NURI

UNWANTED BUT UNFORGETTABLE

by @saddiqahhh

NURI

  
By Saddiqa


FU'AD'S POV

Tunda aka bude masa motar ya shiga back seat, idonsa yake a rufe har zuwa sanda suka isa Bristol. At that moment idan da za'a tambayeshi me yake tunani shi kansa bai sani ba. Kawai dai one thing daya sani shine yaji zuciyarsa tayi wani irin fayau, kamar ya bar wani piece of himself a wani wajen da bai sani ba, wanda bai taba jin haka ba all his life.

Bai wani tsaya delay ba lokacin da driver ya bude masa motar ya fice, yanajin son yagansa shi kadai a kebantaccen waje. Already an riga an kama masa VIP suit, don haka babu bata lokaci ya wuce, staff din suna take masa baya. Umarni ya basu kada wanda ya takura masa, bayan sunje idan yana buqatar wani abun zai kirasu a waya, sannan ya shige ciki. Qaton parlour din ya fara bi da kallo, very simple yet elegant.

Ajiyar zuciya ya sauke yana cire tie din dake wuyansa, yaje wurin switch ya kashe hasken dakin gaba daya, sannan ya wuce bedroom din dake nan qato yana screaming luxury. Shima ya maida wutar dakin dim sannan ya fara unbuttoning shirt din dake jikinsa, yana jin wanka kawai zaiyi ne kawai zai dawo dashi daidai, ko zai dena jin wannan emptiness din da yakeji ajikinsa, daya rasa daga inda ya samo asali.

Bathroom ya fada, ya hada ma kansa warm water, yayi wankan daya bata almost 30mins. Ya fito dab da sallahr Maghrib sanye da black bathrobe data bala'in haskashi, hannunsa daya dauke da black towel yana tsane sumar kansa dake nan curly mai santsi da baqi dake nan akwance akansa. Wurin mirror ya nufa ya tsaya yana bin kansa da kallo, kamin ya dauki dryer ya fara busar da gashin kansa, ya gyara shi tsaf da mayukan da yake amfani dasu. Yadda yake tattala sumar kansa ko wata macen albarka.

Yana kammalawa da kansa ya koma jikinsa, ya shafeshi da signature body lotion and mist dinsa masu mugun kamshi, don duk wani abu da zai buqata duk guards dinsa sun riga da sun sani don haka sun saka masa komai, sunsan fabrics da komai da yake amfani dashi. Yana gamawa ya wuce closet, ya shirya cikin simple outfit na Prada, that's white trouser da white t-shirt da aka rubuta Prada agaba da baqin zare, yazo ya feshe jikinsa da wannan signature perfume din nasa.

Wuri ya samu agefen gado ya zauna, yana daukar wayarsa yayi dialing number din Ummi. Bugu biyu ta dauka, without doing sallama tace "Hayaty sai yanzu zaka kirani bayan nasan ka dade da isa?"  


Goshinsa yayi rubbing yana cewa "gosh I'm sorry Ummi, I'm occupied ne. Site na fara zuwa, sai yanzu ma nazo masaukina. How's everything there Ummi?"

Ajiyar zuciya ta sauke jin yace site yaje, tasan ba lallai ya hadu da ko wacce mace. Ita yanzu babbar damuwarta kada ya kula ko wacce diya mace, bare ya baro mata aiki. Duk kuwa ranar daya fara son wata ta tabbatar kashinta ya bushe, coz Fu'ad idan yana son abu yana so ne da dukkan zuciyarsa. Tasan daga ranar daya fara son wata, sai abinda take gudun ya faru, which is her downfall.

"Lafiya lau Hayaty, bakaci abinci ba ma ko?"  

Kai ya gyada mata kamar tana ganinsa yace "yanzu zanci Ummi..." 

"Oya maza je kaci, idan ka gama sai muyi wayar..."  

Daga haka ta kaste wayar, shi kuma instead of yasa order din abincin just like she said, sai yayi dialing number din Azzam da kullum sai ya kira baya samu. Ya rasa ina ya shiga haka da sam ba'a samunsa, abun is very obvious to him.

Ajiye wayar kawai yayi, yana girgiza kansa tare da cije lips. Zuciyarsa na raya masa yasa a binciko masa inda yake, while a daya side din yana jin ya bari ya dawo don kansa sai ya titsiyeshi.

Rufe idanunsa yayi da niyyar yayi relaxing kamin Maghrib ta karasa. Yana rufe idanunsa, zuciyarsa tayi masa flashback din haduwarsu shida ita. Da sauri ya bude idonsa, yana kallon sama, like... me yasa zaiyi tunaninta? Never in his life ya taba haduwa da wata ta fado masa a tunani bayan sun rabu, sai ita.

Sai dai ahakan ma zuciyarsa ta cigaba da hasko masa fuskarta, wannan goshin nata mai dauke da kwantacciyar baqar sumar data bayyana kadan, da wannan idanun da bai taba ganin idanu masu fizgar hankali kamarsu ba.

Tsaki yayi, yana kawar da tunanin daga ransa, at the same time yana questioning kansa why zai ke yin tunanin wata daga haduwarsu kawai? Agogon dake dakin ya kalla, yaga akwai akalla 20mins kamin lokacin sallah ya shiga. Don haka ya dauki wayarsa da niyyar dannawa, kunnensa ya tariyo masa muryarta, lokacin da take fada masa da wannan muryar shagwabar nata daya kasa barin kansa "kafana zafi yake min, ni ba iya tashi zanyi ba..."

Dakatawa yayi daga danna wayar da yake shirin yi. He admits it, yes bai taba jin muryar da ta kai nata ba, very soft, sweet, melodious and yet captivating.

Wani tsaki ya sakeyi yana cewa "Fu'ad you should be back to your senses, what's wrong with you?" He just sighed, and call yayi order akawo masa fried rice da pepper soup kawai, sai cold watermelon smoothie, hoping Allah yasa ya iya ci. Don all of a sudden yaji kamar an dauke masa appetite dinsa.

As he expected, kasa cin abincin yayi. Yaji kawai ya koshi, don haka bayan an kawo masa ya bude, yaji bazai iya ci ba, sai ya mayar dashi gefe. Ya tashi ya shiga bathroom ya daura alwala, ya fito fuskarsa na disar da ruwan alwala, ya fita zuwa masallaci. Yana son yayi occupying kansa, don karma zuciyarsa ta samu damar yin tunani akan kowa da komai. Tana daga sahun farko sakamakon zuwan da yayi da wuri, sannan ko bayan da aka idar da sallar bai tashi ba, sai yaja can gefe ya dauki Al'qurani ya fara tilawa a zuciyarsa, duk don ya zama occupied. It seems to him when he is idle, zuciyarsa zai ta tuna masa scene din dazu, and hakan kamar haushi ma yake bashi.

Yana nan zaune akayi kiran Isha. He waited har sanda aka tayar itama, yabi nata jam'in. Bayan an idar ya tashi, yayi shafa'i da wuturi, still ya zauna yayi addu'o'insa daya saba, sannan ya tashi ya fita ya koma ciki. Yana shiga ya hadu da guards dinsa, suma dawowarsu kenan daga masallacin, don majority of them are Muslims, sai dai su ana idar da sallar suka fice a masallacin.

Tambayarsa sukayi ko da akwai abinda yake so, yace musu a'a, kowa yaje ya huta, sai gobe kuma idan Allah ya kaimu. Sauqin kan Fu'ad yana mugun burgesu, har suna jin suma idan Allah ya kaisu irin nasa matsayin, babu abinda zai hana suyi koyi da kyawawan dabi'unsa.

Babban abinda zai burgeka da Fu'ad shine simplicity dinsa. No one zaice he owns NoveBuild sam. Yadda yake mu'amala da mutane, kamar ba wani shahararre dan shahararre ba. Ya mugun iya zama da mutane, and that's why babu inda zaije ba'a so shi ba. Wannan halin nasa yana daga cikin abinda yake kara masa farin jini.

Dakinsa ya koma, thinking of abinda zaiyi, it's like babu wani abu da zaiyi. Tunawa da yayi kamar an turo masa mail daga NoveBuild UAE, yasa kai tsaye ya wuce bedroom, ya dauki MacBook dinsa ya duba abinda aka turo masa. Ganin aiki ne, ya zauna yana duba files din da komai da aka turo masa, har ya kai after ten abinda yake yi kenan.

Time din daya kammala is past eleven, still yaji baya son cin abinci. Don haka kawai ya dauki ruwan mara sanyi yasha, sannan ya wuce bathroom ya sake sabon wanka. Ya fito yana kamshin shower gel dinsa. Cikin fararen pyjamas ya shirya kansa, still wannan mayen kamshin nasa yana tashi, duk kuwa da cewa bai saka turaren ba sam. Kawai tsabar yadda yake amfani da turaren ne yasa jikinsa gaba daya ya zama ko yaushe kamshin da yake yi kenan, ko ya saka ko bai saka ba.

Addu'a ya zauna agefen gado yayi na bacci, yana tunawa bai sake kiran Ummi ba, gashi yanzu dare yayi. Haka nan ya kwanta with the intention zai hada ya kirasu duka goben, ita da Abie da sukayi waya tun a site.

A side din damansa ya kwanta, yana sake wata sabuwar addu'ar na bacci, yaja blanket ya rufe zuwa waist dinsa, yana rufe idonsa da yake fatan bacci ya daukeshi immediately.

Sai dai ba baccin ba. Muryarta again yaji tana yi masa echo, kamar yanzun take yin maganar. Bude idonsa yayi, yana sake jan tsaki a fili yace "what's this again?"

Ba muryarta kawai ba, gaba daya kamanninta suka hau dawo masa kai. Tun daga goshinta mai dauke da kwantacciyar baqar suma, har zuwa bakinta da dimples din daya lura kamar tana dashi. Kallo daya yayi mata, amman irin kwakkwaran nan daya haddace yadda fuskarta yake tsaf. Akwai wanda idan kuka hadu dasu, whether kunyi magana ko bakuyi ba, haka zakuyi ta tunasu. To same thing yake faruwa da Fu'ad, da a dole yake son yakice tunaninta. Abinda bai taba faruwa dashi bane wannan, ya hadu da kai ya koma gida yana tunawa da kai, sam baya haka. But today, first in his life hakan yana faruwa dashi.

Babban abinda yake tunawa da ita shine muryarta data tsaye masa a zuciya, sai kuma idanunta. Da tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin idanun da suka fizgi hankalinsa ba kamar nata, koda don baya karewa mata kallo ne oho.............

JANNAH'S POV....

Shiryawa takeyi cikin wani Swiss lace mai ubansun tsada, da akayima dinkin kaftan daya mugun yiwa Jannah kyau. Ita ba wani hadadden kyau gareta ba, kawai 'yar gayu ce da zaisa ana mata kallon kyakkyawa. Wai Zaid ne zaizo zance warenta, shine Mamma ta sakata agaba ta shirya.

Ba tayi musu ba, don ita kanta tana son cire Fa'iz daga ranta ne. Rayuwa dashi taga kamar ba zai faru ba, duk kuwa da har yau har gobe zuciyarta tasa ce ta kasa daina sonsa. Metallic veil ta yafa kalar onion da zai hau da lace din jikinta, ta saka turare kadan yadda ba zai tashi ba, ta dauki wayarta ta fita.

Da kallo Mamma ta bita time din data sauka kasa. Tausayinta ya rufeta, ganin mace har mace amman ta kamu da son wanda bai ma san tana yi ba. "Mamma na tafi."  


"Take care Jannah....Sara zata kawo miki drinks da snacks din.."  

Kai ta gyadawa Mamma kawai, tana fita daga parlour.

Time din data nufi part din da aka sauke Zaid, sai data dan dakata. Zuciyarta na gaya mata dama Fa'iz ne ba Zaid ba, dama Fa'iz tayiwa wannan kwalliyar ba Zaid ba. Ture tunanin komai tayi, ta shige ciki bakinta dauke da sallama aciki ciki.

Yana zaune akan kujerar dake daga farkon shiga parlour, babba ne don zaiyi akalla shekara 45 haka. Gashi da jiki duk da ba wani mai yawa ba, and gashi baqi yasha farin shadda. Dauke idonta Jannah tayi daga kansa, zuciyarta ma hasko mata Fa'iz dinta. Fa'iz dake nan shima ba wai fari ne tas ba, kawai yana da haske kadan. Jikinsa daidai dashi, ko wacce shiga yayi sai yayi kyau, kaji kamar don shi kadai akayi kaya.


Alokacin Jannah ji tayi anya bata yaudari kanta ba kuwa? Anya ba cutar kanta take yi ba? Anya ba zata tari Fa'iz ta fada masa dakon sonsa da take yi ba? Anya zata iya haqura da Fa'iz Aliyyu Ardo kuwa?

To be continued......

#like
#comment
#share