32
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Under team yota's amazing pen
Page 3️⃣2️⃣
Zama tayi kusa da ita hankalinta a tashe, rungumota tayi jikinta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi tace
"Maisa bakya so, kina da wanda kike so ne"
"A'a bani da Amman dai bana son ya Umar"
Ɗan shiru Ammah tayi tana tunanin wannan lamarin dan tana hango yanda zuciyar Ammi zata yi idan wannan al'amari bai faru ba dan ta lura tasa hakan aranta sosai kuma tana farin ciki da hakan
Amman yanzu kuma ita Anisa tace haka, bata san yanda wannan cakwakiyar zata gyaru ba dan tasan hakan zai ɓata ran rayuka da yawa
Numfashi ta sauke tace
"Ammin ki na farin ciki da wannan haɗin, dan ina ga tafi kowa farin ciki da hakan, yanzu baza kiyi dan ammin ki ba, ta sha wahalar rayuwa, yanzu a ganinta in kika yi aure cikin dangin ki da suke sonki suke kaunar ki baza ki wahala ko ki wulakanta a rayuwa ba, sai dai ko wani nufin Allahn, a ganina Umar abokin zama ne na kwarai wanda zakiyi alfahari dashi kuma zai tsaya dake a kowa ni kalan yanayi, kuma itama Ammin ki haka ta duba miki, tasan tunda yana sonki zai kula mata dake fiye da wanda bata sani ba, tunda duk mun san waye shi, ki cire wai baya sakar muku fuska Amman kin San shi me shiga lamuran kannen shine me kula da su, baza kiyi hakan dan kanki da kuma Ammi ba, dan dai kisan idan yana da halin da bai dace ba Ammi bazata taɓa yarda ba duk kawaicinta a kanki kuwa"
Ita dai banda kukan da take jikin Ammah ba abinda tayi ƙoƙarin cewa duk da yanda maganganun suke ƙoƙarin kaiwa inda Ammahn takeson sukai, Amman dai ba wai tana jin zata iya yarda ta auri ya Faruq ba
Bayanta take bubbugawa ahankali ta cigaba da cewa
"Mahaifiyar ki ta sadaukar da komai Saboda farin cikin makusantanta, barin ma ke, to ke baza ki iya sadaukar da wannan abu ɗayan ba wanda daga baya ke zai fi amfana ba ita ba, baza ki iya wannan ba saboda ita, ta shiga ƙalubale kala kala a rayuwarta Amman yanzu tana ganin ta samu farin ciki, har ƴarta ma zata samu farin ciki Amman baza ki cika mata ba"
Kanta ta tura cikin jikinta tana ƙara fashewa da sabon kuka "yah Umar fah, ya uwar, ita bata mai kallon da ya wuce wani da zata iya aure se dai yaya da take jinsu kamar uwa ɗaya uba ɗaya a gare ta, ace kuma ta aure shi, to suma fara rayuwa a ya, kai!!!" maganganun da take kenan a ranta
Amma ce tace
"In baki wani labari"
Kai ta jinjina mata alamar tana jinta amma har lokacin fuskarta na cikin jikinta
Cigaban labarin Ammi
Malam Aliyu Muhammad Yakubu wani mutum ne me neman na kansa, wanda yake rufa ma kan sa, iyayen shi da ƙanwar shi asiri dan da buga bugar da yake ne yake ciyar da gidan su, bashi da ƙaƙƙarar sana'a sai idan yaje yayi dako, ko aikin fulawa ko na barkono ko wani ƙaramar sana'a idan ya samu,
Kuma shike ɗaukar nauyin karatun ƙanwarshi har zuwa sanda tayi candy tayi aure
Suna wannan yanayin da har lokacin ba shida Sana'a sai ƴan kame kame, wadansu lokutan kuma ya je unguwar masu hannu da shuni ko suna buƙatar me gadi ko me gyaran Flowers kodai wani aikin da ba'a rasa ba wanda ake neman namiji agida
Ana haka abokinsa Malam Rabe yace mai wani abokin sa yace ya samo mai wanda ya iya tuƙin mota wani alhaji na neman driver,
Ya iya tuƙin mota saboda a da yana aikin manyan motoci ya kai kaya garuruwa, kuma yayi aiki a gareji ya iya tuƙa motoci saboda wani lokacin idan an gama gyara ana zuwa gwaji, kuma ya taɓa ma wani alhaji drivern mota
Tsautsayi ya rutsa dashi aka ɗauke da ya aike shi wani errand, danma alhajin me fahimta ne , ya yafe mai Amman yace ya je ya nema wani aikin, shi yasa tun lokacin be ƙara neman aikin driver ba
"Baka ganin da wani matsala kuwa" fadin malam Ali
"Babu in Sha Allah, Malam Bala yace alhajin nada kirki, shima jinyar mahaifin shi zai je shi yasa"
Faɗin Malam Rabe
"To Allah ya datar damu da alkhairi"
Wannan ne silar fara aikin Ali driver a gidan papi
follow
_____________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***