving kowa a nasa dish din ya fito ya ajiyewa Zach akan centre table yana cewa "Put your phone down Zach, and eat."
Kallonsa Zach yayi, wannan caring attitude din yana daya daga cikin abinda yasa Afif yake burgeshi sosai. Ga yadda sam baya takura masa akan nasa addinin da hantararsa yana burgeshi shima. An sha fada musu cewa musulmai sam basu da mutunci ko kadan sai yaga sam Afif was different, he's tolerating him yadda take Christian. Bai taba ce masa abinda yake ba daidai yake ba ko yayi masa tayin addinin musulunci ba. Kawai dai Afif din yana yawan yin ibada agabansa and komai suke idan lokacin sallah yayi Afif ajiyewa yake ya tashi yaje yayi sallar nasa sannan yana yawan saka musu channel din da akeyin karatun Qur'ani ko shi da kansa yayi. Ga yana mugun jin dadin Qur'ani don koma yake yana jin Qur'ani ajiyewa yake ya saurara. Kawai yana jin wani peace idan yana sauraren karatun.
"I told you I'm full, Afif."
"Liar. You didn't even have breakfast, Zach."
Miqewa yayi yana cewa "You're such a bother, I swear"
Bai sake kulashi ba har ya gam cin nasa abincin. Tare suka kammala Afif da kansa ya kwashe plates din ya kai kitchen ya wankesu tas ya ajiye ya dawo dakin ya zauna agaban wayarsa.
He was very eager yayi waya dasu Mami that's why ko wayar bai wani jira ya karasa cika ba ya cire daga cajin ya saka SIM card din da yayi na Vodafone sannan ya kunna wayar. Bayan yayi booting kai tsaye ya wuce dialer yayi dialing number din Mami hannunshi har yana rawa. Sai dai har ya karaci ringing dinsa ba'a dauka ba ya sake kira still ba'a dauka ba.
Number din Nuri yayi dialing yana fatan ta dauka itama don she's not a phone fan kamar Mami din itama. Sai dai fatansa bai samu ba don har ya kira times 4 itama bata dauka ba. Dire wayar yayi yana cewa "Their phones are completely useless."
Zach dake kwance yana game ya kalleshi yana cewa "Are you talking to me?"
Kai kawai Afif ya girgiza masa without saying anything. Duk zumudin waya dasu yasa ya koma wani iri don yau bai wani yi concentrating a lectures din da suka yi ba, his thoughts and mind yana tare dasu. Daukar wayar yayi ya mayar dashi cajin da yake yi amman yana zaune agaban wayar yana jiran yaga ko zasuyi calling back. Har around 3 babu wanda ya kira hakan yasa ya dauki wayar yana sake kira hoping wani acikinsu zai dauka.
Allah ya taimakeshi yana kiran Mami yaji an daga, he was emotional at that moment, komai ya tsaya masa cak jin muryar Maminsu tana yi masa sallama. Muryar da yau 15days rabon da yaji ta. Yayi mugun kewarsu just like yadda yasan suma sunyi kewarsa.
Kasa magana yayi ma yana jin Mami na tayin sallama amman yayi shiru. Daga daya side din shima sai yaji Mami tayi shiru for a moment kamin yaji tace "Afif, is that you?"
Hawaye kawai yaji yana bin fuskarsa da bai san na meye ba amman yafi tunanin na tsabar kewarsu da yayi ne. Basu tabayin ko kwana daya ba tare da sunga juna ba amman yau gashi suna kwana na 16.
"Afif, talk to me, please." Ahankali ya amsa da "Mami am, Mamina...ina Adda am?"
Da sauri Mami ta sauke wayar tana kwalawa Nuri dake waje kira "Nuriyya.... Nuriyya zonan ga biyayyenki ya kira." Hulli Nuri tayi da bucket din da take jan ruwa a rijiya ta taho da gudu tana kusan fadawa kan Mami tace "dagaske Mami?"
"Nifa matsalata dake atimes baki da nutsuwa look at you fa...."
Baki ta turo gaba tana cewa "Mami biyayye fa kika ce yana kira where's the phone." A speaker Mami ta saka wayar tana cewa "Afif" da sauri ya amsa da "Mami, Addana...ya kuke? I've missed y'all..."
Kamin ya karasa Nuri ta katseshi tana cewa "You're lying biyayye...ina ka saka wayar muna ta kira switched off. Ka barmu duk cikin tunaninka...ban yafe maka ba..."
Shima da kalar muryar yaran da tayi magana ya mayar mata amsa da "to ai wayar ne ban san yadda akayi ya fadi ba....kuma karki yafe din... Mami I'm sorry nasan na daga miki hankali."
Kamin Mami ta amsa Nuri ta rigata da "dalla can, don ma ka samu an damu da kai."
"That's enough you. Are you Tom and Jerry? Even on a call you can't stop fighting?"
Nuri tayi saurin cewa "biyayye let's do video call, I need to see you...naga ko ka canza, hala ma baka wani cin abinci."
Kallonta Mami tayi tana jinjina kai, kamar ba yanzu suka gama rigima ba now she's doing her sister role. Addu'ar shiriya kawai ta musu aranta tana cewa "Yes, Afif. Let's do a video call. We need to see you."
"Mami is a new phone ban gama setting din wayar ba. Ammn I will call anjima idan nayi setting dinshi.."
"Ok, kana cin abinci ko Afif? Y karatun da sauqi ko? How's the country ma gaba daya? You're all alone ko?" Mami duk ta jera masa tambayar da Nuri da Afif a tare sukayi dariya suna cewa "Come on, Mami. All these questions at once?"
"Ina so naji ya yarona yake ne."
"Mami ya kuke? Hope babu wani problem ko? Babu wani damuwa Mami?"
Shiru Mami da Nuri suka yi suna kallon junansu a lokaci daya........
To be continued...
#like
#comment
#share