NURI

THE ULTIMATUM

by @saddiqahhh

NURI


By Saddiqa



Bai san me yasa ba lokaci daya yaji wani abu ya tokare masa wuya ya kasa wucewa and again ya kasa dauke idonsa akansu ko kifatawa baya yi. Bai san mene ya kai hankalinsa wajen ba har yaji wani irin abu da bai sani ba azuciyarsa, wani feeling da bai taba ji ba, sannan ba irin na jiya daya hadu da yarinyar ba. 

Da kyar ya samu yayi controlling kansa ya dauke idonsa sai dai ya kasa cigaba da abinda yake yi a MacBook dinsa. Bai ji abin ya tsaya masa arai ba sai bayan da driver yayi parking aka bude masa kofa yaji ya kasa fita kamar an dasashi awajen. Ga zuciyarsa tana rudarsa ya juya baya yaga ko har yanzu suna tare amman ya mugun dakewa a matsayinsa na tsayyen namiji ya hana kansa. Rufe idonsa yayi yana jingina ajikin kujerar ya fara ambaton Allah aransa, ya riqa maimatawa abakinsa yana yin different types of zikr har yaji zuciyarsa ta dawo daidai. Abinda ya tsaya masa a wuya yaji kamar ya wuce. Bude idanunsa da suka dan kankance kadan yayi yana kallon yanayin garin dake nan ana zabga rana ga zafi da ake. Matsawa yayi ya sake bude motar da kansa ya fita sai dai duk da haka kawai yaji zuciyarsa tana azalzalarsa kan ya juya ya kalleta amman ya hana kansa hakan. A matsayinsa na namijin da yake kame kansa ga barin kallon mata, wannan ba halinsa bane don baka yasa kai ya wuce ciki guards dinsa suka take masa baya.

Ba wani dadewa yayi ba ya fito don yana son yaje ya gaida Mama kamin magariba kuma yana son yaje ya huta. Don haka ko one hour baiyi ba ya tafi sai dai zuciyarsa ta kasa barinsa ya huta, kwakwalwarsa ta kasa barin tunaninsa ya huta. Ya rasa ma asalin mene damuwarsa da yake tunani akan wadda ko sunanta bai sani ba....

NURI POV

Hade rai tayi sosai. Abinda bata iya ba amman yawan takura mata da maza keyi yasa ta fara koya. Dagowa tayi ta masa kallo daya tana dauke kanta ganin ya tare mata hanya. Kawar da kanta gefe tayi ta tsaya without giving him a second look. Tanajin kamar yau dai zata yankawa Khaleel rashin M, ba'a so dole awajen Nuri 😁

"Nuriyya don Allah ki saurari abinda zan fada miki." Idan iskar dake waren ta kula Khaleel to Nuri ta kulashi. Yadda kasan bata san da wanzuwarsa awajen ba. Kanta agefe kamar wadda ke neman abu amman azahiri idan zaka kallesu daga nesa zaka dauka magana suke saboda yanayin yadda ya tare mata hanya akan machine.

Wani kallo tayi masa tana sake daure fuska tace "kamar mun dade da gama magana da kai Khaleel, to be frank I'm tired of you stalking me, haba mana leave me haka nan mana.... soyayya soyayya soyayya dai..ina da abubuwan da suka fi muhimmanci agabana, for the last time Khaleel I'm not in, ka rabu dani haka nan."

Tunda ta fara maganar yake kallon bakinta har ta kai karshe kamar ma baya jin abinda take cewa. Sai da tayi shiru sannan ya dawo da kallonsa kan fuskarta yana cewa "Kiyi haquri dani Nuri, I will wait for you, as long as you will accept me ..... Zan jiraki har zuwa sanda zaki aminta dani....."

Idan tace bata taba ganin dan takura kamar shi ba tayi karya, ba wai shi kadai ne namiji da yake kulata ba. No, akwai wasu amman shi kadai yafi naci da takurawa rayuwarta.

"Kayi haquri kawai..." Tana fadin haka ta kewaya ta bayansa inda ya tare mata hanya ta wuce ta barshi nan a tsaye yana binta da kallo.

Duk lokacin da yayi deciding ya haqura da Nuri sai ya danyi satikai sai yaji ba zai iya ba. Tana nan maqale a tunaninsa ko yaushe, ko yayi niyyar dena sonta. Yanzu rashin ganinta ne abinda yake damunsa tunda sun koma lectures a old campus.

Kunna machine dinsa yayi ya bar unguwar nasu sai dai zuciyarsa cike da tambayar kansa, ko yayi lacking wani character, wani hali ne da yasa taqi sonsa? Ko kuma don baya da kyau ne? Hakan yasa ya kalli mudubin machine dinsa ya kalli fuskarsa dake nan shi ba wani mugun mai kyau ba amman sam ba za'a kirashi da mummuna ba.

________

Da sallama ta shiga gidan nasu ta tarar da Inna a zaune a bakin kofar dakinta tana cin goro. Da kallo tabi Nuri tana amsa mata sallamar nata aciki-ciki. Hakan bai dameta ba don idan da sabo ta saba da halin Inna.

Dakinsu ta shiga ta tarar da Mami zaune tana ninke kayan da tayi musu wanki dazu bayan tafiyar Nuri. Da kallo Nuri tabi kayan ganin kusan duk nata ne na Mami kadan ne acikin.

"Mami me yasa kika yi? Me yasa baki jirani ba? Nayyi niyyar yi fa during the weekends...."

Kallonta Mami tayi tana cewa "na tashi bani da abinyi. Kin riga da kince da mutane yau babu awara, sai naga da na zauna bana komai gwara na rage wankin...."

Kayan Nuri ta nuna tana cewa "wannan fa ba ragewa kika yi ba Mami, duka kika yi..."

"Uhmmm, munyi waya da biyayyenki dazu wai kun kwana biyu ba kuyi waya ba..."

Kai ta girgiza tana cewa "Mami kinsan wayata ta fara cin kai, bata da strong network sannan data na ma ya qare ni..."

Mami ta kureta da kallo tana cewa "me yasa baki fadamin ba? Ba sai a saka miki ba..."

"Mami ni ba wannan bama. Kinga yau naga level co'ordinator dinmu yayi mana maganar registration fees....."

Dan shiru kadan Mami tayi kamin tace "tarawa nake Nuriyya, amman da na tara Innarku ke amsar kudin bata dawomin dashi...."

Kalar muryar da Mami tayi magana yayi breaking Nuri sosai, kana ji kasan she is desperately needing money to pay for her precious daughter's fees.

"Mami ki dena bata kudin mana.."

"Kinsan halinta dai, sai tace wai ba zamu zauna anan ba..."

"To mu bar mata gidanta mana, ana dole ne..."

Kallon baki da hankali har yanzu Mami tayiwa Nuri ta sake tabbatar da dagaske har yanzu Nuri bata gama hankali ba.

"Muje ina Nuri? Da wanne kudin? Haya fa tsada yake yi yanzu..."

"Ni duk inda zamu je kawai muje har dai ba zamu zauna tare da ita ba...wallahi na gaji da kalar zagin da take miki Mami..."

"Tashi ni kije kiyi wanka kizo kici abinci, kin debo rana......"

Baki Nuri ta turo gaba tana cewa "ke naga kamar sonta kike...."

Mami bata kulata ba sanin neman magana kawai take yi. "Allah ya bani kudi mai albarka da zan daukeki ta nemeki ta rasa..."

Murmushi Mami tayi ba tare data kalleta ba ta cigaba da ninke kayansu da take yi.

Kayanta Nuri ta cire ta daura zaninta na wanka ta fice zuwa toilet. Da ruwan sanyi tayi wankar saboda ana zafi. Ta fito tana bata rai ganin kamar sai tayi diban ruwan data tsana.

Haka ta daura alwala ta dawo ta shirya cikin wata atampha da akayiwa simple doguwar riga a-shape tayi sallahr azahar.

Kamin ta idar da sallar Inna ta fara kiran Mami daga waje tana kwala murya kamar mai kiran na waje.

"Bintu, Bintu ba kya ji ne..." Miqewa Mami tayi tana amsawa "gani nan Inna..." Tashi tayi ta fita wajen Inna data shige dakinta. Itama dakin Innar ta shiga ta samu waje kan wannan matacciyar tabarmar ta zauna kanta a kasa tace "gani Inna."

"Na zata baki ji ba ai."

Kai Mami ta girgiza tana cewa "a'a naji. Ina ninke kaya ne.."

"Sai da kika kammala kuma kika ga damar amsa kirana."

Shiru Mami tayi bata sake cewa komai ba. Inna ta wani tabe baki tana sake karewa Mami kallo. Ta tabbatar da zancen Rabe, Mami ce kalar matar da Alh Labaran yake nema kuma tasan zata burgeshi sosai da sosai.

Zama Inna ta gyara tana cewa "magana za muyi dake ta fahimtar juna..."

Kai Mami ta gyada mata tana cewa "wato Bintu wani al'amari ne yake shirin faruwa dake na alkhairi. Zai yaye miki halin kuncin rayuwa da kika shiga ke da yarinyarki..idan kika amince ina mai tabbatar miki ba ke kadai ba, hatta mu da muke rabe dake talaucin da yayi mana katutu zai rabu damu. Amman idan kin bamu hadin kai kenan"

Shiru Mami tayi tana saurarar Inna dake wannan dogon sharhin wanda kana ji zaka san so take tayi convincing din Mami tun kamin ta fadi abinda yake ranta.

"Bintu kinsan Audu dai ba dawowa zaiyi ba ko?" Wani iri Mami taji jin abinda Inna tace. Wai Abba ba zai dawowa ba? Ita dake zaune tana zaman jiran dawowarsa!

"Wata tara kenan muna shirin shiga na goma Bintu..." Ba sai ta fada mata wannan ba. Ta fita riqe lissafin don an shiga na goman ma tuni na sha daya ake shirin shiga nan da kwanaki kadan.

"Ya kusa shekara baya tare damu Bintu."

Yanzun ma shiru Mami tayi. Duk bata kulata ba, nata ji kawai.

"To zaman jiran nan nasa ba zai miki ba. A matsayinki na 'ya mace wadda ta taba aure tasan meye aure kina ji ko?"

Kai ta gyada mata Inna ta dora da "ni dai a shawarce nake fada miki, ina ganin kiyi aure kawai. Wataqila ki hadu da mai kula miki da yaran nan naki...."

Wani irin kallo ta dago tayiwa Inna kamar bata gama fahimtar abinda take nufi ba "Inna kamar aure naji kince?"

"Eh kwarai aure Bintu. Kinsan a musulunce ba'a fiya son mace ta zauna haka ba ko?" Mami bata kulata ba don tana assimilating kalmar aure data fada har yanzu akanta.

"Amman Inna ni bance ina so ba..."

"Ni naga hakan ya dace. Hakan ne ma yasa na zabo miki wani hamshaqin mai kudin da zai yaye miki damuwarki..."

"Allah ne yake yayewa bayinsa damuwa ba wani can ba Inna..."

Harararta Inna tayi tana cewa "ba wa'azi nace kiyimin ba. Kinga dakata min nasan hanyar masallaci..mun gama magana da Rabe ma don shine yasan halin mutumin sosai. Yana da kyan hali sosai kowa yayi masa wannan shaidar..."

"Inna ina da abinda yafimin aure muhimmanci a yanzu..."

"Fadamin kawai sunnar ce ba kyason rayawa...."

Shiru Mami tayi jin yadda Inna ta hayayyako mata kamar zata daketa.

"Haka kike nufin zaki zaunamin agida kina taramin mutane da sunan s ana'a? Ke ba aure itama wancan mai idon mayun ba tsayayye, jiqaku zanyi a ruwa na sha kome to bari kiji....."

"Kina ji...bara na fito miki a mutum. Nagaji da ganinku anan ne shi yasa ina buqatar gidana ni kadai babu wasu mutane kuna tare min iskar gida..."

Da sauri Mami ta dago tana kallon Inna "amman Inna ke kika yi mana tayin gidan nan...."

"Yanzu kuma nagaji. An kawo maslaha kince ba haka ba...to wallahi sai na aura masa waccan mai idon mayun. Tunda ke kinqi, idan ke bani da iko dake ita ai ina da iko da ita tunda jinina ce ita, 'yar Audu ce...."

Tunda Inna take magana hankalin Mami baiyi tashin da yayi ba kamar yanzu. Tayiwa Nuriyya aure da wani babba can da ba'a sani ba wannan ya mugun dakarta sosai.

"Kije kiyi tunani ko ku barmin gida, ko ki aure Alh Labaran, ko na aurawa Nuriyya shi! Tashi ki barmin daki. Gayyar rashin asali kawai. Daman ba'a abin arziqi da ku ai..."

Har ta fita ta koma dakinsu bata sani ba. Kawai tafiya takeyi tana saka kafarta duk inda ta taka zuciyarta tana fadawa zuzzurfan tunani. Lokaci daya taji jikinta yayi wani mugun yi mata nauyi har tanajin kamar gudun jininta ya karu fiye da yadda yake da. Daman tun farkon satin nan bata wani jin dadi. Tana daurewa ne saboda Nuri kawai.

Ta saka kafarta dakinsu kamin ta bude baki tayi sallama ta yanke jiki fadi......

To be continued....

#like
#comment
#share