A HEART ALREADY TAKEN
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
FU'AD'S POV
Immediately yana komawa motarsa direct Bristol ya wuce saboda sanyin da yake ji na lokaci daya. This time around, gudu yayi abinda bai saba ba saboda yadda yake jin sanyin internally. Yana yin parking ya fito ganin driver dinsa ya miqa masa keyn motar yana fada masa ya gyara don wrong parking yayi da sauri ya wuce ciki saboda yana so yayi wanka da ruwa mai zafi ko zai ji dadi.
Yana shiga dakinsa bathroom ya wuce ya hada ruwa mai zafi a bath tube bayan ya sauya kayan jikinsa da towel ya shiga ciki ya zauna yana sauke ajiyar zuciya jin kamar ruwan yayi masa zafi amman kuma yana buqatar yayi warming jikinsa saboda gudun zazzabi da indai ruwa ya dakesa sai yayi. Sam ya manta indai ya shiga ruwa sai yayi zazzabi mai zafi. Ya tuna dalilin da yasa shi shiga ruwan sai kawai ya lumshe idanunsa yana sake shigewa cikin bath tube din haka kawai ya samu kansa da murmushi aransa yana furta "anything for her!"
At that time ya shiga tunano yadda take komai nata da wannan sanyin da bai sani ba haka take ko kuma wanzuwarsa awaje ne yake sawa ta koma haka don ya lura kamar idan suna tare she's feeling more uncomfortable. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya bayan yayi tunanin dalilin da yasa yake jinta acan cikin zuciyarsa amman bai sani ba. One thing kawai ya sani, which is ya mugun damuwa da ita da duk wani abu da zai shafeta to the extent that baya son ganin damuwarta ko wani abu ya taba masa ita har yake jin kamar he will go far ya kula da ita da komai nata and to give her peace da duk wani abun buqata na rayuwar dan adam.
Bude idanunsa yayi ganin abinda ya kawoshi Kano sam bashi yake ba rather zuciyarsa tana wani wajen daban, wannan karon his heart is with a girl da Allah ya jarabceshi da damuwa da ita which is new to him.
UMMI'S POV......
Tana sanye cikin sky blue applique lace mai touches din blue black da aka yiwa dinkin A-line mai kyau sosai daya dace da shigarta kasancewarta mace mai son gayu kodan bata son ayi mata kallon raini ko kuma kasancewarta mace mai son a ko'ina itace agaba a saman kowa.
Meeting din kungiya za taje hakan yasa ba tayi kwalliya ba sam kawai dai ta saka kaya masu tsada ne ta dauki keyn motarta ta wuce ta fita. Downstairs ta sauka tana wasa da mukullin dake hannunta idonta ya sauka akan Azzam dake zaune yana danna waya.
Shima karar takalminta flat blue black na companyn Zara ya jawo hankalinsa kanta ya dago kai yana kallonta. Shigarta ya qarewa kallo tsaf yana tabe baki ganin yadda komai qanqatar fita idan za tayi sai ta qure wanka.
Dab dashi ta tsaya tana kallon yadda yake binta da kallo tace "ya dai lafiya Mu'az?
"Point of correction Ummi Mu'azzam ko Azzam! meye wani Mu'az kuma?"
Baki ta sake tana kallonsa da mamakin iyayinsa na yau tace "duk da baka san da hakan ba sai yanzu?"
"Nayi upgrading rayuwata ne Ummi duk wani abu da zai ragemin daraja da gayuna bana sonshi beside baki zabamin suna mai dadi ba kamar dai ko yaushe Ummi Fu'ad dinki kika zabawa suna mai dadi ni kuma Mu'azzam. Mu'azzam dinma baiyi miki ba sai kin hada da Mu'az... Me Mu'az fisabilillahi... Daga yau dai karki sake wallahi... Kamar yadda na fada miki ne nayi upgrading rayuwata I will not tolerate any shits yanzu!"
Ya gama kureta da mamaki da yasa ta zama out of words gaba daya banda kallonsa babu abinda take sai can da kyar ta furta "Kai nifa na haifeka ba kai ka haifeni ba... "
"Well na sani fiye da yadda kika sani ma maybe, kawai dai na fada miki ne Ummi ina sake fada miki kuma wannan ya zama karo na karshe da zaki ce Mu'az dinnan... "
Wani banzan kallo ta aika masa tana cewa "ba dole nafi son Fu'ad akanka ba Azzam.. yaron da komai nace yi yake babu second thought... Baya ja dani baya dagamin murya... Kullum burinsa ya farantamin unlike you! Kai kullum burinka ka baqantamin... Ka bata min rai.. ka jawomin magana... Baka taba barina cikin kwanciyar hankali... Ka fadamin me yasa Fu'ad bazai zama wanda nafi so ba?"
Miqewa yayi yana maida wayarsa aljihu ya furta "kinfi sonsa dai saboda yana da abin duniya ni kuma bani dashi!!!"
"Kai enough... I'm not your trash da komai naka zaka na saukewa akaina mind your words akaina idan na tsine maka wallahi sai ta bika!"
Wani kallo yayi mata mai kama da harara yana cewa "ke ya shafa wannan and yes you can idan zaki iya karki manta ni kadai nasan kalar badaqalar da kika aikata a duniya... Ni kadai nasan wannan dukiyar naki duk na haram ne... Blood money!" Yana kaiwa karshe ya juya ya fita yana huci zuciyarsa kamar zata fashe he started regretting ya akayi ma Ummi ta zamo mahaifiyarshi.
While can ya fice ya bar Ummi da baki a sake... Banda zafi babu abinda zuciyarta keyi mata... Bata tabajin danasani irin na haihuwar Azzam ba.. sai taji dama ta zubar da cikinsa lokacin data dauka... He was a total mess to her tunda ga sanda ta dauki cikinsa har zuwa yanzun kuwa.
Da kyar tayi convincing kanta ta fita sai dai cike da bacin rai ta karasa inda suke haduwa kamar kullum. Sai da tayi dagaske sannan ta danne damuwar dake ranta da daura jar kimono kan kayan jikin ta wuce ciki. Kanta a qasa ta samu wajen dake karshe ta zauna ba tare data yi magana ba.
Bonefather da kowa yau kansu aqasa ne kowa yayi shiru acewarsu lokacin sauraran mai share musu kuka ne. Sai bayan minti talatin sannan bonefather ya dago yana binsu da kallo daya bayan daya "shugaba mai jin kukanmu yace munyi aiki mai kyau dukkanmu, don haka akwai tagomashi mai tsoka ga dukkan wani dan kungiya. "
Sadda kansu kasa suka sake yi ba tare da sunce komai ba kowa yana farinciki aransa don sunsan ba karamin samu zasu yi ba indai haka ta faru.
"Sai ke Zuhra.."
Jikinta ya fara bari don tasan probably akwai abinda ya faru "ya muka yi dake akan danki Fu'ad? da muka ce bashi ba aure!"
Kasa tayi da kanta tana bude baki da kyar tace "muna nan akan wannan alqawarin bonefather.. na kuma ja masa kunne akan hakan shima ya yarda..."
"To gashi can a Kano zuciyarsa na tare da wata yarinya daya hadu da ita aranar da yaje Kanon!"
Irin faduwar da gabanta yayi bata jin ko ranar da aka kirata aka sanar da ita gobarar da akayi a shagonta ba tayi ba. Fu'ad yana son wata wannan ai abu ne da bazai taba faruwa ba.. there's no way da zai so wata macen. Tasan halinsa sarai idan yana son abu da zuciya daya yake yi hakan na nufin idan da gaske yana son wata wannan alqawarin dake tsakaninsu da bonefather bazai taba cika ba wanda yake nufin karshenta yazo duk wani fame da dukiya da takeji dashi zai kare, duk wani mugun abu data kulla za'a sani! Me yasa ma ta barshi yaje Kano tun farko? Shine abinda take ta tambayar kanta.
"Kisan yadda za kiyi Zuhra...kinfi kowa sanin abinda zai biyo baya.... Sai kai Lawan!!" Ya juya kan wanda ke gefen Ummi "ya muka yi da kai?"
Sadda kansa qasa yayi yana cewa "saura kiris yallabai na samo kalar wadda kace na aura din lokaci kawai nake jira saboda ta danyi rashin lafiya ne amman da zarar ta warware acikin watan nan komai zai kammalu..."
"Aikinka yana kyau Lawan... Sannan wannan saqon na kowa ne... Shugaba yace babu ku babu sallar la'asar ga duk wani musulmi dake nan wajen sai a kiyaye.." kai duk suka gyada suna cewa "muna godiya"
"Zaku iya tafiya an sallameku" a tare duk suka miqe suka fita daya bayan daya babu wanda ya kula kowa haka suka bar wajen don wannan na daya daga cikin dokokinsu..
Ummi lost in thoughts haka tayi driving back zuwa gida ta fasa zuwa boutique din nata ma da tayi niyyar biyawa daga can. The thought of Fu'ad na can zuciyarsa na tare da wata yaqi barin ranta. Akan gado ta zube tana lalubo wayarta daga jakarta hannunta kamar har rawa yake yi. Bata fatan Fu'ad ya fara so! Don duk ranar daya fara to daga ranar za'a fara kirga faduwarta wanda ba zata taba yarda hakan ya faru ba. Love is forbidden to Fu'ad!!!! There's no way zata bari Fu'ad ya fara so!! No way!!!
FU'AD'S POV....
Minti arba'in ya bata a bathroom din kamin ya fito sanye cikin black bathrobe daya mugun haskashi kasancewarsa fari tas hannunsa daya dauke da baqin towel yana tsane wannan baqar sumar nasa dake da mugun santsi. Yana fitowa wayarsa ya fara ringing hakan yasa yayi hanging towel din nan kan hanger dake bakin bathroom din ya dawo cikin dakin ya dauki wayar. Ganin Ummi ya sashi zama kan gado yana amsawa "Assalamu alaikum Ummi.."
Bata amsa masa sallamar ba kai tsaye ta tafi kan abinda yake damunta "da wacce yarinyar ka hadu a Kano Fu'ad?"
Na dan sakanni haka yaji tunaninsa ya dauke kamar bai gane ba. "Wacce yarinyar ka hadu da ita a Kano?" Ya sake maimaitawa aransa sai dai kamin yayi pounding tunanin Ummi ta katseshi da "ba aiki ya kaika Kano ba daman mace ce ta kai ka? Soyayya ce ta kaika Kano dama?"
"Mace? Soyayya kuma Ummi?" Duk ya tambaya alokaci daya yana jin Ummi na kai tunaninsa high level.
"Eh Fu'ad!!!"
Ya lumshe idonsa yana jin sunansa da take fada har tsakiyar kansa saboda bata saba fada ba..
"Ummi yau Fu'ad kike cewa?"
"Da kana da wani sunan bayan Fu'ad shi zan fada Fu'ad Aliyyu Jimeta!!!"
Rufe idonsa yayi gaba daya yanzu yana jin lokaci daya kansa da zuciyarsa suna relaxing daga sunansa kawai data kira complete.
"Ya muka yi da kai?"
Ya bude idanunsa duka yana saukewa akan agogon dake dakin kalar golden dake nuna karfe 12pm na rana.
"Ina alqawarin da muka yi da kai?"
Ajiyar zuciya ya sauke hadi da kwantawa akan gadon gaba daya yana kallon saman dakin dake dauke da fitulu masu kyau yace "alqawarin me muka yi Ummi?"
"Alqawarin ba zaka kula ko wacce mace arayuwarka ba!"
Har sannan yana kwance yana saurararta "munyi da kai babu kai babu kowacce 'ya mace Fu'ad!!!"
Miqewa zaune yayi yana dan hargitsa sumarsa dake da sauran danshi yace "well, iyaka sanina Ummi ba muyi alqawari ba!! Nasan dai kince karna kula kowacce mace in jira lokacin da kika dibarmin yayi that kin zabamin wadda ta dace dani."
"Then me yasa ka fara kula wata mace ba tare da sani na ba?"
Dan ya mutsa fuskarsa yayi yana jin daban aransa kamar Ummi nason taking control over his life.
"Tambayarka nake Fu'ad wace ce? "
Miqewa tsaye yayi yana nufar mudubi ya kalli kansa tsaf zuciyarsa na hasko masa kammanin Nuri tar kamar tana gabansa yace "wata ce! Wata da bansan komai akanta ba!! All I know is I'm getting attached to her to the extent that nakejin kamar bazan iya jiran lokacin da kika dibarmin ba Ummi!!!!! "
To be continued.....
#like
#comment
#share