NURI

THE LOOK THAT FOLLOWED

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa


Karasowa wajenta Nuri tayi ganin ta dade zaune awajen tana cewa "Mami ki koma kan gadon nan akwai sanyi." Kai Mami ta gyada mata tana miqa mata hannunta alamun ta taimaka mata suka miqe a tare suka koma kan gadon. Sai bayan data taimakawa Mami ta jingina da bangon gadon sannan ta jawo kujerar dake gefe ta matso da ita kusa da Mami ta zauna tana kamo hannayen Mami ta damqe sosai a nata kamar za'a kwace mata ita "Mami me kike so na karin kumallo?" Kallonta Mami tayi for a while kamar tana tunanin abincin da za tace amman ba shi take tunani ba, tana tunanin yadda zata fadawa Nuri komai ne don tasan boyewa bazai taba zama solution ba.

"Mamiiiiii." Nuri ta kirata da dan karfi kadan ganin kamar she's taken away. Kai Mami ta girgiza tana cewa "so kike kaina ya dawo da ciwon ne Nuriyya?"

Da sauri Nuri ta girgiza mata kai tana cewa "I'm sorry, Mami naga fa kin tafi tunani ne. Tunanin me kike?"

"Ina tunanin Afif ne, nasan ya kira jiya zaiji shiru..."

Kai Nuri ta gyada tana cewa "for sure ma ya kira Mami, wayana ma ni akashe yake sai dai naki..."

"Zaki iya komawa gidan ai sai ki tahomin da wayar banson ya kira yau ma yaji shiru."

"To Mami baki fadamin abinda zan dafa miki ba."

"Ki kawomin duk abinda ya samu Nuri, duk abinda muke dashi mai sauqin dafawa kawai ki kawomin karki damu kinji."

Kai Nuri ta gyadawa Mami tana sakin hannunta ta miqe tsaye "Mami ke kadai to zan bari kuma?"

Kai Mami ta gyada mata tana cewa "eh karki dade please kiyi abinda ya kaiki kawai.... And yes don't get involved with Inna."

Wucewa Nuri tayi tana gyara mayafin kanta ta amsawa Mami da to sannan ta fita tana sake juyawa kallon Mami kamar irin zata dawo bata ganta ba haka.

Bata sha wahala ba tana fita ta samu napep da ya kaita har bakin layinsu ta sauka zata bashi kudinsa anan ta tuna ai babu ma kudin a tare da ita. Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsa jiki a sanyaye tace "Baba don Allah kayi haquri na manta da kudin agida bara naje na kawo maka kaga gidan can..." Ta karashe tana nuna masa gidan nasu.

Wani passenger dake napep ya kalleta yana sake kallon agogonsa yace "muje Baba zan biya sauri nake.." da kallo Nuri ta bisu ganin sun tafi gashi ko godiya bata yi masa ba.

Kafada ta dage irin shi ya jiyo ai ba tace ya biya mata ba. Tafiya ta cigaba dayi cikin layin nasu hankali kwance har ta isa bakin gidan ta fara bugawa. Muryar Inna ta jiyo tana cewa "waye anan?"

Shiru tayi kamar bata ji ba ta cigaba da buga gidan da sauri duk don ta kunna Inna and she successfully did it. Don a masife Inna ta bude gidan "wanne dan kwal uban ne yake bugamin gida kamar da kudin ubansa aka sai gidan.."

Kasa-kasa Nuri tace "da kudin nasa kuwa aka sai gidan.." wata harara Inna ta mata ganin itace tana cewa "ke daman kece kike min wannan bugun mafarautan?"

Kasa tayi da kanta ba tare data amsa mata ba tana jiran ta bata hanya "ya na ganki ke kadai ina babar taki?" Nan ma shiru tayi mata kamar ba taji ba "ke ba dake nake magana ba?"

"For goodness sake Inna ina da abinyi zan wuce..."

"Iyeee... Ni kike fadawa haka me idanun mayu? Kai dole ku barmin gida bari uwar taki ta dawo gidan ku tattara ku barmin tunda babu gado.."

A zuciya Nuri ta amsa mata da "ai kuwa akwai..."

Tsaki Inna taja mata tana barin wajen ta koma cikin gidan Nuri ta take mata baya da sauri zuwa dakinsu. Bata tsaya wahalar da kanta ba ta dauki ragowar attaruhu da albasa ta gyara ta jajjaga ta dorawa Mami jollof din taliyar fulawa saboda ita suke da ita available. Kamin ta kammala girkin har dakin nasu ta kintsa ta dan jona wayarta caji ganin suna da wuta. Tana jiyo Inna na kwala mata kira tazo ta debo mata ruwa tayi banza da ita kamar ba taji.

"Ohhh Allah wadaran naka ya lalace...yau nike kiran 'yar Audu tamin banza.. ni ni ni Laure..."

Daga cikin dakin Nuri ta tabe baki tana kwaikwayar yadda Inna take magana tana yiwa kofar wani kallo kamar tana gaban Innar wanda a zahiri sam ba zata iya hakan agabanta ba karfin hali ne kawai yadda take da mugun tsoron nan. Da sauri ta miqe jin kamar abincin Mami yana kauri ta duba taga ya kama tana can wajen kwaikwayon Inna.

Tagumi ta buga tana kallon yadda ya kama a tukunyar kaurin ya cika dakin gashi babu wani sauran ingredients bare ta sake daura wani sannan sarai tasan Mami zata mata fadan yadda abincin ya kama.

A shagwabe ta kalli kofar dakinsu kamar za tayi kuka "duk waccan tsohuwar ce ta jawo min... Wayyo ya zanyi.." sanin bata da option yasata daukar flask ta juye abincin a haka tana tunanin abinda zata cewa Mami idan taje can. 

Coffee color hijab taje ta dauko daga cikin akwatinta sannan ta dauki flask din abincin da sauran abubuwan data hada tana manta wayarta dana Mamin duka. Bata kalli wajen da Inna take ba tasa kai ta fice abinta tana jiyo mitarta ammn tayi kamar ba taji ba wanda hakan yake sake kular da Inna ganin ta maidata kamar mahaukaciya.

Tana fita ta tarar da wani yaran maqocinsu Bilyaminu da yake da burin ganin ya kulata ita kuma tunda ta fahimci hakan take avoiding dinsa. Yanzun ma da sauri ta dauke kanta tana kara sauri ta daure fuska wai ko zaiji shakkarta tayi gaba...


*AFIF-SUHANA 3*

"Yadai naga kina tafiya ahankali Suhan?" Kai ta girgizawa Aunty Mimi tana samun wuri ta zauna kan dining kusa da Narjis dake zaune akan keken yara na zama. Kallonta Suhana tayi kamin ta maida kallonta kan Aunty Mimi "good morning Mummy"

"Morning Suhan how was your night?" Kai ta girgiza mata tana cewa "bad mummy.." tana serving dinta omelette da chips tace "meya faru to.?"

"Kaina ke ciwo."

"Sannu kinji ki gama cin abincin akwai pcm sai ki sha ko?"

"Ok. Su Nadeer yau basu jirani ba kenan?"

"Sun makara ne suma yau shisa Daddy yace ki taho kawai don shima yau sun makarar dashi.."

"Baccin ne Mummy.. akwai dadi over.."

"Mayyar bacci kawai.." tare suka yi dariya ta fara cin abincin while Aunty Mimi ta zauna tana bawa Narjis data cika musu kunne da gwarancinta.

Suhana bata dade tana cin abincin ba ta miqe ganin time yana wucewa zata makara tayiwa Aunty Mimi sallama "sai na dawo mummy.."

"Take care autar Ammi.. wait baki sha maganin ba.."

Suhana da har taje bakin kofar fita a parlourn ta amsanda "idan na dawo mummy zansha.."

"Ok then ki kula Allah ya qara sauqi.."

Da gudu gudu sauri sauri haka ta karasa har bus stop ta samu mai cab ta tare ya kaita makaranta. Sai dai saurin data yi kamar ya kara mata ciwon kan haka dai ta daure har ta isa makarantar ahaka sukayi lecture din farko tana daurewa. Na biyun kam bama tasan me akayi ba saboda wani zazzafan zazzabi daya rufeta rigis ko motsi ba tayi banda rawar sanyi bata yin komai gata da banzan halin rashin sakewa da mutane har yanzu ta kasa yadda ta kula kowa komai on her on zaka ganta babu wanda take kulwa har course mates dinta suna kiranta da Miss ego bama ta sani ba.

Time din sallah yayi ta kasa miqewa taje inda ta saba yin sallar ma saboda zazzabin. Haka aka sake dawowa lecture din yamma babu ma wanda yayi noticing bata da lafiya tana can karshen ajin ta kifa kanta akan desk bata dago ba. Sai can yamma around six ta farka daga baccin daya dauketa na wahala just to find out babu kowa acikin hall din sai ita kadai. Ranar tayi danasanin rashin kula mutane da takeyi wanda hakan yasata fara kukan daya kara mata sabon ciwon kai akan nada da take fama dashi.


Sanin babu wanda zai taimaketa a wannan lokacin yasata da kyar ta miqe tsaye tana dafa bango ta dauki jakarta data cika da littattafai ta rataya abayanta ta fara tafiya da kyar tana yi tana hutawa. Sai data fito taga ashe duhun magariba yayi makarantar yayi shiru babu kowa a ta inda take hakan ya sake sakata sabon kuka. Tana tafiya da kyar tana kuka gashi kamar jiri takeji haka. Da kyar ta iya fitar da kanta can wajen makarantar tana haki ta tsaya zata tsare cab ganinta ya dauke na lokacin saboda wahala, jirin da takeji yasa tayi baya ta fadi. 


Cike da tunanin dalilin da yasa ya kira wayarsu baya samu tun jiya haka yake tafiya yana duba wayarsa ko zaiga kiran daya daga cikinsu. Hankalinsa yana kan wayarsa baya ganin hanya saijin faduwar mutum agabansa yayi wanda ya dawo dashi hankalinsa. A dan tsorace ya kalli kasa idonsa ya sauka akan Suhana dake kwance unconscious kamar she passed out ma.

Da sauri ya zura wayar nasa cikin aljihun wandonsa ya durqusa kasa yana cewa "hey you..." Sai ya rasa me zaice ma a lokacin hakan yasa kawai ya tsayar da cab din da zai wuce don ya fahimci ta suma.

Shi da kansa ya dauketa ya sakata a back seat sannan ya dauki jakarta ya shiga front seat ya zauna yana cewa da driver din ya kaisu nearby hospital. In less than 15mins suka Isa asibitin da suna zuwa aka amsheta aka fara cuku-cukun dubata ganin bata numfashi. 

Numfashi Afif ya sauke yana tura hannunsa cikin sumar kansa dake da yalwa ya samu wuri ya zauna yana bin jakarta da kallo yana tunanin yadda zaiyi contacting 'yan gidansu.

Ganin duhu yayi yasashi miqewa da sauri ya samu waje ya daura alwala yayi sallah anan cikin asibitin sannan ya dawo. Bai dade da dawowa ba likitan daya dubata ya fito hakan yasa Afif miqewa ya karasa wajensa yana tambyarsa yadda take. "She's concious now just the fever, take this..bring this medicines and injections for her now." Amsar takardar Afif yayi yana bin magungunan da kallo kamin ya juya ya nufi pharmacy dake cikin asibitin. 

Yana zuwa ya miqawa pharmacist din takardar ya tsaya ya gama dubawa yace masa suna da duka ya fada masa bills dinsa. Dan dakatawa yayi for a while yana maimaita adadin kudin sanin su kadai ne a tare dashi.

Shiru yayi for some moment kamin ya zaro kudin daga aljihunsa ya miqa masa yana amsar maganin ya koma da sauri sanin likitan yace dashi yayi sauri. Yana komawa ya tarar da likitan tsaye yana jiransa ya miqa masa ya amsa da sauri ya koma ciki shi kuma ya koma ya zauna yana rufe idanunsa duka.

Sai can tunanin ya dauki wayarta ya duba yaga ko zai iya kiran 'yan gidansu ya zo masa. Da sauri ya jawo jakar ya dauko wayar Allah ya taimekashi a time din Uncle Farouk yana kiranta da sauri ya amsa kiran "A ina kika tsaya Suhana? Bakisan dare yayi ba?"

Da kyar ya bude baki yana cewa "she's admitted in the hospital... bata da lafiya.."

"Subhanallah... Wanne asibitin ne?"

"TUM Klinikum Rechts der Isar"

" Ok I'm on my way right away thank you.. "

Kashe wayar Afif yayi yana sauke ajiyar zuciya don ya gaji da zaman asibitin nan yana so yaje gida ya huta yayi karatu ga tunanin Maminsa da addarsa dake ransa suma.

Minti talatin ya kawo Uncle Farouk tare da Aunty Mimi suka sake kiran wayar Suhana dake hannun Afif yayi musu kwatancen inda suke. 


Yana zaune akan kujerun dake bakin kofar dakin da take a kwance yaqi shiga cikin dakin da take har sannan sanin bacci take yi sannan. Kansa yana kasa yana wasa da zoben azurfa dake hannunsa gefensa tarkacen jakar Suhan ne.

Sallamar dayaji yasa shi dago kansa yana tabbatar da Family dinta sun karaso zaije ya huta shima. Karasowa Uncle Farouk yayi yana yi masa sallama ganin jakar Suhan agefensa ya tabbatar dashi suke yin waya. Dagowa Afif yayi yana amsa masa sallamar tare da miqewa tsaye ganinsa babba ya dan matsa gefe yana dan risinar da kansa kasa..

Wani kalar kallo Uncle Farouk yabi Afif dashi yana jin iskar wajen ta dauke masa na wasu sakanni...


To be continued....

#comment
#like
 #share