7-8
"wai ƙawata garin yaya har daddynki ya kamaki nifa abun se ɗauremin kai yakeyi"cewar laila.
"hmmmm kedai bari nima har yanzu na rasa yadda akayi yasan ina wannan guri,wallahi se ganinshi mukayi kawai akanmu,amma yadda Alhajin da naje gurinshi yake magana da daddyna ya gwada kamar sun san juna dashi duk da cewa hankalina atashe yake atime ɗin bazan iya tuno maganganun dashi alhajin yaywa daddyn nawaba"cewar fareeda jiki asanyaye.
"hmmmm shiyasa nake baki shawarar ki mallaki gidan ki naki kamar de ni nan,kinga waye ze shigomin bada izinina ba,sannan ba ruwanki da tsegumin mutane bare a haɗaki da iyayenki amma kika ƙi ba ga irintaba,"cewar laila.
"ƙawata nide yanzu meye abunyi wallahi banida natsuwa ko kaɗan"cewar fareeda.
"bazamuyi saurin ɗaukar mataki akanshi ba se mun jira ya samu sauƙi an sallameku se muyi amfani da hukuncin da ya yanke miki muga abinda mu kuma zamu iya yi ki kwantar da hankalinki kinji ko"cewa laila
Haka suka yini laila na kwantar mata da hankali,se magriba fareeda ta baro gidan,koda ta koma asibiti samu tayi an sallami daddyn nata dan haka gida ta wuce zuciyarta na dukan tara-tara.
Koda ta shiga gidan ba kowa a falon se mummynta,tun kamin tai magana ta rigata"fareeda ina kika shiga kika bar wayarki se kira akeyi baki kusa?"
"wallahi mamy gidan su ƙawata naje na kwanta basu da nisa da asibitin na ɗauka meetingvɗin da daddy ya shiga ze jimane shine yasa seda na koma akace an sallamemu"cewar fareeda jikinta asanyaye.
"fareeda meke faruwa dakene kwana biyunnan ina lura dake tun ranar da aka kai daddynki asibiti kika rage kuzari agidannan,me yake faruwane?"cewar mamy tana binta da kallo me cike da nuna kulawa.
Murmushin yaƙe fareeda tayi tace"mamy fargabar rashin lafiyan daddynne yasa nakoma hakan"ta faɗi bakinta na rawa.
"to ay seki kwantar da hankalinki tunda har Allah yasa ya samu lafiya,yace ma in kin shigo ki sameshi a falonshi yana nemanki"cewar mamy
Ɗora hannu fareeda tayi akai ta fashe da kuka tana faɗin "shikenan na mutu,wayyo Allah na na shiga uku,"cewar fareeda hawaye na cin gudu akumatunta.
Hankali atashe mamy ta dubeta tace"lafiya kike kuwa fareeda meye na shiga uku dan kawai daddynki nanemanki,ko kin masa wani laifinne?"cewar mamyn.
Shuru farida tayi dan bazata iya tonawa kanta asiri agun mahaifiyartataba,tunda de shi daddyn be faɗa mataba,girgiza kai tayi,kawai tana ci gaba da kukan ta nufi ɓangaran falon daddyn nata jikinta na rawa.
Muryarta na rawa tai sallama aƙofar falon sannan ta tura ƙofar ta shiga.
Zaune yake akan carpet ya miƙar da ƙafafunsa,can ƙasa ya amsa sallamar tata fuskarsa ba alamun wasa.
Daga nesa dashi fareeda ta tsuguna tace"Daddy ka yafemin dan Allah wallahi sharrin shaiɗanne,dan Allah... "ya dakatar da ita.
"kimin shuru ban tambayekiba munafuka"cewar daddyn afusace
Zabura tayi sannan tai shuru jikinta na ci gaba kakkarwa,tsoro da danasani suka mamayeta.
"daga yau na haramta miki zuwa makaranta,sannan na haramta miki yin amfani da waya,kuma na baki wata guda kawai ki fito da mijin aure in kuma baki dashi to ki shirya nan da watanni uku zan aurar dake ga duk wanda naga dama"cewar daddy akausashe yana watsa mata harara.
"innalillahiwainnailaihirrajiun daddy kayi haƙuri dan Allah kar ka hanani school ka yafemin wallahi inason in haɗa degree na daddy"cewar fareeda cikin kuka.
"degree ayawon barikiba sauran mutuncina da be gama zubewabane kikeso in barki ki zubarmin,to na gama magana kuma wallahi acikin duka gargaɗin da nai mikin in kika karya guda wallahi sekinyi danasanin zuwa duniya mazaunin ƴata,tashi kibani guri mutuniyar banza,kuma kiba mamynki wayarki ta riƙemin"cewar daddyn afusace.
Ayko da gudu ta fice afalon tana kuka kamar an mata mutuwa.