NURI

A MOMENT LIKE THIS I

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa


"Waye bai zo ba?" Mami ta tambyeta tana ninke kayanta da ta sauya. Kai ta girgiza da sauri tana cewa "uhmmmm uhmmmm babu kowa" Kallonta tayi na sakanni tana so ta fahimci abinda take nufi amman bata gane ba hakan yasa ta miqe tana cewa "anjima za'ayi discharging dinmu Nuriyya In Sha Allah. Yanzu fadamin me kike so kici naje na dafo Miki." Kallon Mami tagi ganin yanzun ta gama cin abinci amman Mami zancen wani take. 

"Me zaki ci anjima naje na dafo miki?" 

"bazanji yunwa ba zuwa lokacin ni karki tafi ki barni ni kadai."

"Ba dadewa zanyi ba ina so na kai kayan nan gida sunyi mana yawa"

"Ni don Allah bana jin yunwa ki zauna zan tayaki daukan kayan"

"Ke ban son musu, as I said ba dadewa zanyi ba kalla duk kayan da muka tara na kwana biyu kawai"

Shiru tayi don idan Mami ta zama serious irin haka hankalinsu suke shiga.

Miqewa Mami tayi ta dauki kayan tana kallonta ganin yadda tayi pouting lips cike da shagwaba yasa tayi murmushi kawai "Allah ya shiryeki Nuriyya, take care bazan dade ba In Sha Allah."

Ahankali ta amsa mata da "sai kin dawo Mamie." Kai ta gyada mata tana fita itama baso take tana barinta ita kadai ba to amman basu da kowa da zai zauna dasu har gwara ma jiya da maqociyarsu Maman Hanif tazo shine ta tafi ta barsu amman yau yayi wuri bata shigo ba.

Wani irin tausayin kansu ne gaba daya ya rufesu ita da yaran nata gaba daya. Though basa tare da Afif amman shima yana can wata qasar all alone, har gwara su da suke su biyu sai dai su dinma kansu kawai suke da. Murmushi kawai Mamin tayi tana addu'ar Allah ya kular mata da yaranta aduk inda zasu samu kansu.

----------

Da kallo Nuri tabi qofar dakin da tana jin hawaye yana cika mata ido. Kawai bata son taga Mamin tayi nisa da ita, she didn't know why kwana biyu take jin haka tare da ita. Hannu ta kai ta share qwallar daya biyo fuskarta tana miqewa ta shiga toilet dake dakin ta wanke fuskarta da hannunta ta tsaya tana kallon kanta amudubi. Gani tayi ta rame kamar dai yadda Mami ke fada mata hakan yasa tayi kalar tausayi tana cewa "Allah sarki Mami shisa take ta mitar rashin cin abincina ashe na rame sosai." Kai ta girgiza tana juyawa ta fita aranta tana fadin dama can haka take. Tsayawa tayi cak tana kallonsa idonta kamar zai fada kansa ga zuciyarta data harba mata lokaci daya.

Kanta ta kalla Allah ya taimaketa abaya ce ajikinta sai tayi saurin kwance dankwalin kanta tayi rolling dashi tunda babba ne. Kasa takowa cikin dakin tayi kawai ta tsaya nan bakin toilet din sai kallonsa take ganin hankalinsa duka yana kan wayarsa. Bata taba qare masa kallo ba sai yau sai take ganin kamar bata taba ganin wanda komai nasa yake daban ba kamar shi, bata sani ba kodan bata fiya kallon maza ne ba yasa bata taba ganin wanda ya kaishi kyau ba.. ba wai kwalliya yayi ba no qarewa ma yana sanye cikin simple outfit na jeans da sky blue shirt da suka mugun yi masa kyau ga dakin tuni ya koma qamshin turaren nan nasa da bata taba jin irinsa ba kamar dai yafi duk mazan data sani iya gayu. 

"Zaki iya zuwa ki zauna idan kin gama qaremin kallon!!"

Wani irin zaro idanu tayi tana saurin dauke idonta daga kansa ta turo baki gaba tana hade fuska irin karma ya kawo mata raini haka. Ganin bata qaraso ba yasa ya dago kansa ya kalleta sai ya tsaya ganin yadda tayi kamar wadda ke jiran qiris din nan. Murmushi yayi yana cewa "zo ki zauna babu wanda zan fadawa kin dade kina kallona"

Wani irin kallo ta sanyawa fuskarta kamar wadda ke shirin yin kuka ba tare data kalleshi ba da kyar tace "ni ban kalleka ba.."

Kai ya gyada yana bude idonsa widely irin ya yadda din nan yace "ohhh ai see ba kallona kika yi ba kawai dan kallona kika yi ko?"

This time around bama tasan ta kalleshi da wannan yanayin nata na shagwaba ko yaushe ba tace "ni ko dan kallonka banyi ba..." Da yake kuka baya mata wuya tuni har ta tara kwalla a idonta.

Miqewa tsaye yayi yana ajiye wayarsa kan kujerar daya tashi ya nufo inda take yana qare mata kallo fuskarsa dauke da murmushi ya tsaya dab da ita "baki kalleni ba na yadda shi kenan."

Da sauri ta daga masa kai wani hawayen yana sake bin fuskarta ya miqa mata handkerchief dinsa yana cewa "to sarkin kuka goge hawayen" qin amsa tayi kamar yadda taqi kallonsa tace "da wanne idon kasan na kalleka to?"

Kawar da fuskarsa yayi yana murmushi mai sauti kadan kamin ya dawo yana kallonta "kin yadda kin kalleni kenan? "

Kai ta sake girgiza masa da sauri tana cewa "ni banyi ba kuma ai banga abin kallo anan ba.." Lokaci daya maganar nata ya dauke kamar an dauke ruwa tana dan wara idanunta jin abinda take shirin fada shima ware idanunsa yayi yadda yaga tayi yana jinjina kai da dan mamaki wato dama tana magana haka "baki ga abin kallo anan ba..." 

Da sauri ta dago kanta tana girgiza masa kai ta karya kanta tace "ni ba haka ba Allah.. ni ka tafi tunda kazo kake min sharri.."

Murmushi sosai yayi yanzu yana kallonta yace "nayi miki sharri?"

Kai ta gyada masa tana cewa "eh sai cewa kake nayi abu kuma banyi ba kuma ai kaine kayi naga"

"Nayi me?" Ya tambaya curiosity all over his face. Bata kalleshi ba tace "kaine kayi duka abinda kace nayi.." yana jinjina kai ya matsa baya yana cewa "na yadda zo ki zauna kin dade a tsaye zaki gaji." Ta gefensa ta wuce tana dauke kanta yadda ba zata kalleshi ba taje ta zauna. Juyowa yayi daga nan inda yake tsaye ya sake qare mata kallo kamin ya qaraso ya zauna a inda ya tashi baice komai ba ya danyi shiru yana mata kallon gefen ido.

Ita dinma kallon gefen idon take masa tana son yin magana amman bata san ta yadda zata fara ba sai can da kyar ta furta "dama zaka zo?"

Dakawata daga turo saqon da yayi niyyar yi yayi ya dago da sauri ya kalleta. Bashi take kalla ba hasalima hannunta take kalla tana warasu kamar mai qirga yatsu nawa take da.

"Kin damu nazo ne?" Ya tambayeta yana bin fuskarta da kallo. Da sauri ta girgiza kai tana cewa "ban damu ba.. me zaisa na damu?" Ta tambya tana son ture tunanin da yake zuwa ranta amman kamar yadda ya fada ne haka kawai taji kamar ta damu da bai zo din ba.

"I'm sorry kinji, tun da safe naso zuwa aiki ne ya riqeni.. ya jikin naki? ko da yake kinji sauqi ma ai tunda har kina iya qarewa mutane kallo.."

A shagwabe ta dago fuskarta ta sauke idanunta akansa kamar zata yi kuka tace "ni na rantse ban kalleka ba...." Sanin tsaf zata iya kuka yasa yayi saurin girgiza mata kai yana cewa "tsokanarki fa nake, baki kalleni ba ko sau daya tunda kika fito..."

Wani kalar kallo tayi masa that caught his attention towards her, zata yi magana sai kawai ta fasa ta koma tsakiyar gadon tayi zamanta tana nade kafarta.

"Ina Mami?" Shiru tayi masa kamar bata ji ba, ya bita da kallo jin bata amsa masa ba and yasan taji sai sai cewa yayi "kinyi fushi ne?"

Kamar ta sake share shi sai taji ba zata iya ba hakan yasa ta daga masa kai alamar eh. Kamar yadda ta saba yiwa mutane da shagwaba shima haka yayi yana cewa "I'm sorry ranki ya dade Nabdi bazan sake ba." Taso ta basar taqi kulashi kamar dai dazu ta kasa daurewa har ta dago ta kalleshi this time around cikin idonsa ta kalla duk kuwa da cewa yana mugun yi mata kwarjinin da bata son hada ido dashi "ba zaka sake ba to?"

Da sauri ya gyada mata kai yana cewa "idan na sake kiyimin duk hukuncin da kika ga dama kinji.." da sauri ta dauke fuskarta daga kallonsa jin kamar tana son yin murmushi saboda yadda yayi kamar wani yaro.

Shima yana murmushi yabi fuskar nata da kallo ganin ta dauke daga kallonsa "amman kinsan rowa babu kyau ko?"

Bata bari ya qarasa ba tayi saurin cewa "don Allah ka tafi bani da lafiya fa kuma sai magana kake sakani yi..." Ta dan saci kallonsa ganin yadda yake kallonta yasa ta dauke fuskarta tana cewa "dama kana magana?" 

Kai ya girgiza mata yana cewa "a'a bana yi ke kadai kawai nake wa.." ta gefen ido ta sake kallonsa kamin tace "in fadi abu zaka yi?" Yadda tayi maganar yasa Fu'ad qura mata ido sosai yana jin kamar he was born to love this girl dake gabanshi "anything for you Nabdi.."

Kallonsa tayi this time around amman ba cikin idonsa ba tace "to kayi shiru don Allah." 

Shiru yayi kamar mai tunanin nan sai ya daga mata kai yana yi mata alamar an gama da hannunsa. Shiru duk suka yi while ita kanta yana kallon gefe shi kuma idonsa akanta kamar mai gadin kada wani abun ya hau kanta. Ahaka suka yi minti kusan biyar dakin ya dauki shiru sosai baka jin komai sai sautin fanka.

"Ka dena kallona manaaa." Unexpectedly, haka yaji muryar nata hakan yasa yadan leqa fuskarta yana cewa "ni ban kalleki ba."

Juyo da fuskarta side din da yake tayi tana cewa "Allah kayi.." shima kamar yadda taqi yadda tayi dazu haka yayi "ni banyi ba da wanne idon kika san na kalleki kenan kema kallona kike?"

Da sauri ta girgiza masa kai abinka da mara wayo tace "ai na gani ne shi yasa...."

Murmushi yayi kawai yana komawa ya jingina da kujerar da yake kai ya dauki wayarsa yana duba lokaci akwai inda yake son zuwa.

"Yause Mami zata dawo?"

"Nasan tana hanya ma."

"Yau za'a sallameku. " Kallonsa tayi irin ya akayi ka sani dinnan ya daga mata kafada kawai. 

"Nuriyya!" Tone din daya kirata kawai is enough ya nuna maka cewa maganar da zaiyi serious magana ne hakan yasa tayi saurin amsawa da "Na'am."

"Idan kun koma gida akwai abinda nake son fada miki yana da muhimmanci sosai kinji." Kallonsa tayi kamin ta daga masa kai ahankali. Shima kallonta yayi yana mata murmushin da ya sakata saurin dauke kanta daga kallonsa ta kawar da fuskarta gefe haka kawai ta samu kanta itama da yin murmushin kamar yadda yayi har dimples dinta suna nunawa. Kallonta yayi yana jin kamar ya fada mata abinda yake son fada mata yanzu amman yasan nan is not the right place.....

To be continued...

#like
#comment
#share