RABO DA KADDARA

Page 5

by @mrsclassywrite

Kauyen Gwaram.

Kauye ne dake Arewa,a cikin kauyan. Gida ne a tsakiyar kauyen, gida ne na kasa mai daki biyu, wanda Malam Sale ya gada wajen iyayensa da suka rasu Gida ne da aka yi da laka, rufin kwano, tsakiyar gidan akwai bishiyar danya.

A cikin wannan gidan mai daki biyu ne Hajja Kaka da mijin ta Malam Sale suke tare da 'ya'yansu uku: Gaddafi shine  babba, Bashirshi ne na  biyu, da Mu'awiyya karami wanda bai kai shiga makaranta ba tukuna.

Hajja Kaka, a lokacin, sana'arta a gida take siyarwa Ba ta zuwa kasuwa. Tana soya kuli-kuli, tana siyar da kayan miya - kanwa, daddawa, yaji. Tana shimfida tabarma a gaban bishiyar gidan matan kauye na zuwa suna saya. Abin da take samu  suke cin abinci da shi.

Gaddafi da Bashir ne kadai suka isa zuwa makaranta a lokacin. Sun fara tun daga firamare. Gaddafi ya fi Bashir aji biyu. Idan Gaddafi yana Primary 6, Bashir yana Primary 4. Sun gama firamare, suka shiga sakandaren Gwaram. A sakandare ma Gaddafi ya fi Bashir aji biyu.

Gaddafi ya kammala sakandare da sakamako mai kyau, Bashir yana SS2. Babu kudin Jami'a. Gaddafi ya shawarci mahaifin su  ya ce zai je birni ya nemi kudi kuma ya amince mishi

A birni, ya fara bin abokinsa yana aikin tuka Napep da hada idan sun tashi suna kai blance.  A haka ya hadu da Alhaji Rabi'u Matawalle - motar Alhajin ta lalace, yana sauri zai je company. Dai dai lokacin Gaddafi ya taho ya tsare shi aiko ya tsaya sukai ciniki ya dauke shi, suna isa ya ciro kudin shi ya bashi ya juya ya shiga cikin company, juyawan da zaiyi yaga Alhaji ya manta da jakan shi ko daya waiga zai mishi magana yaga haya shige , haka ya zauna ya jira shi awa uku a rana harsai daya ga fitowan shi yaji da sauri yamai sallama kafin ya mika mishi jakan Alhaji gashi kayi mantuwa a napep dina. Cikin mamaki alhaji yake kallon sa ganin duk tsawon lokacin nan yana zaune saboda kawai ya bashi mantuwar da yayi a napep din shi Jin dadin amanarsa yasa, Alhajin ya ce, "Ka yi karatu?" Gaddafi ya ce, "Na gama sakandare." Alhajin ya ce, "Ka kawo takardun ka zan baka aiki. Ciki da mamaki Gaddafi ya dago Kai yana kallon sa cikin gamsuwa Alhaji ya daga mishi Kai cikin tabbatar wa"

Wannan shine ranan da ya fara canza rayuwan wannan ahali

Bayan ya hadu da Alhaji Matawalle, Gaddafi , ya koma dakin hayar da yake tare da abokinsa. Ya zauna, ya yi tunani. Sosai kafin ya fadan ma abokin nashi ko mai, shima ya bashi karin gwaiwa. Da asuba, ya shiga mota ya koma Gwaram.

Isarsa Gwaram, Hajja Kaka ta ganshi tayi farin ciki sosai da ganin shi,"Gaddafi! Ka dawo?"

Shima cikin farin ciki Gaddafi ya amsa ma hajja kafin ya zauna akan shinfi dan da ta mishi zama yayi yana fadin mun same ku lafiya hajja ina yaran gidan , lafiya lau muke duk suna makaranta sai anjima zasu shigo suna haka Malam ya shigo shima sun gaisa sosai kafin ya  ba su labarin abin da ya faru - Malam Sale ya kafe shi da ido, kafin yace duk na jika to kuna ganin babu matsala kasan sha'anin mutane yanzu babu gaskiya. Hajja Kaka da wannan da wannan amma ya zamuyi addu'a zamu taya shi dashi a duk inda suke, ta yi masa addu'a mai karfi, addu'ar da ta fito daga zuciya, "Allah ya tai maka , Allah ya bude maka kofofin arziki saboda masu albarka, Allah ya sa wannan ya zama budewar arziki a gare mu baki daya!"

Addu'ar Hajja Kaka karbabbe ce.

Gaddafi ya koma birni. Washegari ya je Danumma Towers da takardunsa na sakandare. Alhaji Matawalle ya bashi aiki. Aiki mai mutunci. Daga mai kawo file, har ya zama mai kula da kayan gini.

Daga nan ne rayuwa ta fara canzawa.

Gaddafi bai ci kudi shi kadai ba. Duk wata, yana tura wa Hajja Kaka kudi. Kudi na farko da ya tura, naira dubu ashirin. Hajja Kaka ta karba, ta yi godiya sosai. 

Ba laifi, ana haka, cikin shekara daya, Gaddafi ya sayi gida a birni. Ba gidan haya ba, gida na kansa! Gida mai babban falo da dakin kwana uku a wata unguwa a Kano. Gida ne da yake da ruwa da wuta, da tiles. Gaddafi ya yi mamaki da kansa wai yau shine da gida a cikin gari Allah mai yin yanda yaso,

Washa garin  ya dawo kauyen Gwaram.

Shiga gidan yayi da sallama Suna zau a tabarma. Hajja koma na share tsakar gidan duk juyowa sukayi suna kallon shi cikin farin cike yan uwan shi suka rungume shi kafin ya gaisar da iyayan nashi ya kasa hakuri sai daya fadan musu Ya ce, "hajja, Baba, na sayi gida a birni. Ku shirya, zamu bar wannan gidan yau ga mai mota can nazo dashi, mu koma birni. Rayuwa ta canza."

Hajja Kaka da Malam Sale sun yi farin ciki sosai! Sun yi kuka na murna. Sun yi sallama da mutanen kauye - makwabtansu da suka saba siyan kuli-kuli da kayan miya . Mutane suka taru, suka yi musu addu'a, "Allah ya sanya muku albarka!" Haka suka dauki kayansu kadan, suka dawo birni. bayan sun saka haya a gidan,

Da isarsu birni, suka shiga gidan mai dakin kwana uku. Hajja Kaka ta fara kuka, "Gaddafi, wannan gidan duka namu ne?"

Rayuwa ta sauya! Yanzu suna samun abinci mai kyau da sutura mai kyau. Yanzu Hajja Kaka bata siyar da komai Gaddafi ya ce, "Hajja, ki huta, ai kin yi ta siyar da kuli-kuli da kayan miya a Gwaram, yanzu lokacin hutawa ne."

Bayan dawowar su birni, Gaddafi ya saka kaninsa Bashir a Jami'a. Bashir wanda yake SS2 a Gwaram, yanzu ya gama sakandare a birni, ya shiga Jami'a yana karatun Business. Karamin kuma, Mu'awiyya, ya saka shi a sakandire mai kyau a birni. Dukansu suna zuwa makaranta da yanzu Mai kyau.

Ana haka, Alhaji Rabi'u Matawalle ya bashi auren 'yarsa Aisha (Miemie) kuma ya hada shi da gidan da zasu zauna da motar da zai rika hawa. Rayuwar su ta sauya tayi kyau sosai!, 

Shima zuwa yanzu Gaddafi ya ci gaba da karatu sosai. Duk da yana aiki, yana zuwa makaranta. Ya yi nisa a karatu yanzu. Ya yi Degree, ya yi Masters. Wajen aiki, har ana tura shi kasashen waje - Dubai, Saudi, London - don kwangiloli.

Ana haka, kanin shi Bashir shima ya kammala karatu, Gaddafi ya bude masa company na siminti. ya hada masa da jari. Sai Mai yawan gaske sai gashi company ya samu karbuwa sosai a Company din siminti ya tashi sosai a Kano. Mutane na zuwa su sayi siminti. 

A lokacin ne kuma karamin su Mu'awiyya yake zuwa ya taimaka masa a company din siminti, suna aiki tare, duk da lokacin bai gama makaranta ba. Mu'awiyya yana koyon kasuwanci.

Ana haka, Bashir yayi aure. Ya auri wata yarinya anan unguwar su a Kano, inda suka dawo daga Gwaram. Yarinyar, Hassana, iyayenta masu karamin karfi ne, mutane masu hakuri da kawaici. Bashir ya kawo ta, suka zauna tare da Hajja Kaka da Malam Sale a gida. Hassana mace ce mai hakuri, mai son yara, mai kawaici.

Lokacin ne kuma Aisha (Miemie) ta haifi yaronta na farko, Muhammad. An yi suna a unguwar masu kudi! An yanka rago, an gayyato manya-manyan mutane. Alhaji Rabi'u Matawalle ya yi farin ciki. Shekaru uku bayan haka, ta sake haihuwa, Usama.

Lokacin ne kuma Mu'awiyya shima yayi aure da matarsa Murshida. Suna zaune a gidan haya a wani anguwa, Alhamdulillah.

Alhamdulillah, Alhamdulillah, Gaddafi arziki ya ci uban na da! Arziki ya yawaita! Ya tuna da iyayensa.

Ya biyawa Hajja Kaka da babansa da matarsa Hajiya Aisha Saudiya, suka je suka sauke farali. Sun yi Hajji! Hajja Kaka ta yi kuka a Ka'aba, tana addu'a, "Allah ka saka wa Gaddafi da alkhairi tare da yan uwan shi"

Bayan dawowar su daga Saudiya, Allah ya yi wa Alhaji Sale (Malam Sale) rasuwa Rashin lafiya ne kwatsam. Gidan ya rude! Sun yi kukan rashin sa sosai! Hajja Kaka ta yi kuka ta ce, "Sale na ya rasu bai ga jikokinsa sun girma ba!" An yi jana'izarsa a Kano, mutane da yawa sun zo.

Bayan shekara biyu da rasuwar Malam Sale, abubuwa sun ci gaba da faruwa. Arziki ya kara yawa.

Alhaji Gaddafi da Alhaji Bashir suka gina wannan katafaren Estate din - Gwaram Estate! Estate ne mai dauke da gidaje da yawa, kowane dangi da part din shi! Suka koma ciki! Gidan mai dakin kwana uku sun bar shi, suka koma Estate mai hawa uku! Kowa da part din shi, da fili mai fadi.

Lokacin da suka koma Gwaram Estate, Muhammad ya fara zuwa makaranta, yana da shekara 4. Yana karami, amma haziki.

Lokacin ne Murshida itama ta haifi Jameel  Amma har lokacin, Hassana shiru, babu haihuwa. Hassana ta shiga damuwa, tana kuka da dare, Bashir yana rarrashinta,.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya.

Hajiya Aisha da Murshida sun sake haihuwa  Hajiya Aisha ta haifi Firdausi, ita kuma Murshida ta haifi Jamila.

Yaruwa tace gaba da tafiya! Yara suna zuwa makaranta masu kyau da tsada a fadin Kano! 

_Muhammad shekara 15, yana SS3 a makaranta
Jameel shekara 13, yana JSS3.
Usama shekara 12, yana JSS2.
Jamila shekara 8, tana Primary 4.
Firdausi shekara 7 da wata ni, tana Primary 4.

Ana haka, lokacin da ba a zata ba, Hassana da Murshida suka samu ciki tare! Murna a wannan family ba a magana! Gidan Gwaram Estate ya cika da murna! Ganin Hassana da ciki bayan shekaru da yawa na jira, sai kowa ya rika rainonta!  cike da kulawa! Hajja Kaka na yi mata addu'a kullum, "Allah ya sauke su lafiya!"

Har lokacin haihuwa yazo. Haihuwar Hassana ta zo da tangarda! Sai da aka mata aiki (CS) a asibiti! Ta kwanta na kwana uku, Bashir bai bar asibiti ba! Sai da Allah ya sa ta haifi yarinyarta mace, wacce ta ci sunan Fatima, sunan Hajja Kaka! Amma yaran gida suna kiranta da Jazzeelah! Farin ciki ya mamaye gida!

Ita kuma Murshida ta samu Abida, itama mace Ta haifa a  Wannan lokacin an yi taron suna gangarimi! An yanka shanu, an gayyato mutane sosai!

Sun ci gaba da rainon yaran su cikin kulawa. Shekaru sun ci gaba da tafiya.

Jamila da Firdausi sun yi aure! Daya ta yi aure a Abuja, daya ta yi aure a Kano!  Mijin daya ma'aikacin gwamnati ne, dayan kuma dan kasuwa ne! An yi aurensu da kayatarwa 

Jameel karatun likita yayi Shi mutum ne mai fara'a da son jama'a, sabanin Muhammad! Jameel kullum yana dariya, yana wasa da yara, yana taimakon mutane! Sabanin Muhammad da yake miskili kwata-kwata, bashi da fara'a, bashi da yawan magana, ga kuma wani irin kwarjini da Allah ya bashi  Kaf yaran gidan suna shakkan Muhammad saboda baya musu da dadi! Yanzu-yanzu yayi ma mutum haro mai tsanani, ba komai bane a wajensa! Dan ma Hajja Kaka ce take masa birki! Shiya karanci harkan kasuwanci ne, gashi tun yana matakin Jami'a ya san ya nemo kudin, har ya fara sana'a a boye, wacce ta kaishi ga wannan matakin kasuwancin da yake yi yanzu! Yana da kamfanoni!

Shima Jameel ya gina asibitin shi babba! Asibitin Jameel Specialist Hospital! Kuma duk da haka ana daukan shi aiki wasu kasashen waje saboda karewarsa wajen tiyatar zuciya! Ana kiran shi Dubai, India, don ya yi aiki!

Bangaren su Abidah da Fatima (Jazzeelah) kuma, yanzu kansu na hayaki, suna sakandire! Sun fara zama 'yan mata! Rashin jidai ba'a magana! Duk da Fatima (Jazzeelah) tafi Abidah tsiwa da fada, amma sai an taba ta! Ita mai gaskiya ce, ba ta yafiya idan aka taba ta! Abidah ita tafi bangaren rashin ji Amma akwai tausayi Ba inda suke zuwa daga makaranta sai gida! Dama Abidah  ta kanje idan kawayenta, tunda suna zuwa mata! Ita kuma Jazzeelah iya kanta, gida daga gida sai gida, gata akwai kunya sosai da kawaici, ta nan bangaren ta biyo mahaifiyarta Hassana!

Wannan shine cikakken tarihin Gwaram Estate!