NURI

TOMORROW WITH YOU

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa



She can't gaskiya! Haqura da Fa'iz shine last abinda za tayi a duniya. She loves Fa'iz and Fa'iz will know. Zata fada masa for sure ba zata iya haqura da shi ba she will even beg him if it comes to that. Ta haqura da dakewar da jurewar, because love can't be hidden.

Da ace Zaid bai ganta ba da juyawa za tayi to amman ya riga da ya ganta. Lokaci daya ta fara jin haushin kalar kwalliyar da tayi wanda Fa'iz kawai ya dace ace ya gani. Kwalliyarta da ita kanta are meant for Fa'iz only.

Hade rai ta samu kanta da yi bayan ta zauna a kujerar dake can nesa dashi a parlourn. Shima yanayinta yasa ya sha jinin jikinsa ya kureta da kallo. Yana son Jannah don ta iya kwalliya, yes 'yar gayu ce lamba daya. "Sannu gimbiya."

"Sannu" ta amsa masa da kyar don tana jin kamar muryarta ma ya haramta kowanne namiji mai sonta yaji har dai ba Fa'iz ba. She will fight for Fa'iz's love with everything she has.

Sallamar Sara ta dawo da ita daga tunanin yadda zata tunkari Fa'iz da zancen. Kallon Sara tayi dake nan kamar ita sak da sak. Gaishe da Zaid tayi sannan ta ajiye tray din dake hannunta ta juya ta fita.

Zaid ya taso ya dawo kujerar dake kusa da wadda Jannah ke kai yana kallonta. So yake suyi magana na fahimtar juna shi da ita.

"Gimbiya ina so muyi magana amman ko yaushe bakya bani dama."

Kallon cikin idonsa Jannah tayi tana cewa "ina matarka Zaid? Me yasa kake so ka aureni?"

"Wallahi kin iya kwalliya sosai na wuce lissafi ita kuma yadda kika san matan kauye...."

Hannu ta daga masa tana miqewa tsaye ba tare data kalleshi ba tace "dakata Zaid, ka riga da ka fadi tun anan...ba zaka zo kana kushe matarka agabana don ka burgeni ba... wannan yana nuna nima nan gaba haka zaka yimin... with all due respect Zaid, please leave. I can't marry a man with your kind of character....." Tana ida fadin haka ta juya ta barshi a zaune sororo yana binta da kallo. Ya zaiyi da ransa idan bai auri Jannah ba shi kuwa? Bai san yana sonta ba sai yanzu data furta masa ba zata iya aurensa ba. Anya ba ta sama zai biyo ba kuwa?

Tana fita ta samu tabi ta baya don karma ta hadu da Mamma a parlour. Allah ya taimaketa har ta shige dakinta bata samu kowa ba. Cilli tayi da mayafinta akan gado ta samu wuri kan sofa ta zauna. Wayarta ta kunna ta fara dialing number din Fa'iz da already ta gama haddaceta tsaf akanta.

Wannan tsoron da takeji idan tana son kiransa sam yau babu. Ta gama karfafa kanta cewa she can do this, zata fada masa tana sonsa ne ayi wadda za'ayi. Sai dai duk ranar daya fada mata baya sonta tana jin karshenta yayi kawai.

Tasan bai da wulaqanci sam, sai ya tabbatar mata ta hanyar picking call dinta a ringing na uku kacal. 

"Assalamu alaikum..." Yayi mata sallama da wannan husky voice din nasa dake sake sawa tayi falling masa.

Kore komai dake shirin taso mata tayi tana amsa masa sallamar da yayi.

Fa'iz a daya side din dake asibiti yana duba files din patient din da yayiwa surgery wannan satin ya amsa mata da "How're you doing, Dr Jannah?"

Tambayar nan nasa has light her up ta amsa masa da "Alhamdulillah, Dr...." Sai ta samu kanta dayin shiru tana tunanin ta yadda zata fara kuma.

"Are you there, Dr Jannah?" Ya tambayeta jin shiru, kai ta gyada kaman yana ganinta tace "ina so muyi magana, Dr.."

Dakatawa yayi daga duba file din, ya ture gefe yana cewa "I'm listening, go ahead..." Rawa bakinta ya fara tana cewa "I don't even know where to start, Dr....."

"Just start from anywhere..."

"Can we meet tomorrow?" Ta tambaya da kyar tana jin a yanzu dai courage din nata ya gudu sai dai zuwa goben idan Allah ya kaimu kuma.
"Yes of course, where should we meet?"

"It's up to you, wherever is convenient for you, Dr."

"What if it doesn't work for you, Dr Jannah?"

"For as long as it works for, zaiyi min nima." murmushi kawai Fa'iz yayi yana cewa "ok then, till tomorrow. I will text you the location. See you..." Yana fadin haka ya kashe wayar ita kuma ta samu kanta da sauke wata katuwar ajiyar zuciya kamar wata wadda tayi wani katon aiki.

Yadda take jin zuciyarta ayanzu ba zata iya haqura da Fa'iz ba no matter what kuwa. Ta jure ta daure ta kai makura yanzu, haqurinta ya qare akan Fa'iz. 

Tashi tayi ta shiga bathroom dinta tayi wani wankan ta shirya kanta cikin wani mustard nighties ta daura baqin dankwali ta kwanta da niyyar anjima ta fita taci abinci duk gudun kada ta hadu da Mamma. Sai dai bata dade da kwanciya ba bacci ya dauketa cike da mafarkai akan Fa'iz ya aminta da soyayyarta......

_AFIF-SUHANA 2_

Dalla-dalla ya fara koya mata assignment din da bai ma wahala bane honestly, while her full attention was on him. She was listening to everything and watching how brilliantly he solved it.

Lokacin da yakai karshe yana gamawa ya ajiye mata pen da jotter din ya miqe tsaye without talking to her ya kama hanyar ficewa daga wajen don karatun yanzu ya fitar masa akai gaba daya. Da kallo ta bisa ganin har ya fice. She didn’t even thank him, but he owed her that at least.

Miqewa tayi itama ta tattara komai nata ta fita zuwa wani private area ta samu wuri tayi sallar Azahar da lokacinsa ya shiga. Bayan ta idar ta miqe ta wuce inda zasuyi last lectures dinsu daya daukesu 2hrs suka fito karfe hudu. Babu wani bata lokaci suna fitowa ta wuce gidan tana jinta gaba daya agajiye.

Da ta koma gidan ma ba wani hutawa tayi ba don zasu fita kaman yadda uncle Farouq yace. Wanka tayi ta shirya cikin wata simple Egyptian abaya ash colour ta tayar da sallar Asr data wuce mata. Bayan ta idar ta koma gaban mudubi ta hau gyara gashin kanta da yake da tsayi daidai ta mishi ponytail ta dauki mayafin abayan ash tayi rolling dashi ta feshe jikinta da different perfumes har kala uku sannan ta fita.

A shirye ta tarar da kowa kamar ma ita kadai ake jira. Ta kalli Nadra da yanzu tafi kowa rawar kai saboda ba harkar makaranta bace. Wajen aunty Mima ta wuce ta amshi Narjis da take nan sak Nadeer. Fita suka yi aunty Mima ta tuqasu zuwa wani private garden dake can off their area, zasu hadu da uncle Farouq acan don yafi masa sauqi daga can.

Suna zuwa suka tarar ya rigasu zuwa ma ya shimfida wani carpet mai kyau a wurin har yayi musu order din variety foods and snacks da drinks. Nadra ta wuce wajensa da gudu tana cewa "daddddd."

Hannu ya bude mata tana zuwa ta fada jikinsa tana cewa "I missed you, daddy." Rungumeta back yayi yana cewa "same here, my princess. How was school?"

Baki ta turo gaba tana cewa "wallahi babu dadi ni kawai acireni Allah malaman are wicked daddy.." daidai Aunty Mima sun karaso wajen ta dungure mata kai tana cewa "qi makaranta kawai, babu mai cireki kima cire rai idan kina tunanin hakan..."

Raurau tayi da idanu zata fara kuka uncle Farouq ya bata haquri. Suhan da abokinta Nadeer suka zauna suna yiwa Nadra dariya data kunnata ta fashe da kuka nan take.

"What's this silliness?" Aunty Mima ta tambyeta tana balla mata harara mai kyau. Uncle Farouq ya matso da ita jikinsa yana cewa "it's okay..."

Narjis dai tana maqale da Suhana da Nadeer throughout har sukayi ciye-ciyensu da shaye-shaye suka kammala suka yi pictures sannan suka tashi suka zaga wajen. Daman iyalan uncle Farouq din sun saba irin wannan outing din idan aka dauki watanni kawai zasu shirya su fita siyi cruising Munich. 

Sosai picnic din yayiwa Suhana dadi ta dauki pictures tayi videos har bata san adadi ba. Kuma tana gamawa take turawa Ammi da Adda Safa. Acan sukayi Maghrib suna idarwa suka dawo gida suka huta after isha kuma kowa ya fito da aikin makarantarsa yana yi. Hajiya Nadra tuni tayi bacci don tacewa Aunty Mima bata da wani assignment which was a lie. Aunty Mima already ta fahimci karya take mata don haka ta duba school bag dinta tsaf ta gano assignment har kala biyu take dashi hakan yasa ta tasota da kuka akayi homework din.....

FA'IZ POV  

Part din Ammi ya shiga yana baza kamshin Baccarat Rouge, yana riqe da hular zanna that went perfectly with his sky blue outfit. It suited him so well.

Bai tarar da Ammi a kasa ba hakan yasa ya wuce upstairs ya tarar da ita a parlourn sama tana kunna burner da tayiwa permanent wuri a every angle dake parlourn. Murmushi yayi time din da suka hada ido ya karasa wajenta ya durqusa yana cewa "Ammi, this scent smells amazing."

Murmushi tayi masa itama tana cewa "sosai, Fu'ad ya fara cewa yana dashi tun kamin na lura yana kamshin kasan pal dinka da mugun son kamshi"

Miqewa yayi yana saka hularsa yace "honestly Ammi, I’ve never seen anyone who loves scent like Fu'ad. You can literally win him over with just perfume..."

"Allah ya bashi macen dake son kamshi..."

Murmushi Fa'iz yayi yana cewa "wai wa yaga pal da mata.." hararar wasa Ammi tayi masa tana cewa "wa ya ganku dai...Kai zo nan.."

Ammi ta fada tana zama kan ottoman sofa dake parlourn. A kasa Fa'iz ya zauna yana kallon Ammi da tayi putting serious face. Nutsuwa tayi sosai tana kare masa kallo tace "Fa'iz."

Ya amsa mata da "na'am." Ta danyi shiru for a moment kamin ta dora da "it's high time you guys started thinking about settling down and getting married, Fa'iz. You're not young anymore. You have a good job and you can take care of a wife, but I notice neither you nor Fu'ad are even thinking about it. At least kai wataran kana zancen amman Fu'ad sam baya zancen ko da wasa... ."

Keyarsa ya fara sosawa yana cewa "Ammi shekarunmu da saura..."

"Ungo nan." Ta fada tana wara masa hannunta tace "gidanku Fa'iz. What more years? You guys are 29, in the next 5 months you'll be 30. You better get yourselves together, okay? at least ku samu wata ku tsayar ku fahimci juna. May Allah bless you with someone good..."

"Aameen Ammi mungode. Sai na dawo." 

"Allah ya tsare." Da Aameen ya amsa mata ya juya ya fita. Motarsa kirar Audi ya shiga yana yiwa Jannah text din 5-star hotel din da zasu hadu acikin restaurant din dake cikinsa sannan ya kunna motarsa ya bar gidan.....

To be continued.....  


#like
#comment
#share