FAR AWAY FROM NURI
by @saddiqahhh
NURI
By Saddiqa
"Fu'ad!" Abie ya kirashi attentively yana kallonsa. He's not that attached to him closely saboda yanayin aikinsa, plus shi kansa Fu'ad boarding school yayi and his university life gaba daya was abroad, so yafi shaquwa sosai da Umminsa.
"What actually was wrong with you? You seem disturbed?" Bai kalli Abie ba coz abinda yake fighting dashi azuciyarsa ya isa, bai son ayi adding mashi salt a ciwonsa "Babu komai Abie, kawai na danyi zazzabi ne kwana biyu, but Alhamdulillah I'm okay now."
"Then let's shift this journey maybe next week.." Da sauri ya girgiza kansa yana kallon Abie dake tsaye yana kallonsa. "A'a Abie I'm okay. I can take care of myself.." A yadda yake jinsa yanzu babu inda yake so yayi nisa da sama da qasar nan. Yaji kamar zamanshi a qasar nan was useless. He needed to go far, far away daga nan, wai ko zai manta abinda ke damunsa. He was heartbroken by his own mother, wadda ke sonsa.
"Take care and please idan kaje ba aiki ka huta kaji." Kai ya gyadwa Abie ba tare da yace komai ba ya juya suka yi sallama ya qarasa jin an fara boarding announcement. Bai juyo ba sam ya kalli Abie don yana ta struggling da zuciyarsa da yaji kamar yanzu da yake shirin yin nisa da qasar komai yafi masa zafi.
Time din daya zauna a seat dinsa yayi fastening seatbelt tun kamin ma ayi announcing ya koma yayi relaxing akujerar yana rufe idonsa. Life was beautiful before ya fara so, he wished bai ma fara ba, he wished bai zo Kano ba, he wished bai hadu da ita ba. Kai, no, haduwa da ita was one of the best things that happened to him, kasancewa da ita was one of his best lifetimes. And he will never regret knowing her, never!
Bai son zuciyarsa nada kalar wannan raunin ba sai jiya zuwa yau. Da kallon duk wanda yake gigicewa a so a mara abin yi yake, but now he sees what they saw, he experienced what they experienced. In fact, nashi love story din was bitter. His love story was different from everyone's love story. Nashi is unique, sai yaji dama bai fara ba da duk he will not go through this. Nasa was incomplete and will never be complete because of his mother da tayi using wani ladder ta datse relationship dinsa.
Ahankali ya bude idonsa da yake nan jajawur har sannan kamar mai ciwon ido ya gyara zamansa sosai jin ana sanarwa a saka seatbelt jirginsu will soon take off. Yana zaune a side din window ne don haka time din da jirgin ya fara gudu ya maida kansa yana kallon qaton filin tashin jirgin absentmindedly. Bai kuma dauke idonsa daga nan ba har sai da jirgin ya tashi ya daidaita a sama suka fara tafiya sannan ya kawar da fuskarsa yana rufe idonsa da suddenly suke masa radadi da yaji amman ya hana kansa kuka ya fara koyar taurin zuciya da da bai dashi.
"This really is our end NURI."
His journey to Houston was terrible, filled with thoughts that he wanted to let go. Sunyi transit a Ethiopia plus Canada amman duk haka nan yake moody. Fuskar nan nashi a mugun daure sosai abinda sam ba halinsa bane ba. Time din da suka je Canada ne ma ya dauki black jacket ya qara akan kayansa saboda yanayin sanyin garin, which is the same acan Houston.
Alhamdulillah sunyi landing lafiya cikin ikon Allah. Kasancewar bai wani zo da kaya mai yawa ba, yawanci yafi so sai yazo ya siya ko asai masa, don haka jakar goyo kawai ya taho da ita all the way from Nigeria. Yana fita departure lounge ya hadu da Fa'iz dake zaune yana jiransa acikin daren don it's already night anan.
Kallo daya yayi wa Fa'iz kamin ya dauke kansa yana nufar inda yake ba tare da ya sake kallonsa ba. Dagowar da Fa'iz zai yi idonsa ya sauka kan Fu'ad da yake tahowa majestically cike da wannan charisma din nasa dake nan, very captivating. Murmushi yayi yana gyara tsaiwarsa ya jira har ya qaraso yana masa murmushi ya furta "And finally, here comes the great CEO that fell in love..."
Jakarsa kawai ya cire ya miqa masa yana yin gaba ba tare daya bashi second look ba tun dazu daya kalleshi. Dan kallon bayansa Fa'iz yayi kamin yayi saurin bin bayansa suna jerawa tare yace, "You're not you Fu'ad. Meke faruwa?" Bai kulashi ba, kawai tafiya yake yi yana zura hannunsa cikin aljihun jacket dinsa saboda sanyi kamar ma snow ake anan garin. Don haka ya juyo yasa hannu ya zare hular sanyin dake kan Fa'iz ya sawa kansa yana qarawa gaba. Hararar bayansa Fa'iz yayi yana cewa "Dan rainin wayo, kasan da sanyin ai ka taho haka.." Winter scarf din dake wuyansa ya cire ya qarasa inda Fu'ad din yake ya daura masa a wuya sannan suka cigaba da tafiya har suka fita wajen da motar Fa'iz din yake suka shiga.
Kallonsa Fa'iz yayi yana jin wani iri kawai saboda yanayinsa daya gani sam is not inviting. Ya zira seatbelt dinsa yana cewa "This is not Nigeria man. Fasten your seatbelt.." Ba tare daya kalli Fa'iz ba ya jawo seatbelt din ya saka sannan ya koma ya kwanta akujeran motar bayan ya jawo hular ya rufe masa rabin fuskarsa.
Kasa tuqa motar Fa'iz yayi kawai yana kallon Fu'ad din. Ko bai fada masa ba yasan something definitely is wrong with him and this is not Fu'ad daya sani. Fu'ad dinsa na da duk abinda ke damunsa yana fada masa ne from the start, then what changed his Pal?
Fu'ad yaji ajikinsa Fa'iz kallonsa yake amman sam bai da niyyar ya bude fuskarsa ya kallesa sai ma gyara kwanciyarsa da yayi baiqi su kwana anan ba.
"I can't drive kana ahaka Pal!" Bai kulashi ba kamar ma baiji shi ba alhalin yaji.
"I knew kana jina Fu'ad. You're killing me.." Nan ma shiru, bai ma yi motsin da zai bashi damar yasan yaji shi ba.
"You're hearing me na sani Fu'ad. I beg you, with all the 99 Names of Allah the Almighty, ka fadamin abinda yake damunka. This is so unusual of you Pal.. My Pal was not like this.. This is a total version of you."
Instead of Fu'ad ya kulashi sai miqewa yayi yana maida hular kansa sama ya bude idonsa yana bude motar ya fita gaba daya. Allah ya taimakeshi, yana fita ya tare cab ya hau yana barin Fa'iz da sakin baki yana kallonsa.
"What really is wrong with him?" Sai yayi tsaki kawai yana jan motar nasa yabi bayansu har zuwa sanda suka Isa the Post Oak Hotel. Ganin Fu'ad ya nufi ciki yasa ya fita shima yabi bayansa yana kiran sunansa amman yadda kasan dutse yake kira haka. Don haka ya cigaba da bin bayansa har zuwa sanda suka isa wajen receptionist, duk yana tsaye ya gama purchasing dakin da zai zauna yana ta masa magana yayi banza dashi. Dole ya cigaba da bin bayansa har zuwa cikin dakin nasa dake nan very luxurious one.
Abinda zai baku mamaki was Fu'ad duk yasan Fa'iz yana binshi amman tun wannan kallon da ya masa na farko a airport har yanzu bai bashi second look ba.
Akan sofa Fa'iz ya zauna ya tallafe kumatunsa yana qurawa Fu'ad ido kamar ya samu TV. While shi Fu'ad jacket din jikinsa da Winter scarf din ya cire duk ya ajje gefe sannan ya shiga bathroom ya hada ruwan wanka mai zafi saboda sam bai son amfani da ruwa mara zafi ko mai dumi especially da yanayinsa yake na sanyi kadan sai mura.
Time din daya bata a bathroom din ya kusan one hour, almost 30mins plus akan yadda yake, and it's like komai nasa ya fara canzawa gradually. Kawai bai jin dadin komai haka. And that's with the sudden attitude change, yaji baya son magana, he prefers silence, yaji bai son hayaniya, he prefers being alone. Yaji bai son kowa, in fact he wants to continue his life alone. Amman yaga alamun being in Houston kamar will add to what he's struggling with, don haka yayi making mind dinsa daga ya duba Abbu gobe zai yanki ticket ya wuce Dubai. Can ne babu kowa da zai takura masa kuma yana da branch acan. At least zai ke zuwa office yana aiki ko don ya debe masa kewa.
Da wani kalar kallon qurilla Fa'iz ya bishi yana so yaga ko ya canza fata ne kalar wannnan dadewar da yayi. Ganin yana nan yadda yake bai canza ba sai ma kamar fadawar da yaga yayi yasa ya koma ya jingina da jikin kujerar yana murmuring. With all the murmuring da yake, Fu'ad bai nuna yasan da zamansa anan ba, and the worst part of it is bayan ya gama sauya kayansa zuwa pyjamas sai ya nufo inda yake, yasa hannu ya miqar dashi ya fitar dashi can bakin qofar dakin without saying anything. Ya juya yayi slamming qofar a bayansa.
Fa'iz feels like ya durawa Fu'ad ashar at that time, he was like what the heck is going akan Fu'ad. Idan ma ranshi ne abace, why not confide in him or better ya danne duk abinda ke bata masa rai idan bazai iya confiding da kowa ba. He feels like ya rabu dashi ya koma apartment dinsu amman ina, he can't. It was Fu'ad Aliyyu Jimeta, his one and only brother da yake da a duniya and only friend. Friend din da zai tsaya masa through every thick and thin, then why mesa shi ba zai tsaya masa ba through this hard phase, duk da bai san asalin abinda ke faruwa ba amman koma mene ya fahimci babba ne. Abinda zai saka Fu'ad ya canza gaba daya haka is definitely big........
To be continued..
#like
#comment
#share