NURI

AFIF-SUHANA 4

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa


"Mummy kiyi min dambun couscous yau shi nake son ci." Kallonta Aunty Mimi tayi tana jinjina mata kai "an gama auta yau da bakinki kike fadar abinda zaki ci Masha Allah lafiya ta samu.."

Murmushi Suhana tayi tana daga kai "ai dama naji sauqi sosai kawai I have no appetite shisa bancin abinci amman yau naji kamar zanci wannan din."

"In Sha Allah zan miki auta.. yanzu kike so?"

"A'a da dare bayan Isha.."

"Allah ya kaimu anjiman.."

"Nagode Mummy."

"Don't mention it."

Murmushi Suhan tayi tana daukar wayarta ta fara dannawa hankalinta yana tafiya can gaba daya. Yaran suna wajen mai koya musu karatun islamia da Uncle Farouk ya dauko musu hakan yasa gidan yayi shiru na lokacin.

"Wai ni kuwa kinsan wanda ya kawo ki asibitin nan?"

Shiru Suhan tayi tana tuna washegarin ranar da Afif yaje har asibitin ya sake dubata abinda ya sake burge uncle Farouk dashi kenan plus dama ga zargin da yake akansa.

Kai Suhan ta gyada mata ahankali "makarantar mu daya Mummy and he once solved some problems for me."

Kai Aunty Mimi ta gyada mata tana cewa "uhmmmm yana da kirki sosai wallahi ga sanin ya kamata"

Shiru Suhana tayi tana duban screen din wayarta sai can ta dago tana kallon Aunty Mimi "mummy tun ranar dana fara ganinsa kinsan da wa yayi min kama?"

Kai Aunty Mimi ta girgiza mata tana kallonta, Suhana ta juyo gaba daya tana kallon Aunty Mimi tace "Abbu! Ko baki ga kamar ba?"

Kai Aunty Mimi ta girgiza tana kallonta itama tace "a'a auta na gani tun ranar daya kai ki asibiti har Uncle dinku ya rude sosai ranar kuma har yanzu ya kasa yadda shi din ba jininku bane!"

"Jininmu?" Suhan ta tambyeta da mamaki "eh yace kamar yayi yawa komai nasa exactly irin na Abbu ne fa hatta da sautin muryarsa Uncle dinku yace irin na Abbu ne kawai dai shi akwai yarinta shi yasa ya kasa haqura yau yayi inviting dinsa gidan nan ma."

"Gidan nan kuma mummy? Me zaiyi anan din to?"

"He invited him here for dinner duk da ma yace da kyar yaron ya yadda shi kuma Daddy yace he wants to treat him to a meal because he helped his daughter.."

Qasa Suhan tayi da kanta tana cewa "cin abinci sai kace baya ci Mummy don Allah..."

Wani kallo Aunty Mimi tayi mata har za tayi magana sai tayi shiru kawai tana daukar nata wayar ta fara dannawa tana rabuwa da shirmen Suhan din. Itama ganin Aunty bata kulata ba sai ta maida nata hankalin kan wayarta.

Immediately after Maghrib Aunty Mimi ta shiga kitchen ta fara dafa varieties of foods. Kala uku kawai tayi ciki harda abincin 9ja tuwon semovita da miyar agushi da yayi kyau a ido sai ta hada da dambun couscous din suhana plus juices na natural fruits guda biyu. Sai bayan Isha ta kammala ta bar gyaran kitchen din wa maid dinsu ta haye sama ta gyara kanta sannan tayi sallahr Isha. Bata dade da idarwa ba Uncle Farouk ya shigo dakinta sanye cikin farar jallabiya wanda yayi indicating ya dawo har yayi wanka ya sauya kayan daya fita dasu.

Miqewa Aunty Mimi tayi ta ninke abin sallar nata ta maida inda take ajiyewa sannan ta karasa wajen da Uncle Farouk ya zauna ta zauna agefensa.

"Sannu da dawowa Azeez.." kallonta yayi fuskarsa dauke da murmushi "sannu darling ygd?"

"Alhamdulillah."

"Kinsha aiki ko? Ga Suhan ba kwarin jikin tayaki aiki!"

"Ba mai wahala nayi ba ai girkin simple foods na dafa yazo ne?"

"Kai ya gyada mata "eh yazo.. darling yau na kara tabbatar da yaron nan yana da alaqa damu kinsan me yayi? "

Kai ta girgiza masa ya riqo hannunta yana cewa "kinsan family dinmu idan suna mura suna da wani sara to same naga yayi yau har na tambayeshi lafiya yace mura yake and he was used to it indai yana yi..."

Leaning tayi ajikinsa tana cewa "to ta ina kuka hadu Azeez?"

"Shine abin tambayar darling.. I really don't know taya? Ni nasan bamu da wani dangi da bamu san dashi ba sai....." Da sauri ya zabura yana dago Aunty Mimi daga jikinsa ya kalleta "wait Mimi... FADIMATU!!!"

Kallon cikin idonsa Aunty Mimi tayi da mamaki tana cewa "Fadimatu Kuma? Meye hadinsa da Fadimatu?"

"Yes Fadimatu Mimi... Zai kasance komai nasa yana kama dana Abbu ne only and only if ya kasance jinin Fadimatun Abbu ne!!!"

Widely haka Aunty Mimi ta bude idanunta tana gyara zamanta da kyau "da gaskiyarka Azeez..idan kuwa hakane zamu iya sanin inda fadimatu take ta hanyarsa ne kawai.."

Kai ya gyada mata yana cewa "da kuwa bansan kalar farincikin da Abbu zaiyi ba dama gobe nake shirin tafiya Houston dubashi... "

"nace zan bika kaqi yadda Azeez."

"Darling ki bari muga yadda jikin Abbun yayi kinga yau akayi aikin and it was successful Alhamdulillah. Ki bari sai ya farfado sai muje duka har yara mu duboshi ko?"

Baki ta turo masa kamar yarinya "naji  amman don babu yadda na iya da kai ne Azeez.."

Murmushi yayi yana miqewa tsaye itama ya miqar da ita "muje mun barshi shi kadai.."

Tare suka fita uncle Farouk ya sauka kasa Aunty Mimi ta shiga dakin Suhan don kiranta.

Akwance ta tarar da ita tana kallo a tab dinta hankalinta gaba daya ya tafi ga film din da take kalla banda murmushi babu abinda take.

"Aikin kenan kallon wannan masu jajayen kunnuwan.."

Tana zabga murmushi ta dago tana cewa "ba zaki gane bane Aunty Mimi wallahi suna tsumani ne sai na riqa hangomu tare da Hamma F.."

Wani kallo Aunty Mimi tayi mata irin har yanzu kina nan dai Suhan "Fu'ad again Suhana? Ba an kwabeki kan Fu'ad ba? Yayanki ne shi din fa"

"Amman akwai aure tsakaninmu Aunty Mimi.. he was my cousin and I'm into him Aunty Mimi da gaske ina son Hamma Fu'ad!!"

Shiru Aunty Mimi tayi duk da ita kanta bata san dalilin da yasa aka ce babu ita babu Fu'ad ba amman da zata so hadin nasu.

"Tashi muje mu ci abinci kinji.."

Hawaye ne ya ciko idon Suhan tana kallon Aunty Mimi tace "kema irin na Ammi zaki min Mummy? Me yasa kuka kasa yadda dani ne wai? Me yasa kuka ce ni da Hamma F are not meant for each other why?" Wannan karan hawaye ne ya biyo fuskarta time din data zo karshen maganarta.

Agefenta Aunty Mimi ta zauna tana riqo hannayenta tace "ban sani ba Suhana.. ban san dalilin ba kuma shi kansa Uncle Farouk bai san dalilin ba? Babu wanda yasan dalilin Suhana!! And yes kamar yadda kika ce ne Fu'ad was just your cousin don haka akwai aure a tsakaninku..."

"Aunty don Allah... Ki taimakamin to tunda Ammi ta kasa yadda dani ita da Abbie wallahi da gaske ina son Hamma Fu'ad da zuciya daya don Allah Aunty ki tayani mu fadawa Hamma Fu'ad.."

Tausayin Suhan ne ya rufe Aunty Mimi hakan yasa ta rungumeta ajikinta tana rarrashinta "it's okay auta.. ya isa I'll help you sai dai karki manta ke mace ce taya zaki zama wadda zata fara cewa tana son namiji?"

"Amman Aunty ba nice farko ba? Nana khadija Allah ya qara mata yarda ita tayi proposing auren Ma'aiki sallallahu Alaihi wasallam don haka wannan ba komai bane sunna ce mai kyau Mummy.."

Kai Aunty Mimi ta gyada mata tana dagota daga jikinta "hakane Suhana.. ni kuma nayi miki alqawari I will help you har ki samu zuciyar Fu'ad, zan tayaki wannan yaqin kinji..."

Murmushi Suhana tayi tana damqe hannun Aunty Mimi tace "amman Mummy karki fadawa Uncle kinsan shi duk abinda Abbie yace baya musu..."

"Ba zai sani ba har sai Fu'ad ya fara sonki shima ya fada musu da kansu ko?" Kai ta gyada mata da sauri tana rungumeta tightly  "thank you so much Mummy Allah ya saka miki da alkhairi."

"Aameen auta taso muje kici abinci nayi miki couscous din da kika ce."

Tare suka miqe bayan Suhan ta yafa mayafi ajikinta suka fita zuwa kasa inda suka tarar da Afif zaune aqasa while Uncle Farouk akan kujera "ya ka zauna akasa Afif"

Murmushi kawai Afif yayi yana yin kasa da kansa Uncle Farouk yace "kema dai kya fada nayi nayi dashi ya zauna yaqi yadda.."

"To ai shikenan Bismillah let's go and eat."

Miqewa uncle Farouk yayi yana sake cewa da Afif ya taso suka wuce dinning tare. Shi dai Afif duk wani iri yake jinsa especially bayan tambayoyin da Uncle Farouk yayi masa da yaga kamr yayi yawa haka.

Aunty Mimi ce tayi serving dinsa komai data girka tana yi tana harararsu Nadra da suka cika musu kunne.

Har aka fara cin abincin Nadra surutu take sai da Uncle Farouk ya mata tsawa sannan ta nutsu har aka kammala kuma bata sake magana ba.

Afif dai kansa yana kasa yana taba abincin da aka zuba masa kuma tuwon semovita kawai yaci shima tabawa yayi don ya kasa sakewa dasu.

Suhan dai hankalinta gaba daya yana kan maganar da suka yi da Aunty Mimi har ta kagu su kammala cin abincin su sake maganar yadda zata jawo hankalin Fu'ad kanta.......

To be continued....

#like
#commenr
#Share