EVERY SOUL WILL TASTE DEATH
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
FU'ADS POV
3days later......
Gaba daya ya ajiye aikinsa aside, hankalinsa da tunaninsa duka yana wurin Ahad da har yanzu yake nan unconscious. Kullum yana asibitin duk da bai farka ba amman saboda Mama yake zuwa. He was always there saboda ita duk da tana daurewa amman kallo daya zaka yi mata kasan akwai damuwar danta a tare da ita. Jiya nan ya fara shirin fitar dashi waje ayi masa plastic surgery, ya duba yaga best hospitals din da suka iya plastic surgery sai ya zaba masa John's Hopkins hospital USA. Ko Mama bai fadawa ba yafi so sai shirin da komai ya kammala sannan zuwa nan da next week In Allah ya yarda.
Umminsa ta dawo hayyacinta already ta koma gida, sai dai the fact that Fu'ad bai wuni tare da ita hurts her. Ya fada mata abinda ya faru da Ahad din but her response makes him thinks otherwise. Har gwara Fu'ad akan Azzam da bai dubata ba sam in fact tun ranar da incidence din ya faru bai kwana agida ba yana can bin mata hotels hotels. A haukansa wai an gama masa da Fu'ad don bai bi takan media ba sam yana can yana sabon Allah. Ga bad bai kirashi ba shima, tunda bad ya fahimci basuyi aikin daidai ba sannan yaga IG ne akan case din ya tattara yaronsa suka bar qasar ta boyayyiyar hanya zuwa Benin republic. Basu bar any trace da za'a ganesu ba banda daukar da CCTV na ministry yayi shima sam ba za'a san waye ba coz fuskarsa na sanye da mask ko anyi bincike za'a samu blank evidence ne.
He was driving very gently kaman baya so, indai fita bana aiki bane is hard ka ganshi tare da guards dinsa. National hospital ya nufa yau baije da wuri yadda saba zuwa ba Ummi ta riqeshi wai ya fifita Ahad akanta, that itama ai tsautsayi ya fada mata. Da kyar ya samu ta rabu dashi bayan ya bata assurance din zai gina mata sabon mall wanda yafi na da. Yana parking ya wuce inda suke har yanzu suna ICU don ko sau daya Ahad bai farka ba. Mama da 'yan uwanta guda biyu plus Zannira ya tarar a bakin ward din daga waje. Wurinsu ya karasa ya gaidasu suka amsa suna tambayarshi ya dawainiya don bills din gaba daya are on him tun farko har yanzu.
Ciki ya wuce zaiyi magana da likitan dake kula da Ahad akan fitar dashi da zaiyi. Shigarsa yayi daidai da likitoci suna nufar dakin da Ahad din yake a haukace. Wata nurse Fu'ad ya nufa yana tambayarta lafiya ta sanar dashi numfashinsa ne yake shirin daukewa gaba daya.
He tried sosai yayi calming kansa ya tsaya a wurin yana addu'a sosai wa Ahad. Su Mama hankalinsu a tashe suka karaso wurin kowa fuskarsa dauke da damuwa. Fu'ad bai kallesu ba sam don bai son ganin tashin hankalin da mama ke ciki.
Suna tsaye ne daga bakin wurin kowa cike da fargaba tare da addu'ar samun lafiya wa Ahad, sai dai kana naka Allah yana nasa and na Allah is the best.
Fu'ad da yake bakin ƙofar ya jiyo muryar wani likita yana cewa "time of death 2:30pm." For a moment sai brain dinsa ya manta ma'anar death din gaba daya, ya tafi tunani sosai yana son tuna me kalmar yake nufi doctors din suka fito kowa yana zare hand gloves dinsa yana disposing.
Mama ta riga kowa zuwa wurin likitocin cike da son jin halin da Ahad dinta yake ciki. "Likita ya farka ko, yana lafiya ko, zan iya ganinsa yanzun?"
Kai kawai likitan ya gyada mata yana kare musu kallo. Yana fargabar ya sanar dasu abinda ya faru. Basu ba hatta shi yaji mutuwar Ahad, bai taba haduwa da patient din da yake mugun tausayawa ba Irin Ahad. Ya fahimci yadda kowa ya damu dashi tunaninsa yadda zasu dauki zancensa a zuciyoyinsu but baya da option din daya wuce wannan.
"Kuyi haquri Mama, kullu nafsin zā'iqatul maut!!!!!" Likitan ya shiga sahun wanda ba zasu manta dashi ba. Ya sanar dasu rashin da ba zai goge daga kansu ba.
Ahad was no more! Ya amsa kiran Ubangijin talikai. Baiyi doguwar jinya ba Allah ya taqaita masa. Though su zasu fi so ya kasance a tare dasu amman it was decreed cewa zai mutu within 32 years as a result of an acid incidence.
Baya Mama tayi kaman zata fadi aka tareta da kyau. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un take son furtawa amman ta kasa, kalmar ta dauke daga bakinta gaba daya likewise sauran dake tare da ita.
Fu'ad anan shine wanda mutuwar tafi daka sama da sauran idan ka cire Mama. Kwakwalwarsa ta tafi tuno masa haduwarsu na farko da Ahad a Lagos, yaje neman aiki wani company dake construction atime din sune famous don year din Fu'ad ya gina NoveBuild so it's not that popular. Yadda aka wulaqanta Ahad din ya fito yana suratai ya gama neman aiki don akwaishi da zuciya baison a takashi.
Fu'ad din sai ya nufi takardunsa daya watsar akasa ya kwashe masa su yana duba qualifications dinsa an that is how it started, Fu'ad employed him a NoveBuild tun a lokacin suna da branch guda daya kawai. Yadda da amanar da Ahad yake dashi yasa gradually Fu'ad yafi aminta dashi kan kowa, shaquwa ya fara building kansa a tare dasu har ya kai idan ka dauke Fa'iz Ahad shine next wanda Fu'ad zai kalla ya kira aboki. A wurin Ahad bai da kamar Fu'ad. Ya taimakeshi taimakon da har ya koma ga Allah bazai manta ba. Kullum cikin kyautata masa yake har zuwa yau daya koma ga mahaliccinsa. Fu'ad was a gem a wurin Ahad da mamansa. Cigaban NoveBuild right from first branch that was in Lagos ya samu tare da dedication din Ahad har zuwa kan Kano branch din nan da ake ginawa. Fu'ad will never forget Ahad in his life. Ko matsala ya taso kamin Fu'ad ya sani Ahad zaiyi solving with his own penny said dai Fu'ad yaji a labari.
Ahankali bakinsa ya fara furta kalmar Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un yana samun wuri ya zauna. Yana tuna tsokanarshi na karshen da Ahad yayi sanda zasu rabu kamin incidence din ya faru. Ya mugun dakewa a matsayinsa na namiji a tare dasu Mama. Ko bama wannan ba shi din namiji ne mai mugun dauriya don haka bayan ya samu nustuwa ya miqe ya nufi wurinsu Mama. She was somehow suffocating a dalilin shock din data shiga dole aka bata gado itama anan asibitin. In no time 'yan uwa kowa ya san rashin Ahad, bama 'yan uwa ba a media gaba daya ya tafi viral wannan da aka sawa acid din ya rasa ransa.
Sai a sannan Azzam ya samu news ashe ha Fu'ad aka sawa ba. Karamin hauka yayi yana jin da tuni Fu'ad ya tafi ya bashi fili da tuni yanzu burinsa zai cika, he will run NoveBuild without Fu'ad amman bad ya bata masa aiki.
5hours laters.....
An sallami Mama hatta da gawan Ahad an basu sun koma gida duk da sai zuwa gobe za'a sallaceshi don dare yayi sannan 'yanuwansa na Kano zasu karaso gobe ne.
Fa'iz was there tare da pal dinsa, shima yaji mutuwar Ahad din don a dalilin Fu'ad suka saba. Is like babu wanda zaiji yadda Ahad ya rasa ransa baiji tausayinsa yayi masa addu'a ba duk kalar mutuwar zuciyarsa kuwa don hatta Ummi taji mutuwarsa don one thing with Ummi is ta tsani mutuwa a rayuwarta. Ko'a hira bata so a ambaci mutuwa.
Washegari dubban mutane ne suka sallaci gawar Ahad a dalilin case dinsa da yadda ya mutu ya baza duniya gaba daya. Mutane from many places a abuja wanda basu hada jini dashi ba were there plus ga various people from NoveBuild Lagos branch.
Ko bama wannan ba kirkin Ahad yaci ya jawo masa jama'a bare abinda ya faru. Fu'ad yadda kasan Azzam ne ya rasu haka ya koma though he was not down amman kana kallonsa zaka san anyi masa mutuwa likewise wanda yake tare dasu.
An binne Ahad cike da fatan za'a bi masa haqqinsa, an binneshi cike da fatan mutuwar ya zamar masa hutu. Zuciya daya tal ta dauki alhakin tono duk wanda yayi wannan aikin, yaci alwashin ko waye sai yasa ayi masa abinda yasa akayiwa Ahad, wannan shine burin Fu'ad da yakejin idan ya cika yanzu bai da wani matsala. He will not let ko waye ya tafi haka nan babu hukunci ashe ma Ahad din is not worth it a wurinsa.
One week later...
Komai ya dawo normal sai dai zuciyoyi da yawa suna cikin alhinin rashin Ahad wanda suka barshi aransu suna yi masa addu'a ne kawai.
Fu'ad ya rage son zama shi kadai da yake so da saboda yana zama shi kadai Ahad ke zuwan masa rai that's why ko yaushe yanzu yana tare da Fa'iz ko ya kwana agidan Ammi ko Fa'iz yazo nan gidansu su kwana tare. Yayi many things na sadaqah jariya for his Ahad. Mama ta koma Kano ita da 'yan uwanta daman saboda Ahad take zaune a Abuja and yanzu babu shi.
UMMI'S POV
Ta shirya kanta cikin wata super exclusive wax mai ubansun tsada zata fita taje taron bikin 'yar qawarta, kamar ta manta da halin da take ciki haka. Ummi akwai son nunawa mutane akwai kudi, tana son duk abu idan ya tashi ta baje bajinta yadda baki zai ta zancenta. Ko wannan bikin duk da yau kawai zata je amman kalar gudunmawar data bayar wadda ta karba awurin Fu'ad ne is something else, mahaukatan kudi ta bayar duk don ta burge. Box din gold jewelleries dinta ta dauka zata saka don fitar yau na daban ne a wurinta.
Tana bude box din ta sandare ganin half of the jewelleries basa nan. Ta zata gani daidai ne ba tayi ba don haka ta sake rufewa ta bude but still daidai ta gani ashe. Kunsan mutuniyarku babu tawakkali nan da nan ta hau zage zage da kalamai na zallar sabo. Bata gama dawowa daga shock din rasa gwalagwalanta ba sai ga kira daga kungiyarsu.
Wannan kiran ya mantar da ita tashin hankalin rasa sarqoqinta da take ciki. Bata san mene kuma yanzu zasu ce da ita ba. Bayan sun karar mata da dukiyarta kaf she was really afraid of them don basu taba hukuntata ba suna mugun daga mata kafa kan wani dalili known to them.
Mantawa tayi da wani biki da za taje ta fita kai tsaye ta fada motarta zuwa kungiya. Ba'a saba musu idan sun kira, kome kake da sun kira kawai ka ajiye malam ko sallah ce kuwa (Allah Ka kare mana zuqatanmu daga batacciyar hanya).
Bata yi sauri kalar na ranar ba don akwai sauran fargaba a tare da ita na me kuma zasuyi mata yanzu.
Wurin yau bai cika kamar ranar ba yawanci heads ne kawai na wurin anan sai ita da aka kirawo yanzu. Shiga tayi haka nan cike da bin doka ta sadda kanta qasa har zuwa sanda ta zauna. Ta miqa gaisuwa tunda yau ba taro ake ba muryarta yana rawa kamar ba ita ce wannan egoistic woman din ba.
Bonefather ya qare mata kallo tsaf kamin yayi gyaran murya yana cewa Zuhra Mamman..."
Rusunar da kanta ta sakeyi alamun ta amsa Bonefather ya gyada kai yana cewa "we call you here saboda zamuyi miki favour guda daya da zai dawo miki da dukiyarki!" Sauran kadan tayi breaking rule ta dago fuskarta Allah ya taimaketa ta tuna.
"Favour din shine....." Sai yayi shiru kamar dai yana ja mata aji haka.
"Zakiyi tayin kudi har karshen rayuwarki da sharadin danki da kike so FU'AD..." Ya sake dakatawa yana kallon Ummi da tayi qasa da kai tana jiran jin abinda zai fito daga bakinsa.
"Da sharadin FU'AD ba zai taba yin aure a rayuwarshi ba!!!!!!!"
To be continued.....
#like
#comment
#share