NURI

THE DAY THEIR PATHS COLLIDED

by @saddiqahhh

NURI 

By Saddiqa

JANNAH'S POV

Yau kimanin wata biyu kenan data bar aiki. Tun Mama na saka rai zata koma har ta fara zargin lallai akwai abinda Jannah ke boyewa. Dama duk ta lura da yadda take ware kanta, yadda take son kadaici wani abune sabo daga Jannah. Jannah dake da son jama'a, this is unlike her.

Tana kwance akan gadonta tun dazu bayan data gama girkin rana tazo tayi sallah take kwance. Idonta biyu ba bacci take ba, abinda ya zamar mata cuta shi take.

Sallamar Mama ya dawo da ita hayyacinta amman bata motsa ba, tayi kamar baccin take. Kare mata kallo tsaf Mamma tayi kamin ta karasa kusa da ita ta zauna. Ta fahimci idonta biyu ba baccin take ba. Shiru tayi na dan wani lokaci before saying "so you're going to hide your problems from me too, Jannah?"

Runtse idonta da kyau tayi tana cigaba da pretending bacci take. "Wake up let's talk. I'm tired of watching you. Open up and tell me what's bothering you."

Kamar ba zata tashi ba haka dai ta motsa tunda dai ta fahimci Mamma ta gane ba baccin take ba. Zama tayi tana facing din Mamma amman kanta yana kasa. Mamma ta kare mata kallo tsaf ganin yadda ta fada kamar tayi rashin lafiya.

"Mene yake damunki Jannah?" Shiru babu amsa. Bata san me za tace ba sam.

"What is wrong with you, Jannah?" Yanzun ma shiru tayi ta kasa magana. Da mugun nauyi ta bude baki ta fadawa Mamma asalin damuwarta.

"Am I not talking to Jannah?" Da sauri ta girgiza mata kai amman still ta kasa magana.

"Sai na fadawa Abbanku zaki fada kenan?" Da sauri ta dago kanta ta kalli Mamma. Sai a sannan Mamma ta lura da hawayen dake kwance a idanunta. Hakan ya sake tabbatar mata da lallai abinda yake damun Jannah babba ne.

"It's been two months now. You stopped going to work and you said you were fine. If this is a break, then why are you still home? What's really going on? Or do you have another mother apart from me?"

Da sauri ta girgiza mata kai hawayenta yana biyo fuskarta ta saka hannu da sauri ta share. Muryarta yana rawa ta bude baki ahankali tace "Mamma...."

Kallonta Mamma keyi tana jiran jin abinda za tace "Mammah kawai kike yimin addu'a don Allah, nima bansan mene yake damuna ba."

"Look, I'm not a child. Waye kike so Jannah????"

Da wani kalar sauri ta dago tana kallon Mamma, wa take so? Kenan all this time Mamma ta sani tayi mata shiru? Kawai jira take ta fada mata da bakinta ne. Kasa tayi da kanta tana dannar zuciyarta kar tayi kuka. Ba lokacin da zata boye halin da take ciki bane yanzu. Mamma ta fahimci komai don haka kawai ta fada jikin Mamma ta rungumeta kamkam tana fara rera mata kuka.

Ta kasa danne abinda yake zuciyarta da har Mamma ta fahimta. Ta kasa cire Fa'iz daga ranta ko na rana daya. Abin nata kamar sake kara gaba yake kullum, Fa'iz Aliyyu Ardo ya kasa barin zuciyarta da kwakwalwarta su huta.

Patting bayanta Mamma keyi cike da tausayinta, ta tabbatar abinda zai saka Jannah kuka ba karamin abu bane don tana da mugun dauriya tun asali sannan yazo ya hade da yanayin aikinta.

"Mamma zuciyata ba tayi min adalci ba..." Shiru mamma tayi mata tana jiran ta gama fado duk abubuwan da take boyewa sannan.

"Bata kyauta min ba Mamma....ta kasa son wanda yake sonta sai wanda baya sonta.." shiru dakin ya dauka sai sautin kukan Jannah.

"I've resigned because of him. I thought if I quit, I would stop feeling this way about him... but it's not working... he won't leave my heart, Mamma... it keeps getting worse... I don't know what to do anymore... Mamma, he doesn't even know I'm going through this!!" Yadda ta karashe bai san ina yi dinnan ba zaka tabbatar kamar shi yafi komai tsaya mata arai.

Dagota Mamma tayi ta saka hannu ta share mata hawayen dake fuskarta tace "it's okay, that's enough crying. That's enough... no matter how hard it gets, is with Allah... just be patient, okay? Surrender everything to Allah. He sees you and He will make it easy for you, do you hear me?" Kai Jannah ta gyada mata tana fidgeting yatsunta. Tasan daman idan ta fada haquri za'a bata ita kuma yanzu zuciyarta ba haquri take so ba. Fa'iz din take son samu gaba dayansa amman tasan bata da wani hanya.

"Wayeshi?" Kamar ba zata amsa ba ta bude baki tace "Fa'iz, CMO din asibitinmu!" Kai Mamma ta gyada mata ta rasa abin ce mata sai can ta furta "Quitting your job was not a solution... I will talk to your dad. Maybe we can get you a job at another hospital. Isolating yourself like this will only make things worse for you, Jannah... Allah is with you, In Sha Allah... and it's high time you give Zaid a chance. Maybe with him you will forget, okay?"

Kai kawai Jannah ta gyadawa Mamma amman tasan babu lallai zata iya mantawa da Faiz, mutumin stalks to her heart dearly.

"Ki riqa shiga cikin mutane, wannan zaman shirun shima zai riqa kara miki damuwa ne... don't let me see you like this again, Jannah."

"In Sha Allah Mamma... I will try my best.."

"That's my Jannah. May Allah bless you and choose what is best for you." Ta amsa da Aameen.

Mamma bata barta haka ba ta sakata fitowa suka zauna a kasa ita da sauran qannenta. Da kallo suka bita da farko don kowa ya gama saka mata idon yadda take ware kanta a dakin. Ganin yadda suke binta da kallo yasa ta daure ta saki fuskarta ta sake sosai acikinsu. Sai taji ashe mutane rahama ne, ware kanta da takeyi shine yake kara damuwar Fa'iz a ranta.......

FU'AD'S POV

AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT, KANO.

Da wannan tarin nutsuwar da kamalar tare da cikar haiba yake fitowa harabar airport din guards dinsa suna take masa baya. Yana sanye cikin Ralph Lauren men suit all white, kafarsa sanye cikin wani baqin takalmin sau ciki na kamfanin givenchy daya dace da shigar jikinsa. Hannunsa sanye cikin agogon patek Philips and co ya dan shafa fuskarsa dake sanye cikin dark shade kansa a kasa yana tafiyar nan majestically kamar wani wanda ya hada jini da sarauta haka. Wurin gaba daya kamshin turarensa pur oud LV yake.

Motarsa kirar Urus aka bude masa ya shiga ya zauna silently yana addu'a a ransa. Yanayin yadda ake hada-hada a garin is different, it's not like their city. Samun kansa yayi da bin hanyar da suke bi duka da kallo. Ba yau ya taba zuwa Kano ba, amman duk sanda zai zo sai yaji garin yana burgeshi, yanayin yadda mutane ke hulda da yadda tsarin garin yake daban da Abuja yana burgeshi.

Haka nan ya samu kansa da yin wannan murmushin nasa mai sanyi da baisan dalili ba. Driver ya dauki hanyar wucewa dashi bristol yace dashi ya fara kaishi site yana son ya fara ganin yadda komai yake tafiya tunda akwai lokaci.

Lokacin da suka kai unguwar gradually ya fara jin wani sabon canji a tare dashi. Zuciyarsa ke bugawa ahankali ba yadda take yi ba, hakan yasa shi nutsuwa yana sauraren yadda take bugawa ya lumshe idonsa da suke da mugun haske wanda suke sanye cikin dark shade din daya mugun kara masa kyau na musamman.

Samun kansa yayi da karewa unguwar kallo lokacin da motar nasu ya tsaya. Sabuwar unguwa ce da bata da hayaniya sam. Sannan babbar hanya ce sosai da zai jawo hankalin mutane kan ginin da suke yi. Bai fita ba har bayan 5mins yana jiran wai ko zaiji zuciyarsa ta dawo normal sannan ya fita. Ganin kamar yana shirin batawa kansa lokaci kuma yana son ya gama abinda zaiyi da wuri yaje ya huta yasa ya fito yana zare wannan dark shade din daya kare wannan kyawawan idanun nasa masu mugun haske.

Da yawan ma'aikatan suka karaso wajen suna yi masa barka a matsayinsa na shugaba mai iko da wurin duka. Gaisawa yayi dasu daya bayan daya yana musu tambayoyi kan ginin cike da sakin fuska wanda hakan yasa lokaci daya duk suka sake yadda da halinsa da suke jin labari a bakin wasu daga cikinsu.

Ciki suka shiga bayan yayi assigning mutum daya da zaiyi leading dinsa ko ina na wajen. Yadda komai ya tafi cikin tsari ya mugun burge Fu'ad sosai. He was genuinely impressed by how much work they had done in such a short time........

NURI'S POV

Kamar ko yaushe agajiye ta dawo daga makaranta sai hade rai take abinda ba halinta ba sakamakon wani mai Napep data samu wai dole sai ta bashi number dinta, yaqi barinta ta tafi for the first time a rayuwarta ranar ta surfa masa rashin mutuncin da bata san ta iya ba sannan ya kyaleta ta taho gida.

Tana zuwa gidan ta tarar da babu ruwa ko kadan hakan ya sake bata mata rai kawai ta dire jakarta a tsakiyar dakinsu ta fashe da kuka tana hade kanta da guiwa. Da kallo Mami ta bita ganin ko sallama ba tayi ba ta hau kuka. Ta tabbatar dalilin kukan nata bai cika dalili ba. Kamar ta shareta amman ba zata iya ba don haka ta miqe ta isa wajenta ta zauna ta fara da kare mata kallo tsaf.

Hannu tasa ta cire mata hijab din jikinta wanda ta bata da hawaye ta ajiye gefe. Ta kai hannunta ta dago fuskarta a tsanake ta sake kare mata kallo kamin tace "Waye ya tabamin haskena?"

Sautin kukan nata ta karawa karfi tana kallon Mami da idanunta da har sun canza kala. "Mami Allah nagaji."

"Anzo wajen." Mami ta fada aranta, daman tasan tatsuniyar gizo baya wuce na koqi don haka sai cewa tayi "meya faru Nuriyya?"

"Ni Allah nagaji da diban ruwan nan wallahi, duk jikina ciwo yake yi. Nidai ki samo wani yake dabowa kawai."

"A ina zan samo Nuriyya, kina gani almajiran unguwar ba yawa ne dasu ba ga sam basu da mutunci sai dai su moreka kai bazaka moresu ba."

"Yau kawai kowa yayi taimama Mami nagaji.." tana fadin haka ta miqe ta karasa wajen akwatinta ta zaro wasu kaya marasa nauyi na cotton material mai kalar fari da baqi da akayiwa T-bubu ta sauya da na jikinta ta dauki black jersey veil kawai ta yafa a saman kanta ta juya ta fita ba tare da tace da Mami komai ba.

Kai kawai Mami ta girgiza tana cewa "Allah ya shiryeki." Tasan ruwan ta tafi debowa amman kamar yarinya ta wani sakata agaba da kuka. Itakam bata san yaushe Nuri zata san ta girma ba.

Nuri na fita ta dauki bokiti guda biyu ta fita, bokiti biyu kawai zata debo ranar kuma nasu kawai Inna ta samo mai dibo mata. Abin takaicin tana fita ta tarar da wurin duk maza ne yawanci masu ginin dake aikin ginin wurin da yake burgeta. Ta samu kanta da kare musu kallo tana harararsu kamar sune suka yi mata laifi.

Sanin ba dadewa zasu yi ba yasa ta tsaya jiransu daga nan bakin kofa tana karewa layin kallo ko zata ga wani yaron ta aikeshi sai dai sam babu kowa, layin shiru yawanci yaran unguwar duk suna islamiyya. Idonta ya sauka kan bakin layin da yake jere da wasu motoci bakake sai wata guda daya da take fara wanda bata lura dasu ba dazu da take dawowa saboda ranta da yake a bace. Tsaki tayi tana fara tafiya zuwa wurin diban ruwan ganin sun bar wurin.

Ajiye bokitin tayi ta kunna ruwan ta fara diba ganin babu layi yasa ta koma gida ta dauko sauran kayan ruwan nasu tazo ta ajiye ta samu wuri kawai ta zauna tana kallon yadda ruwan yake cika bokitan. Da wani ya cika zata janye ta tara wani sai turo baki take kamar zata sake fashewa da wani sabon kukan. Ta tabbatar da biyayyenta yana nan ba zata yi wannan aikin ba.

Miqewa tayi ta dauki bokiti daya data cika taf ta dauka bayan sarai tasan an hanata cika bokitin amman tsabar a sama take ranar ta manta. Ta juya ahankali zata tafi taji haushin kare daya sanyata sakin bokitin ya dira a kafarta da nauyinsa. Durqusawa tayi da sauri tana fashewa da kuka, ruwan duk ya sheqo mata ajiki ya jiqata gaba daya. Takaici da zafin da kafarta keyi yasa ta fashe da kuka kamar yarinya.

________

Ta baya suka biyo shi da Ibrahim da yake masa bayanin sauran abinda ya rage a karasa a aikin nasu. Daidai sun karaso ta side din wajen bokitin karen yayi haushin da yasa Fu'ad dago idanunsa, idonsa bai sauka ako'ina ba sai akanta yadda ta fadi ruwa ya jiqata da yadda ta fashe da kuka......

To be continued.....

#like
#comment
#share