A HEART FORCED TO FORGET
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
Pharmacy ya wuce ya amso mata maganin da za tayi amfani dashi sannan ya fita ya wuce motarsa ya fita daga asibitin gaba daya. Restaurant ya tafi nema da zai samo mata abincin da za taci. Ya dade sosai kamin ya samu inda zai sai mata abincin yayi parking ya fita ya samo mata abunda yasan jikinta yana buqata wanda zai gina mata jiki sannan ya dawo ya koma asibitin.
Time din daya koma ita har bacci ya dauketa ma sai Mami kawai zaune agabanta tana kallonta kamar zata mai da ita ciki. Sallama yayi yana shiga ciki Mami ta dago kanta ta kalleshi tana amsa masa sallamar. Karasowa yayi ya tsugunna daga nesa da Mami yana miqa mata pack din magani da abinci dake hannunsa yana cewa "gashi Mami maganinta ne.."
Da wani kalar kallo Mami ta bishi tana jin jikinta gaba daya yana yin sanyi akan yadda yake kula dasu. Though she sensed something, don the way yake abu hatta yadda yake mata magana was something else, the care was physically noticeable in the way he cared about Nuri.
"Dawainiyar tayi yawa.." da sauri ya girgiza mata kai yana cewa "a'a Mami bai yi ba.. zan tafi Allah ya bata lafiya.."
"Aameen Yah Hayyul Qayyum. Mungode Jazakallahu Khairan."
Murmushi kawai yayi yana miqewa tsaye ya juya zai tafi Mami ta kirashi "yaron kirki."
Ya saba da yadda take kiransa don haka kai tsaye ya juyo yana rusunawa qasa ya amsa da "na'am Mami."
"Ban san sunanka ba fa har yanzu."
Murmushin dai ya sake yi kansa a qasa ya amsa mata da "Fu'ad."
Kai Mami ta gyada masa tana murmushin itama tace "Masha Allah Fu'ad Allah ya albarkaci rayuwarka."
Ahankali ya amsa mata da Aameen sannan suka sake yin sallama ya fita. Da kallo Mami ta bishi har ya fita tana cigaba dayi masa addu'a aranta. Kamin ta dawo da kallonta kan Nuri dake kwance tana bacci, wani murmushin kawai ta sake yi tana girgiza kanta irin na manya. Already ta fahimci Fu'ad kamar yana son Nuri amman rashin lafiyar nan nata ya tabbatar mata da hasashenta. Kawai wani lokaci can ta tuna da Nuri ta isheta da kukan banza har take cewa waye ma zai so ta ahaka and here is one unique soul devoted to her.
Share tunanin tayi don ba wannan ne gabanta ba abubuwan da suke gabanta da yawa sosai. Ringing din wayarta yasa tayi saurin daukar wayar kamar yadda ta zata Afif ne don shi kadai ne wanda take waya dashi hatta da Mummynsu Zara nisa yasa amintar yayi rauni sosai don sai afi wata biyu babu wanda ya nemi wani har gwara Nuri da Zaran though suma ba kamar da ba.
"Assalamu alaikum yaron Mami."
Murmushi sosai Afif yayi daga can yana cewa "wa'alaikumus Salam Mamin Afif shi kadai."
Murmushi mami tayi tana kallon Nuri tasan da idonta biyu da tuni sun fara sai da halin "a'a fa Mamin Nuriyya da Afif dai ko.?"
"Ita ba zata iya haqura ba ta barmin ke.?"
"Kai ba zaka iya haqura ka bar mata ni ba?"
"Mamieeeeeee" da dan karfi ya kira sunanta kuma da sigar shagwaba sosai ya kara da "Allah Mami naga kamar tafiyana yasa kin rage sona.."
"Subhanallah.. wace ni da zan rage son autana? Daduwa son yake yi kullum Afif."
Yana dariya yace "yawwa Maminmu.. Mami shikenan wai ni bazanzo na ganku ba har sai nan da two years and a half.."
"Uhmm ya zamuyi.. ka cigaba da haquri kaji Allah ya bada sa'ar abinda kaje nema Afif gashi kamar wasa har kayi shekara daya kamar yau za kaga ka gama duka."
"Allah ya nunamin ranar nan Mami wallahi kamar na jawo haka nake ji"
"Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba."
"Mami Ina Adda ne? "
Kallonta Mami tayi tana cewa "bata jin dadi ne kagan mu a asibiti.."
Da sauri hankali a tashe ya furta "bata da lafiya Mami? Tun yaushe? Kwantar da ita akayi?"
Kai Mami ta daga masa kamar yana gani ta amsa masa da "ba wani abu ne ba fa na tashin hankali Afif.. "
"ba abn tashin hankali ba Mami? Kwantar da ita fa akayi.. "
"Look, it's not that bad Afif. Calm yourself down and pray for her that's all. She will be discharged soon fa ba wani abin ta da hankali bane.. "
Shiru yayi kawai baice komai ba yana jin dama yana da yadda zaiyi ya dawo gida sai dai babu sam. Wai ahaka fa duk Afif bai san abinda ke faruwa ba. Bai san abubuwan da suka faru ba bayan tafiyarsa. Tashinsu daga gidansu, dawowarsu gidan Inna, rashin lafiyar Mami and now Nuri. Na Nurin kawai ya sani amman ji abinda yake yi.
"Afif.." Mami ta kirashi jin yayi shiru "uhmmmm.."
"Uhmm zaka ce min?"
"Sorry Mami na'am."
"Ka kwantar da hankalinka kaji don tana bacci ne ma da idonta biyi zaku gaisa kaji muryarta yana nan yadda yake kila ma kuyi halin naku da kuka saba"
Yana gyara zamansa akan gadon dakinsa ya amsa da "ok Mami.. Allah ya qara sauqi yasa kaffara ne.. ki gaidamin ita idan ta tashi zan kira da wuri gobe In Sha Allah na dubata kiyi mata sannu kinji kice mata biyayyenta yayi kewarta sosai Mami.."
She doesn't know why his words broke her heart like that. Kawai take jin bayan nisan da Afif yayi mata kamar ita da Nuri kaddara na shirin sake nesanta su da wannan kudurin na Inna.
"Zan fada mata in Allah ya yadda karkasa damuwar komai aranka kaji auta." Kansa ya gyada yana cewa "In Sha Allah Mami I will pray for her, for you both Mamina. I missed you both.."
"Ok take care sai anjima."
"Bye Mami ki kularmin daku kinji Mami."
"In Sha Allah Afif.."
Da kallo Mami tabi wayar bayan ya kashe daga can. Haka kawai tana yin murmushi data tuno kalar rayuwar da suka yi da lokacin da Abba yake nan. Life was smooth and enjoyable, komai ya tafi musu yadda suke so kamar su suka tsara. And now within two years, life has completely turned upside down. Abba's dismissal, Afif's journey, and now ita akaran kanta tana shirin yin aure ta bar haskenta!!!!
JANNAH'S POV
Acikin sati biyu kacal ta canza, she tried hard ta ture soyayyar Fa'iz daga ranta. Ta bawa kanta haquri sosai that ita da dan mutan Ardo are not meant for each other. Ta barshi yadda yake as jarabawa daga Allah. Ta fadawa Abbanta ya samo mata wani aikin asibtin sai dai ya bata sharadi zai samo mata ne only and only if ta kawo mijin aure and there tun awajensa ta fada masa Zaid.
Wannan shine babban kuskuren da Jannah tayi arayuwarta, bata tsaya ta duba wanda ya dace da ita ba kawai ta zabi Zaid. Tayi tunanin tunda Fa'iz bai yadda da ita ba shikenan kamar bata da sauran farinciki arayuwa.
Bayan sun gama magana da Abba ta koma part dinsu still ta samu Mamma da maganar ta fada mata ta zabi Zaid as her fiancee ba tare da ta tabbatar da hakan daga Zaid din da kansa ba. Kawai she believed that Zaid yana sonta sannan zai yadda da abinda za tace masa.
And yes, haka akayi daren ranar Zaid ji yayi kamar ya zuba ruwa aqasa ya sha. Tana jin kalar sambatun da yake sai dai sam ko daya babu wanda ya burgeta kawai dai ta bar wayar akunneta ne tana saurarasa don bata da abin cewa.
Zaid da zumudi haka washegari ya sanar da magabantansa aje atambayo masa aure. Ataqaice abangaren Jannah rayuwa ya bude mata sabon shafin kaddararta. Zaid ya kawo kudi an saka rana wata shida tunda suna ganin kamar ta girma tana early thirties ai babu sauran wani zance sannan shi kansa Zaid din babba ne ba yaro ba yana around 46 haka so babu wani jan lokaci da za'a yi.
She tried hard ta ajiye duk wani abu da zai rinqa tuna mata da Fa'iz arayuwarta. Tayi blocking dinsa ta goge duk wani abu da zai tuna mata shi. Ta mugun maida hankali tana cusawa kanta son Zaid da bashi da guri azuciyarta kamar dai tana cutar kanta haka.
Hatta farinciki da walwalar da take ciki, she's faking it. Babu wani abu da take da yake gaskiya kawai ta dauko new face ne ta dorawa tana ganin kamar zata iya... And let's wait and watch wanne kalar kaddara ne yake jiran Jannah agidan Zaid. Did she made the right decision or not?
To be continued...
#like
#comment
#share