UNSPOKEN AND UNRESOLVED
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
Kallon juna suka yi na wasu sakanni kafin Nuri tayi saurin kawar da kanta saboda wani kalar kallo da taga kamar yana yi mata. Shima dauke nasa kan yayi yana kallon compound din asibitin yadda ruwa yake saukowa da yawan gaske. Bude lemar dake hannunsa yayi ya miqa mata yana cewa "take kije ki shiga kar ruwa ya jiqaki.."
Hannunsa tabi da kallo na wasu sakanni kafin ta dago kanta ahankali tana son yin magana amman ta rasa me za tace sai can ta samu courage din furta "kaifa??"
Bakinta da yayi maganar ya fara kalla kamin ya koma kallon idonta dake kallon qasa.. He didn't know why, amman tambyarta sai yaji ya burgesa har hakan ya sanyashi yin murmushi kadan wanda sai ka lura da kyau zaka gani.
"Kije kedai zan biyoki a baya..."
Kai ta gyada masa ahankali tana yin gaba ta wuceshi shi kuma ya take mata baya acikin ruwan har zuwa wurin da motar nasa yake. Kamin su karasa ruwa ya gama jiqasa tsaf saboda mai yawa ake.
Suna shiga motar tun kamin ya gama daidaita zamansa Mami tace dashi "mesa ka shiga ruwa?? Baka tsoron mura ko zazzabi?.. kalla yadda ka jiqe duka fa?
Kasa yayi da kansa yana yin shiru har saida Mami ta kai karshen maganarta yace "ba komai Mami.. I'll change when I get home.."
Kallonsa Mami tayi kawai kamin ta gyada masa kai saying "make sure baka bari sun bushe ajikinka ba..." Ta mudubi ya kalli Mami har ransa yana jin dadin yadda ta nuna kulawa agaresa.
"Nagode Mami.."
"Ba godiya..." Kai ya gyada mata yana kunna motar suka fara tafiya. Nuri dai kanta yana kasa tana wasa da gefen rigarta saboda yadda takejin ta takura saboda a gaba ta zauna kamshin turarensa duk ya cika mata ciki.
Baiyi gudu dasu ba as dama ya saba baya gudu idan yana tuqi plus ga ruwan sama da ake. Hankalinsa gida biyu kusan ya rabashi yana son ya kalli Nuri dake gefensa amman wanzuwar Mami a wajen ya hanashi and he didn't know why burinsa ya kalleta.. kawai yana so idan suna tare yake kallonta baya jin zai gaji da kallon fuskarta. Wannan tunanin yasa shi danyin murmushi kadan wanda sam kona kallonsa ba zaka gane ba.
Har kofar gida ya kaisu yayi parking yana kashe motar. Addu'a Mami ta fara masa tana sake masa godiya kamar ba tayi ba while shi kuma yayi kasa da kansa yana amsawa azuciyarsa haka kawai bai san mesa yake jin nauyin Mami ba kamar irin kunya haka.
Bai kalli Nuri ba saboda Mami yace "ki bata lemar kada ruwa ya jiqata..." Bata jishi ba saboda tunani data tafi kamar bata wajen Mami ta kalleta tana cewa "Nuriyya bakya ji ne?"
Da sauri ta juya ta kalli Mami da wani kalar kallo afuskarta more like shagwaba tace "Mamiiii banji ba faaa..."
Lumshe idonsa yayi yana kasa daurewa yayi mata wani kallon gefen ido irin wanda duk sa idonka ba zaka taba gane ya kalleta ba. Her reaction was something else...not just that... She, as she was, was something else entirely. Everything about her was quite unique and different to him. She was the only girl who could make his heartbeat change over the smallest things.
Kawar da fuskarsa yayi yana kallon sama ganin ruwan kamar ya tsagaita sai yayyafi yasa shi fita wanda yayi daidai da Nuri na fita tare da Mami. Kamar dazu yanzun ma ya tayasu daukar kayansu har bakin kofar gida yayi wa Mami sallama da fatan sauqi ya juya Mami tana sake gode masa Nuri dai tuni ta shige gida don ta mugun kaguwa taga basa tare saboda yadda take jin zuciyarta nayi mata.
Har suka shiga dakinsu Inna bata sani ba tana can tana cin kayan dadinta da tayi kuru ta fitar da kudi ta siyowa kanta, hatta taunar ahankali take yi duk kuwa da tasan babu kowa agidan. Suma basu nemeta a sannan ba gyaran dakinsu suka hau yi tunda kwana biyu basa nan Nuri kuma idan tazo sai dai ta share sama-sama. Cikin minti talatin sun gama gyarashi tsaf tunda ba wasu kaya ne dasu ba shima kuma dakin ba wani girma ne dashi na azo agani ba.
Sai a sannan Mami tace da Nuri suje su gaida Inna. Ba tayi mata musu ba kawai dai far'ar fuskarta ne ya dauke ta miqe tana takewa Mami baya har zuwa dakin Inna dake can karshen gidan a wani dan lungu.
Sallama suka yi wanda yasa Inna yin firgigit ta boye farantin tsirenta da har sannan bata karasa cinyewa ba kasan gado tana goge hannunta da zanin gadon. Wata muguwar harara ta galla musu cike da masifa tace "na baku izinin shigowa ne? Haka ake ku kama ku fadowa mutum daki babu izini?"
Babu wanda yace da ita kala kawai sunyi kasa da kansu ne har ta gaji don kanta da masifar kamin da kyar ta bude baki tana cewa "ga wuri nan ku zauna kuma ba dadewa zaku yi ba yawwa.."
"Gaisheki muka zo yi dama.." Mami ta fada kanta a kasa tana yiwa Nuri alamun ta gaisheta ganin yadda take bin Inna da kallo kamar yau ta taba ganinta.
Instead of ta gaida Inna kamar yadda Mami tace sai cewa tayi "Inna wai naga kullum tsufa kike qara yi gashi naji ance kwanakin nan tsofaffi sai mutuwa suke yi..."
Tuni Inna har ta fara share hawaye da bakin zaninta tana cewa "amman Allah wadaranki mai idanun mayu.. dama na dade da sanin bakya kaunata... Waye ya tsufan kina ganina dar kamar babarki kina cewa na tsufa... Yo da yaushe na tsufa kuma... Wallahi sai dai idan babarki ce tsohuwar amman nikam ko ke bazaki nunamin yarinta ba... Meye kuma tsufa fisabilillahi ina zaune kalau... "
Wani kallo Mami ke yiwa Nuri dake danne dariyar dake zuwar mata ganin bil haqqi da gaske kuka Inna take yi "meye kuma mutuwa ina zaune kalau babu wanda nake fada dashi... Wannan ai mugun alkaba'i ne to ya kare akanki..."
"Kiyi haquri Inna.." Mami ta fada mata ganin dagaske Inna ta dauki zancen Nuri "oya ki bata haquri..."
Tana murmushi ta bawa Inna haquri tana hadawa da "Nidai idan mutuwar tazo ma Allah ya nisanta tsakaninmu dake Inna..."
Sabon kuka Inna ta sake fashewa dashi tana cewa "Allah ya isa dai kawai tsakaninmu mai idon mayu..." Da sauri Mami tace da Nuri "malama fita daga dakin nan.."
"I'm sorry Mami..."
" Fita nace... "
Salin alin ta miqe ta fice tana tabe baki abinta tayi gaba ta shige dakinsu.
"Dama baqar muguwa kika haifa bansani ba Bintu? Ni 'yarki zata zo tana yiwa zancen mutuwa? Ni Laure zata yiwa zancen mutuwa? Kamar ni? Da girmana da mutuncina za'a kiramin mutuwa??" Yadda take maganar zaka san mutuwar kawai ce bata kauna yasa take wannan sambatun.
"To mutuwa dai ba'a nan ba.. danginmu tsayin rai ne dasu wallahi muna yin shekara a kalla dari da tamanin zuwa sama kamin mu fara tsufa ma bare aje ga mutuwa..."
Budar bakin Mami sai cewa tayi "to Inna ai ita mutuwa babu ruwanta da tsufa kowa fa daukarsa take yi ba babba ba yaro..."
" A'uzubillahi minash shaidanin dake kanku ke da 'yarki wallahi... Kuma In Sha Allah mutuwa sai dai ku bani ba... Kema tashi kibi 'yar taki... Kuma wallahi duk nasan kalar zaman da zanyi daku... Ke gidan ma zaku bari na lura mayun ne ku da gaske masu jawa mutum masifa kawai... Fitar min daga daki nace... "
"Alah ya huci zuciyarki Inna... "
"Fitarki ce kawai zata hucen zuciya... "
Miqewa Mami tayi ta fita tana girgiza kanta a haka ta shiga dakinsu ta tarar da Nuri akwance tana danna wayarta. Wajenta ta karasa ta daka mata duka tana cewa "gashi can kinje kin kunnata tana can tana masifar, ban hanaki irin haka ba kinsani sarai ta tsani mutuwa ko??"
Shiru Nuri tayi ba tace komai ba sai sosa inda Mami ta daketa da takeyi fuskarta kamar zata fashe don harta tara hawaye.
"Ni dake ne idan kika sake wannan hawayen ya zubo..."
Kai ta gyada mata tana cewa "tafa san kowa zai mutu ko...Tuna mata fa kawai nayi..."
"To bata buqata kuma karki sake..."
Tana kokarin hana hawayenta zubowa tace "to Mami..." Harararta Mami tayi tana cewa "tashi ki kunnamin wuta ni..."
Miqewa tayi ta karasa wajen kurfotinsu dake dakin ta tsugunna ta fara hada wutar............
JANNAH'S POV
Miqewa tsaye tayi tana ajiye wayarta da tun dazu take dannawa tana jiran reply din Fa'iz data turawa saqo tun shekaran jiya na gaisuwa. Wani iri taji zuciyarta nayi mata ganin baiyi reply ba.
Fita waje tayi wai ta zauna tare da 'yan gidansu saboda ya debe mata kewar rashin dadin da takeji zuciyarta nayi mata. Bata tarar da kowa a parlourn ba sai Sara autar gidansu.
"Yawwa Yah Jannah kinga wani abu don Allah.."
Kusa da Sara ta zauna tana amsar wayarta data muna mata ta karanta tsaf sannan ta kalleta da sauri tana cewa "waye wannan haka Sara?"
"Ban sanshi ba Yaya.. kawai fa tun takuramin yake don Allah yaya kiyi masa magana wallahi har agaban Abba ya rinqa kirana naqi amsawa har Abba ya gane"
"Me zance masa Sara?"
"Kice ya dena takuramin an bada ni. "
"uban waye ya bada ke?" Shiru tayi bata amsa ba.
"Tun yaushe yake miki magana?"
Qasa tayi da kanta tana cewa "almost six months kawai ni bansan ma inda ya sanni ba?"
"Akwai wanda kike kulawa ne ke?"
Kai ta girgiza mata da sauri "babu kowa Yaya.."
"Then ki dena masa wulaqanci Sara it seems babba ne yana da hankali kamar Sara.. sannan six months dinnan kawai ya isa ya tabbatar miki dagske yake sonki ba wasa ba..."
Qasa tayi da kanta tana fidgeting yatsunta ba yace komai ba sai can "yarinya ce fa ni Yaya.."
"Gidanku you're 19 Sara."
Baki ta turo gaba tana yima Jannah wani kallo kamar za tayi kuka. Da kallo Jannah ta bita aranta tana fadar "inama Fa'iz ne yakemin kalar wannan son..." Wannan tunanin kawai ya saka tajii wani iri aranta tayi saurin miqewa tana cewa "think about it Sara we will talk later ina da abinyi..."
Sama ta wuce ta fada dakinta kai tsaye ta nufi wayarta ta duba ko za taga yayi mata reply wa text dinta. Baiyi ba, hakan ya sake kashe mata jiki ta zauna akan sofa dake dakin tana bin simple text din da kallo "barka da rana.. how's your day?"
Bai saba haka ba that's why wannan karan abin ya dameta take tunanin ko saboda yasan tana sonsa ne. Da da bata fada masa ba da tayi masa magana yake mata reply amman yanzu ya canza mata gaba daya.
Ta tuna yadda yayi rejecting dinta hakan yasa hawaye ya cika mata ido "mene yasa na kasa haquri da Fa'iz? I have to give up on him... I will try In Sha Allah wannan karon da gaske nake.."
Tun bayan data fada masa take binsa amman yaqi saurararta duk da ya fada mata gaskiya taqi haqura har ya fara shareta wanda yafi mata komai zafi. Gani take kamar bazata samu namiji kamar Fa'iz Aliyyu Ardo ba....
To be continued....
#like
#comment
#share