17&18
by @nkds
❤️BA DARAJA!!!❤🔥
©® Nainarh KD♡
17–18
Ranar wata Alhamis da rana wuraren k'arfe sha biyu da mintoci, Ruk'ayya ta dawo daga makarantar da take koyarwa da yake a gajiye take ga yunwa da ta kwaso ya sa ko d'aki bata shiga ba, ta baje a nan baranda kan tabarma da lokaci zuwa lokaci idan 'yan mutunci nata suna kusa to sai kaga kamar ba ita ba domin sakin jiki take suyita fira da Halima, yau d'in ma hakan ce ta kasance Halima tana daga zaune akan kujera ta tsakar gida yayin da ba'a jimawa take tashi ta duba girkin da take yi, can sai ga wani d'an saurayi da ba zai wuce shekaru goma sha shida ba ya shigo gidan da sallama, a tare suka amsa ya kuma gaishesu duka cikin girmamawa, yayin da Ruk'ayya ta bishi da kallo tana raya abubuwa da yawa a ranta.
“Mamansu na fa gaza hak'uri ne na dawo to da alama ma dai har yanzu da saura.”
Murmushi Halima ta yi ta ce.
“Mas'ud ke nan lallai kana d'oki da yawa karka damu ai ya kusa.”
Murmushi ya yi.
“Yaran basu dawo makaranta ba kodai naje na taho dasu ne kafin nan ya kammala.”
“Karka damu fa ka manta Abbansu ne yake dawowa da su.”
Halima ta fad'a tana mik'ewa tsaye. Mas'ud wani almajiri da ya zama kamar d'a a gidan Abbas domin tun kafin Ruk'ayya ta shigo gidan Halima take tare da shi kuma abin da ya sa take jin dad'in zama da shi, shi ne sam bashi da rawar kai ga shi da biyayya ba raini kafin ma Halima ta ce ya yi wani abun zai yi, shi ya sa duk kwakwon Abbas shi kansa yaba masa yake sai dai ita Ruk'ayya ata b'angaren ta sam bai yi ma ta ba kuma ba wai dan ya yi ma ta wani abu ba kawai dai ita bai yi ma ta bane, shi ya sa shima da ya lura da hakan sai ya kasance baya ma shiga harkar ta iya kar gaisuwa ke had'asu.
“Wai mene ne ake yi haka da aka k'osa ne?”
Ruk'ayya da ta gaza hak'uri ta tambaya.
Halima tana 'yar dariya ta ce.
“Kedai bar lamarin Mas'ud kawai wai fa miyar wake ne nake gwada yi a yau shi ne duk yabi ya k'osa kamar bai tab'a sha ba.”
A lokacin da Halima ta k'are maganar nata inda ta duba fuskar Ruk'ayya da yanayinta zata lura da yadda ta wani b'ata fuska irin zancen bai ma ta ba or something like this.
“Yawwa magana ma ta k'are ga miya ta kammala.”
Halima ta sake maganar yayin da ta aje tukunyar miyar da ta d'auko a gefe kusa da kular tuwon shinkafa da ta fara gamawa ta sassaka a leda sannan ta zuba a kula. Ita dai Ruk'ayya bata sake cewa komai ba har Halima ta gama bidirinta, zubawa kowa nasa ta yi ta zuba ma Mas'ud nasa ya sama wuri gefe guda ya zauna yana ci yana zuba santsi sai yaban girkin yake musamman miyar yadda taji Maggie ga kifi zuk'u-zuk'u. Cikin jin dad'in yabon girkin da yake yi musamman ma miyar ta aje trayn da ta zuba nasu ita da Ruk'ayya da yake tare suke cin abincin, sai da Ruk'ayya ta shiga d'aki ta shimfid'e Bilkisu dake bacci ta gama b'ata lokaci Halima na jiranta sannan ta fito tana wani shan k'amshi ita a dole an kwaikwayi irin miyar da take yi ta zauna suka fara ci.
“Ta yi dad'i ko?”
Halima da zumud'i ya sa ta tambayeta.
Wani yamutsa fuska ta yi tare da tsame hannunta da ta tuwon da ta yima loma biyu.
“Wa ya fad'a miki haka ake cika kifi a miyar wake? To bai yi ba wannan ai ba dai miyar wake za'a kira shi ba sai dai wani abin daban.”
Ta fad'a tana wani sake yamutsa fuska da kallon mamaki Mas'ud ya bita shi kuwa sai yake ga bai ga aibun miyar ba.
Ita kuwa Halima ba wai k'in yabon miyar da batayi ba ne ya bata haushi sai yadda take wani ya mutsa fuska cike da izgilanci hakan ne yafi sosa ma ta rai.
“Ke dakata ba wani iyayi da felek'e na tambaye ki ba kuma da kike fad'in batayi dad'i ba ko na cika kifi, wannan ke kika jiyo kuma tun da har nayi girki sai anci ko ya yi ma mutum ko bai yi ba, dama kike wannan yamutsa fuska ai ba zuwa nayi nace ki koyamin ba sannan karki d'auka kune kad'ai kuke wannan miyar da zaki nema rainawa mutane hankali.”
Halima ta k'are maganar cikin b'acin rai yayin da Ruk'ayya ta yi mulugui bata ce komai ba ganin yadda Halima ta fusata, suna haka sai ga Abbas shima ya dawo tare da yaran. Ai kuwa ran Ruk'ayya bai b'aci ba sai da Abbas da yaran suma suka dinga yabama girkin, taja tsaki kawai ta shige d'aki kuma koda Abbas ya ce ta fito taci abinci cewa ta yi bata ci abincin bai ma ta ba ya bata kud'i ta yi wani abin, ai kuwa Abbas ya bud'e idonsa ya toka ya soma surfeta da ruwan masifa akan indai ba zata ci ba sai dai ta barshi sai kace ba ita ke yiwa mutane irin girkin suna ci ba sai yau da Halima ta yi zata ce bata ci bayan na Halimar ma yafi dad'i ita nata da take cikama kayan k'amshi. Haka dai ya yi ta yi ta inda yake shiga ba nan yake fita ba. Halin Abbas ne idan ransa ya b'aci dake abin ba zai tsaya iya ku biyo ba, koma a'ina ne ba ruwansa haka zai rufe mace da fad'a ko a tsakar gida ne.
BAYAN KWANA BIYU
Kyawawan 'yan mata su biyu farare sol da su, sanye cikin uniform na makaranta da cikin nutsuwa suke tafe har suka k'ari sa k'ofar gidan su da mamaki suke duban wanda yake tsaye bakin k'ofar.
“Laaa Yaya Mas'ud dama kaine anan kwana biyu baka zo ba kuma Mamma sai nemanka takeyi.”
Juyowa ya yi kamar a firgice da yake ya basu baya ne bai san da isowarsu wurin ba.
“Bakomai Hauwa'u ku shiga gida kun ji.”
Sake kallonsa suke sai dai basu k'ara ce masa komai ba suka shige ciki yayin da Hauwa'u ta wuce d'akin mahaifiyarta haka ita ma Saddiqa ta wuce d'akin Ruk'ayya marik'iyarta.
“Mamma mun dawo.”
“Sannunku da hanya an kwaso gajiya da alama ma yunwar yau tafi ta kullum kodai zaki fara cin abincin ne kafin kiyi wankan?”
Halima ta yi maganar cikin kulawa da soyayya ga d'iyar nata duk da ta kan yi k'ok'arin b'oye hakan kasancewarta na 'yar fari dan ma ko sunanta bata kira idan ma taga mai sunanta bata iya kiran sunan saboda alkunya ga d'an fari.
“A'a Mamma gwara dai na fara wankan zan fi jin dad'i.”
Amsa ma ta Halima ta yi yayin da ita kuma ta fice bayan ta rage kayan jikinta ta d'aura zani, janyo ruwan da zatayi wankan ta yi a rijiya kasancewar lokacin zafi ne sosai.
Halima ta dubeta lokacin da ta dawo d'akin bayan ta yi wakan tana mamatse jiki alamar da ruwan sanyi ta yi wankan.
“Me ya sa bakijin magana ne bana son fa kina wanka da ruwan sanyin nan.”
“Kiyi hak'uri amma zufan ya sa idan bada ruwan sanyin nayi ba bana jin dad'i.”
Shiru ta yi ma ta. Ita kuma hakan ya sa ta shiga neman abin fad'a domin ta lura kamar ta yi fushi ne kuma so take ta huce.
“Kwana biyu Mas'ud shiru, fatana dai ya kasance lafiya ba wani abun ne ya faru ba.”
Muryar Mahaifiyarta ya katse ma ta tunani. Da sauri ta dubeta baki na rawa ta ce.
“Dama bai shigo ba, da zamu shigo gida d'azu muka ganshi yana ta lek'o nan gidan na d'auka ma ya shigo lokacin da nake wanka.”
“Shi Mas'ud d'in kuka gani a waje? To gaskiya bai shigo nan ba ai rabon da na ganshi tun rannan da yamma.”
Halima ta fad'a da mamaki.
“Ikon Allah tabbas shi d'in dai muka gani d'azu amma Bara na sake dubawa ko zan ganshi.”
Hauwa'u ta fad'a tana zura doguwar riga sannan ta d'aura hijjab akai ta fice k'ofar gidan.
Kamar d'azu yanzun ma ganinsa ta yi zaune a k'ofar gidan ya rafka uban tagumi.
“Yaya Mas'ud wai me ya hanaka shigowa ne tuntuni Mamma take jiranka.”
“Hauwa'u ni kaina ina so na shigo sai dai ina so tsoro.”
Da mamaki ta dubesa sai kuma batayi magana ba ta juya gidan da sauri ta sanar ma Halima abin da ya faru.
Mamaki ya sa Halima ta d'auki hijjab ita ma ta lek'o k'ofar gidan daidai lokacin kuma Ruk'ayya da ta dawo daga makarantar da take koyarwa ta iso wurin.
“Mas'ud wani abin ne ya faru ka kasa shigowa gidan?”
Halima ta tambaye sa daidai k'arisowar Ruk'ayya wurin.
“Kiyi hak'uri Mamansu dama mai gidan ne yace kar na sake zuwa.”
Wannan karon mamakin Halima ne ya k'aru.
“Wani mai gidan ke nan, kana nufin Abbas?”
Jinjina ma ta kai ya yi.
“Amma me ya sa?”
“Nima dai kawai haka ya ce min rannan da dare da na dawo karb'ar abinci.”
Da kyar Halima ta danne takaicin ta tare da dubansa ta ce.
“Karka damu ka shigo kayi aikin da ka saba kuma ka ci gaba da zuwa shi kuma Abbas d'in zamuyi magana da shi.”
Kamar zai yi musu sai kuma ya jinjina ma ta kai tare da bin bayanta suka shiga gidan.
“Ka fara zuba min ruwan, wanki nakeso dama nayi.”
“Wanki Mamma da tsakar ranar nan?”
Hauwa'u ta fad'a cikin sub'utar baki sai kuma ta yi saurin kama bakinta tana 'yar dariya ta ce.
“Aina d'auka zaki kai gidan wanki ne”
Ta fad'a ganin irin kallon da Halima ta watsa ma ta.
Halima da take jin ranta ba dad'i na abin da Abbas ya yi, ta dube Hauwa'un ta ce.
“Yau bana jin kai wa, ni zan yi da kaina.”
Jinjina kai Hauwa'un ta yi dan ta lura ran mahaifiyar nata a b'ace yake duk da ita ma ta yi mamakin dalilin da zai sa mahaifin nasu ya yanke hukuncin korar Mas'ud ba tare da wani dalili ba.
“Mamma bara na shiga gidan Anti Zuri ina dawowa yanzu.”
“Karki dad'e kinsan nace miki yanzu zamuyi wanki. Kuma Babanku ya kusa da dawowa.”
Halima ta amsa ma ta tana tattare yankan da ta gama wanda tana shirin kwashe wa ta fita wurin Mas'ud.
Saddiqa da tun lokacin da taga ficewar Hauwa'u daga gidan, ta faki idon Ruk'ayya da ta tun dawowar ta gidan ta lura kamar tana cikin fushi shi ya sa tana ganin ta shige bayi ita ma ta yi wuff ta fice daga gidan.
“Au biyo ni kikayi?”
Hauwa'u ta fad'a tana duban Saddiqa da ta shigo gidan tana sauke hakki.
“Nemawa kaina mafita nayi shi ya sa na gudo dan na lura mutuniyar kamar ranta a b'ace yake kuma nasan a kaina za'a iya hucewa.”
Saddiqa ta yi maganar tana dariya tare da zama kan kujerar tsakar gida. Zuri da suke kira Anti Zuri da ta kasance amarya ce dan ko haihuwa batayi ba kuma gidanta na fuskantar juna ne da gidansu Halima ya sa nan Hauwa'u da Saddiqa suke shiga fira idan suka faki ido kafin mahaifinsu Abbas ya dawo gidan dan yana nan da halinsa na tsauri in ba Makarantar boko ko islamiyya ba baya barin su fita ko k'ofar gida su kuma zaman gidan gundurarsu yake.
Zuri ta fito daga kicin tana yi musu dariya da cewa.
“Kun ga d'iyar Malama Ruk'ayya, Hajiya Saddiqa mai zan samu?”
“Hmmm su d'iyar Malama Ruk'ayya anji jiki mai wannan ta sani ban da gana min azaba.”
“Kedai ki fad'i gaskiya Madam kuna fa cin dad'i idan kuka k'ule d'aga.”
“Hmmm kuma ina k'arb'ar gashi ba, domin har tsoron nayi laifi nake tunanin Matar nan fa barin jikinta yake ina baki labari idan ta wani shak'o wuyana har sai na jiyo k'amshin aljanna take kyale ni wannan 'ya'yanta zasu sha wahala.”
Saddiqa ta fad'a har da rik'e hab'a.
Hauwa'u dake dariya ta ce.
“Irin wad'an nan kuma sai kiga basu iya yi ma nasu 'ya'yan komai ba.”
“Ai kuwa da Allah ya tambaye ta dan yadda take cin zalun 'ya'ya a makaranta har tausayin yaranta nake rannan fa wani saurayi tareni ya yi wai ai yaji labarin ni 'yar ta ce saboda haka sai ya rama dukan da ta yi ma k'anwarsa a kaina, ina baku labari da kyar nasha, domin duk rantsuwa da nakeyi masa a kan ita d'in matar mahaifina ne kawai ba wacce ta haifeni ba k'in yarda ya yi.”
“Lallai kam ai tun da marik'iyarki ce kamar uwa take gareki da ina wurin da na fad'a masa hakan.”
Zuri ta fad'a tana dariya. Sai kuma suka canza wani firan yayin da Zuri take bugan ruwan cikinsu domin taji labarin yadda suke da samarinsu kuma Halima ce ta buk'aci hakan daga gare ta a matsayin ta na uwa ta san ba ko wani irin sirri ne zasu iya tattaunawa da ita ba, shi ya sa saboda tsaro ta saka Zuri take jin ta bakinsu akan irin duk yanayin da suke ciki da samarin nasu duk da Abbas ba bari yake suna kula Samari ba amma kasancewar su farare tass da su kyawawa kuma Akwai farin jinin samarin, ya sa Halima take sanya ido sosai a kansu duka ba ma ga iya Hauwa'u 'yarta ba saboda tana tsoron lalacewar zamani bata da wani rok'o da ya wuce Allah ya tsare su da tarbiyyarsu domin ba saka ido ko iyawarta ne zai yi aiki ba tsare war Ubangiji shi ne jagaba a komai.
HALIMA
“Ina so zamuyi magana ne.”
“Okay.”
Ya fad'a yana sauke wayar hannunsa.
Halima ta ci gaba.
“Me ya faru ka dakatar da Mas'ud daga zuwa gidan nan.”
B'ata fuska ya yi.
“To nan kin tareni saikinji dalilina ke nan, mutum da gidansa bai isa ya yanke hukunci ba sai an nema ba'asi.”
“Nifa idan ka fahimce ni ba wata magana mai zafi nazo da ita ba, kawai tambaya ce nayi, saboda ban ga aibin yaron nan ba yana k'ok'ari sosai kuma yana girmama mu mu duka mai zai sa kace ya bar zuwa haka kawai ai kai ma kasan bakayi adalci ba.”
“Kika ce yana girmama mu? amma shi ne idan Rakiya ta saka shi aiki ba ya yi kuma ko gaisheta bayayi sai dai ya bita da mugun kallo saboda iskanci bayan kuma arziki yake ci a gidan, shi ya sa ni kuma ganin haka nace ya dena zuwa gwara a nema wani kawai.”
Kallonsa kawai Halima takeyi tun da ya fara maganar.
“Au wato ma Ruk'ayya ce ta saka ka koreshi ke nan?”
“Bana son maganar banza fa idan ma ita d'in ne sai me?”
“Ba komai, amma kuma ni ba zan lamunci wannan ba, an had'a k'arya da k'arairayi an sanar da kai ka kuma hau kai ka zauna ba tare da bincike ba gaskiya ya kamata ka sauya ka dinga bincike kafin yanke hukunci saboda haka addini ya koyar, yanke hukunci ba tare da bincike ba ai babu adalci sam, sannan kuma da ta ce baya ma ta aiki ai naga ba ita ta kawo shi gidan ba da zata damu sai ya yi ma ta abin da take so idan almajiri take nema ga su nan rututu a gari, gaskiya ni ba zan d'auki wannan abin ba saboda almajiri nawa ne ba ruwan matarka da shiga lamarinsa ka ja ma ta kunne.”
“Okay, umarni ma kike bani ke nan ko? To ba za'ayi yadda kikeso d'in ba, kuma yaron nan ya k'ara zuwa min gida zakiga abin da zai biyo baya.”
Ya fad'a a fusace.
Halima mik'e wa ta yi ta bar masa d'akin bayan ta ce da shi.
“Sai dai kayi hak'uri ba laifin da ya yi min saboda haka ba zai dena zuwa gidan nan aiki ba.”
Tana fad'a ta yi ficewar ta. Sai dai tana fitowa tsakar gidan ta sake had'uwa da abin da ya b'ata ma ta rai.
Kayan wankin da ta fito da su tana shirin fara wa Abbas ya shigo gidan shi ne kafin ta fito daga d'akinsa har an matsar ma ta da kayan gefe sannan Ruk'ayya ta kafa nata wankin a wurin.
Girgiza kai kurum Halima ta yi dama kad'an ke nan daga halin Ruk'ayya indai taji Halima ta furta zatayi abu to kafin ta aiwatar ita ta yi, Halima ta kasa gane inda matar ta nufa sam.
Komawa d'aki Halima ta yi ta tarar jaririyarta Maryam ta tashi tana cikin shayar da yarinyar ta jiyo tashin muryar Abbas a zafafe da alama fad'a yake musamman da ya kwala kiran sunanta ya sa taji gabanta ya fad'i, bata son tashin hankali tun farkonta ba tun yau ba, ta sha fad'a ma Abbas koda wani abin ne ya faru ya dena yi ma ta irin wannan kiran na mafarauta ko kuma idan laifi ta yi masa yabita ta lalama ba da tashin hankali ko hayagaga ba, amma sam ya kasa gane hakan, bai iya b'acin rai ba idan ransa ya b'aci na komawa sai ya b'aci.
“Kina ina ne kina ji ina kiranki. Wanene ya shiga min d'aki nayi ajiya ban gani ba, koma wanene ya yi gaggawar fitomin da kud'ad'en nan ta lalama tun kafin ran kowa ya b'aci a cikin gidan.”
Wani tashin hankalin ne ya sake ziyartar Halima lokacin da ta fito taji kalamansa da suka saka jaririyar hannunta ta kusan fad'i.
“Ban gane ba, sata kuma?”
Ta fad'a cikin tsananin mamaki da kuma damuwa saboda abin ya daketa.
“Wani irin sata kuma Dan Allah wai ma wani kud'in naka ke nan? kardai kace min duka kud'ad'en nan da ka tattara wanda kayi noma da wanda ka ciyo bashin banki kake k'ok'arin bud'e shago da su?”
Ruk'ayya ta k'are maganar cikin nuna tashin hankali k'arara tana tsame hannunta daga wankin da takeyi, a daidai lokacin kuma Hauwa'u da Saddiqa suka shigo gidan a tare gabansu ya fad'i ganin iyayen nasu tsaye curko-curko ga wani irin mugun kallon da mahaifin nasu ya bisu da shi.
“Daga gidan uban wa kuke?”
Tambayar da ya yi musu a tsawace ya sa Saddiqa zubewa a k'asa tana hawaye.
“Kuka nace kuyi, ba tambayarku nake ba?”
Ya sake fad'a a zafafe.
“Kayi hak'uri Abba daga gidan Anti Zuri muke.”
Hauwa'u ta fad'a cikin dakiya da b'oye tsoronta.
Wani irin duba ya yi ma ta kafin ya mayar da dubansa ga Halima a zafafe ya ce.
“Amma Halima me na fad'a miki game da yaran nan? Ba cewa nayi su dena shiga wannan gidan ba, Bama iya gidan ba waje ma ban yarje su fita ba daga makaranta sai gida, amma shi ne kika bari su fita ko. Zakuci k'aniyarku ku zube a can?”
Jiki na rawa suka koma tsakiyar rana inda ya ce suyi Kneel down domin sun san idan ma suka tsaya bashi hak'uri wani hukuncin zasuja ma kansu.
“Darling muyi maganar kud'in nan kace baka ga kud'i ba bayan kuma a d'akin ka su ke ba kuma wanda ya san da su daga kai sai mu matanta.”
Ruk'ayya ta k'are maganar tana yi ma Halima kallon k'asan ido.
“Ai ina sane domin ba hak'ura zan yi ba dole ma a fito min da kud'ad'en nan hauka ma ake.”
Ya fad'a a zafafe.
“Ah to gwara dai a fito da su kawai in ba dan ma rashin zuciya ba, sata fa me ake da b'arawo gaskiya koma wanene ya d'auki kud'in nan bai kyauta mana ba.”
“Ki fito fili kawai mana kice ni kike zargi dama kin ce ba wanda ya san da batun kud'in sai shi mai kud'in da kuma mu...”
Halima ta yi maganar a zafafe dan ta fara tunzura da habaicin da Ruk'ayyan keyi ma ta a dabarance.
“Ni dai ban ce ba tukunna kuma ai koma wanene b'arawon bincike shi zai nuna.”
Ruk'ayya ta bata amsa a gadarance tana wani k'afafa da d'aga murya.
“Duk ya isheku haka ba wannan shashancin nake da buk'ata ba ni dai kud'ina na sani kuma nake buk'atar a fitomin dasu tun kafin na d'auki mummunar hukuncin akan mace.”
Duk shiru sukayi.
“Wallahi karku d'auka da wasa nake duk gida zaku wuce idan ba'a fitomin da kud'in nan ba wannan wani irin wulak'anci ne mutum ya yi ajiya dan wulak'anci a d'auka sata fa ke nan kuma a gidana a d'akina tsakanin Matana.”
“Baka san gaskiya ba Abbas karka yanke hukuncin da zakazo kana dana sani daga baya kasancewar iya mu kad'ai ne muka san da batun kud'in sannan mu kad'ai muke shiga d'akin ka ba shi ke nuni da cewa mu muka d'auka ba, kar fa ka manta mai son abin ka ya fika dabara.”
Halima ta yi maganar cikin son ankarar da shi b'aranb'aramar da yake shirin yi domin ko'a addinance zato zunubi ne bare kuma akan batu na sata zargi sam babu amfani idan ba an tabbatar ba.
“Wani danasani kuma? Danasanin da zan yi ya wuce na auren b'arayi da nayi ai ke kika san wannan batun ni abin da na sani shi ne kawai a fitomin da kud'ina.”
Ya yi maganar yana nufar k'ofar gidan da niyyar ya rufe a yi wacce duk za'ayi. Yaran kuwa dukkanin su tuni sun fara kuka ba manyan ba ba yaran ba, ganin irin tashin hankalin da yake faruwa a gidansu.
Tabbas taji zafin kalaman Abbas na kiransu b'arayi da ya yi a ganinta koda a cikinsu ne wata ta d'auka masa kud'in ai bai cancanci ya yi musu jam'i ta hanyar kiransu b'arayi ba kuma a tsakar gida gaban yara cikin d'aga murya, shin wani irin shaida yake so mutan anguwa suyi musu, a ganinta ai idan tunani ya gushe hankali ke nemosa. Ganin irin kukan da yaran keyi ya sa ta sauke numfashi tana basu hak'uri da suyi shiru.
“Kuyi shiru kun ji ku shiga d'aki ku jirani.”
Haliman ta fad'a tana had'a kan yaran suka shiga d'aki duka ban da Hauwa'u da Saddiqa da suke zube a rana.
“Ah to ni dai an san kaf gidan mu babu b'arawo mutum ya fito da abin da ya d'auka tun kafin asha kunya wallahi.”
“Ke ki kiyayeni wallahi domin shirun da nakeyi miki ba tsoro ba ne gudun tashin hankali ne, amma tun da na lura ke akuya ce to zan biyo miki duk ta inda kika zab'a.”
Halima ta fad'a a kausashe domin ta kai mak'urar tuk'ewa da halin Ruk'ayya.
“Karki sake kirana da akuya idan ba so kike na nuna miki yadda ake ainihin akuyanci ba wallahi.”
Ruk'ayya ta fad'a tana wani tunkaro Halima gadan-gadan kamar mai shirin kai ma ta duka.
Sai Halima ta yi sororo tana kallonta da kuma jiran abin da zai biyo baya ta lura idan bata take ma matar nan birki ba rainin dake tsakaninsu gaba zai k'ara, ba tun yau ba idan Ruk'ayya tanaso taja ta da fad'a sai ta dinga wani abu kamar irin zata kai ma ta duka d'in nan kamar dai bata da Burin da ya wuce su dambatu ita kuma Halima tun farkonta abin da bata fata ke nan dambe da kishiya amma tun da ta lura duk hak'uri da kau da kan da takeyi ita Ruk'ayyan ba ganewa take ba, tabbas zata bata mamaki sai ta k'ure k'aryar rashin mutunci da tijararta tun da ta lura tashin hankali take da buk'atar suyi to shikenan su zuba su gani shege ka fasa, d'an halak kuma sai yanka!