NURI

AFIF-SUHANA 1

by @saddiqahhh

NURI


By Saddiqa



SUHANA'S POV  
Tana tsaye gaban mudubi tana karewa kanta kallo. Kamar weather din garin ya amsheta sosai don ta sake haske akan nata na da. Shirin makaranta ta gama amman ta tsaya kawai tana karewa kanta kallo kamar she's admiring something new on her. Sanye take cikin ash chiffon abaya da tayi rolling da black jersey veil daya mugun haskata, tayi kyau sosai don tana da kyau irin mai sanyin nan. Wayarta ta dauka dake nan ajiye kan mudubi ta juya ta dauki jakar makarantarta ta fita. 

Tana fitowa ta sauya fuska to a soft expression ta fara tafiya ahankali har ta fito daga hallway din da dakinta yake. Da kallo tabi Nadeer babban dan Uncle Farouq dake around 12yrs. Tana ganinta ya washe baki yana cewa "ywwa Adda don Allah zo kiyi min wannan question din shi kadai na kasa amsawa."  

Jin yace mata Adda yasa ta dawo normal wannan silly face din data dorawa kanta ya dawo normal ance mata Adda. Zama tayi akusa dashi tana cewa "Ina Nadra bata gama shiryawa ba ita?"  


Kai ya gyada mata yana zama kusa da ita ya miqa mata littafin. Karba tayi tana dubawa ganin maths ne yasa lokaci daya ta koya masa don kanta yana mugun jan maths. Kamin su gama Nadra ta fito fuskarta shabe-shabe da hawaye duk ta bata uniform din dashi.  


Dariya Nadeer da Suhana suka fara yi kasa-kasa don tana jinsu zasu sake kunnata. Ta tsani makaranta na wuce misali kullum da kuka take zuwa ta kasa sabawa she's at her 7yrs tana da kanwa mai suna Narjis wadda ke shekara biyu kawai. Aunty Mima mamansu ta biyo bayan Nadra dake kuka tana cewa "ranki mugun baci zaiyi Nadra, banson shashanci kullum ke sai anyi dake hardai akan makaranta ne amman idan wasa ne kece a gaba, bari Abban naku ya fito boarding zance akaiki nagaji kuma."  


Jin boarding yasa Nadra sake fashewa da kuka Aunty Mima ta daka mata tsawa tana cewa "shut the hell Nadra, uff naji daga ke duka zan sa miki kuma, abin naki harda iskanci."  


Da sauri Suhan ta miqe ta karasa wajen Nadra ta riqota jikinta tana cewa "Ayya Momma kiyi haquri haka don Allah." Hadawa tayi da Suhan da Nadra din duk ta zuba musu harara tana cewa "ai dole ki goyi bayanta don halinku daya kam." Murmushi Suhana tayi ta jata suka je suka zauna akan dining tana share mata hawayenta da duk ya bata mata fuska.  


"Look at you Nad, duk kin batamin wannan fuskar taki haba mana 'yan matana..." Baki Nadra ta turo gaba amman bata ce komai ba. Nadeer dai banda tabe baki babu abinda yake, yana tsaye ya gama serving kansa breakfast ya zauna ya fara ci ya rabu dasu. Suhan da kanta tayi serving dinsu chips da omelette a plate daya ta hada musu tea a cups daban daban ta ajiye musu. Ita ta zage taci Nadra kam kadan taci tace ta koshi don haka ta saba dama. Itafa har akwai makaranta to farin cikinta ya tsaya har sai an dawo kuma.  


Uncle Farouq ne ya sauko sanye cikin suits navy blue da suka amsheshi. Shine autansu Abbie da yake at his 46yrs yana aiki as a lecturer a TUM. Kallonsu yayi yana girgiza kai ganin hjy Nadra tana zaune fuskar nan ba annuri. 

"Let's go guys, duk wanda yasan yayi kuka idan muka dawo anjima ba za'aje picnic dashi ba." Wani ware idanu Nadra tayi, anyi zancen inda tafi kauna, harkar wasa da outings sune abinda take mugun kauna. Miqewa Nadeer da Suhan sukayi suna cewa "can't wait..." Sai Nadeer ya kalli Nadra da tsokana yace "su wata kuwa ba zuwa...."

"Dalla can ina ruwanka dani, wallahi Ka fita a idona na rufe..." Yadda kasan itace yayar. Aunty Mima data fito daga kitchen tana ajiye musu lunch box dinsu ta galla mata harara tana cewa "sa'anki ne kike masa magana a haka....." Kasa tayi da kanta tana turo baki. 

"Let's go I have a meeting karku makarar dani...ke kuma ba lecture din 8 ne dake ba kika kak har yanzu baki tafi ba?" Yi Suhan tayi kamar ba da ita yake ba. 7:30 a lokacin kamin a sauke su Nadeer awuce a kaita already 8 zai iya yi. "Kindly call an uber or better kije ki tsare cab ki hau, wannan uwar kin bokon probably ke tayo." 

Kindly Suhan ta miqe ta dauki jakarta ta rataya tayi musu sallama ta fice. Mai cab ta tsare tana fita ta hau tayi masa bayanin inda zai kaita suna schwabing kuma ba wni nisa sosai yake dashi ba daga makarantarsu. 

Waren 8 ta shiga class dinsu Allah ya taimaketa tana shiga lecturer dinsu ya shiga shima daman babu wanda ta saba dashi don haka ita kadai take rayuwarta for now duk da akwai wanda suke mata magana amman bata wani biye musu. Tafi so ta gane yadda makarantar yake da yadda character din 'yan ajin nasu yake before she opens up to them.

After 10 suka fito and sai 12 zasu sake wani class din. Don haka ta wuce wani corner da ta zauna jiya da yake nan very cosy and bai da wani hayaniya sam it looks more like a garden. Tun kamin ta karasa ta ciro wayarta daga jaka tayi dialing number din Ammi. After series of ringing ta dauka.

"Ammi jiya ba muyi waya ba kuma baki neme ni ba, Ammi kin dena sona ne wai?"

"Wannan itace sallamarki Suhan?"

Hannu tasa ta dafe bakinta da sauri tana ware idanunta kamar tana gaban Ammi kamin tayi sauri tace "I'm sorry Ammi, Assalamu alaikum."

"Wa'alaikumus Salam Suhana, how's everything there?"  

"Not fine Ammi."  


"Ysu Uncle dinki?" Ammi ta watsar da wancan amsar data bayar don tasan shirmen Suhan ne kawai.

"They're doing well Ammi. Ammi wai ni sai yaushe zaku zo ne?"

"Watanki nawa acan?" Shiru tayi tana tunanin amsar bayarwa don tasan Ammi sarai tasan ba tayi wata da zuwa ba. "Ko watan fa banyi ba Ammi..." Ta amsa mata da shagwaba daidai tana ƙarasawa garden din ta zauna tana saka wayar a hands free ta ajiyeta agefenta ta ciro wata bottle dinta dake da ruwa mai sanyi.

"Hope kina karatu dai ko?"  

"Yes Ammi, ina Hamma F?"  


"I donno Suhan, har yanzu baki dawo hankalinka ba ko? Fu'ad dai Fu'ad again? Don't call me again hardai kinsan zakiyi mun zancensa ne." Ammi na fadin haka ta kashe kiran. Da kallo Suhan tabi wayar tana cewa "Ammi I just asked fa, I missed him fa... Lemme call him." Da sauri ta dauki wayar tayi dialing number din Fu'ad. Ringing uku kawai yayi picking call din a time din yana side ana nuna masa yadda komai yake "Assalamu alaikum Hamma."

"Wa'alaikumus Salam Suhana how're you?"

"Alhamdulillah Hamma, baka kirani ba ko sau daya kaji yadda nake anan."

"Nasan kina lafiya Suhana.." shiru tayi kamar this is not what she expected as an answer.

"So how's your studies and everyone there?"

"Lafiya lau Hamma..." 

"I'm currently doing something Suhana let's talk some other days kinji..." Kamin ta amsa ma ya kashe wayar. Wani irin abu taji ya tsaya mata na yadda ya amsa mata a gajarce da saurin ending call din da yayi. 

"Hamma F bai damu dani ba.." ta fada da zallar muryar yarinta. Ji tayi kamar ta kira Aira ta fada mata amman tasan she's not available suna lectures don interval din one hour kawai ne a tsakininmu.

"Ba wanda zai fahimceni sai ita..." 

*________*

Tunda ta shigo wajen ta takura masa, wanzuwarta a wurin yasa karatun da yake dena shiga kansa. The way take surutu da daga murya sannan daga ji muryarta akwai sakalci da zallar sangarta a tare da ita. Ba wannan ba damuwarsa kawai yadda tabi ta cika wajen da surutu. He's solving some critical physics questions that need full attention ammn she's diverting his attention.


Dagowa yayi for the first time tun zuwanta wurin kusan 15mins ya sauke idanunsa akanta. Kanta yana kasa ne tana typing text wa Aira, side view din fuskarta kawai ya gani ya mayar da kansa kasa yana addu'a Allah yasa ta kammala surutun haka.

Cigaba da karatunsa yayi sai dai tun bai yi nisa ba yaji ihunta da yasa ya dago da sauri. Tana tsaye tana karkade hannunta har sannan bata dena ihun ba idonta yana duba jikinta kamar dai akwai abinda ta gani daya bata tsoro.

Bai san ya akayi ba sai ganinsa a gabanta yayi yana cewa "hey are you ok?"

Da sauri Suhan ta juyo ta sauke idanunta akansa kaman yadda shima nasa ya fada cikin nata. 

"What is it?" Afif ya sake tambayarta.

Da wannan muryar nata na yara tace "butterfly ne yabi jikina, and it's not beautiful it's somehow scary..." 

Wani banzan kallo yayi mata yana cewa "you're not serious...can you please move out from here? Kin hanani karatu.."  


Cikin idonsa ta kalla tana cewa "to ai bansan kana nan ba nake yin surutun assignment nazo zanyi nan din."

"That's your business not mine, make sure baki kara distracting dina ba if not...."

"Ko ka gina wajen ne..." Juyowa yayi daga tafiyar daya farayi inda ya zauna ya kalleta da kalar rainin da tayi masa magana yace "you either don't have a share anan just like I do..."

"Ohhh haka fa ashe..." Komawa yayi ya zauna itama ta bude jotter dinta ta fara assignment din da ba tayi nisa ba ya kulle mata kai. Ta saba da magana da kanta normally ko a gida don haka assignment dinma tana yi ne kamar wani take koyawa. Duk ta hana Afif karatu gaba daya, banda tsaki babu abinda yake yi akai-akai.

"Yah Allah ya zanyi wannan?" Ta tambayi kanta tana dagowa ta dubi Afif da kansa yake kasa amman kana gani zaka san ba karatun yake ba. Dan dago kanta tayi daga nan tana duban littafinsa taga kamar calculus yake don haka ta miqe da sauri taje inda yake tana karewa abinda yake yi kallo.

For a moment binta da kallo kawai Afif yayi yana tunanin is she really ok. Ita kuwa kawai neman wanda zai koya mata nata aikin take hakan yasa ta manta sam bama tasan waye ba.

Sai data gama duba abinda yake yi tsaf sannan ta dago suka hada idanu. Marairaice masa fuska tayi yadda zai tausaya mata tace "don Allah naga ka iya ka koyamin..."

Miqewa yayi gaba daya yana cewa "ban iya ba..."

"Ba kyau karya....Allah ka iya kuma...kalli fa yadda kayi naka....."

"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakeel..." Tunda yazo Munich zai iya cewa bai hadu da wadda ta takura masa ba kamar wannan acikin kasa da minti talatin ta hanashi sakat.

"Don Allah ka iya wallahi kaji dan kasarmu..." Yanzu kam idanu ya bita dashi, ko waye yace mata kasasrsu daya oho.

Zata sake magana sukaji murya daga bayansu calling Afif. Rufe idonsa Afif yayi ya bude yana cewa "damn it..." Kawai sai yaji yau kamar bai zo makarantar a sa'a ba. Alissa ce stalker dinsa yarinyar da tunda yazo TUM ta kasa barinsa ya huta da takurarta.

"Hi handsome how're you?" Kallonta Suhan tayi kamin ta sake kallon yadda Afif ya dauke kansa ta bude baki za tayi magana Alissa ta rigata da cewa "who's this girl? Is she your sister your look alike..." Samun kansa yayi da kallon Suhan da itama ta kalli Afif din da Alissa ke cewa suna kama. Shi dai bai wani ga kamar da suke ba kawai dai dukansu farare ne that's it bayan wannan. 

"Yeah she's can you please excuse us?" Ya bata amsa da sauri yana cewa Suhan "ina littafin let me show you yadda zakiyi kema ki barni na huta." Da sauri ta miqa masa littafin tana cewa "thank you so much." 
 
"Handsome I want us to discuss something please can we?" 

"I'm not available as you can see..." Zama yayi Suhan ta zauna daga gefensa tana miqa masa pen din hannunta ya amsa without looking at her............

To be continued....  

#like
#comment
#share