THE FIRST SIGHT
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
FU'AD-NURI POV
Janye idanunsa yayi ahankali daga kanta yana zaro wayarsa dake ringing daga aljihu. It was Suhana calling him right after she finished talking with Ammi. Kasancewar he's on work yasa yayi briefing wayar nasu. "Let's go" ya fadawa Ibrahim dake tare dashi suka fara takawa gaba.
"Go to her, kace ta tashi daga zaman da tayi a kasa." Fu'ad ya fadawa Ibrahim referring to Nuri who was crying, and her crying was getting to him. Bai son kuka sam especially daga mace, he really can't stand seeing a woman crying. Ibrahim ya tafi wurin da take nan azaune tana murje inda bokitin ya dira mata akafa da yake mata zafi sosai.
"Sannu baiwar Allah kiyi haquri ki tashi kinji." Idan kasar dake wurin ta kula Ibrahim to Nuri ta kulashi. Yadda kasan bata san da wanzuwarsa awurin ba kuma sarai taji shi bawai ba taji shi ba. Haka ya gaji da mata magana ya koma wurin Fu'ad dake duba saqon da Fa'iz ya turo masa awaya. "Sir, she refused to get up." Aljihu ya mayar da wayarsa yana tabe baki yace "Continue with your work. I think I'm going to handle this myself." Ya fada yana nufar hanyar da Nuri take.
Time din da ya kusanto dab da inda take, both of them, shi da ita, their hearts started beating almost 40% faster. Wanda hakan yasa Nuri ta kasa ko motsi tana cigaba da hawaye. She just assumed maybe there was something wrong with her heart because this felt so unusual.
Shi kansa Fu'ad don namiji ne ya dake sosai amman da ace shi kadai ne ba'a hanya yake ba babu abinda zaisa bai samu wuri ya zauna ba. He started to wonder if maybe something was actually wrong with him too.
Time din daya zo wajen da Nuri take yaso ya wuce ya rabu da ita. Sai dai sautin fitar kukanta da wannan siririyar muryar nata yasa shi tsayawa. Bai san mene ya jashi towards her ba, he just found himself kneeling in front of her. Kanta yana kasa, black jersey veil din data yafa akanta ya dan ja baya kadan daya bawa kwantacciyar baqar sumar kanta damar fitowa kadan data kawata goshinta dake nan dauke da tabon sallah daya mata kyau sosai.
Tsugunnawar da yayi ya haifar da kusanci kadan ba mai yawa ba atsakaninsu wanda ya kara musu abinda suke ji a zukatansu. Nuri dake nan shagwababbiya da kuka bai mata wahala tuni ta kara sound din kukan nata kamar ta manta a waje take haka.
"Assalamu alaikum...." Da kyar ya samu kansa da iya furta mata sallamar don ji yayi gaba daya komai na kansa yana daukewa sakamakon yadda yakejin zuciyarsa. Kasa kwakkwaran mosti Nuri tayi tana shaqar daddadan turarensa na Pur Oud LV daya cika mata hanci. Wani kamshi da tunda take a rayuwarta bata taba jin kamshi mai dadi da sanyaya zuciya kamarsa ba. The scent alone erased half of everything that had been bothering her, from the moment she came back to when the water spilled all over her.
"Hey, can you please stop crying...?" Ahankali ta samu kanta da dago da wannan fuskar nata dake dauke da manyan dara-daran idanuwa masu mugun daukar ido wanda suke dauke da eyelashes baqaqe wuluk da suka jiqe sakamakon kukan da takeyi.
Haduwar idanunsu waje daya yasa Fu'ad saurin furta "Ya Salam!!" Never in his life had he seen what he saw in her eyes. Ba wai kyan idanunta kawai ba. There was something else in there, something he couldn't name. This was the first time he was seeing it in a woman. Bai sani ba ko mata kawai ke dashi and shi ba gwanin kallon mata bane. Da sauri ya dauke idonsa daga kallon cikin idanunta saboda abinda yake gani mai kaifi daga nata idanun kamar bazai iya jurar gani ba.
"Ki tashi kin jiqe da ruwa, go back home...." Juya idanunta tayi da sauri daga kallon nasa idanun da tunda take bata taba haduwa da wanda ya taba yi mata kwarjini a duniya kamarsa ba. Just his presence alone yasa taji iska kamar ta canza tayi mata kadan.
Tsabar yadda takejin wani iri yasa bama tasan sanda ta bude baki without looking at him da wannan muryar nata dake dauke da shagwaba many times tace "kafana zafi yake min, ni ba iya tashi zanyi ba..."
Da sauri ya dawo da fuskarsa daya kawar daga kallonta tun dazu yana sauke idonsa akan cute mouth dinta da tayi magana. Miqewa tsaye yayi yana cewa "you can. Just stand up slowly..." Shiru tayi masa tana fara kokarin miqewa ahankali don dagaske take kafarta wani irin zugi take mata da takejin kamar ba zata iya takawa ba. Da kyar ta tsaya atsaye without looking at him zata fara tafiya yace "where's your house?" Da wannan dogayen yatsun nata ta nuna masa gidansu dake dan gaba kadan da wurin ya gyada kai kawai yana juyawa da kansa ya dauki bokitin nata daya fadi ya tarar mata sabon ruwa ya jira ya cika ya dauka yabi bayanta har zuwa kofar gidansu ya ajiye yana cewa "zansa akawo miki sauran, take care...." Bai jira amsarta ba ya juya ya bar wurin. Samun kanta tayi da bin bayansa da kallo. Dogo ne mai ginannen jiki that's showing cewa yana gyming, fari ne tas don tana ganin yadda fatar keyarsa dake dauke da wani curly black hair ke nunawa sosai.
Ba wannan ba, wannan kamshin data lura kamar daga jikinsa ne take shaqa har yanzu kamar awurin ya fesa ya biyota dashi har nan sannan ya tafi ya bar mata shi. Dauke kallonta daga kansa tayi tana jinta wasai zuciyarta ta dawo normal yadda yake da ba wannan sauyin da takeji tun da safe daya takura mata. Da dingishi ta shiga gida tana sallama. Mami data fito waje fara hada kayan sana'arta ta bita da kallo ganin yadda take tafiya.
"Me ya sameki Nuriyya...." Wani kalar shagwababben kallo tayiwa Mami ta bude baki da muryarta daya fara rawa za tayi kuka daga kawai Mami ta tambyeta Mami ta dakatar da ita saying "Allah y baki haquri, ba kuka nace kiyimin ba. Cewa nayi lafiya naga kina dingishi, me ya faru?"
"Ba bokitin ruwan bane ya fado ya jiqani kuma ya sauka a kafana ba..." Sai a sannan Mami ta lura ashe har jiqewa tayi. "Subhanallah, sannu kinji...." Ta fada tana karasowa wajen da take ta riqota za tayi magana sukaji sallama daga waje ana cewa "Salamu alaikum ga ruwan..." Daga haka sukaji shiru. Kalamansa na karshe suka dawo mata kai daya ce zaisa akawo mata sauran ruwan kenan har ya saka an kawo mata. Kawar da tunaninsa tayi tana kallon Mami tace "Mami ki gasamin kafar."
Kai Mami ta gyada mata tana cewa "In Sha Allah yanzu ma, bara ruwan dana dora yayi zafi jeki canza kaya to." Ciki ta shiga tana tafiya ahankali ta sauya kayanta zuwa wani baqin wando palazzo da white t-shirt ta daura mayafin dake kanta kawai ta samu wuri ta zauna. Wannan mayen kamshin nasa da ta shaqa har yanzu takeji. She looked around to make sure he hadn't come to their house, because she could still smell him.
"Wanne kalar turare ne wannan?" Tayiwa kanta tambayar da bata da amsarta. Shigowar Mami yasa ta dawo daga tunanin da take tabi Mami dake dauke da towel da ruwan zafi a roba da kallo. Daure fuska tam Mami tayi tana zama kusa da ita babu wasa tace "oya, let me see your leg..."
Shiga taitayinta Nuri tayi ganin yadda Mami ta daure fuska ta nustu don tasan ba zata dauki shirmen da za tayi ba kuma. Ita kanta Mamin tayi hakan ne don kar Nuri ta bata mata lokaci da sakalci da tabarar da take bata mamaki. A cikin ruwan zafin da baya da yawa Mami ta sa wani part din towel din sannan ta fito dashi tana riqo kafar Nuri da tayi saurin tasowa zata rungume Mami "don't malama, bansan shirme wallahi, kin sani sarai..."
"Allah Mami akwai zafi....ki yiwa Allah kar kimin da zafi..." Harara mai kyau Mami ta balla mata tana cewa "zan kyaleki keda kafarki Allah."
Shiru tayi tana sakin hannun Mami data damqe tana rufe idanunta. Ita kanta Mami bata wani danna mata da kyau ba don ba kasafai ta fiya son kukan Nurin ba, she was so dear to her. Tana ganin kamar ita kadai take da ita arayuwarta yanzu which is true, Afif yayi nisa sosai da ita.
Just 5 minutes Mami ta gama ta miqe ta fita tana cewa "kizo kici abinci, shine abinda yafi damuna. And don't let me hear that crying voice again, in ba haka ba ranki baci zaiyi....." Baki ta turo gaba da zallar shagwaba tana kallon Mami data gama magana ta fita.
Iska ta shaqa da kyau tana sake jin wannan kamshin daya tashi kanta dazu har yanzu. Abinda yafi tsayawa aranta shine yadda babu wani contact da suka samu, so how come she could still smell him on her?
"Ba zaki fito ki debi abincin ba ko?" Da sauri ta miqe tana takawa ahankali ta fita kamin Mami ta sake magana. Abincin ba wani da yawa ta zuba ba ta wuce without letting Mami ta ganta don zata mata fada akan yadda ta zuba abincin kadan. Ita kuma ji tayi kawai lokaci daya anyi wiping gaba daya yunwar da take ji alhalin da wata azababbiyar yunwa ta dawo.
Dan wanda ta zuba dinma bata iya cinyewa ba ta miqe a sace ta ajiye sannan ta fita zata taya Mami aiki ta kadota tana cewa ta koma ta huta don ta lura idan ta tayata aiki gajiya take kuma gajiyar baya barinta tayi karatu data fara sai bacci. Ita kanta bata san me yasa takejin wani sanyin jiki ba daga haduwarta da wannan mutumin da kallo daya kawai tayi masa, shima idonsa kawai ta kalla tayi saurin dauke kanta don ba zata iya jurar kallonsa ba saboda kwarjinin da yayi mata.
Kwanciya tayi tana daukar wayarta ta fara neman layin Zara tunawa da tayi sun danyi kwana biyu basu yi waya ba. When she called it said the user was busy, so she hung up smiling, knowing Zara was probably talking to her boyfriend. Sai ta mayar da wayar nata wurin Afif da shima baiyi responding ba saboda Suhana data takura masa sai yayi mata assignment.
Ajiye wayar tayi kawai tana yin kwanciya ringingine idonta yana kallon roofing din dakin. Gradually their scene started replaying in her head, from when she first fell to the ground, to when Ibrahim came and talked to her, to when Fu'ad, who she didn't even know, came too. She paused for a moment and asked herself me yasa zuciyarta akan na karshen kawai ya sauya mata ba Ibrahim ba?
Kawar da tunanin tayi tana jawo wani littafin azkar na Mami kawai ta fara karantawa saboda ta daina tunanin da sam bata san dalilin yinsa ba. Tanajin hayaniyar Mami da masu siyan awararta amman haka ta kasa fita ta taya Mami aiki sam, ji tayi gaba daya bata da wani kuzarin yin aiki kamar an kwashe mata dan kuzarin da take ciki.....
To be continued.....
#like
#comment
#share