NURI

TWIST OF FATE

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa


Bai taba sanin jin mutum yana daukewa na wani lokacin ba sai yau. Fadar kalar shocked din da ya shiga ma bata lokaci ne irin like abu ne yazo masa unexpected from the person that brought him to this world, matar da bin umarninta ya zamar masa dole har dai bai sabawa Allah ba.

"Kaji abinda nace maka ko?" Ahankali kamar wanda yake jin tsoro haka ya girgiza mata da kai, muryarsa tana yin rawar da bai san daga ina bane, ya bude baki kamar mai ciwon baki ya furta "a'a.." da kyar.

"Let me make myself clear to you Fu'ad... a matsayina na mahaifiyarka nace idan ka sake ka sake kula wannan yarinyar ka to na yakefa wa duniya har abada and duk ranar daka sake zuwa Kano Allah ya isa tsakanina da kai, kome ne kuwa zai kai ka, koda business dinka ne Fu'ad!!"

Kai ya hau gyada mata several times, kawai har lokacin bai dawo daga shock din da ya shiga ba. Da ace akwai wani akusa dashi, wayar zai miqa masa ya fassara masa abinda Ummi take fada, sai yaji kamar wani yaren Ummi take masa.

Muryrasa na breaking yana magana da kyar yace "Ummi me nayi miki?" Shine kawai abinda ya iya tambyarta alokacin. Duk tarin abubuwan dake ransa, the fact that ta rabashi da yarinyar nan yafi komai tsaya masa arai, akan haramta masa zuwa Kano. Kai wait, ko bata haramta masa Nuri ba, ta haramta masa zama agarin da take. 

Idonsa yayi wani kalar jaa kamar wanda ya kwana ya wuni yana kuka a lokaci daya. "Ban isa da kai ba Fu'ad a matsayina na wacce ta kawowa duniya?" Yau she's using authority words da kana ji kasan yes eh an fa isa da kai. 

Da sauri ya girgiza mata kai yana mugun dakewa. A matsayinsa na tsayayyen namiji ya daga hannunsa da kyar ya nuna kansa yana cewa "nine fa Ummi" irin yana so ya tuna mata shine fa Hayaty dinta da take so take qauna. 

"Kai din Fu'ad shisa na maka haka nasan duk abinda na fada zaka min. Kome ne kuwa, prove this to me Fu'ad. Prove me na isa da kai Fu'ad! You have today kawai ka tattara komai naka ka bar garin nan Fu'ad!"

Kai ya hau gyada mata ba tare daya sake cewa komai ba. Ya zare wayar daga kunnesa ya ajiye gefensa ba tare daya kashe ba, kamar dai lokaci daya yaji an zare masa dukkan wani kuzarinsa. Ya yunqura da nufin tashi tsaye, yaji ya kasa daga kafafunsa. You know there's a kind of state da mutum zai shiga yaji kamar an zare masa lakar jikinsa, to irin kalar wannnan state din Fu'ad ya shiga.

Duk daya fahimci kamar bazai iya tashi ba amman haka ya daure duk kalar azabar da yaji qafarsa nayi masa daya rasa daga ina ne. Yasan dai baya da ciwon qafa sam amman yau, from nowhere, yaji ta fara masa. Yana cije baki haka yayi ta maza ya miqe tsaye yana jin Ummi tana cewa "are you there, Fu'ad?" amman ina, kalmomin da zai amsa mata dasu sun qare. Yaji kamar babu wata kalma data rage masa a duniya.

Da dingishi kamar wanda yake koyon tafiya haka yakai kansa bathroom ya tsaya qasan shower ya sakarwa kansa ruwan sanyi, duk kuwa da yasan yana da matsala da ruwan sanyi. A time din bai ma iya ya tuna yana da matsala da ruwan sanyin ba. Hannu yasa ya dafa glass din jacuzzi da yake ciki yana kurawa spot daya kallo kamar yana so ya fahimci da kalar glass din da aka kera wajen. "A'a, from today's henceforth babu kai babu yarinyar nan ko sake kulata ka kayi ban yafe maka ba!" Kamar duk cikin abubuwan da Ummi ta fada masa wannan yafi tsaya masa arai. Eh, yes wnn zai fi tsaya masa a rai fiye da sauran saboda boundary ne akayi masa da bugun zuciyarsa!! 

Bai san adadin mintina nawa ya bata atsaye anan ba. Kiran sallar magaribar da yaji ne yasa ya miqa hannunsa da kyar ya kashe shower din, sannan ya fara zare kayan jikinsa da suka jiqe sharkaf. Ya jawo towel ya daurawa kugunsa ya fito da kyar yana hada hanya kamar wani wanda yasha yayi tatul. Yana fitowa sanyin AC ya bugeshi, a take jikinsa ya fara rawar sanyi. Da kyar ya iya qarasawa closet ya dauki kaya ya saka, bai damu da ya tsaya ya gyara jikinsa ba. Anan dakin yayi sallar magariba don da gaske wani irin zazzabi ne ya rufeshi lokaci daya, banda karkarwa babu abinda jikinsa yake yi.

Ya dade a takure zaune awajen kamin ya iya miqewa ya samu remote ya kashe AC ya hau kan gadon ya kwanta yana Jan duvet ya rufe jikinsa gaba daya har kansa. A lokacin bai san Ina kansa yake ba kawai gashi nan gashi nan da kyar wani wahalallen baci yayi gaba dashi....

NURI'S POV.....

Bata san dalili ba kawai ta samu kanta da yin murmushi bayan ta shiga cikin gidansu. Ta tsaya anan soron gidan nasu tana ta zabga murmushi ita kadai ba tare data san dalili ba. Kofar gidan nasu dake arufe ta juya ta kalla tana jin kamar ta bude taga ko ya tafi amman bata da wannan courage din sam, kuma ta tabbatar bai tafi ba saboda bata ji qarar tashin motarsa ba alamar yana nan har lokacin kenan. Dan durqusawa tayi ta zura idonta ta wajen mukulli ta leqa taganshi tsaye yana kallon kofar gidan nasu. Da sauri ta ja da baya tana jingina da bango, still wannan murmushin nata mai kyau take har lokacin. Adadin time din daya dauka awajen, adadin dadewar data yi atsaye awajen, har sai data tabbatar ya tafi, ta samu kanta da miqewa tsaye sosai sai alokacin kuma ta dawo hayyacinta ta dungure kanta tana cewa "what's wrong with you Nuriyya?" Karkatar da kanta tayi kamar mai nazarin abinda ke damunta kamin ta girgiza kai kawai tana furta "I'm ok kawai dai kirkinsa ne yayi yawa da kowa will feel what I'm feeling"

Sai lokacin dake ta dawo hayyacinta ta fara jiyo sautin Inna daya cika gidan tana balbale Mami da masifa. Da sauri ta qarasa cikin gidan ta tarar da Inna tsaye ta riqe qugu kamar wadda za tayi dambe, while Mami na tsugunne arakube agefe kanta aqasa kawai tana jiran ta gama masifar nata.

Wani kallo tayiwa Inna kamin ta qarasa wajen Mami tana cewa "Mami, for Allah's sake ki tashi mu bar mata gidan nan bafa wahayi akayi akace dole sai mun zauna agidan nan ba"

"To sannu Nuratu hamshaqiya riqaqqiyar mara kunya, ita uwar taki bata da bakin maidamin magana sai ke." idan iskar dake wajen ta kula Inna to Nuri ta amsa mata. Qoqarin tashin Mami daga tsugunnen kawai take yi.

"Babu inda zamu je idan mun barnan Nuriyya.. kiyi haquri bana so kiyi rayuwa irin nawa.."

"Zanyi irin rayuwar naki Mami babu komai. Let me feel what my mother feels..."

Janyota Mami tayi tana zaunar da ita gefenta ta furta "lokaci ya qure Nuriyya..."

Kamin Nuri ta amsa Inna ta rigata da furta "zamanki dai anan din shine don kinsan dai bazan bar jinin Audu agantale ba ko?"

Basu kulata ba sai cewa da Mami tayi "ina kince baki yadda da auren ba Bintu?" Da sauri ta kalli Inna tana so ta roqeta tayi shiru da maganar saboda Nuri da bata san zancen ba. Ta tsara zama na musamman wanda zata fahimtar da ita komai da manufar auren.

Kallon Inna Nuri tayi kamin ta dauke kanta aranta tana furta "matar nan kamar ta fara shan wani abu wacce Mamin ce za tayi aure?" Sam bata dauki abinda muhimmanci ba hakan yasa ta kalli Mami za tayi magana taji Mami ta furta "na yadda Inna, nayi tunani naga babu inda zamu je. Nan din dai shine rufin asirin mu ko nace shine rufin asirin Nuriyya.."

Baki Nuri ta saki tana kallon Mami, jin Inna ta fara magana sai ta maida kallonta kan Inna tana jinta tana cewa "saura kwana sha daya yau kamar yadda na fada miki kije ki fara shiri..."

Hannu tasa ta dan bugua kanta kamar irin wadda ke mafarkin nan kamin ta dawo kan Mami tana cewa "Mami me kuke magana akai.." Riqota Mami tayi tana miqar da ita tace "taso muje nayi miki bayanin komai.." Bin Mami tayi kamar raqumi da akala har zuwa cikin dakinsu suka zauna gefen katifarsu. Mami ta juyo da fuskarta side din da take ta fara da "I'm sorry haskena..."

Kai ta girgiza da sauri tana cewa "no need Mami, ki dena bani haquri. Kece fa kika kawoni duniya so please Mami.."

"Aure zanyi!!!" Kallon Mami tayi irin what the heck kamin kuma tayi murmushi tana girgiza kanta tana tunanin kodai ba taji daidai ba.

"Tun kamin na fara rashin lafiya Inna ta zabamin wanda zan aura.. "

"Kuma auren nasa zaki yi?" Ba tasan lokacin data furta hakan ba sai jin Mami na cewa "eh Nuri for your well-being, Nuri yace zai biya miki kudin makarantarki harki gama..."

"Kin sai da kanki for me Mami?" Mami tana kallon cikin idonta, ganin yadda kwalla ya cika mata ido yasa ta riqo hannunta tana cewa "bani da kudi Nuriyya, kuma bani da hanyar samunsu sannan ina so na cikawa mahaifinku burinsa na karatunku..."

Kwace hannuunta Nuri tayi tana matsawa baya ta furta "amman baice ta haka za'a cika masa buri ba Mami. Don Allah karki yi, wallahi na haqura da karatun tunda ba shine zai kaini aljanna ba Mami.."

"idan baki goyamin baya ba waye zai goyamin Nuri?"

"Mami bana so. Bana so ki tafi ki barni don Allah.. Mami Abba ya tafi, Afif yayimin nisa, and now kema kin zabi kiyi aure ki barni. Ni kadai, ya zanyi da raina ni kadai, don Allah?"

Kai Mami ta girgiza mata tana cewa "ga innarku nan Nuriyya tayi min alqawarin zata kulamin dake.."

"Kuma kin yadda? Alqawarin Inna daidai yake da alqawarin wanda yaje ya sha giya yayi mankas Mami, for goodness sake kiyi haquri kizo mu bar mata gidanta. Nasan dashi ta miki barazana kika yadda Mami. Allah yana tare damu. He will never forsaken us..."

"Ya kike so nayi da raina Nuriyya? Ko kina so nabi abban naku kawai ki huta sai kiyi rayuwar ke kadai kamar yadda kike buri!!!"

Wani tsayawa cak tayi tana kallin yadda Mami ke magana tana danne saitin zuciyarta. "Baki san yadda nake ji akan auren nan ba, na tabbatar na fiki jin radadin hakan azuciyata! Instead of ki qarfafamin gwiwa, look at what you're doing Nuriyya! So kike zuciyata ta buga na fadi na mutu duk ku huta?"

Kai ta hau girgiza mata tana fara kuka "don Allah Mami kiyi haquri ki dena wannan zancen. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajee'un, Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakeel.. " Rungumeta Mami tayi tightly ajikinta tana sake cewa "for me Nuri, ki amince saboda ni." Kai ta hau gyada mata da sauri tana kuka tace "ki dena kuka don Allah. Wallahi na yadda, na amince Mami, na yadda, na yadda. Ki dena kuka, ki dena zancen mutuwa don Allah. Wayyo Allah na.." Daga Nurin har Mami kuka suke suna rungume da junansu, babu mai rarrashinsu. Ranar batan Abba ya dawo musu sabi fil sun tabbatar da Abba yana nan hakan ma will never happened. It was clearly dai Abba shine bangonsu, shine garkuwarsu!!!!!!

To be continued.....

#like
#comment
#share