THE END OF OUR LOVE STORY
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
FU'AD'S POV
Around 9 ya farka ya time din zazzabin yadan sauka don haka ya miqe tsaye duk da haka da kyar saboda wani weakness da yake ji. Bathroom ya nufa ya daura alwala ya fito ya shimfida abin sallah ya tayar da sallahr Isha da baiyi ba. Ya dade sosai a sallar saboda hatta karatun sallahr ahankali yake yi likewise yadda yake motsa jikinsa duk daurewa yake yi. Bayan ya idar addu'a kawai yayi ya haqura da shafa'i da wutiri ya miqe ya lalubo wayarsa ya kira new PA dinsa. Sai da yayi picking ya tuna ba magana ma zai iya ba don haka ya kashe kiran yayi masa text kan ya duba masa idan akwai available flight adaren duk da yasan is hard a samu.
After 10mins sai ga kiran PA yana fada masa babu flight din dare don haka yace to su shirya su fito da motacinsu zasu tafi a daren. He saw no reason da zai cigaba da zama agarin da aka haramta masa shi garin da aka tsine masa idan ya haura deadline din da aka bashi don haka is better ya bar garin. Haka ya miqe cike da dauriya ya fara tattara kayansa yana hadesu duka a trolley dinsa bai damu da yadda suke a hargitse ba burinsa kawai shine ya bar Kano.
Wajen qarfe goma duka suka hallara ya zama shi kadai suke jira don haka yayi waya yana cewa wani yazo ya daukar masa kayansa ya qarasa shiryawa. Navy hoodie ya dora akan kayansa saboda sanyin da yake ji ya zura sneakers aqafarsa sannan ya fita. Yana fita suka bishi da kallo ganin yanayinsa da ko ba'a fada musu ba sunsan bai da lafiya hakan yasa duk suka yo kansa PA yana cewa "Sir, are you sure you can travel by car? Abuja is far away."
Kai kawai ya gyada masa bai ce komai ba yayi gaba da sauri wani ya qarasa ya bude masa back seat ya shiga yana sauke ajiyar zuciya. Idanunsa ya rufe lokacin da motocin nasu suka fara tafiya suka bar Bristol din yana jin kamar wani sabon zazzabin ne zai dawo masa. Da kansa ya bada umarnin suyi gudu don so yake kamin 1 su Isa Abuja.
Zazzabin ne kuwa ya sake rufeshi da ya sakashi baccin dole acikin motar bai farka ba sai dab da zasu bar Kano. Ya bude idonsa yana bin inda suke da kallo kamin ya zaro wayarshi daga aljihun hoodie din dke jikinsa ya bude ya shiga contacts. Sunan da ya saka mata a wayarsa yayi searching ya fito boldly NABDI with emoji. Qurawa sunan ido yayi kamar yana ganin mai shi ta ciki. A yadda ya tsara shine ace by this hour yanzu ya kirata yaji muryarta tunda ya samu hanyar da zai ke communicating da ita. Ko bama wannan ba yana so ya sake dubata, ya sake jaddada mata cin abinci da bin dokar likita. Wato baka da iko da Qaddararka no matter who you're, now look at him leaving Kano without saying goodbye to her qarewa ma alaqar nasu duk da bai fada mata ba an kawo qarshenta, qarshen ma ta worst way!
Shi kansa bai san dalilinsa na searching sunan nata ba kawai ya samu kansa da yin hakan ne. Ya dago yaga suna border din barin Kano su shiga kaduna. Wani irin karyewa zuciyarsa tayi ahankali ya rufe idonsa aransa yana furta "And this is the end of our love story..." Dumin da yaji yana bin fuskarsa yasa shi kai hannu wajen just to find out that hawaye yake yi. Ya dace ace yayi mamakin hawayen don he can't recalled last time da yayi, ko time din da Pal dinsa bai da lafiya kuwa. Yasan yana da jarumta da dakiya sosai da ba zaka taba cewa kaga raunin Fu'ad ba amman yau duk babu su sunyi nasu wajen, so ba wasa ba malam😂. And he found out that NURI ce rauninsa, she is his weakness kuma bai san son da yake mata ya kai matakin da har zai saka shi a wannan state din ba. Daman can dai yasan shi idan yana son abu da dukka zuciyarsa yake yi hakama idan bai so. To amman bai zata zai fada wa so irin haka ba sai gashi nan yayi ruff in Love, Love that will never be forever!! Love din da iya shi kadai yayi abinsa wadda yake son bata sani ba kuma haka zai tafi ba tare data sani ba. Kamar dai bai da sa'a haka in Love...
Qarfe daya ce ta kaisu Abuja saboda irin gudun da suka yi ahanya plus daman dare ne so babu wani congestion. Gida suka nufa dashi kai tsaye inda suna ajiye shi ya basu umarnin su tafi suma suje su huta sannan ya wuce flat dinsu.
Dakinsa ya wuce wanda yake nan agyare kamar yana nan as a result of gyarashin da kullum Ummi ke sawa ayi. Kan gado ya ajiye gadgets dinsa ya fara rage kayan jikinsa ya fada bathroom yayi wanka da ruwa mai dumi sosai don zazzabin jikin nasa yaji ya sauka gaba daya sai weakness din da yake ji kawai yasan yana yin wankan zai dena ji.
Black jallabiya ya saka wanda ta mugun fitar da hasken fatarsa ya shimfida abin sallah ya yayi nafila plus shafa'i da wutirin da bai yi ba and there ya roqa Allah ya bashi ikon cin jarabawarsa ya kuma zaba musu abinda yake alkhairi shi da NURI. Yasan is hard ya manta da ita, bama is hard ba bazai taba mantawa da ita ba, she is his first love, akanta ya fara so, akanta yasan yadda so yake and he promised himself that ya rufe so daga kanta!!!
Wayarsa ya dauka ya fara duba available flight da zaije Huston gobe Allah ya taimekahi ya samu flight din safe da zai tashi qarfe 10 amman zasu yi transit a two different countries. Wannan bai dameshi ba damuwarsa shine ya bar qasar gaba daya he needs to go far away from the country so that his heart will heal. Ba wani baccin kirki yayi ba ji yayi kamar anyi wiping masa baccin idonsa gaba daya hakan yasa time din asuba nayi kamin ayi kira yaje ya daura alwala ya fita daga gidan gaba daya ya nufi masallacin da ahanya kamin ya qarsa aka yi kiran assalatu.
A masallacin bayan an idar ya hadu da Abie wanda ya riqa binsa da kallon mamaki a iya saninsa Fu'ad yace dashi zai dawo ne idan ya kammala aikinsa and yace dashi aikin nasa da akwai saura to why all of a sudden ya dawo gida?
Tare suka jero da Abie bayan sun kammala azkar dinsu sai dai shiru Fu'ad tun bayan gaisuwar da yayi wa Abie bai sake cewa komai ba. Kallonsa Abie yayi ganin yadda fuskarsa tayi jajawur sosai yace "baka da lafiya ne Fu'ad?"
Da sauri ya girgiza kansa ya bude baki da kyar kamar mai ciwon baki ya amsa masa da "I'm okay kawai stress ne."
"You're overworking Fu'ad ka riqa hutawa mana haba you're a CEO a company dinka please spare yourself."
Kai ya jinjinawa Abie yana cewa, "In Sha Allah zanje Huston Abie."
"Me Kuma za kayi acan?"
"Abbu" kawai ya iya cewa don ji yayi kamar magana tana yi masa wahala.
"Ok amman idan kaje can ka huta nasan Amminku ma ba zata bari kake yin irin yadda kake yi anan ba, haba mutum sai kace engine" Kansa kawai ya daga masa suna shiga cikin gidan tare suka nufi part din Ummi da haka kawai yaji zuciyarsa tana masa dawo masa da tune din Ummi tayi masa magana dashi jiya.
Time din da suka shiga dakinta har ta koma ta kwanta hakan yasa Fu'ad kawai ya juya ya koma part dinsu. Text yayi wa Fa'iz yana fada masa time din da jirginsu zai tashi ya qara masa da bayanin dadewar da zasu yi.
Wani irin urge na barin qasar duk ya damesa to the extent da yake jin dama ya bude ido kawai ya ganshi ba'a qasar ba. And he gradually started feeling hatred for the country. Dan kwantawa yayi da niyyar ya huta tunda ba bacci yake ji ba. Sai dai Allah ya taimakeshi baccin ya bashi hadin kai ya daukeshi da bai farka ba sai 9. Idonsa akan time ya fara sauka hakan yasa ya miqe a zabure ko wanka baiyi ba kawai ya canza jallabiyar dake jikinsa da outfit din Hermes ya dauki duk wasu abu da zai buqata ya hade waje daya ya fita da sauri yana barin wannan qamshin nasa a dakin.
Bai hadu da Azzam ba har ya shiga part din Ummi daya tarar da ita suna breakfast da Abie. Kallonsa tayi ganin yadda ya shigo da sauri kamar wnd yake in a hurry. Sai Kuma tayi murmushi ganin yadda fuskarsa ta canza kawai tasan hukuncin data yanke masa jiya yayi tsauri amman bata da option bayan wannan. Ba zata taba bari Fu'ad yayi aure ba tayi wannan alwashin, bare ma ace waccan yarinyar da aka fada mata ita ce silar rushewarta.
Har qasa ya durqusa ya sake gaida Abie sannan ya gaida Ummi dake kallonsa tana so taga ko yana cikin damuwa sai dai bata karanto hakan ba don bai bada wannan damar ba. Abu daya kawai zaka gane tare dashi shine yadda fuskarsa tayi ja as a result of rashin lafiyar da yayi.
"Abie Ummi zan tafi Huston flight dinmu ya kusa tashi." Wani kalar ajiye spoon dinta Ummi tayi tana cewa, "ban gane Houston ba Fu'ad? Me zaka yi a can? Daga dawowarka kuma Ina zaka je?"
Kasa amsa mata yayi kamar yadda ya kasa kallonta sai Abie ya kalla shima baice komai ba.
"Fu'ad fa ba yaro bane Zuhra ki dena takura masa yaron da nan da shekaru kadan ma aure zaiyi ya bar miki gidan kike wannan maganar akansa zaije ya dubo Abbunsu Fa'iz ne daga can kuma nace ya dauki hutu he's overworking.."
Kai ta hau gyadawa kamar wata kadangaruwa tana kallon Fu'ad da take so ya dago fuskarsa ya kalleta ta bashi saqo da ido amman ina kamar ya gane abinda take shirin yi ko sau daya bai dago ya kalleta ba "tashi muje na kai ka airport din ka makara ma ai."
"Sai na dawo." Ya fada referring to Ummi da bama taji sanda ya fada ba sai son ya kalleta da take. Miqewa yayi suka fita tare da Abie da ya kai shi har airport.....
To be continued
#like
#share
#comment