NURI

HALAL REJECTION II

by @saddiqahhh

NURI


By Saddiqa



In less than 20mins ya isa inda zasu hadu don gudu yayi, is hard yayi tuqi ahankali yafi so yake yin gudu idan yana tuqi that's why suke fada da Ammi indai zai kaita wani wajen unlike Fu'ad da zai iya tuqi a mugun hankali kamar bai so.

Time din da yaje ya rigata isa don haka ya samu wuri can edge din wurin da ba hayaniya yayi zamansa yana order din drinks kawai. Wayarsa ya dauka ya fara dannawa sai ga kiran Fu'ad ya shigo masa. Picking yayi ba wani bata lokaci yana yi masa sallama.

Amsa masa Fu'ad yayi yana cewa "baka nemeni ba Pal.." 

"I'm sorry pal, jiya aiki nayi a clinic acan na kwana ma.."  

"Ok nayi maka uzuri.." murmushi Fa'iz yayi yana cewa "so now how's Kano, how's the branch there?"  

Shiru Fu'ad yayi kamar bazai amsa masa ba kamin yace "Kano ba dadi, daga zuwana naji ni kamar wani mara lafiya tun jiya haka nake jin jikina..."  

"Khairan In Sha Allah, babu wani abu baka fadamin ya site din yake ba."

"Site yana nan, in two to three weeks ma za'a iya gamawa saura abubuwa kadan ina ga tafiya ma zanyi..."

"Ina kuma?"

"USA I'm recieving call akan site din can da ake ginawa wai an samu wani problem though I've assigned someone there amman bana jin zan tafi sai an kammala wannan sannan."

"Anya ba zaka je can ka gani ba Fu'ad..."  

"No Pal yaushe na dawo? this three months da nayi bana kasar nan kusan duka acan fa nayi I've many things dake da muhimmanci a branches din dake nan."

"Ok then, Allah ya taimaka."

"Aameen Pal, thanks lemme go and get ready zanje wurin Mama." 
 
"My regards to her please." 
 
"In Sha Allah"  

Daga haka sukayi sallama daidai yana ajiye wayar sai ga Jannah ta shigo. Sanye cikin super Holland dake da touches din maroon da coffee anyi mata dinkin half bubu da straight skirt, yadda ta daura dankwalinta in style din zara buhari ya mugun yi mata kyau. Ta yafa Chantilly veil babba akanta kalar coffee, yadda take da son gayu haka yake dacewa da jikinta idan tayi.

Kallo daya Fa'iz yayi mata yana maida hankalinsa kan wayarsa da yake duba saqon da aka turo masa daga clinic. Jannah ta bishi da kallo tana jin gaba daya courage din data tattarowa kanta yana yin nasa wajen daga kallon Fa'iz din kawai. Shigarsa ya mugun yi mata kyau na wuce misali, it makes her fall more and more for him.  

She encouraged herself ta qarasa wajen da yake tana yin sallama without looking at him ganin yadda shi kallo daya kawai yayi mata ita kadai ce ta damu dashi har take karewa shigarsa kallo wanda ta tabbatar shi bai ma tantance kalar kayan jikinta ba a kallo dayan da yayi mata.

Dagowa yayi ya sake kallonta time din da tayi sallama yana amsa mata sai dai kamar dazu dauke idonsa yayi daga kallo daya yana cigaba da duba abinda yake dubawa a waya. Zama tayi tana jin kamar ta haqura amman the more tana rayawa kanta haquri the more zuciyarta na sake ingizata kan fada masa a wuce wajen kawai. Fatanta guda daya Allah yasa kar yayi rejecting dinta.

Ajiye wayarsa yayi agefe wannan karon ya kalleta irin kallon da take so din yana cewa "Good morning Dr Jannah."

Kai ta gyada masa tana cewa "morning Dr Fa'iz, how's your night?"

"Alhamdulillah.." sai yayi shiru yana bata space din da zata yi magana dashi tunda itace take buqatar haduwa dashi, sak yadda Fu'ad yake kusan haka Fa'iz yake. Banbancin halinsu kadan kawai Fu'ad yafi Fa'iz simplicity sosai.

"Ya aiki?" Ta tambyeshi saboda tana so ta danyi creating hira kadan da zai sake da ita don ta lura kamar bai wani sake da ita ba which is not like that a wurin Fa'iz.

"Alhamdulillah how's yours? Kin fara wani aikin ne?"

"Kai ta girgiza masa tana cewa "a'a."

"Now lemme ask you, what's the reason da yasa kika ajiye aiki Dr?"

Shiru tayi tana kallonsa kamar yadda yake kallonta kamin ta kawar da idonta tana cewa "there's no reason kawai naji kamar na gaji da aikin ne."
  
Baki Fa'iz ya tabe yana dage kafada alamar ke ya shafa yana cewa "ok, go ahead what is it da kike son muyi magana akai da ba zamuyi a waya ba."

Anzo wajen, zuciyar Jannah ta fara palpitating da sauri jin abinda yace kamar ba shine abinda ya kawota ba. Da kallo ya bita ganin yadda ta sadda kanta kasa ta fara fidgeting fingers dinta kamar wata yarinya. Dauke kansa yayi yana bin wajen da kallo yace "it seems baki da abin fada Dr, can I go?"

Da sauri ta dago kanta tana girgiza masa kai, daya lura da kyau sai yaga kamar hawaye yake gani a idon Dr Jannah. "Ya salam" kawai ya furta aransa yana "Yah Rabbi don't let her say what is in her mind."

Bakinta yana rawa tace ahankali "Dr please......."  

Ya kureta da kallo yana cewa "please what?"  

Dan rufe idonta tayi tana tattarowa kanta sabuwar nutsuwa tare da kwarin gwiwa kamin ta bude idonta ta sauke kansa dake kallonta tace "Dr Fa'iz I think I've fall for you, ba yau ko jiya ba right from the first day I've seen you......."

Baya yayi yana jingina ajikin kujera ya rude idonsa yana budewa aransa yana cewa "Yah Rabbi, me yasa kika kasa haqura just like you decide..." Ya dade da fahimtar Jannah tana sonsa. Tun farkon fara aikinta a Novecare ya fahimci hakan amman the way take dannewa yasa ya bayar cewar zata haqura dashi. Ko resigning dinnnan yasan saboda shi tayi don ya lura bayan ya dawo daga rashin lafiyar da yayi kamar tana shirin kasa danne komai aranta.

Bai so hakan ta faru ba sam, though Jannah ba itace ta farko data fara sonshi ba. Suna da yawa masu crushing akansa dagashi har Pal dinsa. Kusan ma masu crushing akan Fu'ad sunfi yawa don yana da kwarjini shisa har yau aka kasa samun wadda ta tare Fu'ad ta fada masa tana sonshi. Shi kuwa Fa'iz baya da wani kwarjini that's why mata suka fi takura masa.

At that moment rasa abinda zai cewa Jannah yayi, ba wai yana sonta ba. Idan yace yana sonta yayi katuwar karya kawai dai Jannah nada kima da mutunci a idanunsa that's why baiso ta kasance kamar sauran ba.

"Dr kayi shiru..." Muryar da take magana dashi ma kawai ya isa yayi breaking mutum, irin macen nan dake in desperate need of someone she loves dinnan. Bai kalleta ba don karma ta bashi tausayi, don yana ji aransa bazai cuci kansa ba yace yana sonta never, idan baison abu kawai baiso kamar Pal dinsa.

"Dr Jannah...." Ya kirata with a calming voice data saka mata 'yar nustuwa kadan. Gyaran murya yayi yana cewa "Zaki iya rayuwa ba tare dani ba?" 
 
Da sauri ta girgiza masa kai tana son yin magana amman ta kasa. Kansa ma ya kulle ya kasa bata amsa kamar yadda ya saba bawa sauran mata. Kamar yafi ganin kimarta akan duka sauran kuma hakan ba yana nufin he have feelings for her ba sam babu, bayajin komai kan Jannah.

"Ban shiryawa duka wannan yanzu ba Jannah..."

Kamin ya qarasa tayi saurin tarar zancen tana cewa "i will wait for you ko shekara nawa ne Fa'iz...."

Kai ya girgiza yana cewa "mace ce ke, ba lallai a barki agida, zan bata miki lokaci don bana wannan lissafin for now.."  

"I will wait for as long as you will accept my love..."

"Ban miki alqawari ba..."

"Na amince zan jira har lokacin da zaka ji ka yadda dani...."

Kallonta yayi ganin duk ta yanda ya biyo tana da amsa "I'm not...."

"Don Allah karka karasa...na sani...nasan baka sona...na dade da sani..."

Miqewa Fa'iz yayi yana daukar wayarsa yace "look ko abinci baki ci ba zan miki order kici yanzu sannan ki dawo aiki Novecare we're waiting for you...zancen nan kuma mu barshi anan please Jannah, you can build your future ko babu Fa'iz...."

Kai ta girgiza masa tana miqewa tace "I'm full banjin yunwa... Fa'iz don Allah zan jiraka wallahi..."

Kallonta yayi sosai before saying "as you wish Jannah...." Yana fadin haka ya fita da dan sauri don akwai inda zaije yaga kuma kamar ya kusan makara.

Komawa tayi ta samu wuri ta zauna tana jin kanta wani iri. For the first time duk wannan pride din nata da takeji dashi ya zube kaf dinsa. Ta bude baki ta fada masa tana sonsa amman he rejects her. Yes he rejects her, kai tsaye bai fada mata baya da ra'ayi akanta ba amman maganarsa ya nuna hakan. Bai shirya ba means baya da ra'ayi akanta sam but what if nan gaba yaji yana sonta? This is Jannah's heart giving her false hope akan Fa'iz, mutumin da vividly ya nuna mata baya ra'ayinta..........

NURI'S POV

Da kyar ta tashi tayi sallar asuba sakamakon wani ciwon jiki da take danyi kadan kadan duk adalilin diban ruwan da take yawan yi. Tana idar da sallar ta tashi ta fara aikin data saba yi kamar kullum. Ta gama ta shiga wanka don akwai ruwa enough tun wanda ta dibo jiya zai kaisu har yamma hakan yasa yau tayi shirin makarantarta da wuri yau babu makara. Ragowar abincin jiya ta dumama taci abinta ganin Mami ta koma barci yasa bata tadata ba duk kuwa da tasan akwai aikin da zatayi na sana'arta amman tana mugun jin tausayin Mami ne yadda take aiki ko yaushe duk ta canza ta sauya kama, wahala ta kodar da ita kamar ba Mami ba. Mami da ake dauka yayar Nuri ce yanzu duk ta sauya.

Har bayan data kammala cin abincin bata tada Mami ba ta fita abinta tana leqa dakin Inna ta tarar tana baccin nata data saba sai munshari take. Fita tayi tana addu'a ta tarar har wasu sun fara shigowa sanin zasu tada Mami yasa tace dasu yau babu ta safe sai dai ta yamma.

For the first time tunda suka dawo gidan Inna yau ta samu kanta da kasa kallon wannan building din da yake burgeta ko yaushe har take kallonsa idan zata makaranta. Scene din jiya yana maqale aranta bata manta ba, ba kuma ta manta cewa kamar tare da ma'aikatan yake ba duk da baiyi mata kama da ma'aikacin gini awajen ba.

Tana zuwa ta samu napep bata sha wahalar komai ba suka daidaita ya kaita makaranta. Ta samu tayi sabuwar kawa mai suna Fauza dake mugun son Nuri haka kawai. Tun lokacin da Zara kenan take son kulasu amman ganin yadda suke rayuwa su biyu yasa ba tayi musu shisshigi ba, yanzu da babu Zara sai ta fara kula Nuri kadan kadan har Allah yasa Nurin ta fara sakewa da ita.

Around 1 suka fito gaba daya lecture din da zasuyi da yamma malamin yace musu bazai zo ba don haka ta yanke shawarar komawa gida saboda tana da wankin kayanta da zatayi. Kamar bata da sa'a yau haka mai napep yana sauketa a layin gidansu idonta ya sauka kan Khaleel da yake tsaye a bakin layin kan machine dinsa kamar yana tunanin shiga layin. Ji tayi dama akwai wani hanyar bayan wannan ta juya tabi tun kamin ya ganta amman sam babu. Bata da option din daya wuce ta bi ta inda yake.

FU'ADS POV

Yana daga baya yana duba MacBook dinsa da yayi recieving din mail da safen nan. Yana sanye cikin jeans deep blue da blue black long sleeve shirt da suka mugun yi masa kyau don shi yakewa kaya kyau. Kamshin turarensa na Pur Oud LV ya cika motar gaba daya ya danne freshener din dake tashi a motar. Ya gama typing reply zai turawa accountant din NoveBuild UAE yaji zuciyarsa ta fara bugawa sak irin yadda tayi jiya da yamma time din daya hadu da wannan yarinyar da ta kasa barinsa ya huta tun jiya.

Samun kansa yayi da dagowa yabi inda suke da kallo idonsa ya sauka akanta... Sai dai ba ita kadai ba tare da wani dake kan machine yana yi mata magana da baisan me yake cewa ba. Kasa sending message din yayi ya tsaya stiff kawai yana kallonsu baya ko kifta ido.....

To be continued....

#like
#comment
#share