NURI

A NEW VERSION OF HIM

by @saddiqahhh

NURI

By Saddiqa


Ko kadan Fu'ad bai ji komai kan yadda yayi treating Fa'iz ba. Bai ji kamar yayi ba daidai ba kawai one thing da yake so shine kadaici. Hakan yasa yana korarsa daya koma sai ya samu wuri can edge of the ottoman sofa dake dakin ya zauna yana crossing legs dinsa. Hannusa duka biyun ya tsurawa ido yana ganin yadda jini yake gudana ta cikinsu fatar nasa yayi jawur sosai. Hade hannyensa yayi waje daya kamin ya koma yayi relaxing yana kallon saman dakin da aka mugun qawata da fitilu. Haske masa ido yaga sunyi hakan yasa ya miqe yaje ya kashesu duka ya bar dim light kawai yaji kawai yadda zuciyarsa ke cikin duhu haka yake so dakin ya kasance masa.

Komawa yayi ya zauna a inda ya tashi yana kwantar da bayansa jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Wani irin daci yaji zuciyarsa nayi masa to the extent that yake iya ji har bakinsa. And right now yasan babu abinda zai yi wiping wannan abun da yake ji. Ba qaramun qoqari yayi ba na ganin ya ture duk abinda ke cikin ransa amman ina! He can't ba zai ba. Yasan wannan abin will never be erased from memory dinsa.

Yaji dama bai je Kano ba, he regrets being in Kano da hakan duk ba zai faru ba. Da bai samu kansa cikin wannan halin ba. Da Ummi ba tayi masa revealing wannan side of her din da har yanzu bai gama yadda Umminsa dake qaunarsa ce ta yanke masa hukuncin ba. Ummi that loves him, Ummi that loves what he loves ammn yau Ummi was against what he loves harma kamar sama da ransa.

Like shi kansa bai taba tunanin zai yi kalar wannnan son wa wata macen ba never. And the thing is daga jiya zuwa yau maimakon da Ummi ta yanke masa wannan hukuncin yaji ta bar ransa sai ma yaji kamar anyi doubling son da yake yi mata ne. It quietly occurs to him that wallahi yafi sonta yanzu da yayi nesa da ita kan time din da suke kusa da junansu and he started thinking of yadda zai yi tackling rayuwarsa bayan yasan shi dai gaba daya ta haramta agareshi har dai ba Ummi ta janye tsinuwar da tayi ba which for sure yana da tabbacin ba za tayi ba. Kawai yadda tayi masa magana da wannan authority din yasan an gama komai an he feels something da bai taba feeling ba akan Ummi. Ummi never fails him ta kowacce hanya amman akan abinda yake so wannan karan tayi. Bata duba cewa shi mai biyayya ko yaushe bane ta masa haka.

And he started imagining yadda rayuwa zata tafi masa ahaka shi da yake so ya manta da ita yaji komai yana sake renewing kansa plus doubling. How can he continue ahaka? Miqewa zaune yayi yana girgiza kansa ahankali. One thing for sure is zai bi umarnin Ummi amman yasan shi da farinciki Kuma kamar shi kenan. Just kuyi imagining kan ku in his shoes zaku ji yadda yake ji. That feeling na baka taba son wani ba sai yanzu kazo kuma kana mishi so na gaske irin na forever din nan kwatsam kuma wani yazo ya zama barrier ai ba zaka taba mantawa da komai ba sai dai kawai ka shanye komai.

Same thing applies to Fu'ad Aliyyu Jimeta da yake jin yasan ba zai manta da NURI ba never! Amman he will let everything about her go, ya haqura da ita for real, zai yi biyayya wa Umminsa. Amman ta hanya daya kawai hakan zai faru he must change, dole sai ya canza gaba daya, zuciyar Fu'ad din yanzu ba zata iya handling wannan ba don haka he must change. Zai yi facing komai ya ajiye gefe ne da wata sabuwar zuciya, sabuwar zuciyar daya tabbatar zata yi affecting dinsa da wanda yake tare dasu! Ba zaiji dadin canjin ba haka ma wanda suke tare dashi duk ba zasu ji dadin canjin ba. It was simple kawai a new version of him will emerge!!

NURI'S POV

There will never be life without obstacles, there will never be life without challenges!! Besides everyone has his own destiny, his own Qadr which was already decreed before he was born in a book of decree. NURI believes all these difficulties da suke facing are part of their Qadr, tasan Allah yana son yaga haqurinsu ne don haka kawai tayi wiping hawayenta tana barin jikin Mami trying very hard to be strong tace "Mami is okay I'm with you through thick and thin and will forever be with you Mami. We will cross this bridge In Sha Allah..."

Cupping fuskarta Mami tayi tana murmushi da kana gani kasan na dauriya ne kawai ita kanta Mami was down ammn sbd wnn halittar that was so dear to her yasa take qarfafa kanta ko yaushe. "Nuriyya na Allah ya albarkaci rayuwarkj a duk inda zaki tsinci kanki, Allah ya kularmin dake tare da dan uwanki..."

Da sauri ta matsa baya tana girgiza kai ta kalli Mami, wannan addu'ar sak irinta Abba yayi mata ranar da zai bata ya barsu. Ba wai bata son addu'ar bane kawai the fact that Mami ba shirin yin nesa da ita yasa ta ke jin kamar Qaddara na shirin maimaita masa kanta ne.

"Me ya faru Haskena?" Da sauri ta girgizawa Mami kanta tana cewa "a'a babu komai Mami.." qureta da kallo Mami tayi na wasu sakanni trying taga ko wani matsalar ne ammn sam bata ga komai ba iya zallar fear take gani kwance a fuskar Nuri wanda bata san daga ina yake ba. Amman da tayi duba da yanayin da suke ciki sai taga dalilai da yawa da zai sa Nuri tayi reacting haka.

"Ki miqa lamarinki duka wa Allah, He sees and bai barin bawansa daya dogara dashi. Karki manta kalar promises din da Allah da kansa yayi wa bayinsa masu haqri da suke tare dashi... Indeed Allah is All-Seeing and All-Hearing Nuriyya... sannan dukkan tsanani yana tare da sauqi.. naji ajikina sauqin ne yake tunkaromu both ni da ku NURI..."

Hawaye sababbi ne suka sake biyo fuskarta tana gyadawa Mami kai bakinta na rawa ta furta "na ydd Mami, sauqin is near In Sha Allah"  rungumeta back Mami tayi tana patting bayanta cike da rarrashi. She prays komai zai wuce, ya dawo musu kamar yadda suke da. Sai dai taya zasu koma da bayan babu Abba?

Kamar Afif ya fahimci halin da suke ciki sai ga kiransa. Hannu kawai Mami ta miqa ta dauko wayar don yana kusa dasu ne tayi picking.

Yana kan gadonsa ya kashe fitilar dakinsa sbd dare ne can sosai ma ya amsawa Mami sallamar ta yana cewa "Mami mafarkinku nayi are you alright naji muryarki wani iri, Ina Adda? Ya jikinta taji sauqi?"

Murmushin da Mami bata shirya ba shi tayi tana cewa "oh come on Afif wanne zan amsa yanzu?"

"Duka mana Mami ki bata idan tana kusa or maybe kawai Mami kisa a handsfree"

Yadda ya fada haka tayi tana dago Nuri dake jikinta tayi saurin wiping mata hawayen dake fuskarta tana mata alama da ido kan tayi hqri kukan ya isa haka nan.

"Adda are you there? Kinji sauqi ko wai ba'a sallameku ba?"

Mami ce ta amsa masa ganin Nuri tana son daidaita kanta ne "ka ganmu nan agida an sallamemu."

"Wai tana Ina Mami tana jina ina magana.."

"I'm here biyayye am, naji sauqi sosai."

"Mami remove the phone from speaker 'yar rainin wayo ce adda wato tana jina tamin banza ki gaya mata fa I'm no match for her..."

Murmushi Mami tayi tana cewa "gsky you're no match for her harda kana qasar waje."

Murmushi yayi jin yau Mami ta biye masa ya qara da "yww Mami am, Kuma wallahi Mami ta ganni yanzu sai ta raina kanta na zama dan gayu ga jikina Mami duk na fa tashi daga Afif din da kuka sani har gyming nake Ina daga qarfe."

Tsaki Nuri tayi tana tabe baki tace "ji to wa zaka burge wallahi banji ka burgeni ba.."

Kwantawa yayi yana cewa "a'a fa fadi gsky nasan nafi wannan mayen naki da kike cewa an bada ke."

Wata uwar harara ta zabga masa don takaici ta tsani ake mata maganar khaleel kamin ta bashi amsa ya qara da "shi gashi nan kamar a hure ya kife kema haka tab kice ku haka zakuyi making couples din wai."

Da sauri ta qarbe wayar daga hannun Mami tana cewa "Kai nifa ba sa'arka bace yawwa Kuma wallahi ka zuba ido muna nan da kai sai na tashi kanka da wanda zan kawo maka."

Baki Mami ta saki tana kallonta tana jin Afif yana cewa "ki tashi kanki dai adda ni ai kin riga da kin tashi kaina da wannan dan jalamangen naki."

Wato dan uwa dan uwa ne duk kalar damuwar da kake ciki indai za kuyi magana dasu za kaji 60 or maybe 50 percent din damuwar naka yayi wani wajen "ka dena hadani dashi Allah, my prince charming was more handsome than you kai who are you compared to him..." Dan dakatawa tayi data kai nan a zancenta jin zuciyarta na hasko mata Fu'ad. Abinda sam bata taba irin wannan zancen wani yazo kanta ba kawai yau all of a sudden Fu'ad come to her mind. Dagowa tayi tana ture tunanin daga ranta zata sake magana taji Mami na cewa "Ashe baku da ta ido ban sani ba yaran nan.."

Sai sannan Nuri ta tuna Mami na waren suke wannan maganar da sauri ta dire wayar tana miqewa irin taji kunyar nan tana sosa qeyarta ta fita daga dakin saying "ba zaka yi ba biyayye.."

Shi da yake namiji ne ko ajikinsa sai cewa yayi "Mami kunya Kuma bayan dake zanyi shawarar wadda zan zaba.."

"Allah ya shiryeku...."

Yana dariya ya amsa da "aameen Mami, Mami na gaji wallahi ina son na dawo gida na ganku nayi missing dinku da dakina? Mami Adda tana gyaramin dakin dai ko?"

Sai a sannan ta tuna shi fa duk bai san halin da suke ciki ba don haka ba ta tsaya yin shiru ta bashi space din gane akwai matsala ba tace "uhmmmm dafatan kana maida hankali a karatu Afif naji kana zancen gyming badai wasa kake da karatunka ba?"

"Oh come on Mami duk rage Lokaci ne yasa na fara fa ba wani abun ba, Allah Ina karatu sosai ma kuwa.. "

"Masha Allah ka cigaba da mai da hankali Allah ya bada sa'a.. "

"Aameen Yah Rabbi Maminmu... " Hira ya dinga jan Mami dashi sam ba taji ta gaji ba. While suna nan suna hirarsu Nuri na can waje ta tsugunna tana tattare musu gidan zuciyarta yana mata tunanin Fu'ad da suddenly ta kasa mantawa dashi and she started wondering me ke faruwa da ita?

To be continued

#like
#comment
#share