THE AIRPORT GOODBYE
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
"All is well Afif, only kewarka kawai." Mami ta fada tana danne duk wani abu da yake ranta. Ajiyar zuciya suka ji ya sauke daga can side din yana cewa "Masha Allah, glad. Allah ya kareminku har na dawo Mami na."
Tare suka amsa da Aameen. Ba wani hira mai tsayi suka yi ba Mami tace yaje ya huta idan anjima sai su cigaba da wayar. Da har zaice bai gaji da jin muryarsu ba ya tuna da assignment dinsa da yake so ya karasa don da dare karatu yake dole suka yi sallamar yana bin wayar da kallo. He hopes all is well, just as Mami said. Yayi observing shirun da suka yi bayan yayi tambayar, sai yake ji ajikinsa kamar akwai wani abu a boye bayan shirun, but what could it be? Shine abinda bai sani ba. He will keep on praying for them fiye da yadda yake yi.
Dago kan da zaiyi ya tarar da idanun Zach akansa, da alama tun bayan fara wayarsa yake kallonsa. "Your family impressed me. The bond, the love, and everything Afif. I wish I was you!"
Cigaba da kallonsa Afif yayi kawai aransa yana jin kamar there's something hidden in Zach's story. Bai taba jin yana zancen family dinsa ba koda wasa and ko yaushe kamar dai shi kadai yake rayuwarsa haka. Duk dama a ƙasashen turawan nan mutum yayi rayuwarsa shi kadai ba sabon abu bane amman zaka ji ko a waya suna communicating da gida ammn banda Zach.
Miqewa tsaye Afif yayi yana cewa "you will be like me or more Zach in the future In Sha Allah." Murmushi Zach yayi yana gyada kai yace "I like your last sentence."
Murmushi Afif din shima yayi masa yana nufar bedroom dinsa yace "I have a lot to do, Zach."
"See you." Miqewa Zach din yayi ya fita kawai ya bar gidan don shi dinma yana da abinyi. Sai dai yanayin bond din daya fahimci akwai tsakanin Afif da family dinsa lingered in his heart. Tun ba yau ba yana yawan begensu and now da yaga yadda suka yi waya sai yaji abin ya mugun burgeshi. Ya tuna nasa parent din that cut ties with him sai yayi tsaki kawai. It quickly occurred to him that musulmai sun fisu samun kwanciyar hankali a yadda yayi observing rayuwar Afif daga haduwarsu duk da ko wata daya ba suyi ba, Allah ya hada jininsu kawai but he loves Afif and his character duk da kasancewarsa musulmi kuwa.
JANNAH'S POV
Dauke kansa yayi daga kallon Jannah yana mata murmushi kadan. And that broke her heart, har wani daukewa taji numfashinta kamar yana yi. Tayi dana sanin fitowa, ita da take tattalin zuciyarta daga raunin da kaunar Fa'iz din ya bar mata.
Kamar dai yanzun, da suka hada ido shine wanda ya fara dauke nasa away from her, it was clear Fa'iz did not love her, she's the only one suffering herself. "Till we meet next, Yah Jannah." Kai kawai Jannah ta dagawa Husna without saying anything to her. Tana gani Husna ta miqe ta fita daga wurin amman ta kasa motsi, kamar dai an dasata a wurin. And she's not even looking at Fa'iz, she's just feeling his presence. Wannan din kamar shine abinda zuciyarta yake so a kwanakin nan, haduwa da Fa'iz Ardo. And now sun hadu but his reaction towards their meeting annoyed her. "Baya sonki Jannah ke kike haukarki." Zuciyarta ta fada mata abinda yake asalin gaskiya. She tried very hard tayi yaqi da zuciyarta ta miqe tsaye tana daukar bag dinta da package din Khumra dinta ta juya without looking at inda Fa'iz yake ta fita tana jin kamar tana barin wani sashe na jikinta a wurin which was Fa'iz.
Bude motarta tayi tana ajiye jakarta da pack din taji sallama a bayanta. Sai da zuciyarta ta tsaya da bugawa na wucen gadi. It was Fa'iz Aliyyu Ardo da take son gani, wannan muryarsa ne, hatta da qamshin turarensa Baccarat Rouge 540 ya tabbatar mata da hakan. Ba qaramin yaqi tayi da zuciyarta ba kamin ta samu courage din juyowa ta sauke idonta akansa ba. Yana tsaye sanye da wani black fabric with a half-jumper style, dinkin da kayan sun bala'in zauna masa ajiki musamman yadda ya saka hular zanna dake kansa, yayi kyau as always.
"Dr. Jannah, where have you been? Kawai na samu resignation letter dinki. Why, please?"
Dauke kanta tayi tana mayarwa kan wasu passers-by "babu komai Dr, I'm planning my future."
Kai Fa'iz ya gyada mata yana cewa "but you can do it, zaki iya kina aikin kina planning your future Jannah."
Dan baya kadan tayi zuciyarta na raya mata "Fa'iz bazai taba barinki haka ba" he's killing her with his vibe, the way he calls her name directly, Jannah, sai taji kamar yafi kowa iya fadar sunanta even herself.
"I will think about it Dr, I have to go. Allah ya bamu alkhairi." Bata jira amsarsa ba ta shige cikin motarta tana jin sanda yace "Allah ya kaimu. Take care."
"Take care." Ta maimaita aranta, was Fa'iz not in love with her? Da sauri ta girgiza kanta tana kunna motarta ta bar wurin "take care is said to everyone. It is not a love language, it is a care language, and Fa'iz cares for all." Ta yadda da wannan din shi kowa nasa ne, amman me yasa ya manta da ita sai yanzu zai wani tuna, abin ya bata haushi. Amman data duba zuciyarta taji ko soyayyar da take masa ya ragu sai taji sam babu ragi sai ma kari kamar. This was her destiny, to love someone who did not knows she loved him.
UMMI'S POV
Bata jira time din fitarta a office ba ta koma gida. She knew sooner or later she would receive a call from their cult group which she was very afraid of. Right now kanta ya mugun kulle da yadda zata samu mafita ta aiwatar da shirinta. Tun kamin aje ko'ina it turned out that wannan karon ma ba zata yi nasara akan Boddo ba. Dukan steering din motar tayi da karfi tana cewa "I hate you Boddo. Ko yaushe ke kike nasara akaina. But I will not let that happen this time, I will ruin Suhana's life by fire by force." A mugun haukace ta qarasa gida, daga yadda take horn ya tabbatar yau ba sauqi don haka kowa na 'yan aikkn gidan suka shiga taitayinsu don sun san slight mistake kawai kora ne.
Aikam har ta karasa cikin dakinta she was looking for someone and the opportunity to release the anger in her head. Jifa tayi da komai dake hannunta akan gadonta tana zaman dirshan akan carpet din dake wurin, gobe by now Suhan tana Munich and today is the deadline. Ahaka ma wai an kara mata sati daya akan wanda aka bata, that was two weeks in total, but a simple thing failed. "May Allah curse Azzam." Don tana jin kamar shine ya hana burinta cika. Wannan ba shine karon farko data taba tsinewa Azzam ba, har dai za tace yayi mata abu baiyi ba hakan take yi. Allah loves Fu'ad because he is calm by nature. It is like Fu'ad baiyi dacen uwa ba, CJN Aliyyu Jimeta baiyi dacen mata ba. Ummi tafi dacewa da matar wani villain din yadda zasu ci kansu da mugun hali.
WASHEGARI.
Flight din 10 Suhan would take, that was why by 8 she had finished getting ready yadda Ammi ta tsaya akanta. Bama Suhan din kawai ba hatta da Ammi, Abbi da Fa'iz sun shirya domin rakasu including Addarsu Safa data buga sakamako tazo tun 7 don da ita aka karasa shirin Suhan din.
Kana kallon fuskar Suhan you will know that she was about to burst into tears, hakan yasa babu wanda yayi kokarin tabota suna son a rabu lafiya don sun san ta fara kukan nan nata shirunta sai Allah.
Fa'iz da kansa yake dauke da trolley dinta duk sukayi gaba suna sakata a tsakiyarsu kowa yana fussing over her. Har suka shiga motocinsu Ammi tana zuba ido ko za taga Addarta amman shiru, hakan yasa tana shiga mota ta fara calling Ummi amman bata dauka ba. She just made an excuse for her don tasan da bata da wani abunyi zata samu damar zuwa.
The journey was silent throughout until they reached Nnamdi Azikiwe International Airport, don parrot din ba halin magana su kuma babu mai tsokanarta yadda suka saba.
She had already done her boarding pass online, haka suka zauna a waiting lounge dukkansu, kowa kallonta yake yana son yi mata magana ana gudun kukanta. Itama Suhan din jira kawai takeyi someone to touch her so she would break down, amman ta lura they're very cautious, abune kowa yasan halinta.
Kamar daga sama sukaji sallamar Fu'ad Aliyyu Jimeta. Instantly Suhan ta dawo daidai, it is like Fu'ad was her mood booster. Ta riga kowa noticing dinsa ba wanda ya lura sai ganin miqewarta tsaye kawai suka yi tana cewa "laaa Hamma F, so you will come too?"
Kai kawai Fu'ad ya gyada mata yana durqusawa gabansu Abbi ya gaidasu da Adda Safa. Har zuwa sanda ya gaisa da Fa'iz, idon Suhan yana kansa. Abbi, Ammi da Safa duk suna kallonta. Ita Ammi yanzu haushi ma taji kamar Suhan din ta fara bata, just look at the way she was staring at Fu'ad like an old witch.
Bayan ya gama gaisawa da Fu'ad ne ya juyo kan Suhana yana kallonta sai dai akwai banbaci a kallon da yake mata da wanda take masa.
"Now Suhana, I'm back to you..."
Kamin ya karasa maganar da zaiyi ta katsehi tana cewa "Hamma F, are you also supporting me going to Munich?"
Kai ya gyada mata yana cewa "Who is Fu'ad over Abbi and Ammi's decision? I'm nobody in their ruling Suhana."
"So you're supporting them Hamma?"
"100%." Wani kalar kallo ta masa tana komawa ta zauna kawai saying to herself "so you do not care about me." Ammi dai banda harara babu abinda take zuba wa Suhan din wanda sam bata lura ba.
Kowa shiru yayi sai Fu'ad da Fa'iz who were having side talks in a low voice. Within a few minutes they heard the boarding announcement, anan ne kuma Suhan ta fara crying for real wai ita fa ba zata rabu dasu ba. Ammi mantawa tayi da haushin data bata, she started comforting her daughter same with Abbi. Fa'iz ne yake gefe, unbothered by her crying drama, amman hatta da Fu'ad duka they were comforting her. A time din Suhan mantawa tayi da wai zuciyarta loves Fu'ad, duk lallabatan da yakeyi kamar yana sake teasing her ne. Sai da Abbi yayi mata warning look sannan.
Her worry was how she would spend four years in a country that was not theirs, ko zata dawo gida ba dadewa za tayi ba zata sake komawa har zuwa lokacin da zata kammala. Even though they gave her full assurance na zasu riqa kai mata ziyara amman hakan bai mata ba.
Fa'iz da kansa ya kamata pulling her trolley, they went ahead. Suna takawa yana mata nasiha politely har suka rabu suna waving goodbyes.
They could not leave until they waited to hear that her flight had taken off, about an hour later, sannan duk suka tafi. Ammi was missing her daughter a lot, dukda sunfi yin fada akan shiri don Suhan sai ana bata wuta, mugun rawar kai gareta. Fa'iz da Fu'ad tare suka wuce don duk office zasuje, Fa'iz dropped Fu'ad at NoveBuild Ltd before going to Novecare Clinic.
To be continued...
#like
#comment
#share